EL-HABEEB HAUSA NOVEL

★__★
KATSINA
K’ofar K’aura.
Shagon d’inki ne wanda ke cikeda matasa wasu na kan keke suna d’inki wasu kuma y’an tayin hira ne.
Wani matashin saurayi wanda ke zaune kan kujera da keken d’inki a gabanshi amma ba d’inkin yakeba wayace a hannunshi yana danne danne.
“Kai! Musty wannan ba k’anwar ka Heedayah bace naga anyi posting a Facebook ana cigiyar ta”. ya k’arasa maganar yana nuno masa wayar hannunshi.
Wanda aka kira da suna Musty ne ya dakata da d’inkin dayake ya mik’a hannu ya karb’i wayar abokin nashi yana kallon screen d’in, baki ya bud’e tareda zaro ido yana k’ara bin hoton da kallo gabanshi na fad’uwa lokaci d’aya cikin rawar baki yace
“Itace wllhy, itace Isma’eel innalillahi wa inna ilaihi rajioun”. Bai saurari cewar kowa ba ya tashi ya fice da sauri ba tareda yabawa Isma’eel d’in wayarshi ba duk aka bishi da kallo.
Machine d’inshi roba roba ya hau yabashi wuta kafin ya figeshi da uban gudu yabar k’ofar shagon.
Yakai kai zai shiga soron gidan kenan sukayi kacib’us da Baba shikuma zai fita, ganinshi duk a rud’e yasa Baba ya shiga tambayar shi lafiya kuwa meya faru?.
“Baba mukoma ciki wani abu Isma’eel ke nunamin yanzu a waya”. Baba bai musa ba ya juya suka koma cikin gidan tare hankalinshi duk a tashe da tunanin abinda ya faru.
Umma tana zaune kan tabarma da wake a tray tana gyarashi suma kan tabarmar suka nemi waje suka zazzauna.
“Lafiya dai Malam na ganku haka kamar ba cikin nutsuwar ku ba?”. Umma ta tambaya ganin yanayin su kamar akwai wani abu dayake faruwa.
“To nima dai zan fita muka had’u dashi zai shigo, muna jinka Mustapha meye ya d’aga maka hankali haka?”.
Zama Mustapha ya gyara yana fad’in
“Yanzu Isma’eel ya nuna min wani hoto wai ta b’ata ana cigiyar ta a Kano”. yayi maganar yana mik’awa Baba wayar, shi kanshi Baba saidaya zaro ido ganin Heedayah k’uru k’uru wai ta b’ata, kalmar innalillahi kawai yake ambata cikin tsananin tashin hankali Heedayah ta b’ata amma meyasa Ramlah bata kira ta sanar dasu halin da ake ciki ba? b’atan d’an mutum sukutum da guda?.
Umma ya mik’awa wayar ta karb’a ta duba hoton dayake ita mace ce akwai raunin zuciya har tafara hawaye ganin Heedayahnta a matsayin wadda ta b’ata dama rabon ayi hakane yasa tabar gabansu tabi Ramlah Kano?
Wayar Baba ya karb’a daga hannun Umma data tsurawa hoton Heedayah ido tana hawaye ya mik’awa Mustapha wayar yana fad’in
“Kiramin y’ar uwarka Ramlatu inji dalilin dayasa ta b’oye mana irin wannan muhimmiyar maganar saboda shashanci”.
Wayarshi ya zaro daga aljihun gaban rigarshi yasa password ta bud’e ya shiga jerin numbers yana neman number Aunt Ramlah.
Bata dad’e tana fara ringing ba akayi picking sai yasata handsfree ya rik’e ta a hannunshi yana amsa sallamar Aunt Ramlah.
“Ramlah Baba ne zakuyi magana dashi gashi a kusa dani”.
“Yauwa dama Mustapha dama ina niyyar kiransu, jin haka yasa gabansu ya k’ara fad’uwa, cikin b’acin rai Baba ya fara magana da fad’in
“Haba Ramlatu, ya ina ganinki kamar mai wayo ashe ba haka bane inbanda sakarci taya zaki b’oye mana irin wannan maganar?.
MG’S SKINCARE
In kid’a ya chanza rawarma semutaru asauyata,
Wani Kaya se amalende
Haka Wani Hadi na musamman se MG’S,
Ina ma’abota amfanida kayan MG’S SKINCARE?
To bana fa tafi bara munqarawa kayanmu inganci muncire muntsefe munkawo maku qayatattun kayan gyaranjiki da Baki taba amfanida irinshiba a wannan qarnin,
Wani irin salo na gishirin kyan daukar magana zakiyi duk kikayi amfanida hadinmu b cika bakiba,ko yayan Hutu basa nuna maki tsadar fataba,duk a 11k fa kachal????????
Beauty kit:11k
Student package:7k
Soap:3k
Bridal kit 18k
Kicire kokonto ki warwaro Lalita kidebi Kaya n kerewa SAA
Chat:08062991549 or 07046881166 or 07067210195
Call:08064532391
Available in Kano and Kaduna
We also have beautiful yet luxury and unique frames for your apartments chat or call 07046881166
Serious buyers only please,
Inamasu bukukuwa????
Kugarzaya @inteesar cakes nd more kuyi order small chops domin bakinku irinsu
Cupcake,fishroll,samosa,spring rolls dama duk kayan kwalam da makulashe kunemata 07067210195
Cika alkawari shine takenmu????
Thank you
EL HABEEB????
©️Oum Hanan.
Writer of DR SAIF
HASKE WRITER’S ASSOCIATION????
(Home of expert & perfect writer’s).
D’imbin godiya ga masu bibiyar littafin nan nagani kuma na yaba sak’onnin ku na riskata ako yaushe thank you very much ALLAH yabar k’auna alkhairin ALLAH yakai muku aduk inda kuke sakallahu khayran.????
No 21.
Gaba d’aya sai Aunt Ramlah ta kasa gane inda maganganun Baba suka dosa musamman dataji yana k’ara fad’in
“Duk duniya su ya kamata ace ta fara sanarwa wannan labarin ta inda yake shiga bata nan yake fita ba itama Umma tasa baki sukayi tayi, sosai hankalin Aunt Ramlah ya tashi dataji Umma na kuka take maganar cikin sanyin murya tace
“Baba, Umma har yanzu fa ban gane akan abinda kuke magana ba wllhy dan ALLAH ku sanar dani laifin danayi”.
“Haba Ramlatu ace Heedayah ta b’ata har kwanaki biyu amma baki sanar damu ba? yarinyar nan fa amana ce a wajenmu idan baki fad’a mana ba wa zaki fad’awa? saifa yanzu da Mustapha yagano hotonta a wayar Isma’ila abokinshi ana cigiyar ta sannan yazo hankali tashe yake nuna mana”.
Aunt Ramlah batasan lokacin datayi murmushi ba idan ta fahimta daidai suma sunga yarinyar nan irin Heedayah suke zaton Heedayahn su ce. Dariya ta d’anyi wadda tasa mamaki ya k’ara kamasu kafin wani yayi magana tace
“Ku kwantar da hankalinku Baba wannan yarinyar ba Heedayah bace yarinyar ku lafiyar ta k’alau muma munga hoton yarinyar haka mukasha mamaki wlhi yanzu ma Abban Nu’aym ya dawo da ita daga makaranta suma shugabannin makarantar sunyi zaton itace da k’yar dai suka yadda shine duk ta tsorata ta kasa zaman school d’in ta biyoshi suka dawo gida”.
“Hukmullah la ajab”. Haka kawai Baba ya fad’a yana faman jijjiga kai, Umma da Mustapha ma sakato sukayi suna saurarar Ramlah cikeda d’imbin al’ajabin abinda take fad’a, yayin da Umma kuma ta d’auki tunanin ta cak ta maidashi wani waje daban tana ayyana abubuwa da dama a k’asan ranta.
Y’ar dariya Aunt Ramlah ta k’ara yi tace
“Baba bari ku tabbatar ma da abinda nake fad’a bari in kirawo ta ku gaisa”. murya tasa ta kira sunan Heedayah da k’arfi wadda suke kitchen itada Zainab suna shirin d’ora abincin rana, Heedayah ta amsa tareda ajiye albasar datake yankawa ta wanke hannunta a sink ta fito daga kitchen d’in zuwa falon inda Aunt Ramlah ke zaune kan kujera, wayar ta mik’a mata tana fad’in
“Su Baba ne zaku gaisa dasu”. karb’a tayi cikin murna tana murmushi takai kunnenta tayi sallama tana gaishe da Baban ya amsa cikin jin dad’i haka ma Umma wadda tuni tabar kukan datake farin ciki ya maye gurbinsa, har da Yah Mustapha saida suka gaisa yayin da Baba ya tubure shi lallai saidai Heedayah ta dawo Katsina shi ya tsorata da wannan al’amari da k’yar Aunt Ramlah ta shawo kanshi ya hak’ura ko dan saboda karatun data fara, haka dai ya hak’ura bada son ranshi ba sai dan irin magiyar da Ramlahn ta dinga zabga masa.
Sun jima suna hira har saida credit d’in ciki ya k’are wayar ta katse sannan suka hak’ura, a tare su Baba suka sauke ajiyar zuciya sai yanzu hankalinsu ya kwanta tashi Mustapha yayi ya d’auki wayarshi data Isma’eel daya taho da ita ya k’ara yimusu sallama ya fita.
Baba ya juya ya kalli inda Umma take yaga itama kallon nashi take kowa da abinda yake tunani a ranshi, numfashi ya sauke yace
“Anya Sa’adatu babu wani b’oyayyen abu a cikin wannan al’amarin? abin nan fa akwai d’aure kai da tsantsar mamaki”.
“Wallahi Malam abinda yake raina kenan tun lokacin danaji ba Heedayah bace yarinyar nan anya ba y’an biyu bane ba kuwa? dan wannan ba za’ace iya kamanni kawai suke da Heedayah ba dan wllhy idan an kwana dubu ana ce min ba Heedayah bace bazan yardaba kaga abu saikace almara”. Umma ta k’arasa maganar tana rik’e hab’arta tana k’ara jinjina girman al’amarin. Shima Baba kai ya shiga jinjinawa hundred percent ya yarda da maganar Umma datace ko y’an biyu ne ba shakka wannan babban al’amari ne dayake buk’atar bincike sosai idan ya kasance hakan ne kuwa zaifi kowa farin ciki zai sada Heedayah da asalin iyayenta duk da yasan ba k’aramin rud’ani da tashin hankali Heedayah zata shiga ba lamarin zai girgizata, Baba sun dad’e suna k’ara tisa maganar da Umma kafin shima ya tashi yayi mata sallama ya fita dama ya fitan wani abin ne ya dawo dashi.