EL-HABEEB HAUSA NOVEL

Matuk'a Aleeyu yake kula da Seeyamah zuwa yanzu harta fara sabawa da zaman kad'aitakar da wannan azzalumin ya gadar mata, wani har hira suke zama suyi da Aleeyu. Habeeb kuwa tun ranar dayaje batada lafiya har akayi mata allura bai k'ara zuwa ba ako yaushe dai yana kiran Aleeyu yaji lafiyar ta, sau d'aya ya tab'a cewa Aleeyun ya bata suyi magana shima ba wata maganar arzik'i bace cewa yayi idan ta shirya barin gidan ta fad'awa Aleeyu shikuma zaizo ta fad'a masa waye shi da dalilin dayasa take masa BASAJA bai saurari cewarta bama ya datse kiran tasha kuka a ranar har saida kanta yayi ciwo Aleeyu yana rarrashinta bama ta kulashi ba ta cigaba da kukanta zuciyarta na mata zafi.
Ta b’angaren Mujaheed kuwa sosai yasa ido akan duk wani takun abokin nashi batare dashi Habeeb d’in yasani ba, yayi busy sosai cikin kwanakin dan anfara ginin d’aya kamfanin na sark’ok’i da fidda design d’insu hakan yasa sam baya samun lokacin kanshi ma.
Police suna iya bakin k’ok’arinsu matsalar da har yanzu wad’anda sukayi garkuwar da ita basu kira waya anji daga garesu ba bare aji kud’in da zasu yanka wanda za’a fanshe ta har abi diddiginsu abin dai sai addu’ar ALLAH ya bayyana ta kawai.
★★__★★.
K’arar spoon kawai ke tashi a dinning area d’in Ummi da Neehlah su kad’ai ne masu cin abincin Habeeb kam wayace a hannunshi yana ta faman danne danne kanshi a k’asa ga abincin a gabanshi amma kota kanshi baibi ba hakan yasa da Ummi ta gaji tace
“Ajiye wayar nan ka kama abinci kaci”. d’agowa yayi ya kalli Ummin ya d’an b’ata fuska da fad’in
“I’m full fa Ummi tea ma kawai is okay”.
Had’e rai Ummi tayi tace
“Ban yardaba Abbuna meyasa kake son yin wasa da cikinka ne? maza kaci abinci kafin inyi maka d’ura yanzun”.
Dariya ce ta tahowa Neehlah jin abinda Ummi ta fad’a tayi saurin maidata tana toshe bakinta ya ganta sarai hakan yasa ya had’e rai sosai yana hararar ta yace
“Tashi kibar wajen nan”. a marairaice ta d’ago tana kallonshi kafin ta maida kallonta kan Ummi taji ko zatayi magana mutumin nan ya cika takura wllhy indai yana waje ba damar mutum ya sake.
“Akan me? banason rigima fa Abbu ya tana cin abincin ta zakace ta tashi kai waye ya takura maka? ka kuma ajiye wayar nan kayi abinda yake gabanka”.
Saidaya dallawa Neehlah harara wadda duk take a tsorace kafin ya ajiye wayar a kusa dashi yaja plate d’in gabanshi ya fara ci, kad’an ya tsakura ya ture plate d’in ko ruwa baisha ba ya yagi tissue yana goge bakinshi lokaci d’aya yana mik’ewa tsaye tareda d’aukar wayarshi, yana shirin barin wajen Ummi tace.
“Zauna, Hajiya Inna ta kawomin k’ararka d’azu dana shiga gaisheta”.
Zama ya k’ara yi yana kallon Ummin yaji abinda zatace ya yatsina fuska yace
“Ummi ki k’yale tsohuwar nan ita indai bata fad’i laifin mutum ba batajin dad’i”. d’an rank’washi Ummi ta sakar masa a kanshi ya dafe wajen kuwa yana b’ata fuska yace
“Kai Ummi me tace nayi ne? nifa rabon damu had’u ma harna manta”.
“Eh, ai akan hakan ne tace ka daina shiga gaisheta gaba d’aya why?”.
“Oops! wllhy Ummi ayyuka ne suka sha min kai saboda ginin danace miki za’a fara amma insha ALLAH yau idan nadawo office zan shiga mu gaisa kafin ta kawo wani laifin tace nayi”. duka Ummi takai masa ya goce da sauri yana murmushi ya tashi yayi mata sallama ya fita daga falon ta bishi da kallo tana murmushi.
Baki Neehlah ta tura tace
“Please Ummi ki samowa Yah Habeeb mata yayi aure ni wllhy yana takuramin dayawa”.
Dariya Ummi tayi tace
“Nice ma zan samo masa? shi zai nemo abarshi da kanshi”. Cikeda shagwab’a tace
“To ai Ummi shifa baya kula mata bare yasamu matar aure ALLAH nina gaji da zamanshi a gidan nan kawai kibada sadakar shi”.
“Lallai Neehlah kiyi addu’a kar yaji wannan maganar Abbun nawa zan bayar sadaka?”. Ummi ta k’arasa maganar tana dariya, itama Neehlahn saidata fad’i hakan saikuma tayi saurin toshe bakinta tana rarraba ido cikin falon kamar wadda zata ganshi Ummi nayi mata dariya.
Kamar yadda yayi alk'awari washegari yana dawowa daga office bai k'arasa gidansu ba yayi parking a k'ofar gidan Hajiya dan yanzu shi yake driving d'in da kanshi ya sallami driver'n sai jefi jefi idan yaji bayajin yin tuk'in yake nemanshi suma bodyguard d'in duk ya sallamesu dama bawani so yake ba Mujaheed ne ya kawo shawarar hakan lokacin daya dawo zai fara aiki a matsayin shi na C.E.O. da yak'i yarda munafukin saiyaje ya had'ashi da Kawu Sulaiman shima ya kirashi yace ya kamata hakan yanzu kuwa ya kori kowa.
Sanye yake cikin American suit black and white wandon da rigar ne bak’ake sai walk’iya suke yayin da shirt d’in ciki ta kasance fara k’al mai dogon hannu butterfly tied yayi amfani dashi shima black color ya matse k’ugunshi da bak’ar belt ta kamfanin D&G k’afarshi bak’in takalmi ne cover shoe na kamfanin Gucci kamar yadda hannunshi ma ke d’aure da bak’in agogon fata na Gucci yayi matuk’ar yin kyau sai baza k’amshi yake mai sanyin k’amshi da sanya nutsuwa.
Da k’akk’arfan takun nan nashi mai cikeda kuzari da koshin lafiya da ubangiji ya wadata shi da ita yake takawa har zuwa inda k’ofar da ake shiga falon Hajiya duk da irin gaishe shi d’in da maigadi yakeyi hannu kawai ya d’aga masa.
Hannu yasa ya kama handle d’in k’ofar ya bud’e ya shiga bakinshi d’auke da mak’alalliyar sallama wanda ya saba yinta a saman leb’enshi ya shiga cikin falon.
Idanu, baki, hanci da dukkan gangar jikinshi ya saki yana kallon inda Hajiya Inna take zaune ga yarinyar dayasa aka k’wamuso masa zaune kusa da ita tana ta mata surutu sunata dariya suman tsaye yayi ya runtse idonshi zuciyarshi na kai da kawowa ya damk’e hannayenshi ya k’ara bud’e idanunshi da tunanin basu gwada masa daidai bane saidai still tana nan yana ganinta ita d’ince dai ba wata ba.
“K’araso mana maigidana yau an tuna dani kenan duk da nasan yanzu haka Afeefah ce tayi maka magana”.
Sam baiji wani irin maganganu Hajiyan keyi ba Heedayah kawai yake kallo wadda tun shigowarshi tayi tsuru tsuru ta sunkuyar da kanta k’asa kamar munafuka tana wasa da yatsun hannunta wad’anda suka sha jan lalle ya kama sosai har yayi maroon color.
Wani irin juyawa yayi da dukkan k’arfinshi da wata irin sassarfa ya fice daga falon cikin wani irin taku kamar zaki Hajiya da Heedayah suka bishi da kallo baki bud’e….
Mrs Salees Mu’az ????
EL HABEEB????
©️Oum Hanan.
Writer of DR SAIF
HASKE WRITER’S ASSOCIATION????
(Home of expert & perfect writer’s).
Wato reader’s kunsan ta kan mugunta ko???????? kowa fata da burinshi yaga yadda Gashua zaiyi idan yaje yaga yarinyar gidan Hajiya daban wadda yasa aka k’wamuso masa itama kunsan gogan naku ai jarumi ne ???? mazewa zaiyi ya basar kamar baiga komaiba koya kukace ????????.
No 22.
“ALLAH mai iko lafiyar Habibu k’alau kuwa yaro saikace mai jinnu”. Hajiya tayi maganar tana kallon Heedayah bayan fitar Habeeb, itadai Heedayah batace komaiba to me zatace? duka fa wannan ce had’uwarsu ta biyu bayan wadda suka had’u akan layi, baki Hajiya ta tab’e tana fad’in
“ALLAH ya kyauta”.
Da wani irin sauri yake tafiya lokaci d’aya yana lalubo number wayar Aleeyu ya sauke masa tijara da kwandon masifa wane d’an iskan ne yace yayi sakaci har tasamu damar fitowa? akanme zai bari yarinyar nan ta gudo gashi har ta k’ara zuwa wajen Hajiya saidai kuma sam wayar Aleeyun tak’i shiga hakan yasa ranshi ya k’ara b’aci sosai tsaki kawai yake faman saki yana cije lips, dama a wajen gate yayi parking d’in motarshi bai shigo da ita ciki ba. Bai saurari maigadi daya taso dan ya bud’e masa k’ofar ba ya bud’e da kanshi ya fice tamkar zai tashi sama maigadi ya bishi da kallon mamaki.
Har ya bud’e k’ofar motar zai shiga saikuma ya fasa yayi tsaye rik’e da murfin motar kanshi a k’asa yana wani tunani idan ya tafi yabar yarinyar nan anan ai yayi rashin dabara ma dole yasan yadda yayi ya fita da ita dan k’ara tabbatarwa waccan ce kokuma watace daban, dan haka ya juyo a sukwane yakoma cikin gidan bayan ya aro nutsuwa ya d’ora saman fuskarshi.
Har lokacin Hajiya da Heedayah suna zaune sai gashi ya k’ara shigowa baiyi magana ba ya nemi kujera 1sitter ya zauna yayi crossing legs d’inshi yana girgizasu, Heedayah kam kallon ikon ALLAH kawai take cikin ranta take fad’in
“Da gani wannan mutumin ba mutunci zaiyi ba wllhy jifa yadda yazo ya zauna yana wani girgije girgijen k’afa”.
“Tohh yau kuma da wannan aka shigo?”. cewar Hajiya tana kallonshi, shidai baice uffan ba sai gaisheta dayayi ta amsa tana masa mitar kwana biyu ya yada ita, kamar mai ciwon baki yace
“I’m very busy Hajiya but I’m sorry yanzu ma wucewa zanyi akwai important issues dazan gabatar”. yayi maganar yana satar kallon Heedayah ta k’asan idanunshi ba wanda zaiyi zaton ita d’in yake kallo saboda yasan takunshi.
“Aifa agogo sarkin y’an aiki ina zaka aiki ina kadawo aiki, tohh ALLAH dai ya taimaka yabada sa’a amma kana k’ok’ari kam ALLAH yaji k’an mahaifinka”.
Da Amin ya amsa itama Heedayah ta amsa, tsaye ya mik’e ya d’auko wallet d’inshi a aljihun bayan wandonshi ya bud’e ya ciro kud’i masu yawa ya ajiyewa Hajiya a gefenta ta shiga yimasa godiya tana sa masa albarka duk cikin jikokinta tafi cin gajiyar Habeeb zuwa goma idan zaiyi saiya mata kyauta kuma ba k’arama ba banda sauran kayan buk’atu na yau da kullum dayake aiko mata dasu duk da cewa dai bata nemi komai ta rasaba haka yake kyauta a jininshi take.
“Yauwa Habibu tafi da yarinyar nan ka kai min ita gida dan ALLAH dama shirin tafiya take yanzu”. Cak ya tsaya daga shirin fita dayake jin abinda Hajiya ta fad’a, daga Hajiyan har Heedayah sunyi zaton zai musawa abinda Hajiyan tace saikuma sukaji yace
“Okay I’m waiting”. yana fad’in haka yasa kai ya fice daga falon. (Yo dama nema yake ina zai musa ????).
“Ni Hajiya da kin k’yaleni kawai na tafi wllhy”. Heedayah tace tana tura baki, dariya Hajiya tayi tace
“A’a gashi dai zai tafi d’in ke ba sauk’i na nemar miki bama samun abin hawa a layin nan namu ma ai aikine tashi maza kiyi da jiki Habibu d’an gaggawa ne bai son jira”. Haka nan ba dan ranta yaso ba ta tashi tasa hijabinta wanda ya tsaya mata iya gwiwar ta mai hannu ash color wanda yahau da atamfar jikinta kalar ash da fari ta rataya side bag d’inta mai sark’a ta yiwa Hajiya sallama, cikin kud’in da Habeeb ya ajiye mata ta zaro 5k ta bawa Heedayah farko k’in karb’a ma tayi sai dataga Hajiyan ta had’e rai sosai zata fara fad’a sannan ta amsa tayi godiya ta zurasu a jaka, farkon shigowa falon inda takalmin ta yake ta k’arasa ta saka Hajiya har k’ofar falon ta rakata sannan suka k’ara yin sallama ta tafi tana tunanin ya zasu k’are da wannan jikan Hajiyan yai ta wani cin d’aci yana cika da batsewa yana ma mutane muzurai itadai yai mata wllhy ba k’yaleshi zatayi ba. tayi maganar a fili har da murgud’a baki.
Habeeb bai san hidimar datake bama yana zaune cikin mota yana jiranta sai sakin tsaki yake yana duba agogon hannunshi, tunda ta fito daga gidan ya k’ura mata ido ta cikin glass d’in motarshi cije baki yake yana wassafa irin d’iban albarka da rashin mutuncin dazai shuka mata idan harya kasance itace (Sam ya manta da idan itace d’in dole ta razana idan ta ganshi amma wannan ko a jikinta sai ya alak’anta hakan da duk cikin makircin ta ne).
A hankali ta k’araso ta bud’e front seat ta shiga ko gama daidaita zamanta batayi ba ya figi motar yabar layin, kauda kai kawai tayi tana tab’e baki dama tasan dame Hajiya ta had’ata.
A wani irin slow motar take tafiya ga sanyin A.C da daddad’an k’amshin turarenshi dana freshner d’in motar da suka had’u suka cakud’e suka bada wani lafiyayyen k’amshi wanda yasa dole Heedayah ta lumshe idanunta tana sakin k’aramar ajiyar zuciya wadda ita kad’ai taji abarta. Duk a zatonta zai tambayeta ta fad’a masa address d’in inda zai kaita saikuma taga ya d’auki wata hanyar daban hakan yasa ta juya ta kalleshi taga ko b’arin datake bai kalla ba taga dai tafiya yake hankali kwance ya murtuke fuska.
“Wai Malam ina zaka kaini ne bafa nan bace hanyar gidan”.tace hankali tashe tana kallonshi, idan kujerar dayake kai ta tankata to shima ya tanka kawai ya cigaba da bawa mota wuta hankalinta ya k’ara tashi kamar zata sakar masa kuka tace
“Dan ALLAH bawan ALLAH kayi hak’uri ka saukeni insamu abin hawa please”. Habeeb dai gabanshi kawai yake kallo yana driving d’inshi magiya ta cigaba dayi masa akan ya sauketa amma yayi biris da ita, ganin dai magiyar bazata kaita ba yasa cikeda tsiwa da rashin kunya take fad’in
“Wllhy ko ka tsaya in fita ko inyi maka ihu yanzun nan in tara maka jama’a”. ta k’arasa maganar tana k’ok’arin bud’e motar saidai da alamu anyi locking d’inta.
Sai a lokacin Habeeb ya d’an juyo ya kalleta wani murmushin gefen baki ya sakar mata kafin yace
“Koba ihu ba? kiyi ihun mana kiga idan akwai wanda zaizo ya ceceki anan stupid d’in yarinya kawai”. ya ida maganar yana hararar ta ya juya ya cigaba da tuk’inshi
“To wai ina zaka kaini ne?”. Da k’arfi tayi maganar cikin muryar kuka tana faman juye juye kan kujerar datake tak’i zama waje d’aya.
Kai tsaye batare daya juyo ya kalleta ba yace
“Zan siyar dake ne ki nutsu kuma ki daina min mutsu mutsun nan inba hakaba zan baki mamaki yanzun nan”. yadda ya k’arasa maganar cikin hargitsattsiyar murya yasa tayi gum da bakinta ta zauna sosai gabanta na fad’uwa shiyasa fa dama tacewa Hajiya bazata biyoshi ba yanzu batasan gidan uwar dazai kaita ba ga magreebah takawo kai.
Haka suka cigaba da tafiya ba tare daya k’ara kallon side d’in datake ba, lokaci lokaci take sanya hannu tana d’auke k’wallar dake taho mata da haka har suka k’arasa lamid’o crescent dayake farkon shiga layin ne suna fara tafiya bayan sun shiga layin yayi parking, kallon inda yayi parking d’in tayi taga wani plat house ne mai kyau sosai kafin tayi yunk’urin yin wata magana ya fice daga motar da azama takai hannu zata bud’e ta fice taji anyi Lock d’inta ba damar fita.
“Wllhy bazan yafe maka kukan daka sani ba aikin banza nunar rana kawai”. tace tana share hawayen idanunta da hijab d’inta.
Knocking door yayi bayan ya shiga gidan ba dad’ewa Aleeyu yazo ya bud’e masa k’ofar daga irin kallon dayake jifan Aleeyu dashi yasha jinin jikinshi saiya matsa masa hanya ya shiga hannayenshi zube cikin aljihun suit d’inshi yana k’arewa falon kallo kamar yaune ya tab’a shiga cikinshi, Aleeyu ya rufe k’ofar yabi bayanshi yana fad’in
“Yallab’ai barka da zuwa”.
Bai amsa ba sai idanu daya tsare Aleeyun dashi, wasu irin idanuwa ALLAH ya bashi kaifafa wanda ko d’a namiji ya kalla dasu wanda aka kalla d’in yakan rissina duk tsaurin ra’ayin shi kuwa bare y’a mace da cikin y’an sakanni yake ladabtar da ko wacece ta cikin idanunshi, k’asa Aleeyu yayi da kanshi yana sosa kai da tunanin laifin me yayi ne ake masa wannan kallon tuhumar?
“Where is she?”. haka kawai ya cewa Aleeyun fuskarshi a d’aure.
“Tana ciki yallab’ai”. Aleeyu ya bashi amsa.
“Sure?”.
“Yes sir”.
Har yanzu dai zuciyar shi bata gama yarda da abinda yake tunani ba hakan yasa batare dayace komi ba ya shiga takawa zuwa bedroom d’in da Seeyamah take ya kama handle d’in k’ofar ya bud’e a hankali wani irin bugawa gabanshi yayi lokacin daya hangeta a zaune kan pray mat da k’aramin Alqur’an a hannunta tana karantawa a hankali, koda wasa Seeyamah bata d’ago kaiba dan duk zatonta Aleeyu ne kawai sai ta cigaba da karatun ta.
Ajiyar zuciya da numfashi ya sauke a lokaci d’aya yana dafe goshinshi yanzu dai ko yanaso ko bayaso dolenshi ya yarda su d’in twins ne wani abu ya rabasu to meye ya rabasu d’in? amsar da bazai iya bawa kanshi amsa ba dan haka yaja k’ofar ya k’ara rufewa ya juya. Seeyamah datake ta jiran taga shigowar Aleeyu taji shiru saita d’ago kai ta kalli k’ofar taga an rufeta sai a lokacin kuma k’amshin mutumin da bazata tab’a mantawa dashi ba ya iso hancinta to ko shine yazo? rabon data sashi a idanunta tun ranar da akayi mata allura bata bari tunanin shi yayi tsaho ba ta yakice ta cigaba da karatun ta.
“Ka cigaba da kula da ita zuwa jibi zaka maida ita inda ka d’aukota ka gane?”.
Kai Aleeyu ya gyad’a cikeda jin dad’i dan harga ALLAH ya mugun gajiya da wannan zaman ALLAH yasa karya canza ra’ayi dan sarai yasan halin ogan nashi wahainiya ne wajen canza kala.
Kud’i ya ciro masu yawa ya bashi sannan ya fice daga falon.
Tunanika kala kala ne ke masa yawo cikin k’wanyar kanshi ya zama dole yaje ya zauna da Hajiya suyi magana yaji wannan yarinyar datake zuwa wajenta ita d’in wacece? meye had’in Hajiyar da ita? yana ganin komai yazo k’arshe yanzu dole ya saki yarinyar nan kafin wani ya ankare.
Yana fitowa yasa remote ya bud’e motar ya k’arasa ya shiga, tunda ya shiga motar take faman hararar shi jitake tamkar ta kikkifa masa mari, tayi zaton yana shigowa zai tada motar su tafi sai taga kawai ya rufe idanunshi gamida yin relaxing akan seat d’inshi kamar wanda zaiyi barci gashi dama Aunt Ramlah sau biyu tana kiranta taji ta shiru har yanzu bata koma ba sai k’arya tayi mata tace tana gidan Hajiyan yanzu dai zata taho har Aunt Ramlahn nayi mata fad’an magreebah data kai.
Wani bak’in ciki ne ya kama Heedayah mutumin nan mugun d’an latsi ne wllhy ya kawota inda bata soba, ya shiga ya barta tun d’azu tana zaman jiranshi and now yazo kuma ya wani hakimce kan kujera kamar ma bashida alamun tafiya.
“Nidai dan ALLAH ka budemin in tafi wai malam meye hakane”. Cikin masifa tayi maganar tana hararar shi.
Habeeb da har lokacin bai bud’e idanunshi ba kuma a lokacin ne kalmar nan ta nunar rana ta fad’o masa a rai dan shifa har yanzu bai yadda yarinyar nan ba zaginshi tayi ba dan haka yau saita fad’a masa ma’anar ta sannan zai maida ita gida tunda ita fitsararriya ce batada kunya shikuma wancan d’an iskan ba abinda ya sani a hausar ma sai tsabar cika bakin shi bahaushe ne, batare daya bud’e ido ba k’asa k’asa kamar wanda aka tilasta yace
“Definition of nunan rana nakeso in sani”.
Baki Heedayah ta bud’e tana zaro ido jin abinda ya fad’a ita wllhy sam ta manta ma ta tab’a fad’a masa wannan kalmar yanzun ma haushin ya tafi ya barta ne yasa tace haka wannan guy d’in d’an bala’i ne wlhi, fuska ta marairaice tana kallonshi…..