EL-HABEEB HAUSA NOVEL

EL-HABEEB HAUSA NOVEL

Maryam Ibraheem Aleeyu
Mrs Salees Mu’az ????

EL HABEEB????

©️Oum Hanan.
Writer of DR SAIF.

HASKE WRITER’S ASSOCIATION????
(Home of expert & perfect writer’s).

This page all dedicated to

Aunt jamila
Mom sayyeed
Aunt Fareedah
Maryam Bello
Maryam Shuwa
Habeebah zailani
Haleemah Dayyab
Lubnah
Oum Ramlah
Mummy musaddiq
Ice
Aisha
Smiling
Mammyn Baffah
Humayrah
Da sauran wad’anda ma basuji sunayen suba duk nagode ALLAH yabar zumunchi da k’aunar juna jazakumullah khair ????.

No 23.

Taga alamun gayen nan masifa da bala’in mutum bashi zaisa ya canza ra’ayin abinda yayi niyya ba dan haka ta marairaice murya tace
“Dan ALLAH bawan ALLAH ka taimakeni ka budemin in fita bama saika kaini ba please”.
Idanunshi ya bud’e ya kalleta ba shiri tayi k’asa da kanta gabanta na fad’uwa saboda kaifin idanunshi, cikin dakakkiyar murya yace
Ashe kuwa zamu kwana anan kenan dan sai kin fad’amin abinda kike nufi da kalmar nan”. Batayi gigin k’ara d’agowa bare ta kalleshi tace
“Nifa ban tab’a fad’a maka haka bafa”.
Kamar bazaiyi magana ba saikuma yace
“Kinyi zaton na manta ne? Habeeb baya mantuwa idan kin shirya tafiya zuwa gida yanzu ki fad’amin”. ya k’arasa maganar yana k’ara maida kanshi kan seat d’in ya kwantar harda lumshe ido, Heedayah ji take tamkar ta tsala ihu meyasa bazai fahimta bane? magreebah fa tayi har tafara jiyo kiran sallah a unguwar, ta bud’e baki zatayi magana kenan ya rigata da cewa
“Wato kinyi amfani da salon zagi irin na hausawa kin zageni ko?”. Ido Heedayah ta zaro sosai tace
“Zagi kuma? wllhy nifa ba zaginka nayi ba ALLAH”. Tayi maganar kamar wadda zata sakar masa kuka, ba tare daya d’ago kanshi daga kan kujerar ba ya bud’e idanunshi yace
“Ba zagi bane? meye to?”.
Saidata tura baki cikeda shagwab’a tace
“Kawai fa gani nayi farinka yayi yawa mu a hausa idan akaga irin fararen nan basuda k’wari sai ace musu nunar rana amma wllhy ba zagi bane”.
Idanunshi ya d’an waro ya taso daga kan kujerar yana fad’in
“Sa’anki ne ni? ko abokin wasanki ne ni d’in, nine mara k’wari ko?”. ya ida maganar yana nuna k’irjinshi da d’an yatsanshi.
“Nidai kayi hak’uri please ka maidani gida Auntyna tana ta kira tun d’azu taji shiru ban komaba”. Kai kawai yake kad’awa ya tada motar kuma bawai dan maganar datayi masa ba kawai idan ya cigaba da zama anan zaiyi missing sallah ne da saiya tsaya ta nuna masa inane bashida k’warin a jikinshi shi zata rainawa hankali?.
Tafiyar kurame ce akayi ko tari ba wanda ya k’ara yi bayan sun tafi kowa da irin tunanin dayake a ranshi, gaba d’aya shi tunanin Habeeb ya tafi kan ya akayi suna matsayin twins amma d’aya a gidan marayu meyasa hakan? lallai akwai wani b’oyayyen sirri ma’ana ita wannan dayake gani a wajen Hajiya itace take tare da iyayensu? duk yadda akayi ita ta gidan marayun ta b’ata ne tun tana yarinya, dole zaiyi bincike akai amma kafin nan saiya zauna da Hajiya yaji tarihin wannan d’in saboda yasan ta ina zai fara binciken nashi. Haka ya dinga sak’a da warwara har lokacin da suka iso gidan Aunt Ramlah ta hanyar kwatance da Heedayah take masa, yana yin parking Heedayah tasa hannu da sauri da nufin ta bud’e k’ofar motar taji ta a rufe gam runtse ido tayi cikeda takaicin abinda guy d’in nan yake mata ta fuskanci mugun d’an tijara ne amma yanzu ita take nema dole ta kwantar da kai dan haka ta kalleshi a marairaice kafin ma tayi magana yasan abinda zata fad’a shima kuma sauri yake dan haka yayi unlocked tanajin alamun an bud’e tayi saurin bud’ewa ta fice ko godiya bata tsaya yimasa ba.
Nagode nunar rana”. tace tana d’an d’aga murya yadda zaijita tana fad’a ta shige gidan da sauri tana dariya, baisan ya akayi ba ya tsinci kanshi da sakin wani munafukin murmushi yana cije baki wato yarinyar nan ta maidashi wani abokin wasanta ko? ALLAH ya k’ara had’ashi da ita zatayi masa bayani ne dalla dalla wata k’aramar k’wafa ya saki yana jijjiga kanshi yabar unguwar da gudu.
Tana shiga ta samu Aunt Ramlah dasu Nu’aym a falo suna kallo ita Zainab taje gida sai gobe zata dawo, sallamar datayi Aunt Ramlah ta amsa tana binta da kallo tasamu kujera ta zauna tana mata sannu da gida Aunt Ramlah ta amsa tana fad’in
“Ke kuwa ina kika tsaya haka har magreebah kuma kinsan nida Abban Nu’aym bamuson kuna kaiwa dare a waje”.
Shiru ta d’anyi kafin ta lalubo abinda zatace
“Aunt Ramlah kinsan Hajiya fa akwai labari ita ta tsareni da hira”. Harara Aunt Ramlah ta jefa mata tace
“Kar kiyiwa Hajiya k’arya ai munyi waya da ita tun wuri tace ta had’aki da jikanta zai kawoki gida”. jin aikin gama ya riga ya gama ma baki ta tab’e tace
“Wllhy Aunt Ramlah wani jikanta ne irin arrogant man d’in nan bashida dad’in sha’ani saidaya fara biyawa dani wani gida ya shiga ya dad’e yabarni cikin mota sannan ya fito muka taho”. Kai kawai Aunt Ramlah ta kad’a tana fad’in
“To ai saiki tashi ki shiga ciki kiyi sallah”. tashin tayi ta d’auki jakarta ta wuce bedroom d’insu.

__
Kwana Habeeb yayi yana tunanin su Seeyamah da yadda zai b’ullowa lamarin, dan haka yana tashi da safe bayan yayi wanka ya shirya yaje ya gaida Ummi ya fita ya nufi gidan Kawu Sulaiman inda ana ne Hajiyan take, sai daya shiga side d’in Kawu Sulaiman d’in suka gaisa dashi da matarshi Hajiya Rahma sannan ya fito ya shiga sashin Hajiya.
Tana zaune taci wankanta da sabuwar atamfar ta ta kashe d’aurinta irin na tsofaffi sai k’amshin turaren wuta ne yake tashi a falon, tana ganinshi ta washe baki tana masa sannu da zuwa, waje yasamu ya zauna yana gaisheta ta amsa cikin sakin fuska tana tambayar shi lafiyar su Ummi tareda yimasa tayin abin karyawa yace yayi breakfast a gida.
“Hajiya nazo ne muyi wata magana dake please”. zamanta ta k’ara gyarawa tace
“Toh Habibu ALLAH yasa dai lafiya?”.
Jimm ya d’anyi kafin yace
“Hajiya yarinyar nan ta jiya da kika had’ani da ita in kaita gida…..tun kafin ya k’arasa abinda zai fad’a d’in Hajiya ta wani washe baki tana fad’in
“Alhmdulillah ALLAH nagode maka, ai karka damu Habibu ni d’in nan zan tsaya maka tsayin daka in shige maka gaba har sainaga tabbatuwar al’amarin nan ALLAH yasa alkhairi masha ALLAH abu yayi kyau ALLAH yasa ayi damu”. Duk saiya rasa gane inda maganganun Hajiyan suka dosa ya wani had’e rai yana yatsine fuska yace
“Wai me kike nufi ne Hajiya?”.
“A’a ban gane me nake nufiba? inace kaga yarinya kanaso kazo kanaso in shiga maganar”.
“OMG! tsohuwar nan kinada matsala wllhy ni na miki kama da wanda zai auri k’aramar yarinya kamar wannan haba ki daina ma wannan zancen please”. Tuni Hajiya ta tamke fuska tace
“Heedayahn ce yarinya? ALLAH na tuba idan a kauye ne yanzu ai Heedayah tayi wajen yara uku a’a jaririya ce k’arewar yarinta”. Hajiya ta k’arasa maganar cikin fad’a tana maka masa harara, goshinshi ya d’an dafe yana murza fatar goshin yace
“Nifa ba hayaniya nazo kimin ba Hajiya wata magana ce very important takawo ni akan yarinyar nan”.
“Ina jinka”. cewar Hajiya ta wani juyar dakai gefe ita a lallai ba haka taso ba.
“Inaso insan asalin yarinyar nan da abinda ya had’aku har take zuwa wajen ki?”.
“Duk wannan bin k’wakk’wafin na meye kuma?”. Ido ya lumshe yana d’an taune lips d’inshi cikeda gajiyawa da maganar dayake tun d’azun yace
“Hajiya dan ALLAH, kaina yafara ciwo saboda maganar danake tun d’azu ki taimaka please ki gayamin”.
Baki Hajiya ta tab’e tace
“Yaron kawunka Sulaiman ne mijin yayarta kuma y’an Katsina ne can shi Muhammadun ya aurota”.
Kai ya shiga jijjigawa yana fad’in
“Kenan y’ar Katsina ce ita d’in?”.
“K’warai kuwa dalilin zuwanta kuwa shine yaron dazata aura ne ya rasu ana saura sati d’aya biki ta shiga cikin matsanancin hali shiyasa yayar ta taho da ita ko zata samu sauk’in abinda take ji”.
“Thank you Hajiya”. yace yana mik’ewa tsaye, da kallo ta bishi tana fad’in
“Wai duk wad’annan tarin tambayoyin na menene saikace wani d’an jarida”.
Hannayenshi duka ya zube cikin aljihun wandonshi ya saki wani miskilin murmushi yace
“Bazaki gane bane Hajiya, nina wuce ayi mana addu’a”. daga haka yasa kai ya fice daga falon yabar Hajiya tana rakashi da kallon mamaki.
Kamar ance ya waiwaya bayanshi bayan fitowarshi gidan Hajiya ya hangi wata matashiyar budurwa kamar Heedayah wadda a yanzu yakejin sunanta a bakin Hajiya zata shiga gidan Alhaji Saminu wani mak’ocin su Kawu Sulaiman ne kuma abokinshi gidaje uku ne ya raba tsakanin su da gidan Kawu Sulaiman d’in, da sauri ya juya da sassarfa ya nufi gidan saidai kafin ya k’arasa harta shige gidan.
“Oh my God!”. Yace yana kai hannu kanshi yana yamutsa sumar kanshi gaba d’aya ya kasa barin k’ofar gidan ya shiga sintiri a k’ofar gidan kamar d’an doka sai faman kai da kawowa yake daga k’arshe daya gaji da zaryar saiya jingina jikin wata mota daya gani a k’ofar gidan yayi crossing legs d’inshi hannayenshi duka biyun ya cusasu cikin aljihun jeans d’in dayake jikinshi, idanunshi k’urr akan k’ofar gidan yana jiran fitowarta.
Jawaheer tazo aiken Mummyn tane Hajiya Saudah wadda matar Alhaji Saminun Hajiya Kareemah k’awar tace sosai a yadda Mummyn take bata labari tare sukayi school tun zamanin y’anmatancin su, to yau d’in ma wani sak’o tazo kawowa Hajiya Kareemahn.
Wayace kare a kunnenta ta fito daga gidan tana amsawa, tsaye tayi daga inda take tana k’are masa kallo idan bata manta ba shine gayen nan daya tab’a tareta a ShopRite har yana mata wasu maganganu data kasa fahimtarsu a lokacin to meya kawoshi nan unguwar? koma d’an gidan ne bata saniba? koma dai waye shi ba damuwar ta bace.
“I will call you back”. abinda ta fad’a kenan ta kashe wayar ta nufo inda yake tsaye dan d’aukar motar ta fuskar nan tata a d’inke.
Ido cikin ido suke kallon juna kowa fuska a tamke kamar wad’anda aka aikowa sak’on mutuwa, shigar jikinta yake bi da kallo yana k’ara had’e rai jeans ne pencil dark blue da farar riga body hook data matseta sai kimono ash color data d’ora akai da wani siririn ash gyale datayi rolling dashi, k’afarta sanye cikin hill shoes black color mai igiya da wata black hand bag dake mak’ale a hannunta, wato yarinyar nan RUWA BIYU ce yau tasa kayan arzik’i gobe tasa na tsiya ko jiya ma hijabi ne ai a jikinta lokacin daya d’auketa a motarshi amma dubi irin shigar datayi yau sosai ranshi ya b’aci yau saiya titsiyeta ta fad’a masa uban dayasa take wannan d’abiar dama ga haushin nunar rana data k’ara cemasa jiya bayan ya sauketa…..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38Next page

Leave a Reply

Back to top button