EL-HABEEB HAUSA NOVEL

Afwan a k’ara hak’uri dani yanayin yadda page d’in yake zuwa ba yawa sosai harkar mai iyali sai hak’uri naji mutane dayawa na complain page d’in yana kad’an I’m so sorry????????????????.
Sai masu bina PC suna cewa in basu book din nan daga farko dan ALLAH suyi hak’uri su dinga tambaya a group abin zaimin yawa ga typing ga turawa daga farko kuma anfara nisa mutum ba d’aya ba ba biyu ba dayawa duk da nasan k’auna ce ta kawo hakan amma dai ayi hak’uri a dinga tambaya cikin grup.
Nagode.
Maryam Ibraheem Aleeyu
Mrs Salees Mu’az ????
EL HABEEB????
©️Oum Hanan.
Writer of DR SAIF.
HASKE WRITER’S ASSOCIATION????
(Home of expert & perfect writer’s).
Special thanks for
Ameenah Abubakar, Husnah Abdullahi, Mum Elham, Haneefah S.G, Maryam kabuga, Aseeyah Buhari, Mrs Kabeer, Miss Ayshaa, Rabi’atu Musa, Maman sadeeq, Mum Farouq, Oum Anwaar. jazakumullah khair all nagode sosai da yadda kuke nunawa book din nan k’auna fatan alkhairi ????.
No 24.
Cikeda b'acin rai yake kallonta harta k'araso inda yake tsaye ko motsi baiyi ba bare ya matsa daga jikin motar duk da alamu sun nuna masa motar tace tunda gashi tazo inda yake.
“Excuse me”. Ta fad’a cikin had’e rai bayan k’arasawar ta tana wani kad’a car key d’in dake hannunta, sam bai nuna ma yasan abinda ta fad’a d’in ba sai kallon takaici dayake binta dashi yanajin tamkar ya daddalla mata mari hakan yasa ta k’ara k’uluwa ganin irin kallon rainin dayake mata.
“Wai Malam baka jine? bakaji abinda nake fad’a ba? ko kurma ne ban saniba?”. Ta jero masa tambayoyin a lokaci d’aya tana wani yatsina fuska, sai a lokacin ya d’ago daga jikin motar yayi mata tsaye a gabanta ido cikin ido suke kallon juna kafin cikin b’acin rai ya fara fad’in
“Meyasa ke bakida kamun kai ne? yau kiyi shigar arzik’i gobe kiyi ta tsiya why? kina tallan jikinki a waje saboda bakida hankali meyake damunki ne?”. Ya k’arasa maganar yana wani zare mata ido, cikeda d’imbin mamaki take kallonshi da tunanin anya mutumin nan kanshi d’aya kuwa? to inba hakaba ina ruwanshi da ita dazai tsareta yana mata wasu maganganu marasa kai taga alamun saita kafta masa rashin mutunci sannan zai shafa mata lafiya dan haka cikin masifa tace
“Kai dallah malam bansan hauka, ya zakazo ka tareni kana min wani soki burutsu a ina ka sanni? meye had’ina dakai?”. Ta ida maganar tareda jan wani dogon tsaki wanda Habeeb ya jishi har tsakiyar kanshi tsabar yadda ranshi ya b’aci baisan ya akayi ba sai gani yayi ya canza musu position d’in tsayuwar tasu ita ta koma jikin motar shikuma yana tsaye a gabanta ya matseta da k’irjinshi sai huci yake idanunshi sun fara canza kala, cikeda bala’i yake fad’in
“Waye mahaukaci? nace wa kike kira da mahaukaci?”. Ya k’arasa maganar cikin tsawa, batare da shayin komai ba ta kalli cikin idanunshi cikin tsiwa da rashin kunya tace
“An fad’a maka haka, me zakayi? ko akwai matakin da zaka d’auka ne? inba hauka ba ni ban sanka ba kazo kaita min wasu shirmen maganganu wllhy idan bakayi was……Wata wawar damk’a yayiwa bakinta wanda yasa dolenta tayi shiru ba shiri ta saki wata siririyar k’ara amma tsabar taurin kai bata daina antaya masa uwar harara ba tamkar idanunta zasu fad’o k’asa duk kuwa da irin zafin dake ratsa ta, sai daya cije baki kafin ya had’e leb’enta na sama dana k’asa ya murje da dukkan k’arfinshi ta k’ara sakin wata k’arar kuka take so tayi saboda azaba amma bazata iya kuka a gabanshi ba ai kamar ta kasa ne yaga lagonta dan haka ta shanye kukanta ta cigaba da watsa masa harara, so take ta tureshi saboda yadda kusan nasu tayi yawa gaba d’aya yayi mata rumfa ya babbake ko ina bata ganin komai sai shi d’in, a fusace yace
“Bakinki yasan irin kalmar da zaki dinga fad’a a kaina Habeeb ya wuce da saninki very stupid”. Hannu tasa da k’arfi ta fincike hannunshi ta yarfar dashi gefe tace
“Dalla Malam sakeni, idan ka saba iskanci da y’an mata to Jawaheer tafi k’arfinka wllhy aikin banza kawai”.
Sunan dayaji ta fad’a ne yasa mamaki ya kamashi idan bai manta ba Heedayah yaji Hajiya ta ambata amma ita kuma wannan yaji ta ambaci wani sunan daban mai hakan yake nufi? bai ankara ba yaji ta tureshi saboda yadda ya shiga rud’ani, tsugunawa tayi ta d’auki kayan hannunta da suka watse lokacin daya fincikota.
Yana gani ta bud’e motar ta shiga mamaki yasa ya kasa hasala komai bare yayi yunk’urin binta.
“ALLAH ya isa mugu azzalumi”. tace tana lek’o da kanta ta window’n motar kafin ta bata wuta tabar layin da gudu, tsaye yayi kawai ya kama k’ugunshi da duka hannayenshi yabi motar da kallo har zuwa lokacin da motar ta b’acewa ganinshi.
“Yaa Ilahee”. Ya ambaci hakan yana dafe goshinshi gami da runtse idanunshi gam g kanshi ke wani irin sarawa yana jujjuyawa wai kodai aljanu ne keson bud’e masa ido ne? Seeyamah, Heedayah again kuma wata Jawaheer daban? hakan na nufin triplets ne kenan? kokuma dai Heedayahn ce Jawaheer? gaba d’aya k’wanyar kanshi ta d’auki zafi ya rasa wane tunanin ma zaiyi.
Kamar wanda aka mintsina ya zabura da sauri ya nufi gida, kai tsaye side d’inshi ya nufa yana shiga ya wuce kitchen ya d’auko swan water medium size bottle ya fito tsakiyar falon ya tsaya ya b’alle murfin robar ya kafa kai ya shiga kwankwad’ar ruwan duk da irin sanyin dayake dashi kuwa sai daya shanye shi tas sannan yayi jifa da robar ya rik’e k’ugunshi da hannu d’aya d’ayan kuma ya shiga yamutsa lallausar sumar shi mak’wallaton shi sai kai da kawo yake yana sauke numfashi idanunshi a rufe sam yayi ragon azanci daya bita yaga itakuma inane gidansu shifa yanzu yafara zargin maybe yaran nan aljanu ne suke masa yawo da hankali Seeyamah gidan marayu, Heedayah Katsina ance gidan yayarta take da zama and now Jawaheer itama anan Kano kai wannan lamari akwa mugun d’aure kai amma insha ALLAH zaibi komai step by step domin gano gaskiyar lamari, tabbas akwai wani b’oyayyen sirri inba hakaba ace yara har uku a matsayin su na triplets amma kowa da inda yake rayuwa?
Wani dogon numfashi yaja ya zube bisa kujera idanunshi a rufe yayi relaxing sosai yana cije lips.
Kusan mintuna biyar yana zaune a haka ko cikakken motsi bayayi har lokacin bai bud’e idanunshi ba sai sak’a da warwara yake kan ta inda ya kamata ya fara da lamarin.
Bud’e k’ofar da akayi aka shigo ita tasa ya bud’e idanunshi a hankali ya kalli wanda ya shigo d’in cikakken saurayi ne kamar shi wanda zasuyi kusan sa’anni dashi shima dogo ne saidai shi yanada y’ar k’iba kad’an very handsome guy ne bashi da hasken fata sosai amma kallo d’aya zakayi masa kasan hutu yasamu gurin zama a jikinshi duba da yadda fatar jikinshi take wani shek’i da d’aukar ido.
Shigar k’ananun kaya ne a jikinshi blue black d’in jeans ne da lemon green d’in riga mai gajerun hannuwa wanda hakan yaba cikakkun damatsen shi bayyana sai P.cap blue black daya d’ora a kanshi, tunda ya shigo falon shima k’amshin turarenshi ya cika ko ina ya had’e dana Habeeb wanda ke zaune har lokacin yana binshi da kallo ko motsi baiyi ba, duk da cewa yayi farin cikin ganinshi kuwa.
Cikeda fara’a da murna ya k’arasa kujerar da Habeeb yake ya zauna kusa dashi.
“Matsalata dakai kenan wulak’anci d’an balarabe duk lokacin da muka d’auka bamu had’u ba amma ji irin tarbar daka yimin saboda bakada mutunci”. Ya fad’a yana dukan kafad’ar Habeeb d’in da tashi kafad’ar, harara ya watsa masa kafin ya tashi zaune sosai yace
“Zaka iya komawa inda ka fito indai saina tashi nayi hauka nayi ihu saboda ganinka saikace wani ubana”.
“Halin dai yana nan yadda nasani a baya”. MUHSEEN yace yana d’an tab’e baki da jijjiga kai, cikin yaren larabci Habeeb ya bashi amsa.
“A’a fa karka zageni Malam muma fa munajin larabcin nan ma ismuka, aina tazhab……. kafin ya k’arasa Habeeb yasa dariya (Yaudai naga dariyar Gashua ????).
“D’an iskan abokina”. ya fad’a cikin dariyar tareda kamoshi ya rungume, shima Muhseen d’in dariyar yake suka rungume juna cikin farin ciki.
Muhseen d’an gidan abokin Abbu ne Alhaji Usman Shareef sun had’u ne ta harkar kasuwancin su ALLAH ya had’a jininsu, bayan kammala karatunshi dayayi lokacin daya dawo 9ja suka had’u ta silar iyayen nasu daga nan suka k’ulla abokantaka duk da Habeeb d’in ma bai bawa zumunchin nasu wani muhimmanci ba amma shikam Muhseen ya d’aukakeshi sosai kuma yana hak’urin zama dashi har a yanzu Alhaji Usman d’in bai yada suba jefi jefi yana zuwa suna gaisawa da Ummi dasu Hajiya da Kawu Sulaiman, shima dai irin Mujaheed ne bakin abin magana basa gani su k’yale dayake ta dalilin Habeeb d’in shima Mujaheed d’in sun saba dashi. shikuma engineering ya karanta yana aiki a wani babban kamfani na software a Abuja amma dayake iyayenshi y’an Kano ne yasa yake yawan zuwa sosai yanzu ma dalilin dad’ewar shi baizo ba sunje wani course ne a Italy na watanni kan abinda ya shafi aikinsu na engineer.
Anan kuma hira ta b’arke tsakaninsu duk da dai duk rabinta ma Muhseen d’inne ke yinta, sun dad’e anan sannan suka tashi Habeeb yayi masa jagora zuwa part d’in Ummi dan ya gaisheta, itama tayi murna da ganinshi bayan sun gaisa suka fito compound d’in gidan sukayi sallama Muhseen ya shiga motarshi ya tafi shima Habeeb part d’inshi ya koma dan d’auko key d’in motarshi ya tafi office dama wancan banzan sai kiranshi yake a waya, duk abinnan da ake tunanin triplets na nan daram mak’ale a ranshi da tunanin samun mafita.