EL-HABEEB HAUSA NOVEL

Yammacin ranar.
Danger ce ta tsaida motoci, cikin wad’anda aka tsayar d’in harda Mujaheed wanda bayan tashin shi daga wajen aiki ya biya ta wani waje, tsaki kawai yake ja yana duba agogon hannunshi saboda sauri yake yakoma gida yanada uzurin da zaiyi, kamar ance ya waiga gefenshi ya hango Aleeyu shima zaune a cikin mota yana jira a bada hannu, shifa dama ya dad’e baiga Aleeyun ba to yayi zaton ko har dashi ya kora ne abinda ya k’ara bashi mamaki bai wuce ganin yadda Habeeb yake yawan yin waya da Aleeyu ba dama gashi yana zargin Habeeb d’in akan Seeyamah hakan yasa lokacin da aka bada hannu yabi bayan Aleeyu.
Tiryan tiryan ya dinga bin Aleeyu batare daya bari yagane shi yake bi ba har lokacin da suka isa unguwar ta lamid’o crescent Aleeyu ya shiga cikin unguwar shikuma Mujaheed anan bakin titi yayi parking ya fito ya dinga takawa a k’afa yana bin Aleeyu bayan ya toshe idanunshi da bak’in glass ga face mask dayasa, binshi yake yana mamakin unguwar da sukazo d’in sun tab’a zuwa da Habeeb ya nuna masa wani plat house daya siya kuma idan bai manta ba nan unguwar ne.
Aleeyu bai dad’e yana tafiya ba yayi parking a k’ofar wani gida, ido Mujaheed ya zaro ganin k’ofar gidan dayayi parking d’in nan ai shine gidan da Gashua ya kawoshi d’in hakan na nufin……bai k’arasa tunanin shiba yaga Aleeyu ya fito daga cikin motar da sauri yasamu wani d’an lungu ya lab’e ya lek’o da kanshi yana kallon Aleeyu ya bud’e gidan ya shiga da wata leda mai d’auke da tambarin sunan wani gidan abinci a hannunshi, mamaki, tsoro, al’ajabi gamida d’imbin tararrabin abinda zaije ya tarar ne a cikin gidan suka sandarar dashi a tsaye a wajen kardai abinda ya dad’e yana zargi tun bayan sanarwar b’atan Seeyamah daya gani ya tabbata idan kuwa hakane me yake damun Gashua? ta ina ya kamata ya shiga gidan addu’a yake a cikin ranshi ALLAH yasa Aleeyun ya fito ko zai samu hanyar shiga yaga meye a ciki.
Addu’ar shi taci kuwa dan Aleeyu bai dad’e da shiga gidan ba sai gashi ya k’ara fitowa da sauri ya k’ara lab’ewa har Aleeyun yazo ya k’ara wucewa a mota yabar layin.
Cikin hanzari Mujaheed ya fito daga d’an lungun dayake ya nufi gidan, cikin sa’a kuma yana tura k’ofar gate d’in yaji ta bud’e abin mamaki, shiga yayi ya maida k’ofar ya rufe yana k’arewa gidan kallo. A hankali ya shiga takawa zuwa k’ofar babban falo na gidan itama dai yana murd’a handle d’in yaji ta a bud’e shiga yayi ya rufe yana bin ko ina na falon da kallo an k’awata ko ina yaji royal chair shi a lokacin da Habeeb d’in ma ya kawoshi ba asa komai a cikin gidan ba.
Dube dube ya shiga yi ko zaiga wani abin amma ba komai hakan yasa ya maida akalar binciken nashi kan d’akunan barcin gidan na b’angaren dama nan ma duk inda ya bud’e ba abinda yake gani a ciki, d’ayan b’arin yakoma ya bud’e bedroom na farko yaga ba komai gaba yayi yasa hannu ya bud’e na biyun idanunshi suka d’auko masa hoton Seeyamah tana zaune akan gado ta tsurawa waje d’aya ido da alamu ta fad’a cikin zuzzurfan tunani, kamar ko yaushe babban hijabine a jikinta ta rufe ko ina na jikinta hatta k’afafunta ba’a ganinsu fuskar tace kawai ta bayyana.
Wani mugun bugawa k’irjinshi yayi zuciyarshi tamkar zatayi tsalle ta fito tsabar tsorata da yayi da abinda idanunshi suka gani har wani jiri jiri ne yaji yana neman kada shi…..
Masu buk’atar a tallata musu hajarsu zasu iya nemana ta wannan number
09139964697.
Maryam Ibraheem Aleeyu
Mrs Salees Mu’az ????
EL HABEEB????
©️Oum Hanan.
Writer of DR SAIF.
HASKE WRITER’S ASSOCIATION????
(Home of expert & perfect writer’s).
Jama’a bafa paid book bane anata tambaya na har nagaji da amsawa ???? free book ne.
No 25.
Seeyamah ma hankalinta ta maida kan k'ofar taga wani tsaye yana kallonta ba Aleeyu bane sannan kuma ba wancan mutumin dayasa aka k'wamuso ta bane tunda shi yafi wannan d'in datake gani tsayi gashi kuma ya rufe idanunshi, sosai gabanta ya buga tafara tunanin kodai wani ne daban yazo ya cutar da ita? A hankali ya shiga takawa zuwa cikin bedroom d'in yana k'ara jin mamakin abinda yasa Gashua ya kawo wannan yarinyar gidan nan.
A tsorace ta shiga ja baya kamar zatayi kuka tana kallon yadda yake k’ara kunsanto ta, yana zuwa bakin gadon ya tsuguna kan gwiwoyinsa yana cigaba da kallonta wani mugun tausayin ta na k’ara ratsashi.
“Dan ALLAH karka cutar dani bawan ALLAH kayi hak’uri I’m sorry please”. ta fad’a cikin rawar murya tana had’e hannayenta waje d’aya alamun rok’o idanunta duk sun cika da ruwan hawaye, gam ya runtse idanunshi cikin tsananin tausayin ta, hannu yasa ya zare glass d’in idonshi da face mask d’in fuskarshi ido ta zaro ganinshi datayi a gidan nan dan bazata tab’a mantawa da fuskar bawan ALLAHn nan ba shine yayi sanadin komawar ta gidan marayun bayan wannan ogan na Aleeyu ya koreta, duk saitaji wata nutsuwa na shigarta tana rok’on ALLAH ta sanadiyyar shi ta fita daga cikin wannan prison d’in kana ganin fuskar shi kasan mutumin kirki ne.
Ganinshi yasa ta saki wani marayan kuka na tausayin kanta da halin datake ciki, da sauri ya tashi ya zauna bakin gadon kusa da ita cikin taushin murya data had’u data rarrashi yace
“Please Seeyamah stop crying I’m so sorry”. ya k’arasa maganar kamar shima zaiyi kukan gamida zaro wani kyakkyawan k’aramin hanky fari mai adon pink d’in flowers a jiki ya mik’a mata daga aljihunshi ya mik’a mata sai tashin k’amshi mai dad’i yake, hannu tasa ta karba ta shiga sharewa tana sharewar wasu na k’ara zubowa.
“Please I’m sorry mana Seeyah, kiyi shiru ya isa haka uhmm? ko kinaso kanki yayi ciwo?”. A hankali ta girgiza masa kai.
“Ko so kike nima inyi kukan?”. Nan ma kai ta girgiza masa
“Okay yanzu ki fad’amin waye ya kawoki nan gidan kuma tun yaushe kike anan?”. ya ida maganar tareda zaro wayarshi daga aljihu ya danna recording ya ajiyeta kusa dashi, cikin kuka Seeyamah take fad’in
“Ba wannan abokin naka bane wanda ya tab’a korata daga gidan marayu yasa aka d’auko ni ya kawoni nan”.
“Why me kikayi masa?”. Yace yana k’ok’arin had’iye b’acin ranshi hak’ik’a Habeeb ya bashi mamaki.
“Wallahi ni bansan me nayi masa ba kawai yasa an d’aukoni yacemin wai meyasa nake bibiyar rayuwar shi kuma dole saina fad’a masa waye shi sannan zai maidani na rantse da ALLAH ban sanshi ba bansan wani abu game dashi ba ka taimakeni dan ALLAH”. tayi maganar tana shirin k’ara sakin wani kukan cikin sauri yace
“No no Seeyah don’t cry please insha ALLAH zaki bar gidan nan kinji?”.
Kai ta gyad’a masa tana fad’in
“Ka tafi dani yanzu dan ALLAH”.
Kai ya girgiza yace
“Ba yanzu ba Seeyamah ki kwantar da hankalinki kinji kamar kin fita kin gama ne yanzu dai karki fad’awa kowa zuwana shima Aleeyun dayake tsaronki karki nuna masa nazo zan dawo anjima ko gobe in tafi dake relax ur self ok?”. Sosai ta marairaice fuska tana kallonshi gani take tamkar idan ya riga ya tafi bazai dawoba jitake tamkar ta rik’eshi saiya tafi da ita.
Murmushi ya d’an saki yace
“I’m promise to u insha ALLAH karki damu”. ya k’arasa maganar yana mik’ewa tsaye ya maida wayarshi cikin aljihu ya juya zai tafi.
“Dan ALLAH karka k’i dawowa ka taimakeni”. Mujaheed ya tsinkayi muryar Seeyamah na fad’a cikin rauni.
Wani irin tausayin tane ya k’ara shigarshi ya runtse ido tsigar jikinshi na tashi a hankali ya juyo ya kalleta tareda sakar mata wani murmushin yak’e cikin k’asa k’asa da murya yace
“I’ll promise insha ALLAH”. daga nan bai saurari abinda zatace ba ya fice da sauri zuciyarshi na bugawa. Yana fita Seeyamah ta k’ara sakin wani kukan ta cusa kanta tsakanin gwiwarta tana rizgar kukanta gani take tamkar shikenan Mujaheed ya tafi bazai dawoba.
Ya dad’e sosai zaune a cikin motarshi ya kwantar da kanshi kan seat d’in motar idanunshi a rufe har lokacin bai gama dawowa daga rud’ani da d’imbin mamakin abinda yasa Gashua ya gark’ame Seeyamah ba me yake nema a duniyar nan? meye ubangiji baiyi masa ba da har zaiyi garkuwa da yarinya, yarinyar ma ta gidan marayu wadda idan ba’a tausaya mata ba ai ba’a cutar da ita ba, tsaki yaja a karo na ba adadi yana tunanin ta ina zai fara yanzu? bazai tab’a bari Gashua yayi abinda ranshi yakeso ba saiya gane kuskuren shi anya ba police kawai zaije yayi k’arar Gashua ba? da sauri ya girgiza kai a fili ya furta
“No impossible, to kodai Habeeb zai samu da maganar nan ma kai ya girgiza yasan Gashua farin sani kamar yunwar cikinshi yanzu yana iya yayi masa maganar ya nuna sam baisan ma wani abu makamancin wannan ba ko ya nuna yayi d’in ya d’auki matakin da duk yake ganin zai d’auka dan haka ma bazai yimasa maganar ba Ummi kawai ya kamata ya samu ba wani zancen ya rufa masa asiri yayi ba daidai ba yanaso kuma har cikin ranshi yaji ba daidai d’in yayi ba a nuna masa kuskuren shi, sosai ya aminta da shawarar da zuciyarshi ta bashi hundred percent dan haka cikin hanzari ya tada motar kai tsaye ya nufi gidansu Habeeb wajen Ummi.