EL-HABEEB HAUSA NOVEL

★_★
Shiru falon ya d’auka bakajin komai sai k’arar air conditioner dake d’akin bayan Ummi ta gama saurarar abinda Mujaheed yaje mata dashi ya kuma kunna mata recording d’in dayayi da abinda Seeyamah take fad’a, ba k’aramin rud’ani da tashin hankali Ummi ta shiga ba a lokacin ta shiga b’acin rai fiye da tunanin mai karatu abin ya tab’ata fiye da tsammani d’anta na cikinta wanda ta haifa shine yayi kidnapping me yake nema a rayuwar nan? wane mataki ne bai taka ba a rayuwar shi? jikinta har rawa yake ta d’auki wayarta ta lalubo number Habeeb d’in ta danna masa kira sai sauke numfashi take sama sama fuskarta tayi jawur saboda b’acin rai, Mujaheed kanshi saiyaji dama baizo mata da maganar ba amma kuma hakan shine daidai bai kamata ya rufe maganar ba bawai dan bayason Habeeb d’in ba kokuma yanaso ranshi ya b’aci bane hasalima yana matuk’ar gudun b’acin ran Habeeb kuma har a yanzun yanaji baiyi wani abu wanda ba daidai ba.
Habeeb na d’aga kiran Ummi tace yazo tana nemanshi duk inda yake kuma duk abinda yake ya bari yazo, sam bata saurari tambayar dayake mata ba na lafiya kuwa meyake faruwa ta kashe wayarta ta ajiyeta gefe sai gaman girgiza k’afa take tana huci.
Nan suka cigaba da zama ita da Mujaheed ba wanda ya k’ara yin wata magana, ko cikakkun mintuna goma ba’a rufa ba Habeeb ya shigo cikin falon kamar ko yaushe sallama a ciki ciki, Mujaheed nema kawai ya amsa sallamar Ummi kam wani irin mugun kallo tabi Habeeb dashi wanda take yasha jinin jikinshi gabanshi ya fad’i, ido suka had’a da Mujaheed ya wurga masa wani kallo duk da baisan ainihin abinda yake faruwa ba.
Gefen Mujaheed ya zauna kusa da k’afafun Ummi yana saurarar abinda Ummin zatace, hannu ta mik’awa Mujaheed sanin abinda take nufi yasa ya d’ora mata wayar akan hannunta bayan ya cire pattern, play ta danna sannan ta mik’awa Habeeb wayar kallonta yayi cikin rashin fahimta tsawar data daka masa ne da kuma muryar yarinya dayaji tana magana tana kuka yasa yayi hanzarin karb’a. Ido ya d’an zaro jin abinda yarinyar take fad’a gabanshi yayi wata irin bugawa ba shiri ya mik’e tsaye yana bin Mujaheed da wani irin mugun kallo shima Mujaheed d’in k’yar yake kallon Habeeb d’in ba tareda shayin komai ba.
Tsaye Ummi ta mik’e ta tsaya a gaban Habeeb tana binshi da wani tuhumammen kallo cikin rawar murya Ummi tace
“Abbuna meka aikata haka? me kakeso ka zama ne? me kake nema a rayuwar ka da har saikayi garkuwa da mutane? nace me kake nema?”. ta k’arasa maganar cikin tsawa tareda sakar masa wani mahaukacin mari a kuncinsa na dama kafin ya dawo daga tsananin rud’ani da mamakin daya shiga na marin da Ummin tayi masa ta k’ara bashi wani marin a kumatunshi na hagu, da sauri Mujaheed ya taso ya rik’e hannun Ummi lokacin datake niyyar k’ara kai masa wani marin.
“Dan ALLAH Ummi kiyi hak’uri ki zauna dashi kuyi magana ta fahimta kiji dalilin shi na d’aukar yarinyar please Ummi I’m sorry”.
“Har wani dalili yake dashi dan ubanshi dazai d’auke yarinyar jama’a? ka sani idan har wani abu yasamu yarinyar mutane ALLAH bazai tab’a barinka ba shashasha sakarai saikuma ta canza harshe cikin yaren larabci ta shiga zazzagawa Habeeb fad’a ta inda ta shiga ba tanan take fita ba, Habeeb dai yana tsaye tamkar wanda aka dasa kanshi a k’asa idanunshi har wasu ruwa suka tara tsabar bala’in dake cinshi duk wannan fad’an da Ummi take sama sama yake jinta kawai yana kissima yadda zaici uban Aleeyu dashi kanshi Mujaheed d’in tunda munafuki ne shi ta yaya har ya gano Seeyamah tana wajenshi? koda yake ba laifinshi bane duk laifin Aleeyu ne da baiyi sakaci ba da duk haka bata faru ba zai nuna masa waye HABEEB GASHUA.
Mayafin doguwar rigar dake jikinta Ummi ta gyara ta cewa Mujaheed suje ya kaita wajen yarinyar, tun kafin taga yarinyar tausayin ta ya kamata kuma take taci burin insha ALLAH tabar gidan marayun kenan ita zata d’auke ta tadawo hannunta da zama zata zame mata uwa uba zatayi mata gatan da zatayiwa d’an data haifa a cikinta.
Fita sukayi suka barshi nan tsaye har lokacin bai d’ago kanshi ba ajiyar zuciya kawai yake saukewa ta b’acin rai idanunshi sun kad’a sunyi jawur jijiyoyin kanshi duk sun fito rad’a rad’a dasu, suna fita Mujaheed ya dawo falon kusa da Habeeb yaje ya tsaya yace
“Kayi hak’uri abokina banyi haka dan in b’ata maka raiba kokuma dan in had’aka da Ummi ba hakan danayi shine daidai I’m so sorry Ummi tace kazo mutafi tare”. bai jira amsawar shiba yayi hanyar fita dan yasan idan zai kwana yana masa magana a lokacin dai bazai tankashi ba gari banza ma anyi magana ya share mutum bare yanzu da ranshi yake a b’ace? ai sai abinda mutum yagani kawai.
Sai a lokacin Habeeb ya d’ago kai yabi bayan Mujaheed da wani irin kallo na tsabar takaici jiyake tamkar yayi masa d’iban karan mahaukaciya wllhy sai yaci ubanshi badai shi yayiwa haka ba? k’wafa ya saki da k’arfi yana jijjiga kai gamida cije baki, da k’arfi yake takawa kamar zai tashi sama ya fita daga falon….
Alhmdulillah nasamu sauk’i ku tayani addu’ar ALLAH yasa kar ya dawo tunda akayi cikon dai har yanzu bai k’ara tashi ba ALLAH yasa ya tafi kenan nagode sosai da addu’oen ku a gareni sakallahu khayran????.
Yaudai Gashua ansha maruka???? fuskar zata k’ara nuna yanzun????.
Wasu zasuce Mujaheed bai kyauta ba nidai yamin daidai aradu ko nice haka zanyi masa????
Maryam Ibraheem Aleeyu
Mrs Salees Mu’az ????
09139964697.
EL HABEEB????
©️Oum Hanan.
Writer of DR SAIF.
HASKE WRITER’S ASSOCIATION????
(Home of expert & perfect writer’s).
No 26.
Yana fita yaga Ummi da Mujaheed har sun shiga motar da ake kai Ummi unguwa ƙatuwar Jeef ce black color sai walƙiya take, bai nufi inda suke ba saiya nufi inda yayi parking ɗin tashi motar a fusace ya buɗe ya shiga yana shirin tada ita yaga Mujaheed ya fito daga ya nufo inda yake, so yayi ya figi motar tashi yabar gidan sai kuma ya fasa ya cigaba da kallon Mujaheed ɗin ya fito ya lakaɗa masa dukan tsiya.
Glass ɗin motar Mujaheed ya ƙwanƙwasa bayan isowar shi sai daya mula sannan ya zuge glass ɗin tareda watsawa Mujaheed wani banzan kallo, cikin matse dariya Mujaheed yace
“Ummi tace ka fito mu tafi gaba ɗaya”. Banza Habeeb yayi masa ya ƙara cewa
“Wai bakaji abinda nace bane Gashua?”. A fusace ya ɗago ya kalleshi cikin kufula yace
“Na rantse idan baka ƙyaleni ba zan take ka da mota a wajen nan”.
Ido Mujaheed ya zaro sosai yayi baya da sauri yana ɗage hannaye sama cikin son bada haushi yace
“Innalillahi! bayan kidnapping ɗin kisan kai zaka fara Gashua?”. Wani ƙululun baƙin ciki ne ya tokare maƙwogwaron Habeeb saidai bai tankawa Mujaheed ɗin ba dan yana tarashi ne wllhy saiyaci uwarshi tunda munafuki ne shi, fitowa yayi daga motar bammm ya maida murfin ƙofar da uban ƙarfi ya nufi inda Ummi take Mujaheed ya rufa masa baya yana masa dariya.
Front seat ya buɗe ya shiga Mujaheed kuma ya shiga driver seat bayan ƙarasowar shi ya tada motar suka fita daga gidan.
Tunda suka tafi ba wanda yayi magana kowa da abinda yake saƙawa a cikin zuciyarshi jefi jefi Mujaheed ke juyowa ya kalli Habeeb so yake yayi tsokana amma ganin Ummi a wajen kuma bata cikin yanayi mai daɗi yasa yaja bakinshi ya tsuke, shima Habeeb ɗin dayaga hakan kawai saiya kwantar da kanshi bayan kujera ya rufe idanunsa dan zai iya kaiwa Mujaheed ɗin naushi batare daya sani ba.
Parking sukayi a ƙofar gidan Mujaheed da Ummi suka fito daga motar shikam gogan naku yasani sarai anzo amma ko motsi yaƙi yi yayi bakam dashi, Ummi ce ta buɗe side ɗin dayake da larabci ta shiga yimasa cikin faɗa kamar zata dakeshi ba shiri ya fito yana wani kumbura fuska kamar zaiyi kuka, gaba Ummi ta tasa shi tabi bayanshi shi dama Mujaheed tuni yana bakin ƙofar yana knocking da alamu Aleeyun yana ciki.
Ba’a daɗe ba sukaji muryar Aleeyu yana tambayar waye? shiru akayi ba wanda yayi magana sai Ummi ce data kalli Habeeb wanda ya gane ma’anar kallon datayi masa dan haka murya ƙasa ƙasa irin wanda aka takurawa ɗin nan ya amsawa Aleeyu daya buɗe ƙofar shine.
Mamaki ne ya cika Aleeyu yasan ko lokacin dayake ɗan yawan zuwa gidan farko farkon kawo Seeyamah kenan baya masa knocking saidai ya kirashi a waya yazo ya buɗe masa, bai damu ba kuma bai kawo komai cikin ranshi ba dan yasan halin ubangidan nashi bauɗaɗɗen mutum ne da ba’a gane gabanshi bare bayanshi yau kuma ra’ayin knocking ɗin yayi dan haka kai tsaye ya buɗe ƙofar yayi tozali da Habeeb ɗin tsaye bakin ƙofar ya soke hannayenshi cikin aljihun wandonshi yana binshi da wani matsiyacin kallo mai hautsina zuciyar duk wanda akayiwa, wata faɗuwar gaba ce ta sameshi lokaci ɗaya musamman mutanen daya hanga a bayan Habeeb ɗin da sauri ya kauce yabasu hanya suka shiga yana gaida Ummi amma sam bata kulashi ba ta shige ciki suka rufa mata baya banda faɗuwa ba abinda gaban Aleeyu yake shikenan yasan yau yarasa aikinsa tun daga irin kallon da oga Habeeb ke jifanshi dashi daga ni ba sauƙi, Mujaheed ne ya yiwa Ummi jagora zuwa ɗakin da Seeyamah take Habeeb kam daga falo ya coge yayi tsaye tamkar wani dogari har lokacin bai cire hannayenshi daga cikin aljihun wandonshi ba, Aleeyu dayake duk a tsorace ya buɗe baki zaiyi magana kenan Habeeb ya jefeshi da wani irin kallo cikin tsawa yace
“Stop it! idan ka sake ka furta kalma ɗaya a nan zan baka mamaki Aleeyu very stupid”.
Dole tasa Aleeyu yaja bakinshi ya tsuke ya sunkuyar da kanshi ƙasa yana jiran jin abinda zai biyo baya yasan dai ya riga ya rasa aikinsa duk da dai baisan laifin dayayi ba tunda har lokacin baisan cewa Mujaheed yazo gidan ba kawai dai yayi tsammanin gano shi ɗin da akayi ya ɗauke yarinyar ne ya ɓata masa rai haka.
Tana zaune daga ƙasan gadon kan rug ɗin dake shimfiɗe a ƙasa ta cusa kanta tsakanin gwiwoyinta duk da dai ba kuka take ba, jin an buɗe ƙofa an shigo yasa ta ɗago kanta da sauri ta kalli bakin ƙofar tayi arba da Mujaheed da kuma wata mata wadda kallo ɗaya tayi mata taga tsantsar kamannin su da wanda ya ƙwamuso ta, tsaye ta miƙe da sauri tana cigaba da kallonsu har suka ƙaraso inda take hannuwanta Ummi ta riƙo suka tsirawa juna ido kafin Ummi ta janyota jikinta ta rungume ta tsam a jikinta tamkar ta santa, wani irin kuka Seeyamah ta saki wanda tun farkon zuwanta gidan rabon datayi irin shi. Patting ɗin bayanta Ummi ta shiga yi cikin tsananin tausayinta lokaci ɗaya wata soyayyar yarinyar da ƙaunarta na ratsata, Mujaheed yana gefe sai kallonsu yake yana murmushi cikin farin ciki.
Ɗago ta Ummi tayi tasa hannu tana share mata hawaye da faɗin
“I’m sorry daga yau kukan ki ya ƙare yarinya kisa a ranki kin samu UWA nikuma daga yau na samu ƳA insha ALLAH muna tare har abada”. Wani kukan ne ya ƙara tahowa Seeyamah ta ƙara faɗawa jikin Ummi tana kukan, murmushi Ummi tayi ta kalli Mujaheed tace
“Mujaheed mu tafi kasan orphanage house ɗin ko?”.
“Eh Ummi na sani”. Mujaheed ya bata amsa
“Okay let’s go”. tace tana maida Seeyamah gefenta na dama ta rungume ta Mujaheed yayi gaba sukabi bayansa Seeyamah na maƙale jikin Ummi kamar wani zai rabasu.
Har lokacin Habeeb da Aleeyu na tsaye cikin falon su Ummi suka fito, sosai gaban Seeyamah ya faɗi lokacin data ga Habeeb dan batayi tsammanin tare suke ba a tsorace ta ƙara shigewa jikin Ummi shi kuma ya bita da wani mugun kallo wanda yasa ta ƙara tsorata tayi hanzarin sadda kanta ƙasa, har sukaje bakin ƙofar fita daga falon Habeeb bai biyosu ba kuma bashida niyyar biyo ɗin jira yake su Ummi su fita ya yiwa Aleeyu rashin mutunci juyowa Ummi tayi ta kalleshi sai data harareshi kafin cikin faɗa tace
“Tsayuwar me kake a nan?”.
Baice komai ba ya nufi ƙofa, kallon Aleeyu tayi wanda tun ɗazu ya kasa ɗagowa ya haɗa ido da kowa Ummi tace
“Kaima mai tayashi ɗin ba tsayawa zakayi ba tahowa zakayi mu tafi tare muji dalilin dayasa kuka aikatawa baiwar ALLAH wannan abin kai da maigidan naka”. Bata saurari cewar shi ba ta fice Aleeyu yabi bayanta jikinsa duk a sanyaye.
Mujaheed ne mai driving ɗin Habeeb na gefenshi sai cika yake yana batsewa fuskar nan tamkar an aiko masa da saƙon mutuwa ba alamun rahma sam, Mujaheed yana so yayi dariya yana tsoro dan yasan wllhy a yadda yake ɗin nan tsaf zai iya kai masa duka shi yadda ya haɗe ran nema ya bashi dariya.
Ummi, Seeyamah da Aleeyu sune zaune a back seat Seeyamah ta kwantar da kanta kan kafaɗar Ummi jefi jefi tana sakin ajiyar zuciya motar shiru ko tari ba wanda yayi a ciki kowa da saƙe saƙen dayake a ransa da haka har suka ƙarasa orphanage house ɗin su Seeyamah, kallo ɗaya zaka yiwa Seeyamah ka hango zallar farin ciki da murnar datake ciki wanda har ya bayyana kan kyakkyawar fuskarta sai murmushi take saki ba tareda ita kanta tasan tanayi ɗin ba.
Tunda mutanen gidan suka ƙyalla ido sukaga Seeyamah gidan ya ruɗe ya kacame da murna da ƙyar suka yakice wani daga cikin ƴan gidan marayun yayi musu iso zuwa babban office ɗin gidan, gaba ɗayansu suka shiga nan da nan aka sanar da dawowar Seeyamah sai gashi cikin ƙanƙanin lokaci office ɗin ya cika da mutane maza da mata kowa cikeda farin ciki da murnar ganin Seeyamah ta dawo cikin ƙoshin lafiya ba abinda ya sameta.
Bayan ƴan gaishe gaishe da akayi da Ummi da sauran mutanen ɗakin sannan Ummi ta fara rattabo musu yadda al’amarin ya kasance tayi da hausa ta haɗa da turanci saboda yanayin hausar tata.
Tashi tayi ta nufi inda Habeeb yake tsaye tun shigowar su yaƙi zama ma gaba ɗaya sai faman muzurai yake daga tsaye saikace soja, hannunsa ta kamo ta kaishi har gaban shugaban gidan marayun Alhaji Abubakar Imam ta damƙa hannun Habeeb ɗin a na Alhaji Abubakar Imam ɗin tace
“Wannan ɗana ne dana haifa da cikina kuma a yanzu zan damƙa muku shi a hannunku kuna da damar da zaku kai ƙarar shi gaba abi muku haƙƙin ku a kanshi nidai na fita duk hukuncin da kuka yanke daidai ne”. Kowa baki ya buɗe cikin ofishin cikeda mamakin karamci da dattaku irin na matar nan lallai su Ummi basuda yawa a zamanin nan, Habeeb kam wani ƙululun abune ya tokare masa ƙirjinsa ganin abinda Ummi take masa tamkar bata sonsa huci kawai yake fitarwa yana ɗan lumshe ido tsabar yadda ranshi ya ɓaci.
Murmushi Alhaji Abubakar yayi yace
“Naji daɗi sosai Hajiya kuma samun irinku a wannan zamanin da gaskiya tayi ƙaranci sai an tona madalla da samun uwa kamar ki wannan abu da kikayi yasa naji na yafewa yaronki tunda alhmdulillah Seeyamah ta dawo hannunmu cikin ƙoshin lafiya ba abinda ya sameta babban burin mu kenan kulawa da amanar da ALLAH ya bamu mun gode sosai ALLAH ya saka da alkhairi”.
Kai Ummi ta kaɗa tana murmushi tace
“Jazakallah khair nagode sosai nima sai abu na gaba inaso insa hannu zan ɗauki Seeyamah daga gidan nan daga yau nayi alƙawarin bazata ƙara kukan rashin mahaifa ba insha ALLAH kun yarda zaku bani?”.
Kabbara ƴan ɗakin suka ɗauka cikeda farin ciki.
“Masha ALLAH masha ALLAH, ubangiji ya faranta miki kamar yadda kika faranta mana mun gode sosai ALLAH ya ƙara girma da sutura yayiwa zuri’ar ki albarka”. maganganun da suka dinga tashi kenan cikin office ɗin kowa yana yiwa Ummi addu’ar gamawa lafiya.
“Zo nan ƴata”. Ummi tace fuskarta ɗauke da mayalwacin murmushi tareda miƙawa Seeyamah hannu, cikin sassarfa Seeyamah ta taho ta faɗa jikin Ummin tana sakin wani kuka mai taɓa zuciyar mai sauraro cikin shashsheƙar kuka Seeyamah tace
“Nagode Hajiya”.
Ɗagota Ummi tayi ta girgiza mata kai tana murmushi tace
“Daga yau da sunan uwa zaki kirani sunan da kowane ɗa yake kiran mahaifiyarsa dashi ki kirani da Ummi kamar yadda yarana na cikina suke kirana dashi”.
“Nagode UMMI”. Seeyamah tace cikin wani kukan tana ƙara faɗawa jikin Ummi ta matseta tsam itama tana goge ƙwallar data taho mata, duk ɗakin saiya rikice kowa ka gani fuskar shi ɗauke da murmushi na jin daɗi.
Ogah Habeeb kam yana tsaye ba wanda ya ƙara bi ta kanshi, shikenan yanzu yarinyar nan ta koma gidansu da zama? wani irin kallo zata dinga yimasa kenan? shidai angama dashi kawai….