EL-HABEEB HAUSA NOVEL

EL-HABEEB HAUSA NOVEL

Manage please????????

Maryam Ibraheem Aleeyu
Mrs Salees Mu’az ????

EL HABEEB????

©️Oum Hanan.
Writer of DR SAIF.

HASKE WRITER’S ASSOCIATION????
(Home of expert & perfect writer’s).

No 27.

Wata takarda aka bawa Ummi tayi signing bayan sun ƙara tattaunawa tsakanin Ummi da Alhaji Abubakar Imam daga nan aka rakosu har bakin motar su sukayi musu sallama, suna ta ƙara jaddada godiyarsu ga Ummi, rungume juna Seeyamah da aminanta Fadeelah da Khairat sukayi suna kukan rabuwa sosai suke jin rabuwar da zasuyi tana taɓa zuciyar su tun suna yara suke tare a yadda suka samu labari ma kusan rana ɗaya aka kawo su gidan sunyi matuƙar shaƙuwa tare suke yin komai ba abinda yake rabasu gashi yau rana ɗaya za'a rabasu, Ummi ce ta ƙarasa wajen cikin tausaya wa take rarrashin su da faɗin sunada damar zuwa a duk lokacin da suka so ganinta suje gidan ƙofar ta a buɗe take, da rarrashi dai da ban baki tasamu sukayi shiru.

Duk abin nan da ake Habeeb yana kallon su ta cikin glass ɗin motar dan tun fitowar su ya shige mota ba tareda daya kula kowa ba, ta ciki yake kallon kowa ɗaiɗai yana ayyana abubuwa da dama a cikin ranshi. Idanu ya lumshe yana sakin tsaki lokacin dayaga Ummi tana rarrashin su Seeyamah har yanzu abinda ya faru bai daina ɗaure masa kai ba daki daki yake tuno komai daga lokacin dayasa aka ɗauke yarinyar da zaman datayi a gidan shi ƙarƙashin kulawar Aleeyu zuwa yanzu da komai ya bayyana har gashi Ummi ta ɗauki nauyin kulawa da ita a yanzu, numfashi ya sauke mai nauyi yana ƙara jan wani tsakin ganin har lokacin ba wanda yazo ya shiga motar da niyyar tafiya ya rasa me suke tattaunawa tun ɗazu haka, da zaman ya ishe shi saiya zaro wayarshi daga aljihu ya shiga latse latse.
Sai zuwa can sannan su Ummi suka shigo motar bai kula kowa ba kamar yadda ba wanda ya kulashi, sai bayan sun hau kan titi ne ya kula akwai wata ƙaramar mota dake bin bayansu ko tantama bayayi daga gidan marayun ne aka biyo bayan su dan aga mazaunin Seeyamahn a yanzu, ƙarfi da yaji dai Ummi ta ƙara musu yawan ƴan gidan.
Suna yin parking ya fice daga motar ya nufi side ɗinshi Mujaheed yaso yabi bayan shi yayi masa magana Ummi ta dakatar dashi.
Har cikin gidan Ummi tayi musu jagora suka shiga daga nan suka ɗan ƙara tattaunawa tareda ƙara damƙa amanar Seeyamah a hannun Ummi ta ƙara jaddada musu ta karɓa da hannu bibbiyu saidai fatan ALLAH ya tayata ruƙo. Daga nan sukayi mata sallama har cikin compound ɗin inda motar su take Ummi ta rakosu har suka tada motar suka fita daga gidan su Ummi na tsaye itada Mujaheed da Seeyamah da itama tayi musu rakiya.
Sam Ummi bata lura da Aleeyu dake cikin compound ɗin ba sai lokacin da suke shirin komawa cikin gidan, yana tsaye kusa da wata fulawa kanshi a sunkuye tunanin shi ɗaya haɗuwa da Habeeb shikenan yasan ƙarshen aikinsa yazo gashi da shine yake taimakawa iyayenshi da ƴan uwansa saboda shi kansa ya sani Habeeb yana masa biya mai kyau kuɗin dayake bashi yafi na aikinsa Habeeb mai yawan alkhairi ne hakan yasa yake jin daɗin aiki dashi kuma yake samun abinda zai taimakawa iyayenshi a wadace, yayi karatu sosai inda har yayi degree ɗinshi na
“Mujaheed kira min yaron can”. Ummi tace tana kallon Mujaheed, amsawa yayi sannan ya nufi inda Aleeyu yake tsaye har ya ƙarasa bai sani ba sai daya dafa kafaɗarshi sannan ya zabura ya kalli wanda ya taɓa shi ɗin yaga Mujaheed ne tsaye duk sai yaji kunya ta kamashi dukansu kunyar su yake ji a halin yanzu.
“Barka dai yallaɓai”. yayi maganar a rarrabe yana ƙara yin ƙasa da kanshi.
“Barka dai, muje Ummi tana son ganinka”. Mujaheed yace yana yin gaba ba tare daya tsaya jin amsar shiba, shikenan ta faru ta ƙare Aleeyu ya ayyana cikin ranshi yana bin bayan Mujaheed.
Rissinawa yayi yana gaida Ummi bayan ƙarasawar su amsawa Ummi tayi ba yabo ba fallasa tana ƙare masa kallo a girme ma zai girmewa Habeeb amma saboda yanada kuɗi ya zama shine babban sai abinda yace masa yake aiwatarwa, sai data gyara tsayuwar ta sannan tace
“Yanzu yaro abinda kayi ka aikata daidai kenan? meyasa ka biyewa sakarcin Abbuna kuka aikata wannan mummunan aikin? a shekarun ka kaine ya kamata ace ka saitashi a hanya idan kaga yana shirin yin ba daidai ba
‘Kutt bala’i Gashuan ne zai yarda Aleeyu ya shiga sha’anin shi har yayi masa gyara? ai koni sai nayi da gaske sai anci uban juna kafin a daidaita dama ni kaɗai ne nake ɗan iyawa dashi’. Mujaheed ne yayi maganar cikin zuciyarshi yana kaɗa kai wani murmushi na suɓuce masa kan fuskarsa cigaba Ummi tayi da faɗin
“Kun taɓa tunanin halin da kuka jefata itada ƴan uwanta wani irin tashin hankali suka shiga kun taɓa tunanin wannan? kai kawai Aleeyu yake jijjigawa yana ƙara yin dana sani kan abinda ya aikata.
“Ayi haƙuri Hajiya nayi nasan nayi ba daidai ba ayi min afwah insha ALLAH hakan bazata ƙara faruwa ba”. Wani nannauyan numfashi Ummi ta sauke kafin tace
“Shikenan ya wuce ALLAH ya yafe mana gaba ɗaya a kiyaye dan ALLAH a dinga kuma auna abu a mizanin hankali kafin a aiwatar dashi”.
“Insha ALLAH Hajiya nagode sosai ALLAH ya saka da alkhairi ya ƙara girma”.
Duk da Ameen suka amsa Ummi tace
“Bayan wannan aikin da kake a ƙarƙashin Abbuna akwai wani aiki daban dakake yine?”. Kai Aleeyu ya girgiza yace
“Bana yin komai Hajiya kasancewar ogah mai yawan alkhairi ne koyaushe cikin miƙawa yake hakan yasa banyi yunƙurin neman wani aikin ba tunda abinda yake biyana dashi yana isata harkokin rayuwarta”.
“To daga yau zaka bar aiki a ƙarƙashin shi…..ido Aleeyu ya runtse cikin faɗuwar gaba dama yasan sai anyi haka
“Meye matakin karatun ka?”. yaji Ummi ta tambaye shi, idanunsa ya buɗe yace
“Nayi har degree biyu duk akan business na nemi aiki ban samuba hakan yasa lokacin dana samu labarin mai kamfanin H.I.A GASHUA yana neman ma’aikata wanda zasu zama bodyguard ɗinshi nazo kuma cikin sa’a nasamu aikin”.
Kai Ummi ta jinjina tace
“Shikenan zamuyi magana da Alhaji Sulaiman kawun yaran nan ya saka cikin harkar kasuwancin amma yanzu dai kaje gida ka ƙyale Abbuna”.
Sosai Aleeyu ya shiga zuba godiya a wajen Ummi dayi mata addu’a, har suka suka bar wajen itada Seeyamah, Mujaheed ya dafa kafaɗarshi yana faɗin
“Ya isa haka Malam Aleeyu yanzu dai muje kabawa Boss ɗin naka haƙuri yau an haɗa masa zafi dayawa”.
“Anya yallaɓai zan iya tunkarar ogah a yanzu kuwa?”. cewar Aleeyu.
“Ba damuwa muje gara ayita a ƙare ai yadda kasan kuturu haka yake wajen zuciya shegen”. Dariya ce ta kufcewa Aleeyu shima Mujaheed ɗin dariyar yayi yana nufar part ɗin Habeeb Aleeyu ya mara masa baya.
Kamar koyaushe falon banda sanyi ba abinda yake fitarwa ya ƙure A.C sai bankawa kanshi sanyi yake, can suka hangoshi kan kujera ya ɗora kafa ɗaya kan ɗaya sai girgizasu yake sarai yaji an shigo ɗin amma yaƙi ɗagowa yaga waye duk da dai yasan bazai wuce Mujaheed ba.
Ƙarasawa inda yake sukayi Mujaheed ya zauna kusa dashi Aleeyu kuma gefe yasamu ya zauna kan tattausan carpet ɗin dake malale a wajen.
“Ranka ya daɗe ga Aleeyu nan na kawo zai baka haƙuri bisa sakaci dayayi na amanar daka damƙa masa har Mujaheed yayi nasarar shiga gidan yaga abinda ake ɓoyewa a ciki”. Mujaheed yayi maganar yana ƙunshe dariyar dake cinsa.
“I’m so sorry Boss banyi hakan dan na ɓata maka ba forgive me dan ALLAH”. Aleeyu yace yana haɗe hannayen shi guri ɗaya alamun roƙo.
“Get out from my room”. yace yana wani lumshe ido na ɓacin rai.
“Dan ALLAH ka…….”I said get out”. Habeeb ya katse Aleeyu cikin tsawa wanda dole tasa Aleeyun yaja bakinshi ya tsuke.
“Kaga Aleeyu tashi kaje abinka rabu dashi ni banga ma laifin dakayi ba da har kake ta wani binshi kana bashi haƙuri ya daɗe bai haƙuran ba dan ubanshi tashi kaje”. tashi Aleeyu yayi ya fita daga falon bayan ya yiwa Mujaheed sallama yana ta mamakin yadda Mujaheed ɗin yake zagin Habeeb ɗin kai tsaye batare da wani shayin komai ba.
Baki Mujaheed ya buɗe zaiyi magana a fusace Habeeb yace
“Ka sake kai min magana ubanka zanci wllhy ɗan iska mara mutunci”. ya ƙarasa maganar yana komawa bayan kujerar yayi relaxing yana cigaba da kaɗa ƙafa sai huci yake yana cije baki, baki Mujaheed ya hangame yana kallonshi kafin yayi murmushi yace
“Duk naji na kuma gode da zagin da kayi min amma ka sani Gashua banyi hakan dan in ɓata maka ba nayi hakane dan in ceto ka daga halakar dakake shirin faɗawa a ciki I’m sorry to say kai…….”Dan zaka faɗawa Ummi? meyasa ka sakota cikin maganar? meyasa bazaka sameni muyi magana dakai ba kasa mahaifiyata tana fushi dani why Mujaheed?”. duk sai Mujaheed ɗin yaji jikinsa yayi sanyi amma har a lokacin baiji wai abinda yayi ba daidai bane yanzu ba gashi ta sanadin hakan ba Ummi ɗauki yarinyar, murmushi ya ɗan saki kafin yace
“Gashua bakada fahimtar da zamu zauna muyi magana dakai ta fahimta a tsakanina dakai kai ɗin wani irin mutum ne mai wuyar sha’ani wanda ake rasa gane hagunshi da damanshi dole tasa na samu Ummi da maganar saboda kai ɗin ba zaka fahimce ni ba…..”Kazo ka sameni dan muyi magana kaga naƙi fahimtar ka? maganar banza kawai kake”. ya katse Mujaheed a fusace, dariya Mujaheed yayi yace
“Haba ɗan balarabe yau nafara saninka? kokuma yau nafara zama dakai? Ummi ce kawai zance zata fini sanin halayyar ka saboda ita takawo ka duniyar close the chapter now tambaya ɗaya gareni yanzu meyasa ka ɗauke Seeyamah wane laifi tayi maka? a ina ma ka santa da har tayi maka laifin da zaka yanke mata irin wannan hukuncin? Please answer me”.
Wani banzan kallo Habeeb ya jefa masa yace
“Zaka iya shaƙeni sai in faɗa maka mara mutunci”. sosai Mujaheed ya ƙyalƙyale da dariya yace
“Kaji ba in ance maka bauɗaɗɗen mutum kace ba haka ba any way nidai nayi abinda ya dace kar ALLAH yasa ka faɗa min abinda ya haɗaku muna zaune a shararren waje zamuji koma menene I’m sorry fa da marukan da Ummi ta daddalla maka ta sanadina ga fuskar nan har yanzu bata washe ba wllhy ta ƙara ja sos…..hannu Habeeb ya dunƙule yana miƙewa tsaye da niyyar kaiwa Mujaheed dukan da saiya kusa sumar dashi ganin haka yasa Mujaheed ɗin yayi hanzarin tashi yabar falon da gudu yana dariya.
Tsaye Habeeb yayi yabi bayan Mujaheed ɗin da kallo, Mujaheed yana masa abinda yaga dama ba wanda yake faɗa masa magana son ranshi irin Mujaheed saikuma Muhseen daya biyo bayanshi.
Juyawa yayi ya shiga bedroom ɗinshi ya cire kayan jikinsa ya shiga bathroom, yana tsaye saitin shower ruwa na tsiyaya a jikinshi ya zama dole yazo yafara bincike kan yaran nan dayake tunanin su ɗin triplets ne….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38Next page

Leave a Reply

Back to top button