EL-HABEEB HAUSA NOVEL

Maryam Ibraheem Aleeyu????
EL–HABEEB????
©️Oum Hanan.
HASKE WRITER’S ASSOCIATION????
(Home of expert & perfect writer’s)
No 3.
Yasani komai daren dad’ewa zai nemesu dan haka kullum cikin kwantarwa da mahaifiyarsu hankali yake saboda yadda ta d’aga hankalinta sosai gani take tamkar shikenan fa d’anta ya tafi kenan bazai k’ara waiwayar gida ba daga k’arshe tasawa zuciyarta dangana ta cigaba da binshi da addu’ar ALLAH ya kare mata shi a ko ina yake a matsayinsu na iyaye wanda ko yaya suka furta kalma mara dad’i a kanshi saita bishi ta nakasta rayuwar shi bai kamata suyiwa yaronsu mugun baki ba ya k’ara lalacewa.
Sosai akasha shagalin bikin Ibraheem Ahmad Gashua da Afeefah Habeeb Al-Hussain naira tayi kuka kasancewar harkar ta masu arzik'i ce dan shima mahaifin Afeefah mai kud'i ne sosai.
Bayan kwanakin da aka d’iba ana shan shagalin biki amarya ta tare a gidanta na wani abokin kasuwancin shi balarabe daya bashi aro kafin ya mallaki nashi plat house ne wanda aka b’ata lokaci wajen tsarashi kuma ya tsarun an k’ayatashi sosai. Nan fa aka shiga cin amarci kowa yana k’ok’arin farantawa d’an uwanshi rai da nuna irin tsantsar soyayyar da sukewa junansu Afeefah na shan kulawa da tarairaya tsabarsu a wajen Ibraheem duk abinda yasan zai faranta mata shiyake yi haka itama a nata b’angaren.
Shekarar su d’aya da aure ALLAH ya bata ciki kuma har lokacin bai tab’a tunanin waiwayar gida ba kuma ko sau d’aya bai tab’a gwada koda kiran waya ba kawai matarshi yasa a gaba musamman data samu cikin nan sai kulawar ta ninka ta baya fiye da tsammanin mai karatu har zuwa lokacin da ALLAH ya sauketa lafiya ya azurtasu da samun k’aruwar d’a namiji wanda gaba d’aya zubinshi da kamannin shi na asalin jinin larabawan ne babu ta inda ya d’auko mahaifinshi komai na mahaifiyarshi ne. Fad’ar irin farin ciki da murnar da wannan ahali sukayi ma b’ata baki ne amma tabbas sunyi matuk’ar farin cikin zuwan jaririn duniya musamman Alhaji Ibraheem Gashua daya d’auki son duniya ya aza kan jaririn nan da ranar suna ta zagayo yaro yaci sunan mahaifin Afeefah wato HABEEB ba k’aramin dad’i Afeefah taji ba a lokacin saboda karar dayayi mata yasawa first born son d’insu sunan babanta ta rungume shi tana fad’a masa wasu kalmomi masu tsada na soyayya da nuna jin dad’i da godiya duk da larabci take maganar wanda yakejin yaren sosai a yanzu saboda zama da Afeefah, rungumeta ya k’ara yi sosai a jikinshi yana murmushi na jin dad’in ya faranta mata.
Ta b’angaren Habeeb Al-Hussain ma wanda suke kira da Abi yaji dad’i k’warai da gaske na samun takwara dayayi tuni yaji yaron ya k’ara kwanta masa cikin ranshi tuni ya shiga yimasa kyaututtuka na alfarma abinka ga wad’anda sukaci suka tada kai da naira. Ba k’aramar dukiya aka salwantar ba wajen sunan yaron ga kyaututtuka dayake ta faman sha tako ina daga b’angaren kakannin shi na wajen uwa kowa son yaron yake da nuna masa k’auna.
Afeefah ta cigaba da rainon yaronta cikin tsananin kulawa da taka tsantsan kan duk abinda zai cutar dashi ya taso cikin gata kowa ji dashi yake. Yarone daya taso da mugun k’ok’ari fikrah, zalak’a, da tarin baiwa suka fito k’uru k’uru tun yana k’ananun shekarunshi abu d’aya zaka fad’a masa ya d’aukeshi a kanshi koda da wasa ka fad’a kuwa musamman dayake samun k’warin gwiwa daga mahaifanshi dasu Abi.
Saida Habeeb ya shekara biyar sannan Afeefah wadda yake kira da Ummi ta k’ara wata haihuwar wannan karon mace tasamu wadda suka rad’a mata suna Mashhoodah, sai a lokacin Ummi ta fara tuntub’ar Ibraheem Gashua wanda Habeeb ke kiranshi da Abbu a yanzu batun zuwa gida da nuna masa lallai ya kamata ace ya waiwayi gida haka yaje yaga halin da suke ciki ya kuma gabatar dasu a matsayinsu na iyalinshi tunda ga zuri’a sun fara tarawa, mirsisi Abbu yayi yace sam ba yanzu zai komaba idan ya tashi tafiya ma saidai kawai yace ta shirya su tafi amma dai ba yanzu ba ya fad’i hakan ne saboda tsoron komawa dayake baisan da irin kalamin dazai tunkari iyayen nashi ba idan ya koma yasani shi babban mai laifi ne a wajensu ya bijire musu yayi fatali da maganar da suka gindaya masa saboda soyayyar Afeefah data rufe masa ido yana tsoron komawa saboda baisan yadda zasu karb’eshi ba amma hak’ik’a cikin shekara d’aya data wuce zuwa yanzu yana yawan tunanin gida yakan yi mafarkinsu sosai tabbas yana son komawa k’asar sa ta haihuwa. Wannan abinda ya fad’a d’in shine harya haifar musu y’ar hatsaniya tsakanin shi da Ummi wanda wannan shine karo na farko a rayuwar aurensu dasuka samu matsala dan sosai yake biye mata sai abinda takeso akeyi a ganinta lokaci yayi daya dace ace taga mahaifarshi, iyayenshi y’an uwanshi dama tushenshi gaba d’aya.
Itama saitayi fushin bata k’ara tayar masa da maganar zuwa 9ja ba shima bai k’ara yimata maganar ba ta zubawa dai sarautar ALLAH ido taga iya gudun ruwanshi.
10yrs After.
Habeeb yanada shekaru goma a duniya yayin da Mashhoodah take da biyar ALLAH ya d’auki ran Abi sakamakon ciwon ciki daya turnuk’e shi lokaci d’aya rai yayi halinshi mutuwar data jijjiga familyn su da sauran abokan arzik’i musamman ma iyalinshi da sukafi kowa jinta su Ummi sunyi kuka kamar ba gobe mutuwar uba wani babban gib’i ne a rayuwar mutum wanda duk wani gata da za’ayiwa mutum shi bazaikai wanda mahaifi zaiyiwa d’anshi ba daga k’arshe dai suka bishi da addu’ar samun rahmar ubangiji da dacewa.
ALLAH kaji k’anmu badan halinmu ba kayi mana rahma badan aikinmu ba dan alfarma da martabar sayyadil wujuud (S.W.A.)????????
★…★…★
Tun bayan rasuwar Abi Abbu yafara ganin y’an canje canje a rayuwar shi especially ta b’angaren kasuwancin shi yaja baya sosai tamkar Abi ne ya tafi da rabin arzik’in nashi ga ciwon hawan jini daya kamu dashi saboda yadda ya saka tunanin gida da iyayenshi a cikin ranshi ga wasu mafarkai dayake game da Malam Ahmad wanda ya kasa gane kansu hakan ya k’ara haddasawa jikin nashi rikicewa sosai k’warai da gaske yakeda buk’atar yasa ahalinshi a idonshi, a lokacin Ummi ta k’ara bijiro masa da maganar zuwa 9ja duk da alk’awarin data d’auka a baya cewar bazata k’ara yimasa maganar zuwa Nigeria ba amma yanayin yadda taga mijin nata tasan damuwarshi dai bata wuce ta gida. Sam bai mata musu ba a lokacin dan haka suka shirya sukaje suka samu mahaifiyar Ummi da maganar a lokacin shekara d’aya kenan da rasuwar Abi, sunyi zaton zasusha fama da ita amma ga mamakin su kai tsaye saita amince dama tuni taga dacewar hakan.
Nan da nan suka fara shirin tafiya Nigeria Abbu farin cikinshi ya kasa b’oyuwa ta gefe d’aya kuma cike yake da tararrabin irin amsar da zasuyi masa.
Cikin y’an kwanaki ya kammala musu duk wasu shirye shiryen tafiya suka d’aga zuwa 9ja k’asarshi ta haihuwa bayan sama da shekaru goma daya d’auka baya nan.
Abinda ya tarar ne a ranar da suka iso yayi matuk’ar girgizashi wato labarin rasuwar Malam Ahmad daya samu shekara d’aya data wuce lokaci d’aya kenan data Abi yayi kuka tamkar ranshi zaibar jikinshi, dana sani da d’imbin nadama suka shigeshi ALLAH bai k’addara saduwarsu ba bare harya nemi gafararshi hak’ik’a rasuwar mahaifin nashi ta dakeshi ya zube gaban Hajiya Inna yana kuka da neman yafiyarta tsakanin d’a da uwa sai ALLAH saitaji duk wani fushi datake dashi na tsahon shekarun ta nemesu ta rasa ta rungume d’anta wani irin dad’i na ratsa zuciyarta, hakama sauran y’an uwan nashi da duk sukazo gidan suka rungume shi cikin farin cikin dawowarshi gida, anan Hajiyan ke sanar dashi ai kafin rasuwar mahaifin nasu yace ya yafe masa duniya da lahira wannan kalma ba k’aramin dad’i tayiwa Abbu ba dama damuwarshi d’aya mahaifinshi daya tafi da tabon b’acin ranshi.
Bayan komai ya natsa ne ya gabatar musu da Ummi da yaransu biyu da ALLAH ya basu hannu bibbiyu suka amshesu basu nuna musu wani abu ba Hajiya ta rungume y’an jikokinta tanajin dad’i sudai kallonsu kawai suke cikin rarraba idon ganin wasu bak’in fuska da basu sansu ba gasu kuma bak’ake ba yadda suka saba ganin farar fata ba.
Da k’yar aka gaggaisa da Ummi saboda ba hausa danma Abbu yakan yimata jefi jefi hakan yasa tasan wasu y’an abubuwan kamar gaisuwa da sauran maganganu marasa tsayi.
Goggo Fatu d’aya daga cikin k’annen shi mata guda hud’u ita kad’ai ce Ummi ta kula tun zuwansu tana binta da wani irin kallo na tsana dan a ganinta Ummin itace silar dayasa d’an uwansu yabarsu na tsahon shekaru batare daya k’ara waiwayar suba dan haka taji da Ummin da yaranta duk ta tsanesu bata k’aunar su.
Sauran kuwa ba ruwansu sun sakarwa Ummi fuska sosai Hajiya ma ta jata a jikinta sosai hakan ba k’aramin dad’i yayiwa Abbu ba nan da nan yaji duk wasu sauran y’an ciwace ciwace sun tafi dama tunanin gida ne da kuma zullumin yadda dangin nashi zasu amshe shi alhmdulillah kuma dayake masu ilmi ne da kuma aiki dashi yasa basu nuna masa komaiba sun d’auki hakan a matsayin k’addarar shi.
Bayan sun huta na y’an kwanaki suka shiga yawon zaga dangi na kusa dana nesa yana gabatar musu da iyalinshi kuma ko ina sukaje ana nunawa Ummi da y’ay’anta soyayya tuni itama taji dangin mijin nata sun shiga ranta dan sunsan abinda suke k’warai da gaske ga karamchi da girmama d’an adam.