EL-HABEEB HAUSA NOVEL

EL-HABEEB HAUSA NOVEL

★__★
Matsananciyar yunwa ke rarakar cikinsa dan rabon da wani abu mai nauyi ya shiga cikinsa harya manta saidai yaita bankawa cikin shi coffee saikuma fruits dayake ma’abocinsu ne, yau kam yaji yana sha’awar yasawa cikin shi ɗan abu mai nauyi gashi har wajen 9:25pm baiji kiran Ummi na yazo yayi dinner ba da alamu fa har yanzu Ummi bata sauka ba, shikam yaga ta kanshi wani lokacin idan Ummi tayi fushi takan daɗe bata sauka ba.
Tashi yayi daga kishingiɗen dayake ya ɗauki wayarshi ya fita daga side ɗinshi ya nufi nasu Ummi, a hankali ya murɗa handle ɗin ƙofar falon ya shiga bakinshi ɗauke da sallama duk da dai ba fitar ta akaji ba motsin da bakinshi yayi ne ya tabbatar musu da yayi sallamar dama Ummi da Neehlah sun saba gani, sallamar kawai Ummi ta amsa ta kawar da kanta daga kallonshi tun daga haka ya ƙara shan jinin jikinsa sai ya cigaba da takawa cikin takun nan nashi mai cikeda izza da mazantaka wanda ya zame masa jinin jikinshi.
Tun shigowar shi Neehlah tayi tsit kamar ruwa ya cinye ta duk wannan surutun datake tai ɗif da ita ta shiga zare ido, ta ɓangaren Seeyamah ma haka nata harya zarta na Neehlah dan ita banda faɗuwa da gabanta yake har wani rawa rawa jikinta ya ɗauka yana ƙara kusantowa gabanta na ƙara faɗuwa wani mugun kwarjini yayi mata sai taji tamkar ya cika falon shi kaɗai ɗinshi, ta ƙasan ido ta ɗan saci kallon shi kayan shan iska ne a jikinshi marasa nauyi na kamfanin Adidas jan wando da farar riga wadda akayi mata ado da jan layi layi irin wandon gashi dai kayan bana kwalliya ko gayu bane amma sun bala’in haskashi dama ba’a maganar ƙamshi dan yana shigowa falon ya ɗume da ƙamshin sa wanda zuwa yanzu ya riga ya rasa zauna a ƙwaƙwalwar Seeyamah duk inda taji shi saita ganeshi.
Kusa da Ummi ya ƙarasa ya zauna ƙasan ƙafafunta ya buɗe baki da niyyar yin magana kawai yaga Ummi ta tashi tabar wajen ta nufi upstairs…….

Saura two pages book one ya ƙare karku manta book two isn’t free ALLAH ya bada abinda za’ayi patronizing ɗina 300 only ALLAH ya bada ikon siya Amin.
Nagode

Maryam Ibraheem Aleeyu
Mrs Salees Mu’az ????

EL HABEEB????

©️Oum Hanan.
Writer of DR SAIF

HASKE WRITER’S ASSOCIATION????
(Home of expert & perfect writer’s).

No 29.

 Da kallo ya bita lokacin da take hayewa upstairs ɗin zuciyar shi na masa wani irin zafi wai Ummin shi ce ke masa haka yau? duk akan wannan yarinyar, Neehlah da Seeyamah ma da kallon suka bita Seeyamah tasan dalilin fushin na Ummi yayin da Neehlah kuma batasan komai akai ba tayi dai mamaki ƙwarai tunda bata taɓa ganin abu makamancin hakan ya shiga tsakanin Ummi da Yah Habeeb ɗin ba kullum rarrashi da lallaɓawa ne tsakanin su to yau kuma meye ya faru?

Ido ya lumshe yana sauke numfashi haɗi da cije baki saboda yadda ranshi ya ɓaci a hankali ya buɗe idanunsa da suka ɗan fara canza launi ya saukesu kansu Seeyamah wani ɓacin ran ne ya ƙara ziyartar sa ganin duk a kanta ne Ummi tayi masa haka gashi kuma ta kunyata shi a gabansu wani mugun kallo daya antaya musu yasa ba shiri Neehlah ta kama hannun Seeyamah suma suka nufi upstairs ɗin jiki na rawa duk da ita Seeyamahn batama ga irin kallon da yake musu ba, da kallo ya bisu har suka ƙarasa hayewa tsaki yaja da ƙarfi ya tashi a fusace ya fita daga falon. Da sauri yake tafiya zuwa part ɗinshi yana shiga ya maida ƙofar da ƙarfi ya rufe ta bada wani sautin ƙara bammm, kan kujera ya zube tareda dafe goshinshi haɗi da lumshe idanunshi yana jin duk ba daɗi basu saba irin haka da Umminshi ba Ummi bata fushi dashi saboda yana ƙoƙarin ganin ya kiyaye ɓacin ranta duk abinda yasan zai ɓata mata bayayi baya ƙaunar fushinta ko kaɗan.
A hankali ya buɗe ido yana furzar da zazzafar iska daga bakinshi ya zama dole yaje yabawa Ummi haƙuri yanzu bazai iya haƙurin zuwa safiya bama, cikin hanzari ya miƙe tsaye ya ƙara ficewa daga falon ya ƙara nufar part ɗinsu Ummi, falon ba kowa kamar yadda ya fita ya barshi yana shiga kai tsaye ya nufi upstairs zuwa bedroom ɗin Ummi. A bakin ƙofar ya tsaya yayi knocking daga ciki Ummi ta amsa cewar a shigo handle ɗin ƙofar ya kama ya buɗe ya shiga tareda sallama tana zaune kan sofa da wani littafi a hannunta na addu’oe tana dubawa gabanta kawai ya zube ya dafa gwiwoyinta da duka hannayenshi cikin marairaicewa ya fara mata magana cikin harshen larabci yana haɗawa da turanci banza tayi masa kamar bata ganshi ba hakan yasa ya ƙara marairaice murya kamar zaiyi kuka.
Littafin hannunta ta ajiye ta ƙura masa ido duk saiya bata tausayi basu saba irin wannan a tsakaninsu ba ita kanta tasan yaron nata yana matuƙar gudun ɓacin ranta.
“Zauna sosai muyi magana”. tace har lokacin bata saki fuskarta ba, zamewa yayi yai zaman dirshan a gabanta tareda kamo hannayenta ya riƙe su gam cikin nashi hannun yana kallon ta, dariya yabata sosai ganin yadda yayi ɗin kamar irin ƙananan yaran nan duk yabi ya wani shasshake mata gimtse dariyar ta tayi ta ƙara haɗe fuska dan a yau take so taji dalilin shi na ɓoye Seeyamah baiwar ALLAH yarinyar data taso gidan marayu bataji ba bata ganiba.
“Bakason ɓacin raina ko?”. da sauri ya gyaɗa mata kai
“Kanaso kuma in sauka daga fushin danake dakai?”. Nan ma kai ya jijjiga mata alamun tabbatarwa, kai ta jinjina itama tana gyara zamanta tare da faɗin
“Dalilin ka na ɓoye Seeyamah nakeso inji yanzun nan”. ido ya ɗan zaro dan baiyi zaton abinda zata faɗa kenan ba.
“Ummi please abar maganar nan k…..”Shut up”. Ummi ta katse shi cikin tsawa, shiru yayi ya sunkuyar da kanshi ƙasa cikin faɗa Ummi tace
“Tashi kabani waje tunda banida matsayin da zaka faɗa min”.
“I’m sorry Ummi please zan faɗa miki”.
“Ina jinka”. cewar Ummi tana kallonshi.
Bashida yadda zaiyi UWA tafi ƙarfin wasa dole ya sanar da ita abinda bata saniba, daki daki a tsanake ya shiga bata labari tun farkon haɗuwarsu da Heedayah akan layi da haɗuwa da yayi da Jawaheer again kuma yaga Seeyamah a gidan marayu da irin zargin da yayi na itace take sauya kamanni take bibiyarshi duk inda yaje hakan yasa ya ɗauke ta da nufin saita faɗa masa inda ta sanshi da dalilin dayasa take binshi sannan zai saketa har zuwa lokacin da Mujaheed yabi diddigin inda take yazo ya faɗa mata.
Sosai Ummi ta nutsu tana jin wannan labarin mai cikeda al’ajabi idan ta fahimta yaran su uku ne kenan kuma duk kamar su ɗaya kuma kowacce da inda take tsai tayi da ranta tana auna kan labarin lallai ko waye dole ya rikice ko ita kanta abin ya matuƙar ɗaure mata kai da shiga ruɗani.
Nannauyan numfashi ta sauke kafin tace
“A ina ita yarinyar daka gani a gidan Hajiyan take?”. A taƙaice yabata labarin Heedayah kamar yadda Hajiya ta sanar dashi yaje kuma yaga har gidan ranar da Hajiya tasa ya maida ita gida.
Kai kawai Ummi take jinjinawa cikin zuciyarta tana ayyana wasu abubuwa masu tarin yawa idan har hasashen ta zai zama gaskiya to yaran nan ƴan uku ne maybe wani abun ya tarwatsa su kuma ba wadda tasan da zaman ɗaya a cikinsu danƙari akwai cakwakiya cikin al’amarin nan warware shi sai ALLAH.
“Ita waccan yarinyar da kake gani a shopping mall ɗin kasan inane gidansu?”.
“No Ummi har yanzu bansan inane gidansu ba shine nakeso inyi bincike dan gano gaskiyar al’amarin”.
Kai Ummi ta jinjina tana faɗin
“Hakan yayi tun farko ma da abinda kayi kenan ka tsaya shirme da sakarci tabbas lamarin yana buƙatar bincike kuma na baka goyon baya hundred percent dan ta hakane za’a gano iyayen su na asali jikina yana bani duk inda yaran nan suka fito daga babban ahali suke sanin abinda ya tarwatsa su kuma sai ALLAH zanfi kowa farin ciki idan aka gano real parents ɗinsu ALLAH ya bada sa’a”.
Cikin farin ciki yake kallon Ummin yana ƙara jin wani ƙwarin gwiwa na shigarshi ada bai bawa abin muhimmanci ba kamar yadda yake jinshi yanzu cikin ranshi saboda mahaifiyarsa data shigo cikin lamarin.
“Thank you so much Ummi”. yace murmushi na suɓucewa kan fuskarsa, itama murmushin ta saki tana faɗin
“Karka damu nidai fatana karka shiga cikin lokacin aikinka abi komai a sannu har zuwa lokacin da ALLAH zai bayyana mana abinda ke ɓoye kar ayi gaggawa idan kana buƙatar wata shawara ka sameni”.
“Insha ALLAH Ummi thank you very much”.
Kanshi kawai ta shafa tana murmushi shikuma yayi kissing hannunta.
“Good night Ummi”. ya faɗa yana miƙewa tsaye da niyyar barin bedroom ɗin Ummi ta dakatar dashi da faɗin
“Ya kamata gobe idan ALLAH ya kaimu kuje da Seeyamah a samar mata kayan sawa”. tuni yanayin fuskarsa ya canza ya wani haɗe rai yace
“Ummi driver fa?”.
“Ɗazu yake sanar dani anyi masa waya daga ƙauyensu mahaifiyarsa ba lafiya zaije ganota”. Ummi ta amsa masa tana tsareshi da ido, shiru kawai yayi yana murza fatar goshinsa daya tattareta shine ma zai kaita siyan kayan sai kace wani ɗan aikinta?
“Bakaji abinda nace bane wai Abbuna?”. Ummi ta katse masa tunanin dayake, sai daya zura hannu ɗaya a aljihu ɗayan kuma ya shiga shafa sumar kanshi kafin yace
“Naji Ummi amma kawai sai a ganni nakai yara siyayya please Ummi suje kawai da Neehlah ko nawane zan bayar ta ɗauki duk abinda takeso”. ya ƙarasa maganar yana marairaice murya kar ma Ummin tace zata takura masa shifa gani yake hakan kamar zubar da girma da ajinshi ne kawai a ganshi ya raka yara siyayya.
“Kai ɗin kai zaka kaisu, meye a ciki dan ka rakasu? ba yayansu bane?”. zaiyi magana Ummi ta dakatar dashi ta hanyar ɗaga masa hannu dolenshi ya amsa mata da to sannan ya ƙara yimata sallama ya fice daga bedroom ɗin ta bishi da kallo tana girgiza kai, gani yake wani uban aiki ne kaisu siyayyar da zaiyi.
Direct kitchen ya wuce bayan komawa part ɗinshi ya haɗa coffee yadawo falo ya zauna kan 1sitter ya miƙe ƙafafunshi kan center table ya fara sha duk da yadda yake fitar da turirin zafi kuwa ya riga ya saba sha da zafi haka. Bayan yagama sha ma sai daya ɗan jima zaune anan sannan ya shiga bedroom yayi wanka ya ɗaura alwalah ya fito ya shirya cikin pyjamas dark purple masu kauri ya fesa turare sannan ya tada sallah, raka’a biyu yayi, yayi addu’oe ya shafa sannan ya kwanta bayan ya karanto addu’ar kwanciya barci ya shafe jikinsa.
Asubah ta gari Mr Habeeb Gashua ????.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38Next page

Leave a Reply

Back to top button