EL-HABEEB HAUSA NOVEL

★★★_★★★
Duk bakin bed suka nema suka zauna bayan hawowar su upstairs Neehlah tace
“Sisi kinga Yah Habeeb ɗin ko?”. murmushi kawai Seeyamah tayi ta gyaɗa mata kai batare datace komai ba dan har yanzu bata wani gama dawowa daidai ba gabanta kuma bai daina faɗuwa ba, baki Neehlah ta taɓe tace
“Kinga irin halin nashi ko? yanzu haka wani laifin ya yiwa Ummi shine zai huce a kanmu inajin da bamu gudo ba da duka zai kai mana”. ƴar dariya Seeyamah ta ƙaƙalo nan ɗinma dai bata tofa tata ba to itakam me zatace a kansa? kuma alƙawari ta ɗaukarwa kanta insha ALLAHU ba zata dinga shiga sabgar shiba dan ita harga ALLAH kallon mara mutunci take masa.
Ita ta fara shiga bathroom tayi wanka kafin ta fito har Neehlah ta fito mata da night dress doguwar riga har ƙasa orange color da baƙar hula tana fitowa ta shirya itakuma Neehlah ta shiga bathroom ɗin dan yin wankan.
Ko bayan da sukayi addu’a suka kwanta Neehlah tana ta jan Seeyamah da hira taƙi biye mata sosai ita haka ALLAH yayi ta magana bata dameta ba da haka har barci ya ɗauke su.
Bayan sallahr asubah Neehlah barci ta koma Seeyamah kam kasa komawa tayi ta cigaba da zama bisa dardumar tana karanto azkar can ƙasan zuciyar ta tana ƙara godewa ubangiji kan wannan ni’imar dayayi mata bayan tsahon shekaru sha takwas data ɗauka zaune a gidan marayu yau rana ɗaya ubangiji ya turo baiwar shi dan ta share mata hawayenta yau gata itama an maida ita ƴa kamar kowane ƴaƴa za’a bata dukkan gata da kulawa tana fata da burin ace wata rana zata zauna da iyayenta haka batasan wani irin kalar farin ciki da murna zatayi ba a duk ranar data haɗu da iyayenta saidai abinda bata saniba a raye suke? kokuwa a mace? wani abu ne yasa suka banzatar da ita suka wofintar da rayuwar ta haka? ba zato taji hawaye na bin kumatunta ranta na wani irin suya batada mutum ɗaya da zata iya nunawa a faɗin duniyar nan wanda zata bugi ƙirji ta nuna shi tace wannan ɗan uwanta ne shi kanshi wanda ya tsinto ta ya kawota gidan marayun ance tunda ya kawota bai ƙara dawowa ba ba’a ƙara ganinshi ba, hijabin ta tasa ta share hawayen fuskar ta.
Tun batasan kanta ba take ji a jikinta kamar wata rana iyayenta zasu nemeta kamar zatayi rayuwa da iyayenta bayan rayuwar gidan marayu datayi da farko koma dai meye tana roƙon ubangiji ya zaɓa mata mafi alkhairi idan da rabon zasu haɗu ɗin ALLAH ya haɗa fuskokinsu da alkhairi. Ta daɗe zaune a wajen cikin tunani daga bisani tayi addu’a ta shafa ta tashi ta ninke dardumar ta ajiyeta a mazaunin ta, ƙofa ta buɗe ta fita ta sauka downstairs ta shiga dube duben inda zataga abin shara cikin sa’a ta gansu da abin yin mopping dama abinda ta sauko nema ɗin kenan dan haka ta ɗauka ta koma upstairs ɗin ta fara gyaran ɗakin tayi shara da mopping ta wanke toilet duk Neehlah tana kwance tana uban barci batasan abinda take ba.
Downstairs ta ƙara saukowa nan ma ta hau gyaranshi duk da dai ba wani datti a ciki ta share tayi mopping ta maida kayan sharar inda ta gansu ta koma bedroom ɗin har lokacin Neehlah bata tashi ba dayake ba school yau, kwanciya ta ƙara yi itama dan ba ƙaramin gajiyar da ita mopping ɗin falon yayi ba saboda girman shi bata daɗe ba kuwa barci ya ƙara yin gaba da ita.
Lokacin da suka tashi ƙarfe goma ta kusa wanka sukayi Neehlah tace ta buɗe wardrobe ta zaɓi duk kalar kayan da sukayi mata ta ɗauka tasa, saita rasa ma wanda zata ɗauka ɗin saboda yawansu kayane gasu nan birjik laces, atamfofi, material’s, dogayen riguna,shaddoji da English wear sai wanda ka zaɓa lallai masu kuɗi sun more ba abinda ya damesu (A naki ganin ko? kowane ɗan adam baya rasa abinda yake damunsa).
Wata atamfa ta zaƙulo riga da siket saidai tana ɗauko ta ma taga sabuwa ce ko sakawa ma ba’ayi ba niyyar maidawa tayi Neehlah tace sam bata isa ta maida taba tasa kawai meye amfanin kayan, ash color ce atamfar da touch ɗin fari da baƙi ɗinkin simple ne bawata kwalliya kuma sunyi mata matuƙar kyau ta shafa turaruka, hijabinta ta ɗauka zata zumbula Neehlah ta ƙwace ta ɗauko mata mayafi ash mai ɗan girma tace shi zata saka ita ko gajiya batayi da saka hijabi, haka dai ta karɓa ta yafashi tana jinta duk wani iri saboda bata saba ba tafi ganewa hijabanta masu girma tai ta yawo a cikinsu.
Neehlah doguwar riga kawai tasa ƙirar Saudi blue black ta yafa gyalen rigar suka sauka ƙasa dan yin breakfast.
Saukowar Ummi kenan suma suka sauko cikeda farin ciki take kallonsu tana amsa gaisuwar su kafin ta ɗora da faɗin mai yi musu gyara tazo ɗazu tace mata an gyara ko ina kuma tasan ita tayi kar ta ƙara yi akwai masu zuwa suyi ta amsa da to daga nan suka wuce dinning Neehlah tayi serving ɗinsu dama Ummi batasa ran ganin Habeeb yanzu ba dan indai ba ranar aiki bace sai yakai ƙarfe ɗaya bai shigo yayi breakfast ba.
Seeyamah ce ta gyara kan dinning ɗin bayan sun gama duk da yadda Ummi ta hanata kuwa ta kwashe kayan da aka ɓata taje kitchen ta ɗaurayesu daga nan suka koma upstairs dama tuni Ummi ta koma bedroom, Indian film Neehlah ta kunna musu a system ɗinta suka fara kallo.
Sai wajen 12:45pm sannan ya shigo gaida Ummi bedroom ɗin nata ya shiga suka gaisa yana shirin fitowa ta ƙara tuna masa maganar fitar da zasuyi dasu Seeyamah anjima to ya ya iya? dolenshi ya amsa dan shi harya manta ma, falon ya dawo yayi breakfast ya ƙara ficewa zuwa nashi part ɗin, fita yayi ma daga gidan gaba ɗaya zuwa inda ake ginin kamfaninsu yaga yadda aikin yake tafiya sannan ya ƙara dawowa gida.
Layin Mujaheed ya kira ya faɗa masa anjima da yamma zai masa rakiya dan shikam bazai tafi daga shi saisu ba kamar wani direbansu sam ya manta ma wai fushi yake da Mujaheed ɗin, kira biyu yayi amma duk ba’ayi picking ba sai ana ukun sannan aka ɗaga cikin jin haushi yace
“ALLAH MJ idan ina kiranka baka picking akan lokaci saina dinga cin ubanka dan iskanci sai ayita kiranka bazakayi picking ba sai kaga dama”.
“To mara mutunci kasan uzurin dayake hanani ɗauka ne zakamin tijara”.
“Wani uzuri gareka daya wuce iskanci? ka shirya anjima after Asr zaka rakani shopping mall”.
“Shopping Mall kuma? babynka zakayiwa siyayya ne?”.
“Nabi babyn da gudu dalla malam ka shirya da wuri”. bai jira cewar Mujaheed ba ya yanke kiran yana cije baki ALLAH ya tsareshi da wannan ɓata lokacin shikam shi har yanada time ɗin wata mace bare har ya zauna yana wannan shirmen.
Sosai Mujaheed ya ƙyalƙyale da dariya jin abinda Gashua ya faɗa wai yabi baby da gudu wllhy wasa wasa Gashua ɗan air ne a bakinshi ma yaji wannan kalmar fa shine harya riƙe ta haka shi sam baiyi zaton ma zai sauko haka da wuri ba a yadda ya san shi da shegiyar zuciya da riƙon bala’i, girgiza kai kawai yayi yana ƙara sakin wata dariyar……
Maryam Ibraheem Aleeyu
Mrs Salees Mu’az ????
09139964697
EL HABEEB????
©️Oum Hanan.
Writer of DR SAIF.
HASKE WRITER’S ASSOCIATION????
(Home of expert & perfect writer’s).
No 30.
Ya daɗe zaune bayan sun gama waya da Mujaheed kafin ya tashi ya wuce bedroom, kayan jikinsa ya cire ya rage daga shi sai boxer da singlet farare tas ya shiga bathroom yayi wanka. bayan fitowar shi ya shirya cikin ƙananan kaya baƙin jeans ne da riga peach color mai gajeren hannu ya ɗaura baƙin agogon fata sai P. Cap kalar rigar daya ɗora a kanshi ya sanya baƙin takalmi sawu ciki yana cikin fesa turare wayarshi ta fara ringing bai kulata ba sai daya gama fesa turaren sannan ya isa inda take lokacin harta katse wani kiran ya ƙara shigowa yasan dai bazai wuce Mujaheed ba picking yayi yakai kunnenshi batare dayace komai ba ya ƙara komawa gaban mirror'n ya tsaya ya ɗauki wani turaren yana fesawa daga can ɓangaren Mujaheed yace
“Gashua ka gama shiryawa ne?”. Da ƙyar ya buɗe baki yace
“Yes”.
“Okay nima na shirya gani nan zuwa”.
“Ok”. yace tareda katse wayar ya ajiye kwalbar turaren ya fito falo, zama yayi ya shiga latse latsen waya.
Daga Seeyamahn har Neehlah ba wadda taso Ummi ta haɗasu tafiya da Habeeb Seeyamah dai batace komai ba to me zatace? itafa jinta take tamkar ƴar aiki a gidan Neehlah kam fuska ta shagwaɓe tana faɗin
“Kai Ummi ALLAH da baki haɗamu da Yah Habeeb ba takuramu kawai zaiyi bazai bari ma ayi siyayyar cikin kwanciyar hankali da nutsuwa ba”.
Harararta Ummin tayi tace
“Sha zamanki tunda bazaki ba”.
“Zanje fa Ummi kawai dai Yah Habeeb ɗin ne akwai matsawa wllhy ni banson tafiya tana haɗani dashi”.
“Kin tashi kinje kin shirya kokuwa dai surutu zaki tsaya yi?”. Tashi Neehlah tayi ta fita tana tura baki ko yaya tafiya ta haɗasu ya dinga hantarar mutum kenan yana masa tsawa ina dalili.
Yanzun ma dai da sukayi wanka Neehlah cewa tayi Seeyamah ta zaɓi duk kayan da sukayi mata tasa, wata doguwar riga ta ɗauka ta material multi color tasa ba yadda Neehlah batayi da itaba kan tasa mayafi tace a’a ta bata hijab tasaka tafi sabawa dashi, hijabin ta ɗauko mata pink kalar datafi yawa a jikin material ɗin ta bata ta saka iya gwiwa ne mai hannu tayi kyau sosai sai ƙamshi take.
Neehlah kam mayyar dogayen riguna ce dan haka yanzun ma cikin doguwar rigar ta shirya light brown tayi rolling da mayafin rigar suka zauna zaman jira.
Ba’a daɗe ba sosai Mujaheed ya ƙaraso gidan shigar manyan kaya yayi dayake ma’abocinsu sosai shadda milk color harda hula kalar shaddar kamar wani ango nan compound ma ya tsaya ya kira Habeeb ɗin yace ya fito ya ƙaraso, sai daya kira Ummi yace su Neehlah su fito sannan ya fito daga part ɗin nashi ya rufe ya fito cikin compound ɗin.
A bedroom Ummi ta samesu tace su fita yana jiransu a waje tashi sukayi sukayiwa Ummi sallama sannan suka fito.
Ba ƙaramin daɗi Neehlah da Seeyamah sukaji ba lokacin da suka fito suka hango Mujaheed da alamu dashi zasu fita, suna ƙarasowa suka haɗa baki wajen gaishesu cikin sakin fuska Mujaheed yake amsa musu Gashua kam a cukule ya amsa musu da
“Lafiya”. Tamkar wanda akayiwa dole ya buɗe front seat ya shiga ya hakimce bayan ya cillawa MJ key ɗin motar, Mujaheed da kanshi ya buɗewa su Seeyamah back seat suka shiga ya maida murfin ya rufe sannan ya shiga driver seat ya zauna yana kallon Habeeb da hankalinsa ke kan waya yace
“Wai Gashua ni zanyi driving ɗin ne?”. banza yayi masa baiyi magana ba bai kuma ɗago ya kalleshi ba.
“Kaji?”. Mujaheed ya ƙara faɗa duk cikin neman tsokana da son saiya sashi dai magana.
“A’a ni zanyi”. yace yana juyawa tareda sakar masa harara, dariya Mujaheed yayi yace
“Yaro yaji hausa har dasu baƙar magana haka Gashua”. ya ƙarasa maganar yana ƙoƙarin tayar da motar, ƙaramin tsaki Habeeb yaja tareda maida kanshi kan wayarshi ya cigaba da abinda yake.
Maigadi ne ya buɗe musu gate suka fice daga gidan, saida suka hau kan titi sannan Mujaheed yace
“Ina muka nufa ne Mr. Man?”.
Kamar yadda baiyi magana ba haka ma bai ɗago kai ya kalleshi ba, Mujaheed ya ƙara faɗin
“Wai Gashua bakaji abinda nace bane?”. Nan ma banza yayi masa hakan ya hasala Mujaheed ya juyo yana harararshi da faɗin
“Matsala ta dakai wulaƙanci wllhy kanaji ana maka magana ka ƙyale mutane banza mara mutunci”. Sosai Habeeb ya shaƙa saboda yadda Mujaheed yake kunyata shi da tsinkashi a gaban ƙananan yara su kansu su Seeyamah mamaki ne ya cikasu jin yadda Mujaheed ɗin yake zaginshi musamman Neehlah datafi sanin ko waye yayanta lallai idan ba Mujaheed ɗin ba bataga wanda zaiyi masa haka ya ƙyale ba.
“Autar Ummi ina muka nufa ne? siyayyar me za’ayi?”. Mujaheed ya maida tambayar kan Neehlah, a ɗarare tace
“Kaya ne za’a siyawa Seeyamah”.
“Okay yayi kyau bari mu duba babban shago saimu shiga ko?”.
“Toh Yah Mujaheed”. Neehlah tace taja bakinta tayi shiru.
Mujaheed bai ƙara saurarar Habeeb ba ya maida hankalinsa kan tuƙi sai jefi jefi dayake jan su Neehlah da hira waɗanda sam basu biye masa ba kuma duk yasan ganin wannan uban ƴan baƙin ran ne ya hana Neehlah biye masa a yadda take da ɗan banzan surutun nan, sai yaja bakinshi yayi shiru aka shiga yin tafiyar kurame ba mai magana titin Nassarawa ya hau yana ɗan dudduba kan hanya inda zaiga gurin saida kaya, ganin motar ta ɗauki shiru yasa Mujaheed yayi connecting da wayarshi yasa waƙa ya fara saurara yana bin waƙar.
Ido Habeeb ya ɗan runtse yanajin kiɗan har cikin ƙwaƙwalwar kanshi kamar a tsakiyar kanshi akeyi ALLAHn da yayi shi ya tsani hayaniya koya take.
“Please MJ ka kashe banaso”. yace cikin cool voice yana ɓata fuska.
“Why?”. cewar Mujaheed yana wani kaɗa kai alamun waƙar ba ƙaramin daɗi take masa ba, a ɗan fusace Habeeb yace
“Saboda motata ce inada iko da ita”.
Murmushi Mujaheed yayi tareda ɗan taɓe baki yace
“Gori zakamin Gashua? daɗin abin nima dai inada motar nan kuma ina zamana ka kirani in maka rakiya haba saikace wanda ya ɗauko gawa a mota kai ba za’ayi hira dakai ba Neehlah saboda tsoron ka itama taƙi sakin jiki na kunna waƙa kace ba haka ba to ya kakeso ayi Gashua? kai bazakayi nishaɗi ba bazaka bar wani yayi ba”.
“Kawai ka kashe banason hayaniya banda ɗan iska ne kai meye abin saurara a waƙoƙin nan ba ma’ana ba komai”.
“Eh a ƙyaleni ni inaso a haka tafiya dakai matsala ne wllhy Gashua naji ka ƙara nemana rakiya wani wajen ba inda zanje”.
“ALLAH kayi wasa zan saukeka a tsakiyar hanyar nan”.
“Ka daɗe baka saukeni ba Gashua”. Mujaheed ya faɗa yana dariya, ƙwafa kawai Habeeb ya saki ya maida kanshi kan wayarshi, su dai su Seeyamah suna baya sunajin irin dramar dasu Mujaheed suke tafkawa dama ai abokan wasa ne Neehlah ta ayyana cikin ranta.
“Bari dai in ɗan rage volume badan halinka ba karka tadamin iska yanzu”. yayi maganar yana ƙara sakin wata dariyar tareda kai hannu ya rage ƙarar, dariya ce sosai ta kama Neehlah jin abinda Yah Mujaheed ya faɗa wai karya tada masa iska amma ba damar yi dole ta haɗiye abarta ta sunkuyar da kai tana murmushi, Mujaheed yana kallonta ta mirror’n motar dai dai lokacin ta ƙara ɗago kai suka haɗa ido ya ɗage mata gira haɗi da kashe mata ido tayi saurin ƙara maida kanta ƙasa tana murmushi.
Tun daga nesa ya hango wani ƙaton boutique a side ɗinsu na dama dan haka yayi U town yadawo ɓangaren dama har zuwa daidai boutique ɗin yayi parking tareda kashe motar.
“Gashua munzo fa ka fito muje”.
“Waye zaije ɗin? kuje dasu kawai malam ga ATM nan a biyasu”. ya ida maganar yana karkacewa ya zaro ATM ɗin ya miƙawa Mujaheed
“No ka barshi kawai zan biya kasan kyautatawa maraya ba ƙaramin lada ne dashi ba”. cewar Mujaheed, baki kawai Habeeb ya taɓe tareda ɗage kafaɗu ya maida ATM ɗin aljihu, fita Mujaheed yayi ya buɗewa su Seeyamah da har lokacin basu fita daga motar ba
“Bismillah ƴanmata”. yace yana murmushi idanunsa akan Neehlah yana jifanta da wani irin kallo wanda duk kunya ta kamata, fita sukayi ya rufe ƙofar sannan suka jera a tare zuwa cikin boutique ɗin.
Ƙaton gaske ne ga uban kaya cike sai wanda mutum ya zaɓa matsalar dai kawai duk English wears ne da dogayen riguna dan haka Mujaheed ya yanke shawarar idan sun fita saisu biya inda ake saida abinda ya shafi atamfofi da laces, kasa ɗaukar komai Seeyamah tayi ganin haka yasa Mujaheed yace Neehlah ta zaɓar mata, nan fa Neehlah ta shiga zaɓa Seeyamah tace batason masu wando hakan yasa Neehlah ta fara duba mata masu skirt irin masu faɗin nan tace banda masu matsewa.
Ruwan ido yasa har aka ɗauki wani lokaci Neehlah bata zaɓi kayan kirki ba Seeyamah da Mujaheed dai suna biye da ita a baya sai faman surutu take zabgawa.
Jin shiru shiru basu fitoba yasa haushi ya kama Habeeb ganin yadda suka shanya shi haka tun ɗazu sun manta dashi number Mujaheed ya kira, yanajin kiran dama ya ayyana da ƙyar idan ba Gashua bane yana dubawa kuwa yaga shi ɗinne murmushi ya saki yayi picking yakai wayar kunnenshi tun kafin yayi magana yaji muryar Habeeb na faɗin
“Wai uwar me kuke zaɓa ne haka MJ?”.
“Ban saniba dalla malam in kana jira ka jiramu in baka iyawa ka tafi abinka ɗan takurar bala’i”. Bai jira cewar shi ba ya katse kiran yana dariya yasan ya gama kunna shi, ƙwafa yayi yana sakin huci wllhy Mujaheed ya gama rainashi bari ya tafi ɗin sa nemi abinda zai dawo dasu gida.
“Oh my God”. ya furta hakan a hankali yana lumshe ido lokaci ɗaya yana shafa sumar kanshi daga gaba zuwa baya tunawa da yayi key ɗin motar baya wajensa yana wajen Mujaheed tsaki yaja ya ƙara dannawa Mujaheed wani kiran
“ALLAH ya shiryeka abokina”. Mujaheed ya faɗa a fili yana ƴar dariya gami da picking yakai kunnenshi yana jiran yaji abinda zai faɗa
“Ka fito ka kawomin key ɗin yanzu”.
“Me zakayi?”. Mujaheed yace yana ɗan zaro ido
“Ba damuwar ka bace”. yabashi amsa a zafafe
“Idan kaga na fito to mun gama siyayyar da zamuyi ne ai kanada ƙafafu ka shigo ka karɓa mana mara mutunci”. yana faɗar haka yayi hanging calling ɗin yana dariya tareda faɗin
“Autar Ummi quickly please wannan yayan naki bai cika M ba”. juyowa tayi tana ɗan ɓata fuska ta shagwaɓe murya tace
“Kai Yah Mujaheed Yah Habeeb ɗin?”.
“Ah ba gaskiya na faɗa ba? ke kanki kinsan halin yayanki ai saidai ki take saboda kinajin tsoronshi”.
Baki ta ɗan taɓe tace
“Gaskiya kam Yah Mujaheed kana fama wllhy kaida kuke tare dashi kullum”.
“To yana iya? ALLAH ya riga ya haɗa ni kaina watarana shakkar shi nake dan dai kawai ina mazewa ne”. Dariya Seeyamah da Neehlah sukayi shima Mujaheed dariyar ya shiga tayasu yana ƙara cewa Neehlah tayi sauri ta zaɓi abinda zata zaɓa su tafi kafin Gashua ya fashe…..