EL-HABEEB HAUSA NOVEL

EL-HABEEB HAUSA NOVEL

Zan ƙara yawan pages ɗin ko zuwa 35 ne saimu tsaya kafin mu ɗora book two ALLAH ya bada ikon siya amin

Afwan da yadda yanayin typing ɗin yake zuwa ban cika jin daɗi ba ga hidimar iyali ALLAH yasa mudace.

Maryam Ibraheem Aleeyu
Mrs Salees Mu’az ????
09139964697

EL HABEEB????

©️Oum Hanan.
Writer of DR SAIF

HASKE WRITER’S ASSOCIATION????
(Home of expert & perfect writer’s).

Anata tambaya ta book one ya ƙare ne? ƙasan page ɗina na yau na sanar cewar zan ƙara 5 pages saɓanin baya danace iya 30 page book one zai ƙare yanzu zai ƙare ne a 35 pages fatan kun fahimta nagode sosai ????

No 31

Kamar yadda Mujaheed ɗin ya faɗa kuwa Habeeb ya cika yai fam ƙiris yake jira ya fashe sai faman girgiza ƙafa yake yana cije baki shi damuwarshi ma yadda Mujaheed yake kunyata shi a gaban ƙananan yaran su Neehlah daya sani ma tun farko da Mujaheed ɗin ya haɗasu suka taho shi yayi zamansa dan dai kawai kuma Ummi zatace baibi umarnin ta ba.
Neehlah dai jin Yah Habeeb nata faman dokawa Mujaheed kira yasa ba shiri sauri sauri ta zaɓi abinda ya kamata ta zaɓa ɗin daga kan English wear dogayen riguna, huluna takalma da sauran kayayyakin adon mata, wajen biya sukaje Mujaheed ya biyasu aka zuba musu a ƙatuwar leda sannan suka fito ma’aikacin wajen ya biyosu da kaya niƙi niƙi booth ya buɗe masa yasa a ciki lokacin har su Seeyamah sun shiga motar, shima Mujaheed zagayawa yayi ya shiga driver seat ya zauna ya kalli Gashua wanda tun fitowar su ya ƙara haɗe rai yana faman muzurai.
“Yadai Mr Habeeb Gashua mun barka kanata jira ko?”. cikin salon tsokana yayi maganar yana dariya, idan kujerar da Habeeb yake zaune kai tayi magana to shima ya tankawa Mujaheed, wata dariyar Mujaheed ya ƙara saki yace
“ALLAH dai ya biya Ogah mun tuba ayi mana afwah kanmu bisa ƙafafunmu”. ya ƙarasa maganar yana kama kunnuwan shi.
“Na rantse zan fasa maka baki Mujaheed”. ya faɗa a hasale yana kallonshi, ido Mujaheed ya zaro tareda buɗe baki yace
“ALLAH ya baka haƙuri Boss”.
Tsaki Habeeb ya saki yayi relaxing kan seat ɗinshi ya rufe idanunshi gami da harɗe hannayenshi kan ƙirjinshi yana faman jijjiga ƙafafu, motar Mujaheed ya tayar ya harbata kan titi suka tafi.
Tunda suka tafi ba wanda yayi magana a cikinsu har suka isa Mudassir & brothers shi Habeeb ma duk zaton shi gida suka dawo dayaji anyi parking yana buɗe idanunshi ya gansu a wani waje daban Mujaheed ya kalla kafin yace
“Nan kuma ina ka kawomu MJ?”.
“Mudassir & brothers ne”. Mujaheed ya bashi amsa.
“Ina ne haka?”. yace yana yamutsa fuska.
“Wajen siyar da atamfofi ne da sauran manyan kaya can inda muka baro babu irinsu”.
Shiru kawai yayi baice komai ba hakan yasa su Seeyamah suka fita suka tsaya suna jiran Mujaheed ɗin ya fito su shiga.
“Yanzun ma bazaka shiga ba Gashua?”. cewar Mujaheed yana kallonshi.
“Ka fini sani ai”. amsar daya bashi kenan yana danna waya.
“Sorry yanzu zamu fito ba daɗewa zamuyi ba”. Mujaheed yace yana ƙoƙarin buɗe murfin motar ya fita.
“Ku daɗe ma mana kagani idan banci ubanka ba daga kai har su ɗin”. dariya kawai Mujaheed yayi ya fita daga motar ya maida murfin ya rufe, relaxing ya ƙara yi sosai yana latsa waya yau dai yaga ta kanshi sai yawo ake dashi cikin gari.
Mujaheed bai daɗe da shiga ba kiran abokin nan nashi da suka haɗu a Dubai lokacin dayaje karatu can ya shigo wayarsa Auwal Mahmoud Azare wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen koyawa Gashua hausa ba laifi suna zumunci ta waya bayan ƙare karatunsu kuma shima Auwal ɗin ne ya fara nemansa, murmushi yayi yai picking tareda kai wayar kunnenshi saidai bai furta komai ba shima Auwal yasan bazai furta ɗin ba dan haka yace
“ALLAH ya taimaki Ogah”.
“Azire ya kake?”. Dariya Auwal yasa yana faɗin
“Azare nefa sunan mutumina tun zamanin school nake gyara maka amma har yanzu baka iyaba”.
Haɗe rai Habeeb yayi yace
“Kai ka sani dai”.
Wata dariyar Auwal yayi yace
“Na shigo garinku fa yau Kano yanzu haka ina cikinta”.
“Serious?”.
“Yeah munzo ɗaurin aure ne na wani abokin mu daya auri ƴar Kano so su sun wuce ma tun ɗazu nikuma na wuce Mandawari gidan wani kawuna sai gobe zan wuce da safe nace bari in nemeka mu gaisa”.
“Oops gashi bana gida yanzu ya za’ayi inaso mu haɗu”.
“Kana ina?”.
Kai ya ɗaga ya ƙara kallon ginin dan harya manta sunan da Mujaheed ya faɗa masa ɗazu sunan wajen ya faɗawa Auwal yace ba matsala gasu nan zasuzo shida ɗan kawun nasa zai rakoshi daga haka suka katse wayar.
Nan ma siyayya sosai Mujaheed yayiwa Seeyamah harta rasa bakin magana harda Neehlah itama saida yayi mata tata siyayyar.
Cikin ma’aikatan wajen ne ya rakosu da kayan wajen mota bayan sun biya akasa musu a booth.
Mujaheed na shirin tada motar bayan su Neehlah sun shiga yaji Habeeb yace
“Wait…..akwai wanda nake jira zaizo yanzu”.
“Waye?”. Mujaheed ya tambaya
“Auwal wanda mukayi school ɗaya a Dubai”. yabashi amsa batare daya kalleshi ba.
“Maimakon yaje gida ya jiramu Gashua?”.
“Ina ruwanka? ban cika son shisshigi cikin al’amurana ba”. yace yana harararshi, baki Mujaheed ya taɓe bai dai ce komai ba.
Nan suka cigaba da zama kowa ya kama waya yanata danne danne har zuwa lokacin dasu Auwal suka ƙaraso wajen, Habeeb da Mujaheed suka fita suka taresu.
Jikin motar Auwal suka tsaya suna gaisawa da tambayar bayan rabuwa sosai Habeeb yayi murna da ganin Auwal Mujaheed dayake yanada saurin sabo nan da nan suka saba da Auwal da ɗaya saurayin daya rakoshi Abbas.
Wayarshi dake hannunshi ya nemo number Neehlah ya kirata cikin faɗuwar gaba ta ɗaga kiran, tana kai kunnenta taji shi cikeda faɗa yana faɗin
“Idan kika sake nazo wajen nan saina karya ki dan ubanki kina ganina da baƙo kinfi ƙarfin kizo ki gaisheshi ko?”. bai jira abinda zatace ba ya kashe wayar.
“Yaa ALLAH”. Neehlah tace tana dafe goshinta shidai mutumin nan idan bai ƙaƙalo laifi ya ɗorawa mutum ba bayajin daɗi yanzu meye laifinta anan? hannun Seeyamah taja tana faɗin
“Please Sisi zo ki rakani in gaishe da baƙon Yah Habeeb kafin a karyani a kanshi”.
Fuska Seeyamah ta yatsina tace
“Nidai kam Neehlah da kinje kin dawo kawai nifa tsoron yayan can naki nake wllhy”.
“Dan ALLAH kizo muje please banason zuwa ni kaɗai wllhy”. Ganin yadda duk ta damu yasa Seeyamah ta buɗe murfin motar ta fita itama Neehlah ta fita suka nufi inda su Habeeb suke tsaye.
Tunda suka doso inda suke Auwal ya kafe Neehlah da kallo yanajin wani irin al’amari na shigar shi wanda bai taɓa tsintar kanshi cikin yanayin ba, har suka ƙaraso bai ɗauke idanunshi daga kanta ba wanda har Mujaheed da Abbas dake tsaye a wajen suka gane hakan Habeeb dai baisan me akeba dan kanshi na ƙasa da waya a hannunshi, tsaki Neehlah taja cikin ranta ganin irin kallon ƙurillar da wannan abokin na Yah Habeeb yake binta dashi kamar wani maye, rissinawa sukayi suna gaisheshi lokacin da suka ƙarasa Auwal ya amsa yana wani washe baki, tunda Mujaheed yaga haka wani irin ɓacin rai ya kamashi zuciyar shi ta dinga tafarfasa kawai sai yayi musu sallama ya koma cikin mota ya zauna.
Su Neehlah ma suna gaisheshi suka dawo wajen motar su, ta cikin glass ɗin motar Mujaheed yake kallon yadda Auwal yabi bayan Neehlah da kallo kamar zai biyota sai wani murmushi yake yana shafa sumar kanshi tamkar ya haɗiyi zuciya ya mutu haka yaji a lokacin ko ba’a faɗa masa ba yasan da wani abu a cikin zuciyar Auwal ɗin lallai lokaci yayi daya kamata ya fallasa sirrin zuciyar shi bai taɓa zama yayi maganar data danganci soyayya da Neehlah ba ada bai taɓa tunanin ma sonta yake ba ya ɗauka duk soyayya da shaƙuwa da sukayi na ƴan uwantaka ne sai baya bayan nan ya gane cewar sonta yake.
Suna zuwa suka shiga motar Neehlah na ƙara jan wani tsakin ta tsani kallo a rayuwarta kuma tanajin idanun mutumin a kanta lokacin da suka juya baya, shima Abbas wanda suke tare da Auwal mota ya shiga yana jiran Auwal ɗin.
“Mutumina wai wace wannan yarinyar da kuke kama da ita ne? badai ƙanwarka bace?”.
“Yes she is my sister”. habeeb ya bashi amsa.
“Wow masha ALLAH amma baka taɓa faɗa min kanada ƙanwa haka ba Gashua”. Auwal yace yana murmushi.
“Kasan komai kamawa take”. cewar Habeeb.
“Gaskiya ne amma fa she’s very beautiful tayi ba ƙarya yaushe zakuyi mata aure ne?”.
Sai daya dalla masa harara kafin yace
“Ina ruwanka?”. dariya Auwal yayi yace
“Kaifa ba’a maganar arziƙi dakai abokina naga dai ƙanwarmu ce kuma kasan hausawa sunce idan kaga kare yana shinshinar takalmi to ɗauka zaiyi”.
Wani banzan kallo Habeeb ya jefawa Auwal yace
“Kunada matsala wllhy shiyasa dole ƙananan yara su rainaku bakuda girma saina jikinku”.
“Eh munji ɗin kaidai har yanzu bazaka canza ba wannan shegen son girman naka yana nan muna nan mun zuba ido muga wadda zaka aura”.
“ALLAH ya tsareni da auren ƙaramar yarinya kowa ma mara aikin yine irinku”.
“Lokaci ne zai nuna mana hakan dude kaidai kayi addu’ar ALLAH yasa karka folawa ƙaramar yarinya wllhy duk wani girma da jiji da kai bakasan lokacin da zaka saukeshi ba kazo kana ƴar murya”.
Tsaki Habeeb yayi kawai duk ya ɗauki maganganun Auwal ɗin shirme auren ƙaramar yarinya ko ɗorawa kai wahala.
Sallama sukayi da Auwal wanda yake ta ƙara yimasa maganar Neehlah yaƙi kulashi Auwal ya shiga motar shi shima Habeeb ya nufi tasu motar.
Tunda suka tafi Mujaheed baiyi magana ba jin ranshi yake duk ba daɗi shi kanshi habeeb ya lura da canjin yanayin da Mujaheed ɗin ya shiga ya buɗe baki ya tambaye shi dalilin hakan ne yake jin wahala.
Neehlah da Seeyamah ma sun kula da Mujaheed ɗin ya daina walwala duk da basu san meya canza shi ba.
Hanyar unguwar su ya nufa yana faɗin
“Su fara zuwa can ɗin basai ya koma ta gidansu ba, Habeeb dai bai tankashi ba har zuwa gidan su Mujaheed ɗin daga nan yayi musu sallama ya sauka Habeeb ya koma driver seat ɗin dan cigaba da tuƙin, amma maimakon ya fara driving ɗin saiya ɗauki waya kawai ya fara dannen dannen waya, kallon juna Seeyamah da Neehlah sukayi cikin mamaki…..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38Next page

Leave a Reply

Back to top button