EL-HABEEB HAUSA NOVEL

EL-HABEEB HAUSA NOVEL

Afwan kamar kullum????

A ƙara haƙuri dai yanayin labarin ne yanada tsayi sosai so banaso muyi gaggawa mubi komai hankali har zuwa lokacin da ALLAH zaisa muje inda mukeson zuwa

Maryam Ibraheem Aleeyu
Mrs Salees Mu’az ????
09139964697

EL HABEEB????

©️Oum Hanan.
Writer of DR SAIF.

HASKE WRITER’S ASSOCIATION????
(Home of expert & perfect writer’s).

No 32.

Sunfi ƙarfin 20min a wajen batare da sun tafi ba kokuma ya buɗe baki yace musu wani abu gaba ɗaya sun gaji da zaman cikin motar, hankalinshi kwance yake latse latsen wayarshi.

Sai zuwa yanzu ne Neehlah ta fara tunanin dalilin dayasa yaƙi tafiya idan suka tafi a haka ya zama kamar wani direbansu kenan ya buɗe baki yace wata ta dawo front seat a cikinsu shine ba zaiyi ba kai jama’a ALLAH ya shiryi mutumin nan.
Bakinta takai saitin kunnen Seeyamah ƙasa ƙasa kamar munafuka tace
“Sisi ki taimaka ki koma gaba nasan abinda yasa yaƙi tafiya kenan wllhy ba kuma zai buɗe baki yace wata a cikinmu ta koma ba”. Ido Seeyamah ta ɗan zaro itama cikin ƙasa ƙasa da murya tace
“Nifa tsoronshi nakeji Neehlah please ke ki koma gaban”. Kai Neehlah ta girgiza tana shagwaɓe fuska tareda zungurin Seeyamah cikin raɗa tace
“Please and please Sisi kar muyi haka dake mana”. Kan dole Seeyamah ta buɗe murfin motar ta fita jikinta har rawa yake ta buɗe front seat ta zauna, bai juyo ya kalli wadda ta zauna ɗin ba haka kuma bai bar danna wayar dayake ba, Seeyamah gaba ɗaya a tsorace take gani take kamar zaiyi mata wani abun.
Saida aka kwashi kusan mintuna biyar sannan ya ajiye wayar ya tada motar suka tafi a tare Neehlah da Seeyamah suka saki ƙaramar ajiyar zuciya, tafiyar kurame dai aka ƙara yi har zuwa lokacin da suka ƙarasa gida. Idi mai bawa fulawa ruwa shine ya shigar musu da kayan sukabi bayanshi, Habeeb ma kuwa cikin motar suka barshi sukayi gaba Neehlah na faɗin tunda dai sun fito lafiya alhmdulillah yau dai Mr ɗacin rai ya zama direba.
Bedroom ɗin Ummi suka fara shiga suka sanar da ita dawowarsu tayi musu sannu da zuwa daga nan suka wuce nasu bedroom ɗin lokacin anata kiran sallahr magreebah, suna shiga sukayi alwalah suka gabatar da farali sannan suka koma bedroom ɗin Ummi suna nuna mata kayan anan Neehlah take faɗawa Ummi ai duk Yah Mujaheed shine ya biya kuɗin siyayyar Ummi taji daɗi sosai ta shiga sa masa albarka.
Bayan sallahr Esha’e Ummi ta shiga gidan su Hajiya Inna zuwa lokacin tasan Alhaji Sulaiman yadawo gida dan tanaso tayi magana dasu, part ɗin Alhaji Sulaiman ɗin ta fara shiga suka gaisa dashi da matarshi ta sanar dashi akwai maganar datake so suyi dashi da Hajiya nan yace mata taje sashin Hajiyan ta jirashi zaizo.
Cikin tsantsar kulawa da mutunta juna Ummi da Hajiya suka gaisa daga nan suka fara taɓa hira har lokacin da Alhaji Sulaiman ya shigo sashen.
A tsanake daki daki Ummi ta shiga yiwa su Hajiya bayani daga lokacin da Mujaheed yazo mata da bayanin komai da gidan dataje ta ɗauko yarinyar ta maida ita gidan marayun ta gangaro kan ɗauko yarinyar datayi zuwa gidanta dan cigaba da riƙonta a taƙaice dai tana neman afwarsu na yadda ta yanke hukuncin ɗaukar yarinyar ba tareda neman shawarar su ba.
Sunyi mamaki ƙwarai kuma daga Hajiya har Alhaji Sulaiman sunga sanarwar da akayi ta sace yarinyar ashe habeeb ne ya ɗauke ta, sai yanzu Hajiya ta fara tunano lokacin daya shigo yaga Heedayah a wajenta irin yanayin daya shiga da kuma neman ƙarin bayani dayazo ji a wajen ta ikon ALLAH kenan Heedayah ƴan biyu ne? to amma kuma Ramlah bata taɓa faɗa mata ba tace mata Heedayah ita kaɗai ce ƙanwarta, idan hakane kuwa itama zataso ace Habibu ya binciko musu gaskiyar lamarin abin akwai ɗaure kai sosai.
Duk cikinsu ba wanda ya kushe abinda Ummin tayi saima yaba mata da sukayi taimakon maraya ai ba ƙaramin lada gareshi ba ubangiji yanason masu taimakawa marayu kuma ɗa na kowa ne, sun ƙara tattauna maganar sannan Ummi tayi musu sallama zata tafi Alhaji Sulaiman na ƙara jaddada mata duk hidimar yarinyar idan ta tashi ayi masa magana Ummi tayi godiya, daf da zata fita daga falon ta tsinkayi muryar Hajiya na faɗin gobe ta turo mata Neehlah da yarinyar cikin girmamawa Ummi ta amsa mata da insha ALLAH zata turosu. Har ta fito ta tuna da maganar Aleeyu ta sake komawa ta roƙi alfarmar ya taimaka ya samar masa wani aikin cikin harkokin kasuwancinsa, ba tare da wata gardama ba ya amince yace insha ALLAHU zai duba yagani mutumin yanada sauƙin kai godiya Ummi tayi ta fita.
Bayan fitar Ummi ma su Hajiya sun ɗan jima suna tattauna maganar da Alhaji Sulaiman har lokacin Hajiya bata daina jinjina al’amarin ba tana ƙara faɗa masa irin tsananin kamannin da yarinyar suke Heedayah mai zuwa wajenta ta yadda ba yadda za’a ga ɗaya ace ba ɗayar bace shi kanshi Alhaji Sulaiman yayi mamaki sosai.
Sai bayan ta koma sannan sukayi dinner, yau basuyi zaman kallo bama suna gama dinner suka haye upstairs suka shige bedroom Neehlah ta taya Seeyamah jera kayan da aka siyo a wardrobe su kuma manyan aka ware su za’a yiwa mai yiwa su Ummi magana yazo ya karɓa a ɗinka mata.
Ummi ma bata daɗe ba ta tashi ta bar falon, lokacin daya shigo ba kowa a falon sai a lokacin ne yazo yin tashi dinner bai wani ci abincin kirki ba ya tashi ya haura sama yaje ya yiwa Ummi saida safe ya sauko ya fita ya koma nashi side ɗin.

★★★__★★★
Washegari bayan sun gama breakfast Ummi ta cewa Neehlah suje da Seeyamah su gaida su Hajiya.
Hajiya sakin baki tayi tana ƙarewa Seeyamah kallo har Seeyamahn ta fara tsarguwa da irin kallon da Hajiya take mata tunanin Hajiya anya ba raina mata hankali akayi ba kuwa ya za’ayi ace wannan ba Heedayah bace? kai al’amarin nan akwai ban mamaki da ɗaurewar kai duk yadda taso ta gasgata eh da gasken ba Heedayah bace ta kasa dan haka ta kira number Aunt Ramlah tace ta haɗata da Heedayah a take Aunt Ramlahn ta miƙawa Heedayah wayar dama suna zaune a falone dukansu lokacin, gaisawa kawai sukayi Hajiya ta kashe wayar
‘Qadeeran Alaa man yasha’u’. Hajiya ta furta cikin zuciyar ta, lallai al’amarin ubangiji da girma yake wannan yafi ace kama kawai suke da juna komai ɗin ne iri ɗaya.
Sun ɗan jima a gidan sannan sukayi mata sallama suka biya ta sashin Alhaji Sulaiman suka gaishe da Hajiya Rahma matarshi shi a lokacin ma ya riga ya fita, har suka fito daga part ɗin Hajiya Rahma batasan ba Heedayah bace duk zatonta itace yau ma tazo gidan.

  Tun daga ranar da sukaje siyayya Seeyamah bata ƙara saka habeeb a ido ba ita hakan ma saiyafi mata daɗi, tana matuƙar jin daɗin zama a gidan koyaushe Ummi cikin janta a jikinta take haka Neehlah sunyi shaƙuwar ban mamaki cikin ƙanƙanin lokaci suna waya da ƙasashen ta na gidan marayu da kuma wasu daga cikin shugabannin gidan marayun ana jin lafiyar juna a wayar Neehlah. 

Yammacin Lahadi.
Habeeb ne ya fito cikin shirin shi na ƙananun kaya kamar yadda ya saba, baƙin wando da brown ɗin riga mai dogayen hannu ƙafarshi sanye cikin rufaffen takalmi na zallar fata baƙi hannunshi kuma ɗaure da agogon fata kalar brown, sai ƙamshi yake bazawa motarshi ya shiga ya fita daga gidan kai tsaye rijiyar zaki ya nufa gidansu Heedayah bai manta gidan ba duk da cewar wancan zuwan da yayi da dare ne lokacin da Hajiya ta haɗashi da mara kunyar yarinyar nan ya kawota dayake a farkon layin ne gidan.
Sai bayan isar shi ƙofar gidan ne ya tuna cewar bama lallai idan yasamu Muhammad ɗin a gida ba.
“Yaa salaam”. ya faɗa ƙasa ƙasa yana dafe goshinshi tareda hura iskar bakinsa yana ƙara kallon gidan ta cikin motarshi so yake ya samu Muhammad ɗin su fara maganar duk da baisan yadda zai ɗauki maganar ba, fita yayi daga motar yana ƙarewa unguwar kallo kafin ya fara takawa cikin takun nutsuwa ya isa bakin gate ɗin gidan ya ƙwanƙwasa ba daɗewa maigadi ya buɗe ƙofar ya leƙo dan ganin mai bugawa, gaisawa sukayi kafin maigadin ya tambaye shi lafiya wa yake nema? tambayar shi yayi ko maigidan yana nan?.
“Kai maigadin ya gyaɗa yace
“Kaci sa’a bai daɗe da dawowa gidan ba wa za’a ce yana magana?”.
Wa zaice masa ne? ya tambayi kanshi yana shafa sumar lallausar sumar kanshi.
“Kace masa daga gidan Alhaji Sulaiman ne”.
“Toh bari a sanar dashi”. maigadin ya faɗa tareda juyawa ya rufe ƙofar.
Mintuna kaɗan ya ƙara buɗe ƙofar yace
“An sanar dashi zuwanka yace a faɗa maka yana fitowa”.
“Thank you so much”. yace a hankali tareda kai hannu aljihun shi na baya ya ciro kuɗi ba tare daya ƙidaya su ba ya miƙawa maigadin, hannu na rawa ya durƙusa har ƙasa ya karɓa ya shiga zabga godiya bai bi takan shi ba ko ya tsaya saurarar godiyar dayake masa ba ya juya ya koma wajen motarshi ya jingina a jiki ya harɗe hannayenshi kan ƙirjinshi ya zubawa gidan idanu.
Uncle Muhammad yana fitowa yayi ido biyu dashi ido ya ɗan zaro yana mamakin abinda ya kawo shi yau Mr. Habeeb Ibraheem Ahmad Gashua C.E.O a H.I.A GASHUA ENTERPRISES ne a gidansa? kuma yake nemansa? da sauri ya ƙarasa fuskarshi ɗauke da murmushi cikin girmamawa Uncle Muhammad ya miƙa masa hannu sukayi musabaha ALLAH ALLAH Uncle Muhammad yake yaji abinda ya kawo Mr. Gashua gurinsa sai faman saƙawa da kwancewa yake a cikin ranshi.
“Nasan kayi mamakin abinda ya kawoni wajenka ko?”. Habeeb yace yana gyara tsayuwar shi, ƴar dariya Uncle Muhammad yayi yace
“Ƙwarai kuwa yallaɓai ALLAH yasa dai ba wani laifin mukayi ba?”.
Kai kawai Habeeb ya girgiza masa alamun a’a, shiru Uncle Muhammad yayi yana jiran Habeeb yayi magana, sai daya ɗan jima kafin yace
“Magana ce akan ƙanwar matarka wadda take zaune a gidanka”.
“Heedayah?”. Uncle Muhammad yace cikin sigar tambaya.
“Yes”. Gashua yace yana jijjiga kai dan gaba ɗaya yama manta sunan nata.
“ALLAH yasa lafiya yallaɓai”. cewar Uncle Muhammad.
“Magana ce nakeso muyi dakai ta sirri a kanta wata magana bata taɓa haɗaku da ita ba game da yarinyar?”.
“Kamar tame fa yallaɓai?”.
Duk saiya rasa abinda zaice masa shifa bai saba irin wannan ba to me zaice masa ne ma? ya tambayi kanshi yana murza fatar goshinsa da hannu ɗaya ɗayan kuma ya sokeshi cikin aljihu.
“Yallaɓai ina saurarar ka”. Uncle Muhammad ya faɗa cikin girmamawa.
Numfashi ya ɗan sauke kafin yace
“Kwanaki bakaga wata yarinya da ake sanarwar ɓatan ta ba a gidajen talabijin da kafofin yaɗa labarai?”.
“Ƙwarai kuwa mun gani”. Uncle Muhammad yabashi amsa
“Kaga kamar su ɗaya da yarinyar gidanka ko?”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38Next page

Leave a Reply

Back to top button