EL-HABEEB HAUSA NOVEL

EL-HABEEB HAUSA NOVEL

Maryam Ibraheem
Mrs Salees Mu’az ????

EL HABEEB????

©️Oum Hanan.
Writer of DR SAIF.

HASKE WRITER’S ASSOCIATION????
(Home of expert & perfect writer’s).

No 33.

“Kaga irinsu ɗaya da yarinyar gidanka ko?”.
“Gaskiya ne muma munyi mamaki sosai lokacin da muka gani”.
“Bakayi zargin wani abu ba lokacin daka gani?”. ( Su Gashua yau an zama ɗan jarida ba jin kai wajen yin magana ).
Cikeda rashin fahimta Uncle Muhammad yake kallonshi ƙasan ranshi yana tunanin ina ruwan Mr. Habeeb ɗin da har yakeson jin ƙwaƙƙwafi.
“Eh to banyi zargin komai ba gaskiya tunda inada tabbacin Heedayah ƙanwar Ramlah ce”.
“Ita ta tabbatar maka da hakan?”. Gashua ya ƙara jefa masa wata tambayar, zuwa lokacin dai Uncle Muhammad ya fara gajiya da waɗannan tambayoyin na Mr. Habeeb mutum saikace wanda yayi karatun jarida? shikam gaskiya duk dayake ganin mutunci da ƙima na Habeeb ɗin bazai iya fallasa wannan sirrin ba idan yayi haka kamar yaci amana ne dan haka kawai saiya jijjiga masa kai alamun tabbatarwa.
Shiru Habeeb yayi yana tunani kafin can wata dabara ta faɗo masa yace
“Please ko zan iya ganin ita Heedayahn?”.
Kawai dan babu yadda zaiyi ne ya ɗaga masa kai saboda wani irin kwarjini dayayi masa cikin idanunshi wanda ubangiji ya halicce shi dashi.
“Bismillah muje daga ciki”. Uncle Muhammad ya faɗa yana nuna masa hanya, har ciki yayi masa jagora ya kaishi wani ƙaramin sitroom a cikin compound ɗin da alamu na saukar baƙi ne.
“Bismillah ka zauna bari ayi mata magana”. cewar Uncle Muhammad yana juyawa yabar wajen, bai zauna ɗin ba saiya shiga ƙarewa ɗakin kallo kujeru ne masu kyau ba laifi sai carpet a tsakiyar kujerun da ƙaramin center table a kai bayan haka ba komai a cikin ɗakin.
A bedroom yasamu Aunt Ramlah tana haɗa kayan wankinta da za’a haɗa a kaiwa mai wankewa sai Nusrah dake kwance kan gado tana barci Nu’aym dama baya gidan sunje weekend shida Zainab gidansu Muhammad ɗin dama yanzu can take yin weekend ɗinta. A taƙaice Uncle Muhammad yayiwa Aunt Ramlah bayanin komai ya faɗa mata kuma ta tura Heedayahn sitroom ɗin baƙi a zuwan takai masa ruwa da lemo kawai, ita kanta Aunt Ramlahn tayi mamaki ta fara tunanin dalilin dayasa yakeso ya tono RUFAFFEN SIRRI wanda ya daɗe a rufe mutumin ma da takejin labarinshi wajen Hajiya mugun miskili ne baya shiga harkar kowa kuma Heedayah ma ta bata labarinshi ance fa ko dariya bayayi to meya sakoshi cikin lamarin?.
Taso tayiwa Uncle Muhammad ɗin musu tsoronta ɗaya kar yaje ya faɗawa Heedayah wata maganar har wani zargi ya ɗarsu cikin zuciyarta abu yazo ya caɓe ba laifin wanda za’a gani sai nata musamman su Baba waɗanda koda wasa basa ƙaunar a nunawa Heedayah wani abu ko kaɗan ne wanda zaisa tayi tunanin wani abun a cikin zuciyar ta, dan dole ta nufi bedroom ɗin su Heedayahn dan cika umarnin mijinta.
A gaban mirror tasamu Heedayah tana shafa lotion fitowar ta wanka kenan bayan ta zura doguwar riga milk color.
“Yauwa Heedayah Abban Nu’aym ne yayi baƙo zaki kai masa ɗan abin taɓawa yana sitroom”. Aunt Ramlah ta faɗa bayan shigar ta bedroom ɗin.
“Tom bari inzo”. ta amsawa Aunt Ramlahn tana ajiye powder hannunta data gama shafawa.
“Okay kiyi sauri”. Aunt Ramlah tace tana juyawa tabar bedroom ɗin, lipglosses ta shafa ya ɗauki shinning sai kwalli datasa ta taje girarta ta kwantar da ita dama a ƙa’idar ta sam bata jagira saboda ALLAH ya hore mata tarin gashin gira a ganinta ɓata lokaci ne ta tsaya ƙarawa da wani abu.
Turare ta shafa sannan tayi rolling da mayafin rigar ta zura plat shoes fari ta fito zuwa falon kitchen ta wuce tasamu Aunt Ramlah ta haɗa komai a tray ruwa lemo da snacks karɓa tayi ta fito ta fita daga falon Aunt Ramlah ta sauke numfashi tana bin bayanta da kallo.
Cikin siririyar muryar ta tayi sallama wadda ta haddasawa Gashua faɗuwar gaba da baisan dalilin taba ya ɗan runtse ido yana cije lips ɗinshi na ƙasa, kasancewar ya bata baya yasa sam bataga ko waye ba kan center table ɗin ta ajiye tray ɗin ta buɗe ruwan ta fara zubawa a glass cup lokaci ɗaya tana gaisheshi jin ba’a amsa ba yasa ta ɗago kai taga wane isasshen ne wannan? tayi sallama bai amsa ba kamar wani arne yanzu kuma ta gaisheshi a matsayin shi na wanda yake gaba da ita still dai bai amsa ba to me yake taƙama dashi ne? ta tsani dizgi a rayuwar ta. Ido ta ɗan zaro ganin wanda ke hakimce akan kujerar ya ɗora ɗaya kan ɗaya yana faman basarwa, dama shine baƙon Uncle Muhammad ɗin? to ya akayi suka san juna? kin manta Uncle Muhammad ɗin yaron Alhaji Sulaiman ne wanda yake kawu a wajen nunar ranar? wata zuciyar ta faɗa mata haka, sosai gabanta ya faɗi ALLAH ALLAH take ta gama zuba ruwan ta fece dan alamun wannan mutumin ba mutunci zaiyi ba.
“Nagode nunar rana”. kalmar data faɗa masa ranar daya dawo da ita gida ta faɗo mata a rai da alamu kuma bayason sunan, tsaye taga ya miƙe cikin salon tafiyar shi na gayu da ƙasaita ya nufi bakin ƙofar falon ya tsaya yayi bake bake hannayenshi duka ya sokesu cikin aljihun wandonshi yana binta da wani munafukin kallo wanda ba kowa ne zai fahimci kallon nata yake ba.
Tuni glass cup ɗin datake zuba ruwan ya kusa cika amma dayake hankalinta sam ba’a wajen yake ba sai dataji ruwa yafara taɓa hannunta data dafa center table ɗin alamun ya cika harya fara zubewa sannan ta ankara, da sauri ta ajiye robar ruwan ta miƙe tsaye da alamu fa guy ɗin nan ɗan neman fitina ne ji yadda yazo ya wani tare mata ƙofar fita ƙundunbala tayi kawai ta nufo bakin ƙofar kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta.
“Excuse me”. tace bayan ƙarasowar ta wajen har lokacin bata ɗago kai ta kalleshi ba, ido ya ɗan rufe ya buɗe yana tuno lokacin da Jawaheer itama ta faɗa masa hakan lokacin daya tsaya jikin motar ta muryar tasu ma kanta iri ɗaya ce bambancin su kawai waccan cikin ɓacin rai da hayaniya ta faɗa wannan kuma kamar irin wadda tayi laifi aka ritsata ɗin nan.
Maimakon ya matsa ɗin saima ya ƙara gyara tsayuwar shi ya kankane ko ina yana mata kallon ƙasan ido har lokacin bai cire hannayenshi daga aljihunshi ba.
“Ple….a..sse”. tayi maganar a rarrabe cikin yanayin shagwaɓa wanda har saida ya ɗan lumshe idanunshi yayi saurin buɗesu a kanta yana ƙara matsawa kusa da ita tayi saurin ja baya ya ƙara binta ta ƙara yin baya taci karo da kujera wadda dolenta tasa ta tsaya ta ɗago kai tayi ƙwal-ƙwal da ido tana kallonshi hannunta akan gefen mayafinta tana wasa dashi ƙirjinta sai bugawa yake kamar wadda tayi tseren gudu gashi kusancin nasu yayi yawa duk yabi ya cikata da sassanyan mayen ƙamshin shi mai matuƙar daɗi da sanya nutsuwa hannu ɗaya ya zaro yakai kanshi yana shafa sumar shi yace
“Ke Heedayah kike ko Hadiye wuce ki koma ciki ki zauna inason magana dake”. ya ƙarasa maganar yana ɗage mata girarshi guda ɗaya.
Baki ta tura cikin jin haushi tace
“Wace magana ce? ni koma meye ka faɗamin a haka amma fa bayan ka matsa baya”. ta ƙarasa maganar cikin ƙunƙuni tana ƙara kumburo baki, bakin nata dama yake ta kallo tun ɗazu yadda take juyashi tana magana yanata faman ƙyalli bai taɓa tunanin akwai wani abu dazai ɗauki hankalin shi a jikin ƴa mace ba sai gashi yau ya shagalta da kallon bakin yarinya yana jin wani irin yanayi a jikinshi daya kasa fassara shi.
“Kinsan me zanyi idan baki koma kin zauna ba?”. ya tambaye ta yana ƙureta da ido, kai ta girgiza kamar zata sakar masa kuka fatanta da burinta a lokacin ya kauce ya bata waje saboda yadda ya matseta kamar wanda zai shige jikinta.
“Rungumar ki zanyi”. yace kanshi tsaye murya ba alamun wasa yana wani karkace kai.
Kutt lallai dama Man ɗin nan ɗan duniya ne bata saniba? itafa koda wasa akace zai saki irin wannan maganar haka bazata yarda ba, da gaske dama maza basuda kunya duk shiru shirun su kuwa dama kuma ance irin masu simi simi ɗin nan kamar munafukai sunfi sanin takan tsiyar. duk cikin ranta take ayyana waɗannan maganganun bayan ta ƙwalalo ido tareda hangame baki tana kallonshi.
“Yes kina mamaki ne? karki ƙara gigin bani umarni ba’a bawa Habeeb umarni saidai shi ya bayar sa’anki ne ni? ko wasa nake dake?
Saikace wata ƴar aikinka. ta faɗa cikin zuciyar ta tana ƙara turo baki, kai ya kaɗa yana cije baki kafin yace
“Zan gyarawa bakin nan zama yanzu idan baki daina turoshi ba ki ƙara gwadawa kuma ki gani”. ya ƙarasa maganar yana zagaye ta ya koma cikin falon ya zauna yayi crossing legs ɗinshi yana wani girgizasu, da harara tabi bayanshi ji take tamkar ta shaƙoshi ya cika rainin hankali wllhy nunar rana kawai.
“In taso kiga tsayina ne?”. ta tsinkayi muryar shi na faɗa, da sauri ta nufi inda yake ƙasan rug ɗin ɗakin ta nema ta zauna ta sadda kanta ƙasa tana jiran taji maganar dayace zasuyi.
Shiru yayi kamar bazai ƙara magana ba harta fara gajiya da zaman ranta fa ya fara ɓaci ALLAH zata masa rashin kunya ta gudu tunda taga alamun shi bashida mutunci.
“Daga wane gari kikazo nan?”. ya jefa mata tambayar, da mamaki ta ɗago tana kallonshi da tunanin tambayar rainin hankalin dayayi mata, taso tayi banza dashi amma kaifin idanunshi daya kafeta dasu yasa batasan lokacin data furta
“Katsina”.
“Me kikazo yi nan ɗin?”.
“Karatu”.
Kai ya jinjina kafin yace
“Ya kuke da matar Muhammad?”.
“Yaya ta ce”.
“Uwa ɗaya uba ɗaya?”. Kai kawai ta gyaɗa masa tanajin tamkar ta fasa ihu wai me yake damun mutumin nan yau? aikin jarida ya koma ne? kokuwa dai bai cikin hayyacinshi inba haka ba meye haɗin shi da ita da zaizo yana mata wasu tambayoyin yaya uwarka ta haifeka.
“Ƴan gidan ku basu taɓa nuna miki wata alama ba?”.
“Alama tame fa?”. ta maida masa da amsa.
“Baku taɓa zama kunyi wata magana da babanki ko mamanki kan abinda ya shafeki ba?”.
“Ni bamu taɓa ba”. tace tana harararshi ta ƙasan ido haushi duk ya isheta, ƙasa ya ɗan yi da kanshi yana murza fatar goshinshi wanda hakan ya zama kamar wata al’adarshi ne yana yawan yin hakan a lokuta da dama, kai ta ɗago ta dinga zabga masa harara harda murguɗa baki tana ganin zai ɗago kai tayi hanzarin maida nata kan ƙasa tareda miƙewa tsaye zata bar ɗakin dan bazata cigaba da zama yana mata waɗannan tambayoyin na rainin hankali ba.
“Sit down ban gama dake ba”. ya faɗa cikin haɗe rai yana mata wani irin kallo…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38Next page

Leave a Reply

Back to top button