EL-HABEEB HAUSA NOVEL

EL-HABEEB HAUSA NOVEL

★★_★★
Kwana biyu Hajiya sam bataji ɗuriyar Heedayah ba dan tun zuwan datayi tasa Habibu ya maida ita bata ƙara dawowa ba batasan wane irin shaƙuwa da soyayya ke tsakanin ta da yarinyar ba tana jinta a ranta sosai dan haka ta fara jajen ta wayar Aunt Ramlah ta kira bayan gaishe gaishe da tambayar iyali Hajiya tace
“Wai nikam ina ƴar gidana Heedayah ne kwana biyu tayi min yaji lafiya kuwa?”. ƴar dariya Aunt Ramlah tayi tace
“Lahh ba komai fa Hajiya kinsan mutuniyar taki ƴar kaga dama ce kuma ko jiya saida mukayi maganar ki da ita”.
“Toh ya kamata dai tazo a gaisa”.
“Insha ALLAH Hajiya gobe ko zuwa jibi zatazo”.
“To ALLAH ya nuna mana da rai da lafiya”.
“Ameen Hajiya ko ayi mata mutumin naki ta taho miki dashi?”. Aunt Ramlah ta faɗa tana dariya cikeda jin daɗi Hajiya tace
“Kaji ƴar albarka ALLAH ya saka miki da alkhairi yayi miki albarka ya raya miki zuri’a”. Da Ameen Aunt Ramlah ta amsa cikin jin daɗi ta ɗora da faɗin
“Kai Hajiya baki raina abin godiya ai bawani abu bane”.
“Kulawa ai yabawa nagode sosai a gaida maigidan”.
“Zaiji insha ALLAH”. Daga haka suka yanke kiran, bayan dawowar Heedayah daga school Aunt Ramlah take yimata maganar wayar da sukayi da Hajiya tana bikon ta taga kwana biyu bata leƙa ta ba, zama Heedayah tayi tana tura baki da faɗin
“Nifa Aunt Ramlah yanzu banson zuwa gidan Hajiyan nan wllhy”.
“Saboda me?”. Aunt Ramlah ta tambaya cikin mamaki, cikin tura baki tace
“Wannan jikan nata mana ɗan takurar da matsawa mutane shi indai aka haɗu dashi ba za’a rabu lafiya ba gashi kamar aljani saidai kawai ki ganshi tsulum ya shigo gidan”.
“To aini kuwa har nayiwa Hajiya alƙawarin zakije gobe ko jibi”.
“Haba Aunt Ramlah ni gaskiya ba inda zanje”. tace kamar zatayi kuka, haɗe rai Aunt Ramlah tayi tace
“Aikuwa baki isa ba inama laifin mai nemanka inajin ko jikokin ta bata nema yadda take nemanki sai kuma hakan ya zama laifi? shi wanda kike maganar shi ai bashi ya haɗamu ba kuma bazai zama sanadiyyar rabamu ba Hajiya mutum ce tasan ƙima da mutuncin ɗan adam duk da irin ɗaukaka da tarin dukiyar da ALLAH ya azurta su da ita bata jin kanta ita wata ce dan haka ki shirya kije ɗin kamar yadda ta nema”.
“To Aunt Ramlah kibari idan Zainab tadawo sai muje tare kokuma ranar Monday idan muka haɗu a school saimu wuce can ɗin ( Dayake Zainab ɗin yanzu duk Friday take wucewa gidansu idan an tashi daga makaranta Heedayah ce kaɗai take dawowa can take weekend ranar Monday sai tazo makaranta daga nan sai su dawo da Heedayahn tare). Kai Aunt Ramlah ta girgiza tace
“A’a bazan saɓa alƙawari ba gaskiya goben kawai ki shirya kije”.
“ALLAH ya kaimu”. Ta faɗa ba dan ranta yaso ba sai dan batason musu da Aunt Ramlahn.
“Yauwa ko ke fa autar Umma goben idan ALLAH ya kaimu zanyi mata dambun tsaki zaki wuce mata dashi”.
“Ba matsala ALLAH ya nuna mana”.
“Ameen”. cewar Aunt Ramlah tana maida kanta kan shirin da ake haskawa a TV.
Data shiga bedroom ma ita kaɗai ta dinga maganganu wllhy koda sun haɗu idan yayi mata ba ƙyaleshi zatayi ba saidai ya kasheta duk da bata fatan ma su haɗun dashi taga alamun shi ba’a yi masa alkunya.
Washegari asabar da wuri ta tashi ta hau gyaran gidan tayiwa Nu’aym da Nusrah wanka ta shiryasu dama indai weekend ne ita take yi musu wanka da safe.
Kitchen ta shiga inda Aunt Ramlah take ta fara tayata aikin datake ita Heedayah breakfast ta haɗa musu itakuma Aunt Ramlah tana harhaɗa kayan dambun da zatayi da zoɓo da zatayi mata so take ta kammala da wuri dayake da wuri ma Uncle Muhammad ɗin ya fita yau saboda wasu kayansu da suka ƙaraso a ranar ko breakfast ma bai tsaya yiba ya fita.
Tare sukayi dambun da Heedayah mai rai da lafiya dayaji kayan lambu dan ma dai ta fahimci Hajiyan ba komai take so ba ta haɗa mata haɗaɗɗen zoɓo mai daɗi tasa mata komai a wani basket madaidaici aka rufe da wani farin ƙyalle suka gyara kitchen ɗin dan Aunt Ramlah ko ƴar aiki batada ita duk da Uncle Muhammad yaso a samo mata tace a’a bataso har wani gagarumin aiki ne a gidan da sai an nemo wata mai aiki? kuma shi aikin datake ai shine rabauta da samun ladan auren dan haka ita bata buƙatar ƴar aiki ALLAH ya hore mata lafiya ta cigaba da ɗawainiya da hidimar gidanta.
Wanka Heedayah ta shiga bayan sun kammala komai, bayan ta fito ta shafa cream ɗin da suke using dashi sama sama tayi kwalliyar ta kamar yadda ta saba kullum powder, lipstick sai kwalli datake zizarawa a fararen idanunta. Doguwar riga ta ɗauko ta atamfa sau ɗaya ma suka taɓa sakata itada Zainab Uncle Muhammad ya kawo musu ita tare, coffee color ce atamfar da ratsin baƙi da milk daga sama ta kamata sosai ta fito da halittar ƙirjinta sosai daga ƙugun ta kuma zuwa ƙasa ta buɗe sosai tayi mata matuƙar kyau ta maƙala ƙaramar barima a kunnenta ta ɗaura baƙin agogon fata ɗaurin ture kaga tsiya tayi na malaha medium size ɗin gyale coffee tayi rolling dashi ta rataya baƙar jaka ta zura plat shoes black ta fesa turare. Masha ALLAH kalmar dana ambata kenan lokacin data gama shiryawa tayi kyau sosai Uncle Muhammad yana ƙoƙari sosai a kansu kuma baya nuna bambanci tsakanin ta da ƙanwarsa a matsayin su na ƴan University da suke shiga cikin jama’a yana ƙoƙarin yaga sun shiga mutane tsaf tsaf haka ne ma Aunt Ramlah tana yawan siya musu kayan makeup a matsayin su na ƴan mata dan ma dai ita kwalliyar bata dameta ba wannan sai Zainab ita ce ƴar kwalliya.
Fita tayi bata samu Aunt Ramlah a falo ba dan haka ta wuce bedroom ɗinta itama a bakin mirror ta sameta tana shafa mai tayi wani wankan murmushi tayi tace
“Masha ALLAH kinga yadda kikayi kyau kuwa autar Umma”.
“Kai Aunt ina wani kyau anan? nida ba kwalliya nake ba?”.
“Kwalliya ai ba ita ce kyau ba Heedayah ke kyan a jikinki yake ALLAH yasa a dace a dawo mana da suruki”. Ta ƙarasa maganar tana dariya gami da rufe robar man data gama shafawa kan mirror ɗin, baki Heedayah ta tura tace
“A’a nikam Aunt Ramlah ni gaskiya karatu zanyi yanzu na fasa auren”.
“Lallai kiyi ta kanki yarinya Baba bazai zuba miki ido kiyi wannan dogon karatun ba bakiga ni iya secondary ma akayi min aure ba kema sa’a kika ci kawai ALLAH dai ya zaɓa mafi alkhairi”. Bata amsa ba sai cewa datayi
“Zan tafi Aunt”.
1k Aunt Ramlah ta ciro a purse ɗinta ta miƙa mata ta karɓa ta fita tana yi mata sallama Nusrah dake kan bed itada Nu’aym yana mata wasa sai ɗaɗɗaga mata hannu take tanaso ta ɗauke ta kissing ɗin kumatunta kawai tayi ta fita tana dariya Aunt Ramlah na bada saƙon gaisuwa wajen Hajiya, kitchen ta shiga ta ɗauki kwandon ta fita taja ƙofar falon.
Tana fita titi tasamu napep ta shiga zuwa unguwar su Hajiya.
Ƙarfe ɗaya da kusan rabi ta shiga gidan side ɗin Alhaji Sulaiman ta fara shiga suka gaisa bata iya zuwa bata shiga sun gaisa da Hajiya Rahma ba saboda mutuncin ta itafa tana tunanin gadon mutunci familyn sukayi nunar rana ne kawai bashida mutunci (Ba ruwan Mero ????????).
Da sallama ta shiga falon Hajiya na zaune tasha kwalliyar ta cikin haɗaɗɗiyar atamfa da gani mai tsada ce taci ɗaurinta Irin na tsaffi sai ƙamshin turaren wuta falon yake wa’azi take kalla a Sunnah TV daga bakin Shiek Abdallah Usman Gadon ƙaya, murna sosai ta bayyana kan fuskar Hajiya tana amsa sallamar lokacin da Heedayah ta shiga ita har mamaki abin ya bata lallai ba ƙaramin so ƴar tsohuwar take mata ba, kusa da ita ta zauna bayan ta ajiye basket ɗin cikin dariya Hajiya tace
“Ah lallai Ramlatu ta cika alƙawari ai da baki zoba da kaina zanzo har gidan nayi biko”.
“Haba dai Hajiya”. Tace tana murmushi tareda saukowa har ƙasa tana gaisheta ta amsa cikin sakin fuska da jin daɗi tana tambayar Aunt Ramlah da yara ta amsa mata da lafiya itama tace a gaisheta daga nan ta gabatar mata da saƙon Aunt Ramlah irin farin cikin da Hajiya ta nuna tamkar ranar aka fara kawo mata taji daɗi sosai ta shiga godiya tanasa mata albarka tace ta kai mata kitchen ai yau abincin ranar ta kenan da dare ma shi zataci abinta Heedayah na dariya ta ɗauki kwandon ta nufi kitchen ta ajiye ta dawo suka cigaba da hirarsu da Hajiya.
“Nikam Hajiya ba kunun gyaɗa ne a gidan nan yau Aunt Ramlah na tsamiya tace a dama nikuma kinsan na gyaɗa ne mutumina”. Heedayah ta faɗa tana kallon Hajiya.
“Kin taki sa’a kuwa yau shi Larai ta dama mana yana nan a kitchen da zafinshi kije ki zubo”.
“Yauwa Hajiya bari inje in zuba”. ta faɗa tana miƙewa tsaye ta nufi kitchen ɗin, itama Hajiya ganin lokacin sallahr zuhr yayi ta tashi ta wuce bedroom ɗinta dan gabatar da farali.
Hajiya na shiga bedroom ɗin shikuma ya shigo falon, sanye yake cikin ƙananan kaya dark ash ɗin trouser da red color ɗin riga mai dogayen hannuwa ya matse ƙugunshi da baƙar belt ta kamfanin D&G ƙafarshi sanye cikin baƙin takalmi cover writs watch ɗin shi ma baƙi ne na fata sumar kan nan tasha gyara sai ƙyalli take zubawa, tunda ya falon ƙamshin jikinshi ya doke wanda falon yake yi ada nashi ya mamaye ko ina zama yayi ya ɗauki waya ya fara latse latse. Jin alamun motsi a kitchen yayi tunanin Hajiyan ce a ciki dan haka ya tashi kanshi tsaye ya nufi hanyar kitchen ɗin yana ƙoƙarin cusa wayarshi cikin aljihu, ta kawo kai kenan zata fito da madaidaicin mug da spoon a ciki wanda ta haɗa kunun gyaɗar a ciki dayasha madara a daidai lokacin shikuma ya kawo kai zai shiga kitchen ɗin sukayi wani mugun karo saboda ba wanda ya kula da tahowar ɗan uwansa goshinta ya bugi ƙirjinshi mug ɗin hannunta yayi kamar zai faɗi hakan yaba damar abinda ke cikin shi yayi uban fallatsi sai a jikin rigar Gashua da nata gaban rigar, a gigice ta zaro ido tana ja baya ganin wanda ke gabanta yana bin rigar jikinshi da kallo data gama ɓaci cikin ƙyanƙyami da ɓacin rai mara misali ɗagowa yayi dan ganin wace shashashar yarinya ce wannan idanunshi ya sauka cikin na Heedayah datayi tsamo tsamo jikinta na ɗan ɓari har lokacin bata gama dawowa daidai ba dan ba ƙaramin tsorata tayi ba musamman ganin wanda sukayi gwaren dashi, wani mugun kallo mai haɗe da harara ya jefa mata kafin ya nufi inda take tsaye baya ta shiga ja tana girgiza masa kai kamar zatayi kuka shikuma ya cigaba da binta fuskar nan ba alamun rahma sam a samanta tana ja baya yana ƙara kusanto ta har lokacin data kai jikin luckers ɗin kitchen ɗin ta yadda ba damar ta ɗara nan da can dole tayi surrender ta tsaya tana dafe baki sai zazzare idanuwa take irin na marasa gaskiya da alamu tsautsayi ne dama ya kawota gidan nan.
Daf da ita ya tsaya kamar zai haɗe jikinshi da nata ya tara mata hannu yana kallon mug ɗin hannunta alamun ta bashi, cikin rawar hannu ta miƙa masa ya karɓa ya ajiye shi can gefe ya juyo yana ƙara matsawa jikinta ba abinda take gani sai shi yama ɗora hannayen shi duka biyun kan luckers ɗin gefe da gefenta yayi mata rumfa yayi kane kane tako ina bata da hanyar guduwa bare tayi tunanin zillewa ta gudu fatan ta da roƙon ta a lokacin ALLAH ya jefo da Hajiya kitchen ɗin ta ceceta dan da gaske kallon mara imani take wa mutumin……

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38Next page

Leave a Reply

Back to top button