EL-HABEEB HAUSA NOVEL

Gaba d’aya sai kasuwancin Abbu ya sake dawo dashi Nigeria dan bayan dawowar tashi arzik’in nashi saiya k’ara hab’aka da d’aukaka.
Alhaji Sulaiman Gashua babban yayansu shiya bashi k’aton gida mai kyau yace yafara zama da iyalinshi anan kafin ya gina nashi yadda zaiyi nashin a nutse daga nan suka cigaba da zama anan tare dasu ya cigaba da ginin daya fara anan kusa da gidan Alhaji Adam Gashua.
Ummi batada matsalar komai sai Goggo Fatu data takura mata itada yaranta har gida take zuwa taci mata mutunci duk da bawai sanin ma metake fad’a tayi ba amma dai tasan zagine da cin mutunci, bata tab’a bari Abbu yasani ba tunda dama bata zuwa sai lokacin da baya nan ta rasa abinda ta tsare mata hantara da zagi kuwa ba wanda bata yiwa Habeeb da Mashhoodah abin baya yiwa Ummi dad’i amma batada yadda zatayi.
Makaranta mai tsada aka nemarwa su Habeeb suka cigaba da karatun su, har yanzu dai Habeeb yana nan da wannan brain d’in tashi da d’auke abu tafar d’aya.
Mrs Salees Mu’az ????
EL–HABEEB ????
©️Oum Hanan.
HASKE WRITER’S ASSOCIATION????
(Home of expert & perfect writer’s)
No 4.
Hakan yasa yana shiga school d’in sunanshi yayi fice daga malaman har d’aliban sonshi suke musamman dayake kyakkyawa balarabe wasu ma kawai kyawun nashi sukeso dan haka kowa ya shiga neman yadda zai k’ulla alak’a da Habeeb.
Zamansu cikin hausawa yasa suka fara jin hausa sosai saidai abinda ba’a rasaba. Haka zamansu ya cigaba da tafiya har Abbu ya kammala ginin daya fara suka koma ciki babban gida ne mai kyau da tsari da aka tsarashi sosai. Tun daga kan Mashhoodah Ummi bata k’ara haihuwa ba saida aka d’ebi kusan wasu shekaru biyar d’in sannan ubangiji ya nufeta da k’ara samun wani cikin sunji dad’i kuma sun yiwa ALLAH godiya daya k’addara musu samun wata haihuwar ta cigaba da rainon cikinta har zuwa lokacin data haihu ta k’ara samun wata y’a macen taci sunan Hajiya wato Karimatu sai suke mata alkunya da Nihlah, Ummi tana yawan zuwa Dubai akai akai dan kaiwa mahaifiyarta ziyara da k’aninta Muhseen.
Bayan wasu shekaru.
Habeeb ya kammala karatunshi na secondary school ya fito kuma da kyakkyawan sakamako wanda Abbu yaji dad’i sosai harya bashi zab’in irin k’asar dayake so ya cigaba da karatunshi kai tsaye yace Dubai yakeso yaje dariya kawai Abbu da Ummi sukayi a lokacin dan sunsan dalilin dayasa ya zab’i Dubai d’in bai wuce shak’uwar dake tsakaninshi da Maman Ummi ba ko ziyara zasu kai musu yafi kowa murna. Tashin farko da Abbu ya k’ara tambayar shi me yakeso ya karanta a can d’in bai wani dogon tunani ba yace irin na Abbun wato business shiyake ra’ayi, jinjina kai kawai Abbu ya dinga yi yanajin dad’i anan suka bishi da addu’ar samun nasara da sa’a shida Ummi, k’arin jin dad’in nasu ma yaron nasu basai ya zauna a Hall ba tunda ga gidansu Ummi shikam gida yaje ai karatun.
Tun daga lokacin Abbu ya shiga yiwa Habeeb shirye shiryen tafiya Dubai shiri yake masa sosai har lokacin tafiyar shi yayi ya d’aga zuwa k’asar Dubai cikeda jin k’warin gwiwar yin abinda ya kaishi k’asar.
Fatan nasara HABEEB GASHUA.
Gidansu Ummi nan ya sauka daga nan yake zuwa school d’in har lokacin bashida yawan magana miskili ne sosai badai ka ganshi yana hira yana raha da mutane ba saidai ya keb’e kanshi kullum cikin karatu yake d’alibai dayawa a makarantar sunyi zaton kurma ne gashi ba wanda yake kulawa yafi gane yayi zamanshi shi kad’ai wani d’an Nigeria ne da suka shiga makarantar kusan lokaci d’aya Auwal Mahmood Azare shiya dinga shige masa yanason suyi abota da Habeeb d’in farko sam baya kulashi saidai yazo ya zauna a inda yake ya k’araci surutunshi amma uffan Habeeb bazaice masa saidai yagaji ya tashi sai daga bayane sannan ya fara d’an kulashi shima bawani sosai ba baya baya.
Ya cigaba da karatunshi cikin kwanciyar hankali da nutsuwa su Abbu na yawan kawo masa ziyara shima kuma idan suka samu hutu yana zuwa ganin gida.
A gurguje.
Bayan wasu shekaru Habeeb ya kammala karatunshi cikeda tarin nasarori wanda hatta makarantar saidata bashi lambar yabo ta jinjina masa kuma. Akwai babban kamfani a k’asar wanda suke kasuwanci da k’asashe daban daban su suka rok’i alfarmar ya zauna yayi aiki dasu tun a lokacin kai tsaye baice musu zaiyi ba bai kuma bazaiyi ba yace dai zaiyi shawara da iyayenshi duk abinda suka zartar shi zaiyi.
Bayan dawowar shi yasamu Abbu ya sanar dashi abinda kamfanin sukace Abbu yaso Habeeb ya zauna yayi aiki a nashi kamfanunuwan ya taimaka masa amma abin alfaharinshi ne ace yaronshi yana aiki a wancan kamfanin na Dubai dan ya sanshi babban kamfani ne sosai kuma a hakan ma su suka nemi dayayi aiki dasu gaskiya yaron nashi mai sa’a ne dan haka kawai ya umarci Habeeb d’in ya koma yayi aiki dasu d’in ALLAH ya taimaka.
Bayan ya d’an huta ya k’ara shiryawa yayi sallama da iyaye da abokan arzik’i ya k’ara komawa Dubai da shirin yin aiki.
Sunji dad’in komawarshi sosai suka bashi gida da had’add’iyar mota mai tsada ya amshi motar dai gidan kam yace yanada inda zai zauna ga k’aton office d’inshi dayaji kayan alfarma bashi dai da matsalar komai alhmdulillah nan da nan ya k’ara fasowa gari tuni y’anmatan larabawa suka fara kai masa hari saidai ko a kwalar rigarshi ba abinda yasha masa kai ko kallo basu isheshi ba hakan yasa wasu dayawa suke ganinshi mai bala’in girman kai da fariya wanda kuma a zahiri ba haka bane kawai dai shi haka ubangiji ya halicceshi sam bai cika son shiga cikin jama’a ba yafiso ya dinga kad’aicewa shi kad’ai gashi bayason surutu ko hayaniya.
Su Ummi sunso zuwa bayan yafara aikin kasancewar sun d’an kwana biyu basuje ba saikuma taji bikin k’aninta Muhseen da za’ayi ya kusa dan haka suka hak’ura sai lokacin da za’ayi bikin sannan sukaje wannan karon harda Hajiya Inna aka tafi suka sha bikin Muhseen da amaryar shi Abeedah, daga nan suka wuce sukayi umrah sannan suka dawo Nigeria.
Bayan dawowar su da y’an watanni ne akayi bikin Mashhoodah inda tasamu mijin cikin y’an uwa dan babban d’an Alhaji Adam ne Musaddeeq wanda tun dawowar su k’asar bayan tafara girma yaji yarinyar ta shiga ranshi sosai baidai bayyana bane sai data kai munzalin fara saurarar samari sannan ya fito ya shiga cikin jerin y’an takara kuma ALLAH yayi shine mijin nata akasha biki iyaye da y’an uwa kowa na murnar wani zumunchin da aka k’ara had’awa. Goggo Fatuu taso wargatsa al’amarin amma ALLAH bai bata iko ba gashi dangi kowa yayi mata caa hakan yasa tayi shiru ta daina sukar lamarin.
“Baifi shekara d’aya da fara aikin ba ALLAH ya yiwa Abbu rasuwa, mutuwar data tab’a mutane da dama kasancewar shi mutumin kirki ga taimakon al’ummar musulmi marasa k’arfi duk inda gidan marayu suke yakan sa a nemosu dan ya taimaka musu, katsam sai waya Habeeb yaji wai Abbunshi ya rasu zuciyarshi ta girgiza k’warai da gaske da wannan labarin daya samu saiya dinga tuno irin wayoyin dasuke dashi a kwanakin kullum magana d’ayace dai ya dinga taimakon na k’asa dashi ya taimaki marayu dan su d’in masu rauni ne suna buk’atar masu kulawa dasu zuciyarshi ta k’ek’ashe ko d’igon hawaye babu sai kukan zuci dayake wanda yafi na fili dan a ganinshi shi akayiwa rasuwar saboda shi yayi rashin mahaifi mai sonshi da k’aunarshi, har a lokacin Goggo Fatu ta samu abinyi ganin a gabanshi aka fitar da gawar Abbu amma ba d’igon hawaye a idanunshi wai dama zubin marasa imani da tausayi gareshi amma mahaifinka ya mutu ka gaza yin kuka kamar yin kukan shi zai dawo da mutum babu wanda yabi ta kanta a lokacin kowa na cikin alhinin mutuwa.