EL-HABEEB HAUSA NOVEL

Bayan rasuwar Abbu da d'an wani lokaci Habeeb ya koma bakin aikinshi cikeda kewar Abbunshi shikenan sun zama marayu a yanzu, gaba d'aya sai Ummi tazama abar tausayi a lokacin takan tuna irin zaman da sukayi dashi cikin kwanciyar hankali da mutunta juna shikenan kuma tasan tayi rashin da har abada bazata maye gurbinshi ba a yanzu gidan daga ita sai Nihlah.
Kamar yadda addini ya tanadar idan mutum ya mutu za’a raba gadonshi haka akayi Abbu ma anyi rabon gadonshi an fitarwa da mahaifiyarshi nata kason sannan y’an uwanshi saikuma iyalanshi hak’ik’a Abbu ya tara dukiya mai tarin yawa ga kadarori inda kowanne saidaya samu kaso mai tsoka cikin abinda aka bashi cikin abinda aka bawa Habeeb da k’annenshi harda babban kamfanin Abbun wanda yafi kowanne kamfani ne dayake had’a cinikayya tsakanin k’asashe gefe d’aya kuma akwai masarrafar k’arfe duk a cikin kamfanin dad’in dad’awa kuma k’aton gidan da suke ciki wanda Abbun ya gina a unguwar Nassarawa G.R.A shima mallakinsu ne sun samu tarin alkhairi dayawa wanda wannan duk baya gaban Habeeb.
Dole ya ajiye aikinshi yadawo Nigeria dan cigaba da kula da wannan kamfanin da sauran abubuwan da aka bar musu, sosai wancan kamfanin na Dubai yaji ba dad’i sunyi bak’in cikin rabuwa dashi dan fara aikinshi a kamfanin ba k’aramin alkhairi yajawo musu ba da k’ara yin suna kullum cikin kawo sabbin dabaru yake ta kwanyar da ALLAH ya bashi ta yadda kamfanin zai k’ara hab’aka kuma suna ganin cigaba sosai hakan yasa lokacin dazai bar aiki masu kamfanin suka yimasa gagarumar kyauta ta kud’i tsabarsu farko ma cewa yayi bayaso bazai karb’a ba saida suka takura masa shima daya tashi ba duka ya amsa ba ya ciri wani abu ya maida musu sauran dan a ganinshi kud’in sunyi yawa.
Bayan dawowar shi yasa aka k’ara gyara kamfanin ya fito ana zamani sosai aka k’ara samun gogaggun ma’aikata aka zuba yafara aiki, Mujaheed shiya d’auka a matsayin P.A d’inshi wato personal assistant manager Mujaheed d’an k’anwar Abbu ne wadda take binshi a haihuwa Hajiya Aisha kuma dama a kamfanin yake aiki yasan takan aikin sosai, bama shi kad’ai ba akwai y’an familyn Gashua dayawa dasuke aiki anan.
Ummi taso ta koma k’asarsu Hajiya Inna ta rok’i alfarmar ta zauna dasu saboda matuk’a take k’aunar Ummin har cikin ranta tanajin dad’in zama da ita k’warai da gaske, tsananin girma da mutuncin Hajiya Inna da Ummi ke gani yasa ta amince bazata iya yimata musu ba saitaga kamar ko dan babu ran d’anta ne amma tabbas taso tafiya tunda bataga zaman dazatayi a nan d’in ba.
Alhaji Sulaiman Gashua shima yadawo kusa da gidan Abbu anan ya tamfatsa gida suka dawo shida iyalanshi da Hajiya Inna dama tana gidanshi.
Har a yau bakin Habeeb bai daidaice da hausa ba magana d’aya zaiyi zaka fahimci ba zallar bahaushe bane a hakan ma Auwal Mahmood Azare wanda sukayi karatu tare shiya taka muhimmiyar rawa wajen koya masa hausa tunda dangin ubanshi hausawa ne so dole watarana zai zauna a cikinsu kamar yasan hakan zata faru kuwa saigashi yadawo cikin nasu dayake yanada brain saiyake d’auke komai duk da yadda hausar take masa wahala amma yana k’ok’arin yinta sosai saidai maganar tashi ce abin dariya idan yanayi shiyasa sau tari suke fad’a da MJ idan yaji yana magana da hausa yayi ta masa dariya shikuma ya hau yaita masa masifa. Ita kanta Ummin har yanzu fama take itama tana magana zaka ganota Nihlah kam dama y’ar garin hausawa ce da hausa ta taso a bakinta dan ma dai tun tana k’arama Ummi tana yawan yimata larabci hakan yasa ta tashi da wasu abubuwan sosai kuma tanajin duk abinda aka fad’a mayarwar ne wani lokacin yake gagararta.
M&S????
SABON SALO SABUWAR TAFIYA…..????
TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B
INA KUKE MAKARANTA??
INA KUKE MASOYA? INA KUKE MAKARANTA LITTATTAFAN HASKE WRITERS??? KU MARMATSO ????️
SABON SALON Namu NA DABAN NE, SABON TAKUN NAMU MAI KAYATARWA NE MAI FADAKARWA MAI ILIMANTARWA MAI GIGITARWA ABANGARAN SOYAYYA, ZAKU KOYI SALO DABAN DABAN DA ILIMI TA BANGARE DA DAMA, SOYAYYAH MAI GIGITA ZUCIYA MAI SAKA NUTSUWA….
TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B
INDA ZAKI KWASHI GARABASAR KARATUN LITTATTAFAI MASU ‘DINBIN FADAKARWA DA SAKA NISHA’DI HAR GUDA BAKWAI.
1- KAUNA CE
NA UMM ASGHAR
2- RUKUQI
NA FEEDHOM
3- WANI SO
NA ZEE YABOUR
4- SO DA ALAKA
NA UMMI AISHA
5- MUGUN GANI
NA SADIYA NASIR DAN
6- ABDUL_HAMEED
NA NANA DISO
7- MUKULLIN ZUCIYA
NA MAMAN KHADY
Daya 200
biyu 400,
guda uku 500
Guda hudu 700
Guda biyar 750
Shida 800 bakwai 1000 da programs
DOMIN MALLAKAR NAKI ZAKI BIYA
(1000) DUBU DAYA KACAL
KAI KA KAI….!
TIRQASHI, DUKA FA WANNAN GARA’BASAR ZA’A BAKU ITA AKAN N1000 KACAL, GA KUMA SHIRYE-SHIRYE HAR GUDA UKU DA ZAMU KOYAR DOMIN YABAWA, JINJINAWA DA KUMA FARANTAWA AGAREKU MASOYAN MU…
1- SHIRIN KOYAR DA GIRKE-GIRKE DOMIN ZUZUTA MAIGIDA????
DAGA CHEF RAHMA NA LELE
2-SHIRIN KOYAR DA YANDA ZAKI TSAFTACE JIKINKI, DA YANDA ZAKI ZAMO CIKIN KAMSHI A KODA YAUSHE WANDA ZAKI HAD’A DA KANKI ACIKIN GIDANKI DOMIN MAQALEWA A ZUCIYAR MAIGIDA
DAGA AYUSHER MUH’D
3-SHIRIN KOYOR DA YANDA ZAKI IYA HADA KAYAN NI’IMA A JIKINKI CIKIN SAUKI DOMIN GYARAN GIDAN AURENKI DA ZAMOWA FITILAR GIDANKI
DAGA HAJJA CE ????
MASHAA ALLAH DUKA FA AKAN NAIRARKI DUBU DAYA KACAL ZAKI KASANCE ACIKIN GROUP DINNAN
GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB’ASAR TAMU ZAKU IYA TURA KU’DINKU (N1000)TA WANNAN ACCOUNT????????
2083371244
ZENITH BANK
AISHA M. SALIS
SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR????????
+447894142004
IDAN KUMA KATIN WAYA NE, ZAKU TURA TA WANNAN LAMBAR????????
07065283730 da Shaidar biya duk ta ciki
GA MUTANENMU NA QASAR NIGER???????? ZAKU IYA TURA KUDINKU TA NITA, AMANA, ALI’ZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR????????
+227 96 91 36 36 RAHINA daga niamey.
MUN GODE.
TOP TEN TAKUN HASKE BATCH B 2022
Wannan garabasar tamai rabo ce???????????????? sa kud’i kad’an ki debi hani’an????????
EL–HABEEB ????
©️Oum Hanan.
HASKE WRITER’S ASSOCIATION????
(Home of expert & perfect writer’s)
No 5.
Haka zatayi ta bak’in rai musamman idan taga Aunt Mashhoodah tazo sun zauna da Ummi sunata hira tunda ita bawai komai ne take jiba.
Back to story.
KATSINA.
K’ofar K’aura.
Madaidaicin d’aki ne wanda aka lailayeshi da siminti sai ledar tsakar d’aki da aka malaleshi da ita sai k’aramin fridge da y’ar k’aramar TV ta jikin bango kallo d’aya dai zaka yiwa gidan ka gano na masu rufin asiri ne da wadatar zuci.
Yarinya ce y’ar kimanin shekara sha bakwai zaune cikin d’akin a kan tabarma sai faman kuka take tamkar ranta zai fita sai wata dattijuwa zaune a gefenta d’aya gefen kuma wata matashiya ce wadda bazata wuce haihuwa d’aya zuwa biyu ba sun sata a tsakiyarsu kukanta take bilhaqqi da gaskiya duk da irin rarrashin da suke mata kuwa amma sai k’arawa kukanta volume take kamar wadda ake yankar naman jikinta.
Wannan matashiyar ce ta dafa kafad’arta a karo na ba adadi tun zamansu a wajen cikin sanyin murya da son yin rarrashi tace
“Haba HEEDAYAH dan ALLAH kiyi shiru haka kar kiyi ciwon kai, tun d’azu fa kike kukan nan ki sassautawa ranki haka mana addu’arki Kabeer yake da buk’ata a halin yanzu ba kukanki ba Kabeer ya mutu kuma muna masa kyakkyawan zaton samun rahmar ubangiji kiyi hak’uri dan ALLAH”.
Cikin shasshek’ar kuka tace
“Aunt Ramlah shikenan fa nida Yah Kabeer mun rabu har abada bazan k’ara ganinshi ba taya zansamu kamar Yah Kabeer Aunt Ramlah? mutumin da tun ina y’ar tatsitsiyata yake dako da d’awainiya da sona yake wahalta min duk d’an abinda ya samu a kaina yake k’arewa koyaushe farin cikina shine nashi taya ba zanyi kuka ba”. Ta k’are maganar tareda fad’awa jikin dattijuwar dake gefenta tana cigaba da kukanta itakuma ta shiga jijjigata tana shafa bayanta alamun rarrashi, lallai dole Heedayah tayi kukan rashin Kabeer ya sota ya nuna mata k’auna duk da irin tarin k’alubalen daya dinga fuskanta daga wajen danginshi da mahaifiyarshi akanta saboda wani dalili wanda basa son had’a auratayya tsakanin d’ansu da ita wanda ita kanta yarinyar bata san dashiba kuma batasan akanme suke nuna mata k’iyayyar ba, saura kwana bakwai bikinsu ALLAH yayi masa rasuwa sakamakon accident din daya samu akan hanyarshi ta zuwa Kaduna inda yake sana’ar shi ko shurawa baiyiba ubangiji ya d’auki abinshi yau kusan sati biyu kenan da rasuwar tashi amma har yanzu Heedayah bata bar yin kukan rashin shiba sosai rasuwar tashi ta bugeta kullum cikin kuka da sambatu duk da rubutun dangana da Malam ke amso mata wajen malamin da suke d’aukar karatu bayan sallahr magreebah abin harya fara bawa Umma tsoro, cikeda tausayawa Aunt Ramlah tace
“Nikam Umma wata shawara mana mezai hana mutafi da Heedayah can Kano ta d’anyi nisa da garin nan ko yayane maybe ta d’an samu salama ta daina yawan tunanin shi amma sai abinda kukace Umma”.
Shiru Umma tayi tana nazarin maganar Ramlah to amma saidai ba lallai bane Malam ya amince ganin ita kad’ai ce a gabansu shi Mustapha ba’asa lissafi dashi shi namiji ne saisu yini ma basu sashi a idonsu ba yana can wajen sana’ar shi ta d’inki.
“Umma ya kikayi shiru ko baki amince bane”. Aunt Ramlah tace tana marairaice murya.
Zama Umma ta gyara tareda k’ara gyarawa Heedayah dake jikinta kwanciya tace
“To ai ni kad’ai bazan yanke hukunci ba Ramlah, tunda ba yaune tafiyar taki ba kibari zuwa anjima idan Malam yadawo saiki tambayeshi idan ya amince ai bawani abu bane saiku tafi taren indai hakan zai samar mata nutsuwa da kwanciyar hankali”.
“Insha ALLAHU ma zai yarda Umma ai hakan saiyafi kinga nan fa tana fita ga gida ga gida ko bataso indai zataga gidansu saiya tuna mata dashi”. cewar Aunt Ramlah.
Kai kawai Umma ta jinjina ta maida kallonta kan Heedayah da kanta ke kan cinyarta tace
“Zakibi Auntyn ki gidanta Heedayah?”.
“Ni Umma banaso inyi nesa dake idan natafi fa bakowa saike kad’ai shi Yah Mustapha ba ganinshi akeba”. Murmushi Umma tayi tana k’ara jin tausayin yarinyar na shigarta, kanta ta shiga shafawa tana fad’in
“Ba komai Heedayahta indai kinason zuwa kije kinji ALLAH yayi miki albarka yabaki miji nagari kije famfo ki wanke fuskarki kizo kici abinci kinga duk yau baki sawa cikinki komai ba”. Amsawa Umman tayi tana k’ara share hawayen idanunta ta tashi ta fita tana gyara d’aurin d’ankwalin ta, duk da kallon tausayi suka bita harta fice kowanne yana k’iyasta halin dazata samu kanta duk ranar datasan ita d’in WACECE ?.
Kamar yadda Umma tacewa Aunt Ramlah ta tambayi Malam idan ya yarda hakan akayi kuwa bayan yadawo sallahr Esha’e yaci abinci ya huta taje ta sameshi da maganar da farko dai k’in amincewa yayi sai data dinga faman magiya sannan ya amince cikin murna da farin ciki take masa godiya ta d’ora da fad’in
“Kaga Baba tunda ga yadda ta kasance idan mukaje sai a samar mata makaranta ta cigaba kafin ALLAH ya kawo mata miji tayi aurenta”. Kai kawai ya jinjina mata yace
“ALLAH yasa hakan shine mafi alkhairi”.
Da ”Ameen” ta amsa sannan ta tashi tabar wajen.
Washegari da daddare Heedayah tana shirya kayanta na tafiya tanayi tana kuka tana k’ara tuna masoyinta ashe babu rabon suyi aure kullum buri da mafarkinsu su mallaki junansu a matsayin ma’aurata ashe babu rabon hakan watannin bikinsu ma da akasa yaji yayi masa yawa haka yaje ya tasa babanshi a gaba yanata masa magiyar dan ALLAH yasamu Malam suyi magana a rage shi wllhy watannin sunyi masa yawa hakan akayi kuwa shima baban nashi ya biye masa yasamu Malam sukayi magana aka sauko da bikin har Mustapha yayanta yanata zaginshi a lokacin wai bashida kunya dayake abokinshi ne, dariya kawai yayi masa a lokacin yana masa gwalo, batasan lokacin data k’ara fashewa dawani irin kuka ba ragowar kayan ma sai Umma ce ta k’arasa shirya mata su.
Washegari wajen k’arfe sha biyu na rana direban Aunt Ramlah yazo d’aukarta, tunda Heedayah taga dai gadan gadan tafiyar za’ayi har ansaka kayansu a mota tafara kuka ta rirrik’e Umma kamar wadda akace idan tatafi bazata k’ara dawowa ba da k’yar Aunt Ramlah ta jata suka fita ko sallama basuyi da Umman ba, bare da suka fito ta kalli gidan su Kabeer saita k’ara fashewa dawani kukan kawai tana tuno irin rayuwar da sukayi dashi mai dad’i shikenan yanzu mai rabawa ta raba saita k’ara tuno yadda idan yazo ganin gida duk ranar dazai koma Kaduna wajen kasuwancin shi haka zatasa masa kukan shagwab’a ita bataso yatafi ya barta haka zai lalace wajen rarrashin ta har sai yaga yasata dariya sannan zai iya tafiya yabar wajen ko wane irin sauri yake kuwa, yau gashi yayi doguwar tafiyar da har abada bazai k’ara dawowa ba bare tace zasu had’u watarana.
A hanya ma saida Aunt Ramlah tayi ta faman rarrashi sannan tasamu tayi shiru daga baya ma barcine ya d’auketa a jikin Aunt Ramlah.