EL-HABEEB HAUSA NOVEL

EL-HABEEB HAUSA NOVEL

★★★
Habeeb ne da Mujaheed zaune a kyakkyawar harabar gidansu Habeeb d’in kusa dawasu shuke shuke masu ban sha’awa da k’ayatarwa kan wasu kujeru na gini sai table da aka had’a shima da abinda akayi kujerun, soft drink’s ne kala kala akai da fruits a yayyanke a plate plate anyi wrapping d’insu da leda.
Habeeb sanye yake cikin riga mai gajeren hannu da wando red color marasa nauyi na kamfanin Adidas wanda sukayi matuk’ar haskashi kasancewar shi fari, Mujaheed kuma manyan kaya ne a jikinshi riga da wando na maroon shadda, kowanne kanshi a sunkuye yake da waya a hannunshi hakan yasa babu mai magana a cikinsu kowa hankalinshi nakan waya can kuma Mujaheed yaga Habeeb ya daina kallon wayar ya k’urawa wata k’aramar bishiya ido kamar wanda yake son lissafa ganyen jikinta kallonshi yake tayi amma sam baisan yanayi ba da alamu yayi nisa cikin duniyar tunani.
“Gashua”. Mujaheed ya ambaci sunanshi cikeda mamakin meye damuwarshi haka?
a hankali ya maida kallonshi kan Mujaheed daya kira sunanshi.
“Are u okay?” Mujaheed ya tambaya.
Saidaya sauke wani nannauyan numfashi sannan yace
“Yes I’m fine”. yace yana zame tattausan slippers d’in k’afarshi ya mik’eta kan table d’in ya maida kanshi kan wayar.
“Banga alamun hakan ba Gashua, yaushe kafara b’oyemin damuwarka? kanaso mufara y’ar haka ne a tsakaninmu ko? kokuma baka yarda dani bane kai kanka kasani bana b’oye maka komai daya shafeni duk wani sirrina na fili dana b’oye kasani Gashua dan me kai kake k’ok’arin b’oyemin bayan kuma nasan akwai wani abu”.
Ido Habeeb ya lumshe yakai hannu yana yamutsa lallausar sumar kanshi kafin ya bud’e ido ya kalli Mujaheed dake kallonshi cikin sanyin murya yace
“MJ, na dad’e a cikin wannan halin tun abin baya damuna yanzu yanaso yayi tasiri a kaina, shiru ya d’anyi kafin ya cigaba da fad’in
“Mafarki nake MJ”.
“Mafarki kuma? kamar yaya Gashua?”. Mujaheed yace cikin mamaki yana kallon Habeeb dake shafa sajen fuskarshi.
“Mafarkin mace”. yabashi amsa kai tsaye batare da tunanin Mujaheed zai fassara maganar ba, cikin matse dariya Mujaheed yace
“Kuna wani abune a cikin mafarkin?”.
Kallon zanci ubanka Habeeb ya jefa masa yace
“Kullum tana zuwa min ne fuskarta a rufe da mayafi saitazo zata bud’e sai in farka narasa yadda zanyi I’m confused MJ”. ya k’arasa maganar yana d’an girgiza kai da cije lips d’inshi na k’asa.
“Tun yaushe kenan?”. cewar Mujaheed.
“Five years”. Habeeb ya bashi amsa. Ido Mujaheed ya zaro yace
“Five years fa kace Gashua? hod’ijam inji fulani gaskiya ya kamata ka tashi tsaye da addu’a indai hakane koma wacece ita ALLAH ya bayyana mana ita tafito fili mu ganta ra’ayul aini bata dinga zuwa cikin mafarki tana susuta mana Boss d’inmu ba koya kace mutumin?”. Banza yayi masa bai kulashi ba Mujaheed yace
“Kokuma wajen masu fassarar mafarki zamuje a fassara mana abinda mafarkin yake nufi?”.
“No, kamar dai yadda ka fad’a d’in zan cigaba da addu’ar amma idona idon yarinyar nan saina hukuntata dan ba k’aramin wuya take bani ba”. yace yana cije lips d’inshi gamida shafa kwantaccen sajenshi.
Dariya sosai Mujaheed ya fashe da ita yace
“How? kaida har yanzu bakaga face d’inta ba ta yaya zaka iya ganeta a fili? kaidai kawai kayi addu’a Gashua kar a kauce hanya ta mafarkin”.

Maryam Ibraheem Aleeyu
Mrs Salees Mu’az ????

EL–HABEEB????

©️Oum Hanan.

HASKE WRITER’S ASSOCIATION????
(Home of expert & perfect writer’s)

Ina mik’a sak’on ta’aziyya ta ga Ummi Aysha dama k’ungiyar mu ta HASKE na rashin mahaifiya datayi ALLAH ubangiji yaji kanta yayi mata rahma yasa aljannace makoma yabawa iyalanta hak’urin rashi ya kyautata namu k’arshen yaji kan dukkan musulmai baki d’aya.

No 6.

A fusace Habeeb ya d’ago ya kalleshi jin yadda yake tamasa fatan kusantar yarinyar duk da a cikin mafarkin ne, cikin harshen shi na hausa da har yau bai gama daidaita ba yafara masa masifa dan duk miskilancin shi idan aka tab’oshi haka yake zagewa yayita bala’i kamar bashine maganar ma take masa wahala ba.
Tsaki Mujaheed yayi yana dafe goshinshi yace
“Ka taimakeni ka daina min masifa da hausa Gashua, ka dinga yimin da turanci yadda zan dinga ganewa amma ni wllhy wannan rub’abb’iyar hausar taka bawani fahimtar ta nakeba kuma kace lallai lallai sai kayi”. Sosai Habeeb ya k’ara shak’a tsaki yaja ya mik’e ya zura slippers d’inshi ya d’auki wayarshi yabar wajen Mujaheed ya bishi yana masa dariya da kiran sunanshi amma ko juyowa baiyiba bare ya kulashi ya shige part d’inshi dake cikin harabar gidan wanda shima zaman kanshi yake dan kamar wani k’aramin gidan ne saboda girman shi.

Kano.
Rijiyar zaki.
A y’an kwanakin da Heedayah tayi a gidan Aunt Ramlah tafara jin dad’in zaman gidan k’warai kuma damuwarta tafara raguwa ta rage tunanin Kabeer ba kamar lokacin datake Katsina ba musamman daya kasance akwai k’anwar mijin Aunt Ramlah d’in a gidan Zainab wadda suke kusan sa’anni da ita saidai Zainab d’in zata d’an girme mata bayan tagama secondary school ya d’aukota tadawo gidanshi da zama da nufin sama mata gurbin karatu a jami’a wanda bayan zuwan Heedayah shi mijin Aunt Ramlahn Uncle Muhammad ya yanke shawarar samar musu tare Aunt Ramlah tayi ta godiya.
Cikin d’an zaman da sukayi suka saba sosai da Zainab ita kanta Zainab d’in sai yanzu zaman gidan yake mata dad’i sab’anin da daga ita sai yaran Aunt Ramlah Nusrah babbar school take tafiya tahfeez tun safe sai yamma sai d’ayar dataci sunan mamansu suke kiranta da Hajiya itakam batafi shekara d’aya bama goyonta ake shiyasa gidan duk yake mata ba dad’i yanzu kam da Heedayah tazo tasamu abokiyar hira.

Ba'a d'auki dogon lokaci ba Uncle Muhammad ya samarwa Heedayah da Zainab gurbin karatu a YUSUF MAITAMA SULE UNIVERSITY  kusa dasu, sunyi murna sosai suka sameshi sukayi masa godiya.

Nan da nan suka fara zuwa d’aukar lecture, Heedayah ta k’ara kyau farinta ya k’ara fitowa sosai Uncle Muhammad yayi musu sabbin d’inkuna da dogayen riguna saboda shiga school ba abinda zata cewa bawan ALLAHn nan saidai ALLAH ya saka masa da alkhairi yasa yagama da duniya lafiya yanada matuk’ar kirki da sanin ya kamata aikuwa ya k’ara fito dasu sosai suke d’aukar wanka idan zasu tafi kuma bana rashin hankali ba dan yawanci ma sunfi using da hijabs irin na yayin nan da akeyi kuma ba ruwansu da shiga shirgin kowa kawai abinda ya kaisu sukeyi.

Uncle Muhammad d’aya daga cikin yaran Alhaji Sulaiman Gashua ne a kasuwa kuma yana jidashi da mutunta shi saboda rik’on gaskiya da amanarshi.
Yauma weekend Aunt Ramlah da yaranta dasu Heedayah suka shirya tsaf dan zuwa gaida Hajiya Inna mahaifiyar Alhaji Sulaiman dama kuma Aunt Ramlahn tana zuwa jefi jefi wajen iyalan Alhaji Sulaiman d’in dakuma wajen Hajiya kuma tasu tazo d’aya da Hajiyan.
Saida Aunt Ramlah lafiyayyen dambun tsaki dayaji gyad’a da zogale sanin yadda Hajiyan ke matuk’ar sonshi ga kuma had’add’en zob’o dayaji kayan had’i wanda shima tasan mutumin Hajiyan ne suka tafi mata dashi.
Uncle Muhammad d’in ne ya kaisu da kanshi ya saukesu ya wuce, b’angaren Alhaji Sulaiman d’in suka fara shiga aka gaggaisa suka d’an tab’a hira da uwargidan shi Hajiya Rahma sannan suka nufi b’angaren Hajiya wanda yake duk a cikin gidan.
Sosai Hajiya tayi murna da ganinsu ta shiga yimusu sannu da zuwa kamar zata goyasu saboda yadda take musu dan taji dad’in zuwansu sosai dama Aunt Ramlah ta saba dan duk lokacin datazo irin tarbar datake mata kenan akwaita da karrama bak’o.
Zama sukayi aka shiga gaggaisawa sannan Aunt Ramlah ta bata abinda tazo mata dashi, aikuwa tasha addu’a daga nan suka shiga hira cikin hirar ne Hajiya Inna ke tambayar Aunt Ramlah ina tasamu kyakkyawar yarinya haka dayake tasan Zainab sun tab’a zuwa sau d’aya da Aunt Ramlah.
Murmushi Aunt Ramlah tayi tace
“K’anwata ce Hajiya”.
“ALLAH sarki takawo miki ziyara kenan?”. cewar Hajiya.
“Wallahi Hajiya saurayin ta dazata aura ne ALLAH yayi masa rasuwa sakamakon accident dayayi ana saura sati d’aya biki ta shiga halin damuwa kullum cikin koke koke to shine zuwan nan danayi na k’arshe muka taho tare to gashi ma har Abban Nusrah ya samar musu makaranta sun fara zuwa itada Zainab”.
Kai Hajiya ta shiga girgizawa cikeda tausayawa tace
“ALLAH sarki, ALLAH yaji k’anshi yayi masa rahma itakuma yabata wani mafi alkhairi”.
Da “Ameen” Aunt Ramlah da Zainab suka amsa yayin da idanun Heedayah suka cika da k’wallah saboda wani abu dataji ya taso mata game da mutuwar Kabeer, a hankali tasa gefen mayafinta ta goge batare da kowa ya lura ba sai Hajiya data ganta tausayinta ya k’ara kamata lallai dagani ba k’aramin so takewa wannan saurayin nata ba lokaci d’aya taji yarinyar ta shiga ranta sosai.
“Malam Muhammad da k’ok’ari an bar muku ne gaba d’aya har dasata a makaranta?”. Hajiya ta fad’a cikin dariya.
Dariya sukayi gaba d’ayansu, cikin dariya Aunt Ramlah tace
“Hajiya ai tunda tafara karatu dole abar mana ita gaba d’aya Hajiya”.
“A’ah kunso yin dai k’wace kawai”. cewar Hajiya tana dariya, nan suka cigaba da hirarsu dayake Hajiya akwai raha haka tayi ta sasu dariya. Sunci sunsha daga abinciccikan da aka aiko musu daga part d’in Alhaji Sulaiman dayake itama Hajiyar daga can ake kawo mata dambun da Aunt Ramlah takai mata shi taci abinta batabi takan fried rice d’in da akayi ba, gashi komai ta wawuro ta mik’o musu irin abunsu na tsaffi gaskiya Hajiya akwai mutunci abinda Heedayah ta dinga fad’a kenan a cikin ranta.
Anan sukayi sallahr magreebah sannan Uncle Muhammad yazo, bayan sun gaisa da Hajiya suka tafi bayan sun shiga sun yiwa Hajiya Rahma sallama tayiwa su Heedayah kyautar kayan makeup su Nusrah kuma biscuits, chocolate dasu sweet’s itama kam akwai mutunci ta fahimci kamar haka familyn suke gaba d’ayansu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38Next page

Leave a Reply

Back to top button