EL-HABEEB HAUSA NOVEL

Tun daga xuwan da sukayi shak’uwa ta shiga tsakanin Hajiya Inna da Heedayah kamar irin sun dad’e d’in nan tare ko bata jeba tayiwa Aunt Ramlah waya tace ta turo mata Heedayah wani lokacin ma daga school suke wucewa itada Zainab.
★★★★★★
Ranar asabar da yammaci lik’is bayan sun taso daga islamiyyar da suke zuwa Aunt Ramlah ta aikesu gidan wata k’awarta zasu karb’o mata sak’o, layi d’aya ne a tsakaninsu ba nisa gidan dan haka a k’afa ma suka shiga takawa suna hirarsu gashi dama layin irin dogon nan ne kuma sam ba yawaitar mutane a layin ko ina shiru.
Heedayah atamfa ce a jikinta riga da siket purple color da bak’i sai hijab kalar atamfar iya gwiwarta mai hannu, itakuma Zainab doguwar rigace pink color tayi rolling da mayafin rigar a hankali suke takawa kamar masu tausayin k’asar.
Tsadaddun motoci ne guda uku bak’ak’e wuluk suka shigo cikin layin da wani irin matsiyacin gudu sukayi kan su Heedayah kamar zasu bankesu ga uban horn dasuke ta dannawa kamar zasu tashi unguwar hakan ya gigita su Heedayah suka rasa inda zasu nufa duk suka diririce ta gefensu sukazo sukabi a tsiyace kamar zasu tashi sama, wani takaici ne ya kama Heedayah ga gabansu dake ta fad’uwa daga ita har Zainab d’in batasan lokacin data tsuguna ta rarumi dutse a k’asa ba ta cillawa motocin duk da irin yadda Zainab take rik’e hannunta dutsen nan bai tsaya ko ina ba sai a bayan motar dake tsakiya wanda hakan yasa dole mai tuk’a motar ya taka birki ba shiri shima na bayanshi ya tsaya na gaban nasu ma ganin sun tsattsaya yasa shima ya tsaya.
Banda dukan uku uku ba abinda zuciyar Heedayah da Zainab keyi tamkar tayi tsalle ta fito waje tsabar tsoro amma saboda k’arfin hali irin na Heedayah haka ta tunkari motocin tun ma kafin taga suwaye zasu fito daga ciki, tsananin tsoro yasa Zainab takasa ko motsawa bare tayi yunk’urin hanata zuwa sai tai tsaye tana kallon Heedayah data tunkaresu lokacin duk sun fiffito daga cikin motar kowanne cikin bak’ak’en suit.
Tun kafin ta k’arasa tafara d’add’aga hannaye tana musu masifa da bala’in makafi ne su dazasu buge mutane kokuwa dai shaye shaye sukaje sukayi yasa suke gudun rashin hankali da tarbiyya a unguwar mutane?. gaba d’ayansu sukayo kanta da nufin gyara mata zama musamman Aliyu babban bodyguard d’in da harya d’aga hannu da nufin kifa mata mari saikuma yaji muryar maigidan nasu wanda shi sai yanzu ne ya fito daga cikin motar.
“Stopped Aleeyuh”. ya fad’a cikin tattausan sound d’inshi kuma cikin wani salon magana mai dad’i, mai maganar nabi da kallo idanuna suka hangomin Habeeb Gashua wanda yake tsaye jikin motar ya dafa murfin motar da hannayenshi yana sanye cikin bak’in wando da farar shirt mai dogayen hannu ya matse wuyanshi da black tie yasha torking da bak’ar belt wanda ya bayyana shafaffen cikinshi dayayi kama da wanda ba’a sawa komai a cikinshi sumar nan tasha uban gyara sai k’yalli take zubawa hakama sajen fuskarshi a kwance luf yasha mayuka masu tsada.
B’oyayyar ajiyar zuciya Heedayah tasaki wanda babu wanda yaji, gaskiya ALLAH ne ya taimaketa da wannan gabjejen k’aton baikai hannu jikinta ba data kad’e har ganyenta dama kuma duk abinda take k’arfin hali ne kawai amma inbanda bugu ba abinda take, kallonta ta maida kanshi ido ta zaro cikin fad’uwar gaba tana kallon tsabar kyau da tsari wanda ubangiji yayi masa.
‘Ashe balarabe ne ma ogan nasu’ ta fad’a cikin ranta, Kai tsaye ta tunkari inda yake tsaye har yanzun idanunshi akan Heedayah dake nufoshi, da masifarta ta k’arasa tana fad’in
“Ashe dama ba d’an k’asar nan bane kazo kake mana abinda kaga dama a garinmu? to ka maida hankalinka wllhy inba hakaba watarana sai an d’aureka.
Maryam Ibraheem Aleeyu
M&S????
EL– HABEEB????
©️Oum Hanan.
HASKE WRITER’S ASSOCIATION????
(Home of expert & perfect writer’s)
No 7.
Shiru kawai Habeeb yayi ya tsurawa d'an k'aramin bakinta wanda keta masifa ido dan maganganun nata ma dayawa ba ganesu yake ba sai faman juya baki take tana fad'a.
Hannu Aleeyu ya k’ara d’agawa da niyyar maketa jin yadda take ta fad’awa Boss d’insu maganganu Habeeb ya k’ara dakatar dashi a tsawace.
“Nunar rana kawai”. Abinda ta fad’a kenan daga k’arshe bayan ta juya masa idanu ta juya tayi tafiyarta kallo kawai ya bita dashi harta koma wajen Zainab dake tsaye a k’ame tana kallon ikon ALLAH da tsabar k’ok’ari irin na Heedayah.
“Dan ALLAH yallab’ai ka barni inje in casa maka yarinyar can mara kunya yarinya k’arama sai fitsara da rashin kunya”.
Kai kawai Habeeb ya girgizawa Aleeyu tare dayi musu alama ta cikin idanunshi subar wajen, nan da nan kuwa kowa ya shige mota shima ya koma ciki Mubarak direban dake jansu ya shiga ya tada motar duk suka bar wajen.
Lafewa ya k’ara yi a back seat d’in kamar yadda yake ada ya lumshe idanunshi yana k’ara hango d’an k’aramin bakin yarinyar data gama musu rashin kunya yanzu kalmar nunar rana d’in data fad’a na masa yawo a brain d’inshi anya ba zaginshi tayi ba kuwa? lallai saiya nemi ma’anar kalmar nunar rana idan ya kasance zagine to kuwa zaisa a nemo masa ita duk cikin fad’in Kano ya koya mata darasi.
“Innalillahi, Heedayah? dama haka kike ban saniba?”. Zainab ta fad’a cikin zaro ido lokacin da Heedayah ta k’arasa wajenta.
Ajiyar zuciya Heedayah ta saki tareda dafe k’irjinta tace
“Wayyo ALLAH nah ashe ni d’in dai jaruma ce ban saniba sai yau”.
“Jarumar gaske kuwa ni ina zan iya irin wannan abinda kikayi”.
“Ke nimafa k’arfin hali ne kawai wlhy amma bakiji yadda k’irjina ke lugude ba”.
“Duk da hakan ma dai kinyi k’ok’ari na sara miki, ke daganin irin motocin nan ai kinsan ba k’aramin mutum bane a ciki”.
Fuska Heedayah ta yatsina tace
“Balarabe ne mafa a ciki nasan duk b’ab’atun dana dingayi ma ba jina yake ba shiyasa ma ya hana bodyguard d’in ya dakeni saboda bayaji nasan da bahaushe ne saiyasa an tumurmusa ni a wajen can, gani nayi kawai yazo k’asar mu kuma garinmu zai raina mana hankali shiyasa nayi musu haka”.
“Nifa tsoro nakeji kar yaje yayi mana wani abun kinsan masu kud’in nan maybe shirun dayayi na d’aukar mataki ne”. cewar Zainab da har yanzu take a tsorace. Hannunta Heedayah taja tana fad’in
“Dallah zomu tafi bai isa yayi mana abinda ALLAH baiyi mana ba”. daga nan suka cigaba da tafiyarsu suna hira sai bayan magreebah suka koma gida dan saida sukayi sallah ma a gidan Aunt Rumaisa k’awar Aunt Ramlahn ta tsaresu tace sai sunyi sallah sunci abinci sannan zasu tafi.
Nunar rana shine kalmar data dinga yiwa Habeeb Gashua yawo a kanshi (Kunji dorawa kai fa reader’s ????). Shi duk zatonshi wani salon zagine da hausawa suke amfani dashi wajen zagin mutum, dan haka a washegarin ranar bayan sunyi wani taro da ma’aikatan kamfanin a babban d’akin taro na kamfanin bayan antashi ya rage daga shi sai Mujaheed a d’akin, ganin yanata kallonshi yasa Mujaheed yace
“Wai kai lafiya kuwa ko kama nake maka da baby dream d’inka ne kake ta kallona haka?”. Tsarabar harara yasamu daga wajen Habeeb kafin yace
“Tambaya zanyi maka”.
Saidaya d’auki ruwan faro dake gabanshi yasha sannan yace
“Ina jinka meyake faruwa?”.
Saidaya cije baki yana wani girgiza k’afa sannan yace
“What the meaning of nunan rana?”. yayi maganar yana tsare Mujaheed da fararen idanuwanshi.
“Nunar rana?”. Mujaheed ya maimaita yana yiwa Habeeb kallon mamaki.
“Yeah”. Habeeb ya amsa masa yana k’ara gyara zaman tie d’inshi.
“Kai Gashua ka cika shirme wllhy d’an fari sak idan kayi wani abun meye na wani son jin ma’anar kalmar nan”.
“Malam zaka fad’amin ne kokuwa”.
“Eh to ya danganta dai shi nunar rana misali kamar yana nufin……shiru yayi yana sosa kai kafin yaja tsaki yace
“Kaji ma’anar ta kwanta min ne gata a raina amma dai kabari zan…..”Shut up ur mouth, d’an iska dama duk k’aryar kai bahaushe ne kake mana k’aramin kalma ya gagareka”.
“Kai banason iskanci fa, cewa nayi ta kwantamin bawai ban saniba gaba d’aya zakamin iskanci”.
“Damuwarka ce”. cewar Habeeb yana hararar shi.
“To wai me zakayi da itane?”. Bai tanka masa ba ya tashi ya tattara takardun dake gabanshi ya diresu a gaban Mujaheed yayi gaba abinshi yana kallon agogon fata dake d’aure a tsintsiyar hannunshi mai cikeda kwantacciyar gargasa bak’a sid’ik, ganin haka yasa shima Mujaheed din ya mik’e ya d’ebi takardun yaji bayanshi.