EL-HABEEB HAUSA NOVEL

Yauma kamar kullum kuma kamar yadda ta saba zuwa masa cikin barcinshi yauma haka yau kuma sai mafarkin nashi ya canza salo dan a yau d’in da kanshi yakai hannu da nufin cire mata mayafin data lullub’e fuskar tata dashi amma baici nasara ba duk yayin daya kai hannu da nufin tab’ata saiyaji wani mugun shocking ya kamashi dole yake janye hannunshi da sauri haka dole ya k’yaleta yanaji yana gani ta juya ta tafi harta b’acewa ganinshi daga nan ya farka daga barcin.
Cikin tsananin b’acin rai ya farka a yanzu wani haushin yarinyar yakeji yadda ta hanashi sukuni a rayuwar shi yarasa uban da zaiyi mata da kullum saitazo gareshi kuma tak’i yarda yaga fuskarta wannan wace irin masifa ce?.
A gaggauce ya shiga bathroom yayi wanka yana k’ara jin haushinta ko makarar nan dayayi ita ta jaza masa.
K’ananun tsaki ya dinga saki lokacin dayake shiryawa cikin k’ananun kaya blue black d’in jeans da black shirt body hook sai bak’in takalmi sawu ciki simple kwalliya ce amma ba k’aramin kyau yayi ba kayan sun amsheshi matuk’a musamman daya toshe idanunshi da black space wanda bawai yasashi dan gayu bane sai dan b’oye idanuwanshi da kallo d’aya za’ayi musu a gane yana cikin damuwa bayason kuma a dameshi da tambaya saikuma hakan yabada citta ????.
Designer’s kala kala ya faffesa masu bala’in k’amshi da sanyi sannan ya fita zuwa gaishe da Ummi bayan ya rufe kofar side d’in nashi.
Kasancewar tasan alhamis ne yana yin azumi shiyasa ma batayi masa tayin breakfast ba bayan sun gaisa sun d’an tab’a hira ya tashi yayi mata sallama ya fita.
Tunda su Aleeyu sukaga yanayin ogan nasu suka san yau a sama yake yafi mu’amala da farin glass duk ranar dayasa bak’i kuwa to kuwa kayi hankali dashi dan zai iya sauke maka dan haka suka dinga kaffa kaffa kowa yana kiyayewa.
Koda suka shiga kamfanin ma da ma’aikata na gaisheshi ko hannun dayake d’aga musu ma basu samu ba a ranar kai tsaye ya wuce ta elevator ma yabi ranar sab’anin da da kullum yake hawa lifter ba wanda dai yayi masa magana tunda dai sun rabu dashi lafiya saikuma idan ya sauko.
Su kansu y’an kamfanin duk wanda yake da appointment dashi a ranar saida yayi hak’uri dan abinda bai taka kara ya karya ba saiya hau mutum da bala’i hatta Mujaheed ranar saida yayi taka tsantsan dashi baisan uwar da akayi masa ba yake ta musu wannan botsare botsaren.
Yaso ya masa iya shege amma ba dama saboda mutanen dake wajen da kuma yadda ya wani had’e rai bazakace yasan wani abu dariya ba duk da dai dama bawai yinta yake ba yafi yin murmushi shima saiya dad’e baiyiba.
Lokacin da suka fito zasu tafi bayan ya tashi aiki a dak’ile yacewa Aleeyu ya fad’awa sauran bodyguard d’in su wuce zasuje wata unguwa shida Aleeyun baya buk’atar rakiyar kowa, cikin rawar jiki Aleeyu yaje ya sanar dasu ga abinda yallab’ai yace daga nan ya shiga back seat Aleeyu ya shiga driver seat ya tada motar yaja suka tafi batare dayasan inda zasuba gashi yanajin tsoron tambaya.
Sai dayaga dai sunata tafiya har lokacin baice masa ga inda zasuba sannan yayi ta maza yace
“Yallab’ai ina muka nufa?”.
Saidaya d’auki y’an mintuna sannan kamar mai ciwon baki yace
“ShopRite”.
“Kaji wata rigimar kuma, me zaije yayi kuma a ShopRite? shidai iya saninshi duk wasu abubuwan amfaninshi musamman ake yimasa order d’insu bai cika using dana nan k’asar ba amma dan fitina yace a kaishi kome zai siya?. Dole ya canza hanya ya d’auki titin dazai sadashi da shopping mall d’in.
Koda suka k’arasa ma sukayi parking bai fitaba gashi dai yana gani anzo amma ko alamun fita bashi dashi, sam Aleeyu bai tanka masa ba suka cigaba da zama a haka. Kamar ance d’ago kanka ya hango wasu saurayi da budurwa sun fito daga cikin Mall d’in sai dariya suke yarinyar cikin matsattsun kaya k’ananu da siririn gyale data d’an yafashi akan tulin gashinta ta manna bak’in google wanda ya kusa mamaye rabin fuskar tata, wani irin bugawa gabanshi yayi ganin kamar yarinyar nan datayi masa rashin kunya ya kuma ganta a gidan Hajiya cikin azama ya cire glasses d’in fuskarshi yana k’ara k’ura mata ido da tunanin kodai kamanni suke da waccan d’in to amma abin mamakin komai na k’irar jikinsu iri d’aya so yake ta cire glass d’in idonta yadda zai gane itace koba itaba.
Kamar tasani kuwa takai hannu ta cire glass d’in ta mak’alashi a gaban matsattsiyar rigar dake jikinta sai faman taunar chewing gum take tana murmushi alamun yanayin datake ciki yana mata dad’i, sosai Habeeb Gashua ya zaro ido ganin yarinyar ce dama ashe tantiriya ce? to uban meya kaita gidan Hajiya? lips d’inshi ya cije tareda lumshe idanunshi yana d’an sauke numfashi, yana bud’e idanunshi yaga har sun shiga mota sun hau kan titi.
Cikin zafin nama ya b’alle murfin motar ya fito ya bud’e front seat yana yiwa Aleeyu alamu ya fito daga motar, zai tsaya tambayar shi ya daka masa tsawa da sauri Aleeyu ya fito shikuma ya shiga yabata wuta kafin ya figeta da uban gudu yabi bayan motar wannan saurayi da budurwar batare daya tsaya saurarar Aleeyu daya rud’e yake tambayar shi lafiya ina zaije?
Tsaye Aleeyu yayi yabi bayan motar da kallo yadda ogan nasu yake bata wuta tamkar yana filin tsere ne ya rasa abinda yake damunshi yau d’in nan da sauri shima Aleeyun ya tare mai napep ya shiga ya nuna masa motar Habeeb dake can nesa dasu yace ita zai dinga bi dole yabi yabi bayanshi mana tunda hakk’in kula da lafiyar shi yana hannunshi.
Haka nan yaji zuciyarshi na masa bala’in zafi ganinta dayayi dawani saurayin ga yanayin shigarta sam babu nutsuwa da kamun kai a cikinta cije baki kawai yake yana sakin k’ananun tsaki da tunanin wai me ma yasa yake binsu ne? meye damuwarshi da ita haka? ina ruwanshi da ita? duk wad’annan tarin tambayoyin bai samu nutsuwar dazai bawa kanshi amsar suba burinshi kawai ya samesu to idan ma ya samesu d’in me zaice musu? me zaice musu a matsayin amsar tambayar da zasuyi masa na dalilin dayasa yake binsu? wata mota dake gabanshi yaso karawa saboda gudun dayake yayi gaggawar kauce mata wanda anan ne motar dayake bi ta b’ace masa b’at rage gudun yayi yana k’ara hahhangawa kozai ganta saidai ba ita ba alamar ta.
“OH my God”. yace da k’arfi yana lumshe ido gamida dukan sitiyarin motar da k’arfin gaske cikin tsananin b’acin rai da takaicin rasasu d’in dayayi.
Gefen titi ya gangara yayi parking ya fito daga motar, hannu d’aya yasa ya rik’e k’ugunshi d’ayan kuma ya cusashi cikin tulin lallausar sumar kanshi mai azabar santsi da laushi yana yamutsa ta kafin ya kaiwa motar duka da k’afarshi wanda yayi daidai da saukar Aleeyu daga napep ko canji bai tsaya karb’a daga wajen mai napep d’in ba ya nufi inda Habeeb Gashua yake tsaye cikin takaici.
“Boss are you okay?”. yace a rud’e yana kallon jikinshi da fatan dai wani abu bai tab’a lafiyar shiba.
“Let’s go”. yace yana cilla masa car key d’in batare daya bashi amsar tambayar dayayi masa ba, cafewa Aleeyu yayi, da kanshi ya bud’e motar ya shiga shima Aleeyun ya shiga ya tada motar suka tafi.
Kishingid’a yayi a bayan motar ya rufe idanunshi gam yana hasko abinda ya faru yanzu ko zuwa zaiyi ya tambayi Hajiya WACECE wannan yarinyar? to kuma kar tayi tunanin wani abu ne a ranshi har yakeson sanin ita wace to wai duk meye ma nasa tunanin yarinyar a ranshi da har zai hana kanshi sukuni gefe d’aya kuma ga ta cikin mafarkin nan.
“Yaa ALLAH”. ya furta hakan can k’asan zuciyarshi yana shafo k’eyarshi zuwa dokin wuyanshi dake cikeda kwantaccen k’ananun gashi.