A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤
_✍????M Shakur_
1️⃣5️⃣
how to subscribe
Zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta WhatsApp number na 07012181461 sainai adding naki a group din danake posting. Zaki iya turo MTN card 300 ta watsapp number na idan baki da bank
littafin nan na kudi ne duk wacce ta karanta batare data biyaba ban yafe mataba, pay anan ko pay a lahira your choice ????????♀️
Fuskarshi ta kalla ganin driving dinshi yake hankalin shi nakan hanya yasa tamika hanunta dake rawa sosai ta karbi wayan tai picking takara akunne. “Aneesa kina ina yanzu?” ahankali tace “muna hanya” da sauri Ammi tace “mutumin ne zai kaiki?” gyadama Ammi kai tayi ahankali tace “eh shine” dan ajiyan zuciya Ammi tasauke tace “to Alhamdulillahi, dazaran kunkai bakin titi akwai Motocin Suleja dayawa saiki shiga kinji idan kin shiga ki kirani ki sanar dani kinji, kidena kuka babu abinda zai saman mini ke okay” gyadama Ammi kai tayi tace “tom” katse wayan Ammi tayi hakan yasa ta janye wayan daga kunenta ta ijiye akan cinyarta tana sauke ajiyan zuciya, ganin sun shigo kan titi yasa ta kallai ganin har lokacin hankalinshi nakan titi yasa tadan gyara murya danji tayi muryan ta yadishe sosai sabida kukan datayi, ahankali tace “uhhhh anan, anan kan titi Ammi na tace na sauka” dan juyo dakai yayi ya kalleta suka hada ido dan lumshe ido kadan yayi yabude kafin ya maida hankalinshi kan tukin dayake yi batare dayace mata komiba, ringing da wayarshi yayi yasa ya kalli wayar dake ajiye gefen shi ganin Abdul ne yasa baiyi picking ba dan yasan nemanshi yakeyi, saida yasake kiranshi akaro na biyu sanan yadaga wayan yakara akunne yay shiru. “where are you Leo? Nafito banmaga motanmu ba don’t tell me kakoma gida, waikai wani irine eh fisabilillahi fa, he’s our friend fa, haka kakeso amana ranan bikin ka eh? Duk abokanen ka suki zuwa sabida baka zuwa nasu?” dan yatsine fuska yayi yace “kacikani da surutu am driving fa” “driving? Driving to where?” dan murmushi yayi kadan yace “idan nadawo we will talk, am tired yanzu” ya katse wayar yamaida kan cinyarshi, ta gefen ido yaga sai share hawayen dasuka shiga zubo mata takeyi hakanan batasan mesa taji tana shakkanshi ba, takasa mai magana dudda batasan inda zai kaita ba, kuma gashi Ammi tace akan titi zai sauketa tahau motan dake kawo mutane Suleja, itadai yau tata takare, bata tabayin dare haka awuriba, tunanin hakan yasa hawaye sai zubowa daga idanunta suke, dan murmushi yayi yasa hanunshi a aljihu yazaro wani clean soft handkerchief dake wani cool kamshi yamika mata, kallon handkerchief din tayi kafin tasa hannu ta share hawayen dake kan fuskarta ta girgizamai kai batare data karba ba alamun a’a, ajiye mata handkerchief din yayi akan cinya yamaida hankalinshi kan tuki fuskarshi nakan hanya, sai share hawaye take dasunki tsayawa saida taga wani signboard an rubuta Suleja 20km yasa tai wani irin murmushin kuka, juyawa tayi da sauri ta kallai juyowa shima yayi ya kalleta dawani irin calm look da yatsar shi yamata pointing handkerchief din dayabata dake kan jikinta, da sauri tadauki handkerchief din ta share fuskar ta tass tareda sauke wani irin ajiyan zuciya mai kara dahar saida yaji, dan murmushi yayi ganin yanda ta natsu dataga sundau hanyan gida.
Gudu yake sosai basu wani jimaba ya kai Sulejan sanan yarage gudu yadan kalleta cikin calm voice dinshi yace “show me the road to your house” gyadakai kai tayi tasa hannu tana nunamai hanyar yanata bi har sukakai anguwan su, a kofar gidansu ta hango Ammin su tsaye sanye da dogon hijabin ta hanunta rikeda waya, da hannu tamai pointing Ammi tace “ga Ammi na nan” rage gudu yayi tareda rage karfin wutan gaban motan sabida karya haska Ammin sosai tun kafin yay parking tawani irin bude motar da gudu tai wajen Ammi data tsare motar da kallo. “Ammi, Ammi, Ammi” kafin Ammi tace ma wani abu taje da gudun gaske tai tsalle ta rungume Ammin kaman wacce tai shekara bataga Ammin nataba, rungumeta tight Ammi tayi tanama Allah godiya. “Alhamdulillah” kafin ta dagota daga jikinta takama habarta da hannu daya tasa dayan hanunta tana share mata fuska tace “Alhamdulillah Allah nagode maka, you are ok ko Aneesa na?” hannun Ammi ta rike tareda gyada matakai tana murmushi hakan yasa Ammi tasake sata ajikinta ta rungumeta, shiru yayi ya tsaya a mota yana kallonsu, looking at affection din Ammi towards Aneesa yasa yaji he just wish Mummy shi was alife to hug him like this, he miss his mum so so sooo much, lumshe ido yayi ahankali zuciyanshi namai wani irin zafi.
Ahankali yajinginar da kanshi da kujera kirjinshi namai wani irin zafi, knocking glass din motar da akayi yasa yabude ido ahankali, Ammi yagani tsaye rungume da Aneesa a gefenta, ahankali ya bude kofar shibai masan mezaiyi ba yadai sami kanshi da kasa daga fuskarshi ya kalleta zaiyi magana Ammi tarigashi. “nagode, nagode bawan Allah, yanda ka taimaki Aneesa Allah ya taimaka maka adukkan al’amuranka, Allah ya haskaka rayuwan ka, kakawo mini ita har gida safe and sound, thank you so much, may Allah reward you abundantly” kasa ma magana yayi sai gyadamata kai da yayi ahankali, ganin haka yasa Ammi tadan bugi kafadar Aneesa da kanta ke kasa tace “bakimai godiya ba Aneesa” ahankali tajuyar da kanta ta kallai har lokacin kanshi akasa dauke idanunta tayi daga kanshi ta maida kan yatsunta data shiga wasa dasu ahankali tace “nagode sosai, Allah yasaka da alkhairi” murmushi Ammi tayi tace “mun gode malam saida safe, wuce mutafi Aneesa” jan hanun Aneesan tayi tasa key tabude kofar gidansu dahar ta kulle ta shiga, dan waigawa Aneesa tayi tasake kallon motar dudda bata iya ganinshi daga wurin amma saida gabanta yafadi da sauri ta shige ta maida kofar tarufe, sukai cikin gida, falo suka shiga ta ijiye souvenir da akabata akasa ta zauna kusada Ammi tana bude jakanta tace “Ammi barina saka chaji tunda akwai wuta, yautun safe bansama wayata chaji ba” ciro wayar tayi daga jaka tana kokarin kunna wayar kwan lantarkin falon yawani irin yin kara ya tarwatse da gudu tarike Ammi sabida tsoron dataji, salati Ammi tayi. “innalillahi tome kuma yasami kwan lantarkin ko karfin wutan yay yawane?” tai maganan tana kunna wutar toculan wayanta ta haska wajen wutan taga yanda yafashe, tsaki Aneesa tayi tace “Ammi dama wanan na dan dari uku baida kyau energy bulb yafi wanan yan darin dakike siyowa kyau, anmafa ce baya jan wutafa, bari naje nasiyo” tai maganan tana zage handbag dinta ta kwaso duka kudin da aka bata ta mikama Ammi tareda zare dubu daya ta mike tsaye tareda daukan hijabinta, Ammi dakebin kudin da kallo tace “wayabaki kudi dayawa haka Aneesa?” dan dariya tayi tace “amaryan tabani wai kudin lallena bari nadawo nabaki labarin abinda ya faru yau” dubu biyu Ammi tazaro cikin kudin tamika mata tace “gashi ki shiga gidan Maman su Muhammadu kice nace gashi injini” karba tayi tace “to” tawuce tafita daga dakin tana haskawa da wayanta dan tsakar gidansu dama babu fitila, bude kofar gidansu tayi tafita tana haska kudin hanunta da waya tacire dubu biyun tarike su separate sanan ta shiga gidan dat is next to them inda Ammi ta aiketa ta mika kudin tafito tana kalle kalle, idanunta ne suka sauka akan motan daya kawota ganin har yanzu motan na wurin baitafi ba, faduwa da gabanta yayi yasa tasauke kai da sauri ta dena kallon motar, tsallakawa tayi dayan side din tai wajen wani shago dayake chan gaba kadan, ta shiga tasayo kwan lantarkin mai kyau nadan dari biyar sanan tajuyo tanadan satan kallon motan tana tafiya towards there house, sosai mamaki yakamata ganin har lokacin motan na wurin tai hanyar kofar gidansu tana kallon motar, hannu tasa zata bude kofar gidansu saikuma ta janye hannun tasake juyowa ta kalli motan to kodai baida lafiya ne? Mutumin da tun dazu yakawo ta aiya kamata ace yatafi by now, in fact yamayi nisa ahanya, kasa hakura tayi ji kaman wani abu na fizganta tafara tafiya so take kawai taduba shi taga ko lafiya, ahankali take tafiya tana kallon motar kafin takarasa gaban motan taga yabude kofan motar hakan yasa ta tsaya chak takasa karasawa tadan kwantar da kanta tana lekawa, ahankali yasa kafarshi yafito daga motar yamaida kofar motar yarufe tareda jingina da motar ya rungume hannayenshi a kirji yana kallonta, faduwa gabanta yayi sosai sabida yanda idanunsu suka hadu da sauri tajuya zata koma ya kira sunanta for the first time. “Aneesah!” tsayawa tayi chak jin yanda yakira sunanta har ranta taji kiran sunan saida duka organs din jikinta suka amsa, murya chan kasa ta yanda ita kadai ne zata ijiyajin meyace calmly yace “come” sosai takejin maganan shi nazuwanma zuciyanta kaman command, kasa jurewa tayi tajuyo ahankali taa kallai, gyada mata kai yayi tareda dan lumshe ido sanan yabude su yadaura akanta, daga kafa tayi ahankali tataho wajen kanta akasa ta tsaya agefen shi kafafun ta nadan rawa sabida wani sanyi dasuke mata da batasan nameba, juyowa yayi yay facing dinta yana kallon yanda take wasa da kwalin kwan fitilan hanunta, murya chan kasa yace “ina kikaje?” batare data kalleshi ba kanta akasa tace “kwan lantarki naje nasayo” shiru yadan yi kafin ahankali yace “maisa baki aiki brother kiba yaje kika fito da dadaddare?” kanta akasa tace “uhm banda brother” “ke kadaine?” yatambaye ta immediately bayan tai maganan, gyadamai kai tayi batare datai magana ba, ahankali yace “what about your Dad?” dago kai tayi ta kalleshi hada ido sukayi da sauri ta maida kanta kasa, ahankali cikin wani irin siriruwar murya tace “yarasu” sosai kalman yarasun yadaki zuciyan shi hakan yasa yay shiru yana kallonta sai chan yace “sorry! Allah ya jikanshi” gyadamai kai tayi kaman zatai kuka dan sosai tuna mata da Baba, ahankali tace “Ameen” sukadanyi shiru batare dawani daga cikinsu yakara cewa wani abuba, dan dago kanta tayi ta kallai ganin ita yake kallo har lokacin yasa tace “in tafi?” girgixa mata kai yayi yace “No” tsayawa tayi duk tanajin wani iri yanda ta tsaya dashi danko kadan bata saba tsayawa da samari ba ita bamata dawani saurayin kirki dan batabasu lokaci. “me kikaje yi agidan bikin nan?” hanunta ta shiga wasa dashi kanta akasa tace “lalle naje yi musu” “lalle? You mean henna? Are you a henna designer?” gyadamai kai tayi tace “eh, na iya” dan murmushi yayi yarinyar nan bala’in burgeshi take bana wasaba, shidai in his life this is the first girl daya taba gani dayaji ta burgeshi, dago kai tayi ahankali kaman wacce take tsoron ta kalleshi tadan kalleshi tace “ya kanwar ka?” dan shiru yayi kafin yadan juyar da idanunshi cikin jin dadi yace “oh Rauda? Dama kin ganeni?” gyadamai kai tayi da sauri tace “eh tundazu ai naganeka, kunyi kama ai da ita saida kafita uhmm…uhmm” muryan ta ya sarke sotake tace yafita kyau amma takasa fadi hakanan taji tanajin kunyan tace mai haka, murmushi yayi sosai ganin takasa fadin abinda takeso tace mai, murya chan kasa cikeda zolaya yace “ashe kin iya kuka haka I tot mara tsoro bata kuka eh Fearless lady?” rufe fuskarta tayi da hijabi da sauri tareda yin murmushi akunyace tai gaba zata wuce dan maganan ta ya mugun bata kunya da sauri yace “wait” tsayawa tayi chak batare data juyowa ba sai murmushi take ya mugun bata kunya, cikeda murmushi tace “wat? kaga Ammi na zata zo tanemeni yanzu nan” tafiya daidai yake hanunshi zube cikin aljihu harya tako ya tsaya abayanta chak, yanda tajishi abayanta yasa taji numfashinta na neman daukewa da sauri tajuyo sukai facing juna yanda taga yana kallonta yasa taji takasa magana sai numfashi take fitarwa da sauri da sauri heart dinta is beating way too fast kuma batasan mesaba sai kyafkyafta ido take, one step yakara ya matso gab da ita ahankali yace “can we be friends Aneesah?”