A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL

Tashi tayi ahankali jikinta duk yay sanyi taja jakanta tareda kashemai wutan dakin tafita ta rufemai kofan falo tawuce part dinsu, ahankali tabude kofar su gudun kar Mama taji ta maida kofar tarufe sanan tadaga akwatin dan karyay kara tai dakinsu, bamata kunna wutaba ta lallaba ta ijiye akwatin gefen gadonta ahankali kaman munafuka, fincikota dataji anyi saida tadan saki gajeren fitsari kunna wutan dakin akayi taga Yayarta Hajara ne tsaye jikin kofa sai maman su data mugun daure fuska tana rike da ita, sosai jikinta yafara rawa hakan yasa tace “M…Mama menayi?” hannu Mama tasa ta dauke ta da lafiyayyen mari ihu tabude baki zatayi Maman su tace “wlh, wlh kikamin ihu ubanki yaji ya shigo dakin nan saina miki abinda bantaba mikiba tunda na haifoki duniya” gyada mata kai tayi tsabagen rudewa tasa hannu takama bakinta tana kuka sosai mara kara, cikin mugun fushi Maman su tace “wato dan ubanki tunda Aliyu yabar garin nan nahuta yanzu yadawo kin fara, Rauda ni, ni, ni nan uwarki karimatu in tsugunna in haifoki kifito tanan Rauda” ta daura hannu gaban zanin jikinta tace “nasha azaban nakuda na kwana biyar, bayana kam har tofin yaasin akamini tsabagen yanda kika shirya karyashi kafin ki fito, sanan dakika tashi fitowan kika fito ta kafa nasha bakar azaba nice yau Rauda kike nunamin wani kasurgumin katon banzan namiji, mai kama da basamuden chan yafi ni ni mahaifiyarki, iyye Rauda? Nasaki ki daukomin zanin gado, Rauda ni zaki watsarma da wankakken zanin gadona fari kal akasa sabida kinga Aliyu, dan ubanki ciki daya kuka fito da Aliyun?” shiru Rauda tayi bata bata amsaba sai uban hawaye dake fitowa daga idanunta, cikin tsananin fushi Mama takara kamo gaban rigan ta bakinta na kumfa tace “kibani amsa, ciki daya kuka fito da Aliyu?” girgiza mata kai tayi cikin kuka tace “Yayan mune Mama” wani mahaukacin mari Mama takara sharara mata tace “dan ubanki menasha taraku nake fadamuku? Aliyu ba dan uwanku bane, babu ruwan ku dashi yanda baida uwa hakama baidaku, kuba yan uwanshi bane, haka zai karake rayuwanshi baisan dadi da soyayyan dan uwaba, ku dauka ko jini vaku hada dashi ba, yaron da ubanku ya fifitashi kan kowa na gidan nan uban me za’ayi dashi eh?” cikin kuka sosai Rauda tace “amma Mama shi aka fara haifa a gidan nan, kafin dukanmu, kuma Dady na nuna yafi sonshi ne sabida duk kunki bama marayan yaron soyayyar mahaifiya dukkun tsaneshi, maiya muku? Bai taba zaginki ba, bai taba miki rashin kunya ba, inya gaisheki baki amsawa bama kya kallonshi saisama yadena, duk kun rabashi da kowa, Anty Hajar ma bata gaidashi duk kun hana kaninshi gaidashi saidai idan sunga Dady ne zasu gaidashi, haba Mama kiji tsoron Allah, d’a na kowane maiya muku eh? Idan yanzu kika mutu akamana haka yaya zaki dingaji akabari” shaketa Mama tayi ahaukace jitake kaman ta kashe ta tace “nikike kirama mutuwa Rauda akan Aliyu? Ba dangin iya bare na Kaka, saidai ke kimutu baniba kinji shegiya wacce ta debo jinin dangin ubanta mai bakin zuciya” ganin idanunta na juyawa yasa Anty Hajara da itama take mugun jin haushin kanwar nata sabida taurin kanta tazo ta cire hanun Mama daga wuyanta tace “ya isa haka Mama” cikin fushi da mugun masifa jikin Mama har barbar yake tace “Hajar ki barni na kasheta, baidai tafison wani kato akan uwarta ba, goben nan zakiji kishiyoyina sun faramin habaici na haifi munafuka, zataci ubanta ne saisa gwara ai aurenta da Khamis ta tattara tabar gidan nan ta tafi gidan mijinta nahuta inba hakaba bakin cikinta zai kasheni ne, dama Khamis din yacemin gobe zaizo yadauke ki kufita kibishi kufita dan kin gama zaman gidan nan balle kije kinama wani kato girki kega kuku yakarata chan daci a restaurant shidai da gidan ubanshi ba amma wlh bazaici abincin gidan ubanshi ba zan gyara miki zamane Rauda” ahankali Hajara trying to calm Maman su down tace “ya isa Mama kiyakuri, Bazata sakeba” dan shiru Maman tayi tana kallon yanda Raudan taduka tana kuka sosai mara kara kafin tai kwafa ta kalli hadadden akwatin data shigo dashi tace “kuma shegen akwatin nan kona shege zanyi” tasa hannu zata dauki akwatin da gudu tarike akwatin cikin kuka tace “Mama dan Allah ki barmin abuna” hannu Mama tasa zata fizge akwatin tarike gamgam tana kuka, cikin kunan rai Hajara tace “wai bazaki saki akwatin ba Rauda kanin ubanki ne yabaki akwatin, kisaki akace” cikin kuka sosai ta girgiza musu kai taki saki dan son abubuwan ciki takeyi sosai, Mama jitayi kaman ta kashe Rauda tahuta zata jibgeta Hajara tai sauri ta tare tasa hannu ta daki hanun Raudan tace “sake shegen akwatin” ta hankadeta tareda fizge akwatin tamikama Mama dan ayanda taga mama tasan zata iya jima Rauda ciwo ayanda ta zuciyan nan. Karban akwatin tayi ta kalli Raudan dake kuka kaman zata mutu tai kwafa tajuya tafita daga dakin tsaki Hajara tayi ta balla mata harara tahau kan gadonsu cikeda takaicin Raudan tai baccinta, sosai Rauda taci kuka harta godema Allah ahaka bacci yay awon gaba da ita awurin.
[4/5, 8:05 AM] Hijabi_muslimah????: A TSAKANKANIN SOYAYYA

         _IN BETWEEN THE LOVE_
        ❤ _Lies another love_❤




        _✍????M Shakur_



                    3️⃣

How to subscribe
zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turamin evidence of payment to WhatsApp number na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting

zaki iya turo katin MTN 300 ta WhatsApp number na 07012181461 sainai adding dinki a group danake posting

Free page

Da asuba ya tashi da kyar shima sabida alarm din gefen gadonshi ne daya saita yatadashi, tashi yayi ya shiga bathroom, yadade aciki kafin yafito cikin wani blue bathrobe, zama yayi abakin gado ya shafa manshi mai kamshi a tsanake sanan yatashi wardrobe dinshi yaje yabude yaciro wani black belted cotton poplin cargo trouser da wata farin logo print t-shirt na Ambush yadauko yasaka, yabude bangaren rigunan sanyin shi yana tunanin wanda zai saka kafin yajawo wata logo embroidered wool fleece jacket itama ta Ambush, yasaka rigan tazauna ajikinshi tamai kyau sosai, yadau designers turarukan shi ya fesa sanan ya shimfida dadduma yay salla yana sallame wa yaji ana bugamai kofa, yatsine kofa yayi sanin mayun nanne, da kyar cikin isa da izza yace “come on in” bude kofa bodyguard din yayi rikeda wata yar karaman tray da small mug of hot coffee kekai, karasowa gabanshi yayi ya ijiye tray kan dadduman yace “have this sir, we are leaving in the next 10min” daure fuska yayi yace “where is d other guard? Lucas is his name right?” yay maganan yana mai alamu da yatsa ayangance, gyadamai kai bodyguard yayi yace “yes he’s Lucas, I left him outside he’s packing out luggage to the car” yatsine fuska yayi as usual yatashi daga kan dadduman yahau kan gadon yazauna yamai pointing coffee da yatsa alamun yabashi ysha, daukan coffee yayi da sauri ya mikamai karba yayi yakai bakinshi yay sipping dan ficili ya zare daga bakinshi batare daya kalli Guard dinba yace “where is my phone? Dad dina yakirani?” “your phone is here sir” yakarasa kusa da bedside lamp yadau wayarshi dat was lying there yadauka ya danna wayar dababu any security lock ajiki yace “No sir, babu miss call din kowa” dan kwafa yayi baisake cewa komiba yacigaba dashan dan coffee ayangance sanan ya gama yatashi ahankali yay gaba bodyguard din ya gyara ko ina sanan ya kashe wuta yabiyoshi waje harya shiga mota yawuce ya shiga gaba suka wuce Airport.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57Next page

Leave a Reply

Back to top button