A TSAKANKANIN SOYAYYA HAUSA NOVEL
_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤
_✍????M Shakur_
5️⃣ & 6️⃣
how to pay your subscription fee
zaki turo 300 ta account dina 3107021073 first bank aisha Muhammad, saiki turo evidence of payment ta WhatsApp number na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting
*for those da prefer su tura kati, you can also send MTN card na 300 ta WhatsApp number na 07012181461 saina loda nasaki a group din danake posting ATSAKANKANIN SOYAYYA
Free page
Sallame salla Ammi tayi
sake kwalamata kira akaro na uku tayi. “Aneesa wai bazaki tashiba, idan kika bari nazo dakin nan sai jikinki yay tsami, kindaisan abubuwan dake gabanki yau ko” da kyar ta iya bude ido jin Ammi na masifa tana kiranta jiya taci aiki a shago bana wasaba saisa tagaji haka, dama duk jumma’a haka take uban aiki a shago dan masu zuwa party nazuwa placing order dayawa kuma duksaitayi, da kyar ta sauko daga gado har bata gani da kyau tana dafa bango tafito daga dakin tafito Ammi tabita da kallo tai tsakar gida bayi ta shiga dan lokacin har gari yasoma wayewa fitowa tayi tadauro alwala takoma daki tadau hijabi ta sanya, akusada Ammi ta tsaya ta kabbarta salla, data idar tai karatun Al qur’ani sanna ta sallame ta gaida Ammi ahankali, amsawa Ammi tayi tace “tashi kije kidaura ruwa a wuta” gyadama Ammi kai tayi ta tashi ta zare hijabin jikinta tafito daga dakin tai kitchen wuta ta kunna ta daura pot din ruwan wanka dake cikeda ruwa tadau tsintsiya ta share tsakar gidan fess sanan ta shiga dakin dakin Ammi ta tattaro ta gyara sanan tawuce nata dakin ta gyaro shima tahada da falo ta gyara tafito da dattin ta kwashe, tadawo ta kunna turaren wuta sanan tafito tasauke ruwan daya soma shirin tausa daga wuta ta daura dumamen tuwo tahada ruwa ta shiga bayi, wanka tayi tana fitowa ta sauke tuwon dayayi tasa miya sanan tai dakinta, mai kawai tashafa tadau doguwan riganta na gida baki ta zura tafito lokacin wajen 8 nasafe ta zuba abincin ta dan tasan Ammi bata breakfast early tadawo ciki ta zauna kusada Ammi tafara cin tuwon dayay dadi miyan harda wake aciki, ahankali takeci harta cinye sanan ta kai kwanon kicin ta wanke hanun ta ta dauraye baki tadawo ta zauna kusa da Ammi, da hannu Ammi tanuna mata dakinta tace “daukomin purse dina” tashi tayi tai hanyar dakin Ammi tafito rikeda wata bakar purse ta zauna kusa da Ammi tamika mata karba tayi tabude purse din ta ciro kudaden dake ciki wanda suke na Aneesan na lallen datakeyi take tara mata dubu biyarne Ammi tamika mata tace “kije kisiyo kayan lallen, sanan kisiyo handglove banson yanda kike bata hanunki haka, kiyi sauri kidawo dan nasan anjima kadan yan lallen zasu fara zuwa yau asabar kina gida” karban kudin tayi tana kallon agogon bangon dakin ganin Takwas da rabine yanzu yasa tace “karfe tara kasuwan lallin ke budewa, Ammi ki faramin tsifan kafin lokacin” tai maganan tana zare hulan kanta tulin kitson kanta datai shuku na hannu yawani zubo har gadon baya, hulan data cire Ammi ta daura ta mayar mata tace “sokike kije kasuwa dakai daya da rabi, aga nan yay kato nan yay kadan, Tara zaki fita yanzu takwas darabi minti talatin yayma kitson nan kadan, yanzu jeki fara shiryawa ne, kafin kigama shirin lokaci yayi” kaman zatai kuka ta tashi tai hanyar dakinta, sip dinta tabude tadauko wani gogaggen atamparta riga da skirt dakeda dilli dillin ja, sai ta dauko jan hijabin ta dayakai mata har guiwa ta maida sip din tarufe tacire rigan jikinta ta shiga shiryawa, riga da skirt din yay mata kyau sosai gaban madubinta taje ta shafa hodanta tadau man baki tashafa a lips din sai abin yay kaman tasa pink lipstick, dawowa tayi tadau hijabin tasaka daya kwanta a fuskarta tadau karaman jakanta tafito, baki Ammi ta tabe tace “kasuwan aka cima kwalliya haka yan mata kodai nai siriki ne akasuwan” akunyace tace “laaaaa Ammi” dariya tadanyi ta dauke kai cikeda kunya tadau kudin dake gefen Ammi tace “nifa hoda kawai na shafa Ammi” tura kudin tayi cikin jaka tayi har lokacin taki kallon Ammi tace “natafi Ammi” “adawo lpy, ki adduan fita daga gidafa, kuma adaga kafa kar aje ana yauki akasuwa hmmm” Ammi tafada cikeda zolaya, murmushi sosai tayi tasa hijabi tace “to, Ammi idan yan lalle sunzo kice sujirani bazan dadeba” “shikenan, saikin dawo, kiyi addu’an fita daga gida” ficewa tayi daga dakin tai addu’a tafita daga gidan.
Around 8:40Am Hajar tabude dakin nasu ta shigo tana kallon Raudan dake kwance kan gadonta idanunta sunyi suntum suntum tace “kije Mama na kiranki adakinta, Khamis kuma yazo yana falo” ko alamun tashi batayi ba hakan yasa Hajar tamata ihu. “wai bazaki tashi kije kiran da mama ke mikiba mara kunya” tashi tayi ahankali tana turo baki tafita daga dakin, dakin Maman su ta shiga, Mama na zaune kan katafaren gadonta ta mimmike kafafun tana shan farfesun kaza, watsa mata harara tayi tace “sai yanzu kikaga daman zuwa rasakunyar beran tanka” ahankali tace “ina kwana Mama” hararanta Mama tasake yi tace “daban kwana ba zaki ganni anan ne?” matsar da farfesun tayi gefe ta sauko daga gadon, gaban wardrobe dinta tayi tabude taciro wani sabon dinkakken atampa na mustard da brown anyi dinkin riga da skirt sai mustard veil da mustard flat shoe mai kyau, mika mata Mama tayi cikin daure fuska tace “ai tun asuba kikai wanka, gasunan shirya anan yanzu nan Hajar zatazo tamiki kwalliya kitafi yana falo” karban kayan tayi ahankali ranta abace ta cire rigan ta ta shiga sakawa ahankali, rigan ta tsaya tana kallo yanda net ne daga ta kirjin ana hango boobs dinta, hannu tasa a wurin ta dago kai ta kalli Mama da itama ita take kallo cikeda masifa tace “miye to?” cikin dan shakakkiyar muryanta tace “ana hango kirjina Mama is net” harara Mama ta watsa mata tace “naga dai Khamis zaki aura har ubanki yasan da zancen, banda haka Khamis dandan Yayata ne na yarda da tarbiyan shi, yaro mai natsuwa da hankali ga kunya, me kike nufi mai zaimiki? Besides wanan dinkin mai net din wuyan ai shinaga yan mata ke yayi yanzu saisa na bada amiki irin shi dan haka karki kara cemin komi” daidai lokacin Hajar tabude kofar dakin ta shigo dauke da kayan kwalliya murmushi sosai Mama tayi tace “kaga yar albarka maijin maganan uwarta, bazaki taba ganin mara dadi ba arayuwanki Hajar saidai kiga daidai, yimata kwalliyan sutafi sai dare yau” murmushi Hajar tayi jin ddin maganan maman su, taja kujera ta zaunar da Raudan data dawo kaman gunki ta shiga mata makeup din, cikin 5min tagama mata sosai tai kyau, tadau gyalen ta yafa mata a kafada tace “tashi kuje” kallon gyalen tayi kaman zatai kuka tace “ahaka Anty, jibi kirjina fa” mugun kallo Mama ta watsa mata tace “barganin kinyi gayu bazai hana na lallasaki da safen nan ba, dan ubanki inya gani aike zai aura ballema Khamis baida kallon nan, wuce muje” ta tasata agaba sukai falo kanta akasa, wani kyakyawan farin guy ne zaune akan daya daga kujerun dake jere a hadadden falon yana sanye da farin shadda dake kyalli taji guga da bugu, ganin Mama yasa ya saukar da kanshi kasa cikeda kunya yana murmushi, dan dariya Mama tayi tace “kagamun dan banzan yaro ni ake kunya kuma yanzu Khimis, lallai duniya ashedai da gaske ne yaro akace za’amai aure natsuwa yake” tai murmushi tace “kaga ga kanwar taka nan tashi kutafi, dan Allah Khamis sai dare kaji zaku dawo ka kaita yawon bude ido, nariga nafadama Babanta zaka kaita wujen Yaya ne, so ba matsala, sai darefa karka manta banso taje wajen shegen Aliyun nan ne, neman hanyar rabata dashi nake ido rufe, tashi kuje adawo lpy, akwai kudi hanunka enough kona kara maka?” tashi yayi yace “akwai Small Mum” gyadakai tayi tace “yauwa saikun dawo to” ta tura kan Raudan dake tsaye gefenta tace “kutafi sai anjiman ku” bude kofa yayi ya fita tabishi ahankali, rakasu Mama tayi har bakin kofa tana murmushi harda sauke ajiyan, tasamu inda ta tura mai taurin kan, taga ta inda Aliyun zai ganta yau, maida kofa tayi tarufe takoma daki.
Tafiya suke a tsakar gidansu da babu kowa sai ma’aikata dake watering plant, Khamis na gaba ita tana baya tana waige ganin Mama takoma daki yasa tajuyo tace “Ya Khamis kaje mota bari nazo” kallon so yamata zaiyi magana tace “please kaji wlh yanzun nan zanzo” gyada mata kai yayi yace “okay” yay gaba, sake kallon dakinsu tayi ganin kofar a kulle yasa ta kwasa da gudu tai shashin Ya Aliyu kafin akamata, bude kofan tayi ta shiga da gudu ta mayar tarufe ganin baya palor yasa tai hanyar bedroom dinshi, knocking kofar tayi ahankali cikin tattausan muryanshi yace “come in” bude kofan tayi ta shiga yana zaune kan gadonshi sanye da white bathrobe yasaka white bathroom slippers rikeda wayarshi yana daddannawa ga cream dinshi agefenshi daya ajiye, murmushi tayi takarasa kusadashi da sauri ta zauna tace “good morning Ya Aliyu” ajiye wayan hanunshi yayi a gefe yadago kai ya kalleta zai amsa sai yay shiru yana kallon fuskarta, dauke kai tayi da sauri dan tasan yanzun nan zai gane tai kuka, hanun yasa yadago fuskarta, Kallonta yayi ahankali yace “wat made u cry?” juyar da kanta tayi da sauri ta mike tsaye tace “dazu ne dazanyi alwalan safe wani kwaro ya shigan min ido, nazo nafadama zan fita ne Yayan mu” kallo yabita dashi ko kadan bai yarda da maganan ta ba yasan dukanta akayi dan tazo wajenshi jiya amma saiya share, ahankali yace “where are you going?” shiru tayi tana dan zaro ido bataso tamishi karya kuma kunya takeji tacemai itada dandan yayar Mama zasu fita. “where are you going?” yasake jefomata tambayan akaro nabiyu kanta tadan sosa tace “uhmm Mama ta aikeni gidan yarta Anty Hauwa ne” dan yatsine fuska yayi yanuna kayan datasaka da yatsa yace “like this?” gyadamai kai tayi tace “Mama tace dole saina sasu” tashi yayi daga kan gadon yamike tsaye, gyalen dake kan kafadarta yaja ya warware gyalen ahankali ya yafamata ya lullube tundaga wuyanta har zuwa cikinta yace “leave the veil like this, cover yourself, your clothes are too expose, be safe okay” gyadamai kai tayi ahankali, sai alokacin yadan sakin mata murmushi yace “saikin dawo nima am going out yanzun nan, take care Angel” murmushi tayi yaja hancinta yace “now go” juyawa tayi da gudu tafita shikuma yacigaba da shiryawa so yake yaje gidan kanwar Dad Momman Suleja.