ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

 A hankali take tattaka steps ɗin benen tana saukowa down, tun da suka ji takon takalmi suka ɗago suna kallonta haƙiƙa sun tsorata da kyawun matar ga yanayinta na  marasa son mutane da hayaniya haka,

Jinjina kai su kayi tare da kallon juna lokaci guda suka mayar dakansu ƙasa,
A second to the last steps na stairs ɗin ta tsaya Curus ! tana kallon tagwayen matan da tagani zaune saman kujerunta sai taga abun kamar a mafarki gadai marshal omar zaune to su waɗannan isassun da suka zauna matan saman kujerunta su wanene ta tambayi kanta, har hannu take sawa tana murza idanunta don ta tabbatar cewa ba mafarki take yi ba,
Idasa saukowa tayi har time ɗin bata sauke idonta ba daga nasu Hosana wani irin kallo take binsu dashi kallon neman ƙarin bayani,
Muryar Omar ce ta katse ta da cewa “barka da fitowa aunty, fatan na same ku lafiya,”
Lokaci guda ta saki fuskarta ta ƙarasa ta zauna saman 1 seater tana cewa ” Yawwa Omar saukar yaushe? wlh bacci ne ya kwashe ni nasan dae ka ce mun zaka zo nan bfr ka wuce abuja,”
Omar yace “Eh hakane, ina yaya ishaq ne?
“Ae bayan kabar nan, shima yayi tafiya,”
Ta faɗi tana kallonsu hosana da jahad, wadanda suka sha jinin jikinsu tuntuni musamman da suka gaisheta sai tayi kamar batagansu ba,
Miƙewa tayi tare da cewa “bari na kawo muku abun ta6awa,”
tayi mgnr tare da wuce wa kitchen, tana shiga ta tsaya riƙe da qugu tana sake sake iri iri aranta.
“Su wanene waɗancan twins ɗin da Omar ya kawomin a gida? hankali na fa bazai kwantaba har Sai nasan su wanene da kuma matsayinsu a wurinsa,”
ta ƙarasa tunanin nata tare da shigewa ciki tana shirya musu Abunsha dana ci,”

Su hosana da jahad kam sunfa shiga taitayinsu tundaga irin kallon da Aunty Babba tayi musu,
“Bacci kike ji ne har yanzu”?
Jahad ce tayiwa hosana tambayar, a kasalance hosana tace “sosai ma ga yunwa ina ji,”
“Wacece ke jin bacci”? Marshal Omar ya tambaya don yaji firar tasu,
Hosama tace “Ni ce, kuma hada yunwa nake ji ma,” tayi maganar tana ɗan turo baki,
Murmushi gefen fuska yasaki yana ɗan kallonta yanayin yadda tayi maganar ba ƙaramin tafiya tayi dashi ba,
” ok ki bari ki fara cin abincin sai ki yi wanka inyaso daga baya sai kiyi baccin ko? ya faɗi yana kallonta, hosana tace “to shikenan,”
Ya jinjina kansa

Shigowa Aunty Babba tayi hannunta ɗauke da tray tinkis tinkis take tafiya, har ta ƙaraso ta ajiye musu shi a saman table ɗin dake kusa da Marshal Omar,
“ki miƙa musu, ni bana buƙatar komai ynx,” ya faɗi yana kallon wayar dake hannunsa dayake dannawa,
daurewa kawai aunty babba takeyi, matsar musu da table ɗin tayi gabansu tace “gashi nan ƴan mata,”
Har haɗa baki sukeyi wurin cewa “mungode,”
Jiki na rawa hosana ta ɗauki coke mai sanyi ta buɗe tashiga ɗaɗɗakar lemun har ta kusa shanyewa duka, jahad kuwa jiki asanyaye ta ɗauki robar swan tana sha,
Jinjina kai aunty Babba tayi ganin yadda yarinyar take ta faman kerma jikinta na rawa taga abunci aranta tace “To fa !
Bayan ta koma ta zauna ta kalli marshal Omar tare da cewa “har yanzu bakayimun bayanin waɗannan twins ɗin ba dana ganku atare,”?
gyara zama Omar yayi cikin natsuwa yasoma magana “Babu buƙatar dogon bayani, na kawosu ne zasu zauna nan atare daku na wani lokaci…….’
Yadda aunty babba ta zabura tsaye yasa shi dakatawa da bayanin yana kallonta yace “lafiya”?
A susuce ta koma tazauna tana cewa “babu komai ci gaba da bayani,”
Ajiyar zuciya yasaku tare da cewa ” zasu zauna anan, kamar yadda nace bana buƙatar kowa ya kashe ko sisin shi akansu, komai suke buƙata lissafi kawai za’a yimun na turo,’
Murmushin yaƙe aunty babba tayi tare da cewa “wannan ae mai sauƙi ne Omar, zasu samu kulawa sosai amma abunda nakeso nasani shin su wanene su?
“Ba buƙatar sani Aunty Laila, kawai a kulamun dasu yadda ya dace,” ya faɗi yana kallonta,
Jinjina kai aunty babba tayi tare da cewa “shikenan za’ayi kamar yadda kace insha Allah,”
Ya amsa da “Okey ynx zan wuce masallaci kafin nadawo pls abasu bedroom ɗin da zasu zauna su huta,”
Ya faɗi tare da miƙewa yasa kai ya fice,

Maida idonta tayi kansu Hosana da jahad fuskarnan a murtuke,
Hosana sai faman cin fried rice ɗin da ta shaƙe a plate takeyi tana korawa da lemu a cup, ko lura da kallon da Aunty babba keyi musu batayi ba,
Sai jahad ce ta ankara da hakan har tayi saurin ajiye spoon ɗin dake hannunta cikin plate gabanta na faɗuwa,
Muryarta ce ta katse su da cewa “kai !! Su wanene ku? ƴa’ƴan waye ku a dangin Su Omar?
dakatawa da cin abincin hosana tayi tana kallonta, murya na rawa jahad tace ” Mu bamusan kowa a dangin shi ba, taimakon mu yayi saboda ya tsince mu cikin wani hali,’
Fashewa da dariya aunty babba tayi har saida suka razana, hannu tashiga tafawa tare da cewa “Wlh kun shiga uku !! meyasa baku bashi shawarar yakai ku Orphanage Home ba? Sai gidana za’a kawomin tsintattu, to bari kuji in faɗa muku Omar yayi gangancin jefa rayuwarku cikin haɗari domin ni bani da Imani wlh,’ ta faɗi a faɗace tana kallonsu
Gabansu ne yayi mugun faɗuwa just now suka zo gidan amma gashi matar gidan ta bayyana musu halinta tabbas akwai matsala,
Shewa tayi “Ahayyye !!! wai ni za’a kawo wa tsintattu na riƙe ae wlh kun shiga uku kuna cikin masifa domin Laila bata da mutunci ,
Sam sun gaza ci gaba da cin abincin jikinsu sai kerma yake yi saboda tsoran wannan matar da ta kira kanta da Mara imani, mara mutunci,
jinkirtawa tayi tana kallonsu tana yatsina fuska kafin tace “me kuka tsaya kuna kallone? Kuci gaba da cin abincin ku domin daga inda Omar yasa ƙafa yabar gidan nan kuda ganin Abinci sai dae kuji ƙamshin sa Wlh,” ta faɗi tare da miƙewa ta wuce room ɗinta dake asaman upstairs,
Tuni hawaye sun soma zubo ma jahad masu zafin gaske har taji ta tsani abincin da take ci ma, ita kuwa hosana jikinta yagama mutuwa jin abunda matar tace wato su da ganin abinci sai dae su ji ƙamshinsa, tuna wannan yasa ta fashe wa da kuka,
Haƙiƙa suna cikin tashin hankali kuwa,

Cikin kuka hosana tace “jahad Mun shiga uku,dama yaya Omar yabarmu gidan goggon mu da aunty saude,’ tayi maganar tana lashe hannunta ga hawaye sha6a sha6a,
Cikin shesshekar kuka jahad tace “hosana duk yadda za’ae karmu bari yaya Omar ya tafi yabarmu agidan nan, wlh kashe mu zatayi tace bata da Imani, kuma xata mana Horon yunwa innalallahi mun yi gudun gara mun faɗa gidan Zago ????

Jikinsu duk ya gama mutuwa ga gajiyar tafiya gashi suna son suyi sallah su ɗan kishin giɗa amma ba halin hakan,

Murya na rawa jahad tace “Hosana ki ci gaba da cin abincin, kwara muci ko na yau ne tunda tace daga yaya Omar yabar gidan sai dae muji ƙamshinsa,
Hannu suka sa Hannu suka ci gaba da cin abincin ba ƙaƙƙautawa, hannu baka hannu ƙurya suna ci suna matsar kwalla,
Sai da suka kammala da komai sannan suka jinkirta suka zauna jiki a mace,

Jin ƙarar shigowar motocin Omar yasanya Aunty babban yin saurin fitowa daga room ɗinta ta sauko down jiki na rawa ta kallesu tare da cewa “Maza ku share hawayen nan dake a fuskarku, wlh muddin ku ga ja Omar ya gane cewa wani abu ya faru saina Murƙusaku a wurin nan, Dallah ni ku taso ku biyoni,
Jiki na kerma suka bi bayanta cikin hanzari takai su wani room ya hadu sosai ba hayani komai simple,
Shiga ciki su kayi rai a6ace tace “ku shiga toilet ku gyara jikin ku, ko da gigin wasa kar na kuskura naga wata ta leƙo d daga ɗakin nan balle ma ta fito!”
Tana gama faɗin hakan ta fuce tana sakin murmushi mugunta,
Falon ta koma ta tattare kayan abincin da sukayi Amfani dashi ta wuce dasu kitchen, tana a cikin kitchen ɗin tajiyo shigowarsa,
Fitowa tayi tana faman sakin murmushi taƙarasa tana faɗin “harka dawo kenan,”
Ya amsa mata da cewa “Eh ina yaran suke,” ya faɗi a yayin da yake zama saman seater,
itama ta zauna tana faɗin “Ae tunda kasa kai ka fuce, bayan sun kammala cin abinci na nuna musu ɗaki ynx haka sun kammala wanka sunyi sallah ynx bacci ma suke yi,”
lumshe ido Omar yayi alamar jin daɗi aransa sannan yace “naso ace na nasake gaisawa dasu don yanzu zan wuce abuja,”
cikin sauri tace “gsky kam, amma fa sunyi nisa a baccin nasu, bai kamata atashe su ba,
Omar yace “hakane kuma, Ni yanzu zan wuce,” ya faɗi tare da miƙewa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74Next page

Leave a Reply

Back to top button