ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

Hakika sehrish ta samu natsuwa a ranta, azmee ta iya kalami masu dadi masu sanyi da ratsa zuciya,
zama tayi ta dinga cusa fruits din dake agabanta cikin bakinta, cikin dadi take shan su,
bayan ta gama dasu ta ajiye plate din ta dauko na meatballs din ta shiga dauka tana jefawa a baki, kunnanta har motsi yake, yayi dadi sosai, yaji kayan kamshi, lokaci zuwa lokaci ta kan hada da cool milk din dake acikin cup, tana kurba ????

Kwance suke rungume da juna, daga su sai dan towel a waist dinsu, da alama daga bathroom suka fito duba da ruwan dake a jikinsu,
“Ayaan ba karamin dadi naji ba wlh’
“game da me kenan ? Jahan ya tambaya yana kara shafa sumar kan ayaaan,
“game da zuwan babban yaya, i felt so happy da junaid ya sanar damu cewa ba date ba time na zuwansu,’
murmushin takaici Jahan ya saki tare da cewa “hmmm da alama bakasan wannan mutumin ba, ni nayi imanin cewa daker babban yaya zai wuce gobe baizo nigeria ba !!!! Ina ji araina !
dan dagowa Ayaan yayi daga jikin jahan yakasance yana kallon face dinsa, cikin kwarkwasa yace “pls stop thinking about that, kawai musa wa ran mu cewa ba nan kusa zai dawo ba, hakan zai bamu courage din ci gaba da jin dadin junan mu,,”
murmushi Jahan ya saki yana kallon cikin kwayar idon Ayaan wadda takasance ash colour ce, mai ruwan toka, mai kyan gaske , shima kallonsa yake yi cikin tsananin sha’awar junansu, zuciyoyinsu na kara azalzalansu akan su kara second round, hannu jahan yasa ya janyo ayaan bakinsu ya hade dana juna ya zura harshensa acikin nasa, nan suka shiga misayar saliva a tsakaninsu,

………………….AUNTY BABBA…………………

zaune take agefen amani sbd dama basu tafi ba, suna jiran zuwansu babban yaya, duk da ita amani acikin garin take , amma abbas ya bata iznin ta zauna ta kwana tunda auntyn ta na nan itama , Inyaso zuwa gobe sai ta dawo gida,
Dukansu suna sanye cikin sleeping dress, riga da wando, masu kyan gaske, kowa ta zubo gashin kanta dayake Allah yabasu,
“Ina sauraronki aunty na” amani tayi mgnr tana kallon auntyn tata dake gefenta saman gado,
“Shiri na musamman ya kamata muyi wa lamarin domin cin nasara akan wadannan zafafan guda biyu, shawo kansu ba abu mai wuya bane, dole sai an hada da shahararrun bokaye, kamar wannan bokon na kurmin dajin nan dake a enugu, “
Xaro ido Amani tayi tare dacewa “Aunty enugu fa kikace ? gsky da kamar wuya wlh,’
Dariya aunty babba tayi tare da cewa “a wurinki ba, ae ni akan na cimma buri na wlh ba abunda bazan iya yi ba, hmmm ke dai kawai abar kaza cikin gashin ta har ynx bakisan wacece yayarki Laila ba, ‘
zugun Amani tayi tana kallonta hankali a tashe, lamarin ya fara bata tsoro “yanzu aunty yaushe zaki enugun?
Cike da kwarin guiwa aunty babba tace “Ni bana aiki cikin gaggawa, a sannu zamu cimma nasara, amma kafin nan muna Bukatar kudade dayawa, don tunkarar wannan bokan ba abu bane mai sauki, dole mu hada karfi da karfe ki tatsar mana wurin abbas nima na tatso wurin Ishaq, daga bisa ni mayi mgnr zuwa can,’
shiru amani tayi ita dai haryanzu akwai karaya atare da ita, cike da kasala tace ” aunty nifa ina tsoro wlh,”
Mtswww aunty babba taja tsoki “ke dallah wane tsoro, aje wannan ma gefe, ke bakisan abunda nake hango mana ba, muddin muka ci nasara akan Babban yayansu da marshal omar to ina mai tabbatar maki da cewa gabadaya zamu rinka juya kowa na family dinnan, sai yadda muka so za’ayi”
ta idasa magabar tana kallon Amani, wadda tayi tsuru tsuru,
ajiyar zuciyata tasaki har zatayi magana wayarta dake saman saman pillow ta soma ringing, da sauri takai hannu ta duba sunan “Babyna” ya bayyana
Aunty babba tace “halan Abbas ne ? Amani tace “eh shine,’
“Yawwa maza ki daga, ki rinka kashe masa murya kina masa ladabi ko mun ci nasara akan kudin da muke bukata,’
amani ta amsa da to, tare da picking call din ta kara a kunne tare fadin ” baby na y kke? nayi kewarka sosae,”
Saurara wa tayi tana sauraran muryar abbas dake cewa “nagaza bacci ne, na fito daga wanka ne, naji ba abunda nake son ji face muryarki,”
Murmushi Amani tasaki tana kallon aunty babba data kura mata ido, cikin sanyin murya tace “nima haka babyna, ynx haka maganarka nake ma,’
“Are u serious ? Zamu yi video call ne inaso naganki cikin sleeping dress din nan naki, ‘
Kallon aunty babba tayi taji me zatace saboda wayar a handsfree take, da ido tayi mata alamar tace masa eh,
“Eh babyna a shirye nake , nima a kagare nake dana ganga, “
Murmushi aunty babba, tayi tare da mike wa ta fita daga dakin tana ji aranta cewa burinta zai cika,

Dare yayi sosai Junaid na dakin abbansu , ya addabe shi ya hana shi sakat, shi ala dole ga auta, suna kwance atare saman king size bed dinsa, junaid ya aza masa kafarsa a saman jikin abbannasu, zallar rigima yake ji,
“Junaid dan Allah ka barni na huta, ka tafi bedroom dinka ka kwanta mana, ko kaje Wurin yayyen ka kwana mana,” abban nasu ne yayi maganar cikin jin bacci,’
cikin shagawaba yace “nafi jin dadin kwanciya ajikin ka abba, In kuma kana so nadaina zuwa kwana nan, tam ka je ka dawo da mommyn mu, “
rai a dan bace abban nasu yace ” kada na sake ji ka kira min sunanta Allah,”
Cikin zolaya junaid yace “kaifa kace kana so Abba, ba wanda yayi maka dole, saboda dadin soyayya ko su Ammi basu sani ba kaje har us ka aurota, wato kaga kyakkyawa, doguwa fara mai dogon gashi ko ?
Yunkura wa abban yayi tare da fadin “bismillah” ya janyo pillow, ya shiga bugun junaid dashi, dama sun saba ya maida shi tamkar tsaransa, kuma Abban ba karamin dadin hakan yake ji ba, cikin kukan wasa junaid kecewa ” Abba dan Allah kadaina ae gsky na fada, wlh momyn mu akwai kyau, shi ya rudaka ma,
Cikin mamaki abban yace “wai junaid ko dan muna kwana shimfida dayane yasa ka raina ni?
dariya suke gaba dayansu, duk yadda yaso junaid ya rufe bakinsa ya daina masa maganar Alexandra (Alekzandra) amma yakiya, dakyar bacci ya kwashe su, su duka,

Insha Allah za’a samu Lunch ko dinner, in Allah ya yarda amma ✨
????????SURGEON GENERAL RAFAYET & MARSHAL OMAR????????

Welcome to Nigeria ????

finally our Stars Sun bayyana ????

????????????ABBAN SOJOJI????????????

ku kaddara cewa page 1 ne wannan domin kuwa yanzu labarin ya soma

Page 57

Writer HAFSAT BATURE ~BossLady~

Bayan ta kammala cin abunda azmee ta kawo mata kitchen ta mayar da kayan, sannan ta dawo ta shiga toilet ta daura Alwala, ta zura hija bi ta shiga jera salloli, bayan ta kammala ta rufe da zafafan addu’o’i tana nema ma rayuwarsu sauki, tasha kuka ayayin da ta daga hannunta sama tana rokon ubangiji, hawaye na gangarowa a idonta,
Ba ita ta kwanta ba sai cikin dare ya taba, sannan ta kwanta, tare da rungumo pillow a chest dinta kamar yadda ta saba, tabbas ranta na bata cewa Babban yaya bazai wuce gobe ba bai dawo ba, saboda taji wani sanyi aranta, amma bata da tabbacin hakan , sai in Allah ya kaimu da rai da lafiya sai kuma in hafsat bature ta so hakan, dayake wuka da nama suna hannunta, ????????????


Mutum biyu ne suka san da zuwan su Abba da junaid sbd sunyi receiving call dinsu in d midnight, a time din mu na nigeria jirginsu zaiyi landing around 9:00am,
A Wani irin haɗaɗɗen katafaren privet jet ne ya ɗauko su, wanda ya kasance mallakin Surgeon general RAFAYET, ya haɗu fiye da tunanin mai tunani, cikinsa bai da banbanci da hamshaqin parlour wanda yaji tsadaddun furnitures, saboda an ƙawata shi da jigunannun furnitures,
Wato Aljannar duniya ce, acikinsa ya ƙawatu, ????
Wasu hamshaƙan leather seats ne acikinsa jigunannun gaske, wanda ko a ido ka kallesu kasan zasu yi tafshi da daɗin zama, masu numfashi irin waɗanda kana zama zasu lumbutse dakai ciki,
A jere suke biyu suna facing ɗin biyu zungura zungura, a tsakankaninsu wani ƙayataccen table ne haɗaɗɗen gaske, mai ɗauke da travel cups wanda abunsha ne acikinsu, tukunna ma shin su wanene acikin jirgin ? ????
tunkan na fara zayyana su zan fara da faɗin tabarakallahu ahsanul khaliqin ????
Haɗaɗɗiyar sura, dogaye ne masu cikakkiyar ƙira irin ta zakuna, irin ta mazan gaske sadaukai kuma jarumai, ƙerarrun gaske, duk inda namiji yakai to su sun zarce nan, komai nasu na kece raini ne ba wasa a tattare dasu babbar harka ne, duk iya haɗamar mace bazata wuce waɗannan handsome stylish guys ɗin ba, buri kowace ƴa mace nesu, a fage na kyau kuwa ba’a magana, ƙarshe ne su, a bangaren wadatar arziki kuwa basai an faɗa maka ba, kana ganin su kasan cewa sun wanku da pawns da dollars, fatar jikinsu kaɗai abun kallo ce, su huɗu ne zaune kowa ya hakimce, jirginsu kawai suke jira yayi landing,
3 daga cikinsu suna sanye cikin expensive dress na suits, biyu launin nasu blue ne ɗayan kuma black ne,
Mutun ɗaya ne baya sanye cikin suits ɗin nan, shin wanene shi? Jikinsa na sanye cikin V-neck shirt , tayi tighting ɗinsa, white colour yayin da yake sanye da army trouser,
Yana da wata irin sura mai matukar rikiɗarwa mai razanarwa mai matukar jan hankali da ƙayatarwa, saboda a halitta dogo ne, mai wani irin faffaɗan ƙirji a buɗe yake, ga wannan six pack din nasa baro baro, ya cika vest ɗin kana ganin zanen ƙirjinsa ga breast ɗinsa sunyi 6ul-6ul ata ciki kana hangensu, daga gani yana gym (motsa jiki) sosai, in ka kalli damtsen hannunsa sai ka tsorata, kana gani kasan cewa yana da matuƙar ƙarfi kamar ɗan wrestling (dambe) haka surarsa take, mutun ne mai ji da ƙarfi,
Idan muka je wurin tommy dinsa kuwa a shafe yake ba alamar tumbi ko kaɗan, yayi flat, tamkar baya zuba abinci acikinsa saboda ɗamewarsa,
Launin fatarsa fari ne sol irin hasken fatar ƴan korea, natural white kasancewarsa half cast (ruwa biyu) mahaifinsa hausa fulani, mahaifiyarsa baturiya, ya kuke ganin abun zai kasance?
A wurin kyau kuwa sai dai muce tubarkallah, domin Allah yayi sa da wani irin ƙayataccen kyau mai matuƙar razanarwa, ko namiji jinsin sa ya kallesa sai ya ƙyasa balle mace, yadda kasan shi ya zana kansa, don duk mun haɗamar bil’ama aka basa damar ya tsara yadda kyansa zai kasance, bazai wuce nasa ba sai dai ma ƙasa da nasa ????
Komai na halittar jikinsa dogo ne, kakkarfa domin Allah ya wadatasa da duk wani abu da mace zata buƙata ajikin ɗa Namiji!
Idan muka koma kan haɗaɗɗiyar suman kansa kuwa mai tsayin gaske wadda ta sauko masa har saman kafadarsa , tasha gyara na musamman ya ɗaure ta, dark brown ce Allah kaɗai yasan nawa ake kashe ma wannan suman wurin gyara,
Hatta gaban forehead ɗinsa sumarce a kwance, ga wani kwantaccen saje mai shegen kyau, eye brows ɗinsa kuwa tamkar an zana ta, tayi wani irin shape ga gashi cike da ita, kiris ya rage jagirarsa su haɗe da juna saboda yawaitar suma a wurin, idan muka koma kan idonsa kuwa yana eyelid (kwarin ido) wadatacce wanda ke lullu6e da eyeballs ɗinsa, yana da dogayen eye lashes masu cukowa da tsari, ga kyan gaske
Allah yabasa kyawawan idanuwa ga girma ga su so sexy, farare tass tass masu ɗauke da kwayar ido, blue colour masu shining masu ɗaukar ido,
daga ƙasa kuwa dogon hancinsa ne, ba wai irin ziƙau ɗinnan ba, a’a mai tsari dai dai wa daida, daga nan kuwa sai pink lips ɗinsa tamkar ya shafa jan baki, ga skin din la66ansa irin mai squeeze ɗinnan ce,
Cikin natsuwa yake daddana laptop ɗin dake gabansa saman table, ƙirar Luvaglio wadda price ɗinta yakai $1 million ne (dala miliyan ɗaya) a naira kuwa yakai 600millions, miliyan ɗari shidda, cikin natsuwa yake daddana ta da zira ziran yatsunsa, hannunsa na sanye da wrist watch kirar piaget emperador temple ce, farashin ta yayi $3.5 million a naira kuwa ba’a magana billions ne ke magana,
Zan iya cewa duk macen da zata so shi ba don Allah bane, zai yi wuya asamu macen da zata so shi hakanan kawai ba don wani abu nasa ba, kamar kyansa, tarin dukiyarda shi kansa baisan adadinta ba, surar jikinsa ga kuma ilimin addini dana zamani, komai ya haɗa komai nasa is Extraordinary,
Basu kadai bane acikin jirgin akwai wasu gabza gabzan soldiers wadanda suke a matsayin security guards nasu, mostly dinsu black americans ne, ba wasa a tare dasu, basa ji basa gani umarni kawai suke jira su aiwatar ????
Bakowa bane wannan face SURGEON GENERAL RAFAYET ???? wanda kowa ke zumuɗin ganinsa, wanda hafsat bature da sehrish suke kwakwar ganinsa, tare da mamee da kuma readers????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74Next page

Leave a Reply

Back to top button