ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

Kwan ! kwan !kwan taji an knocking , cikin sauri ta karasa ta bude kopan azmi ce tsaye fuskanta da murmushi tace “tukur ina fata ka shirya sbd ynx zamuje na nuna maka yarda abun aikin yake ,”

Cikin girmamawa sehrish tace “toh hajiya ,”

Azmi tayi mata wani irin kallo har gaban sehrish ya tashi a tunaninta ta gano lagwanta , amma sai taji tace “stop calling me hajiya , my name is azmi call me by my name , cos we re d same , am a house maid just like u ,”

taka rasa mgnr tare da fice wa tana cewa “follow me” rishi ta bi bayanta tana d’an murmushi ,

Kitchen suka shiga amma sehrish ta gaza gane a ina suke , haduwar wurin ce ta rikitar da ita , an kawata komai na kitchen din da dukkannin abubuwan da akeso,

Sam ta manta aiki ya kawosu sai faman kalle-kalle take yi , sai da taji muryar azmi a kunnanta sannan ta dawo dai dai

“tukur ynx bamu da enough time , we’ll make a dinner now in yaso zuwa tomorrow i will explain everything to u , Especially zama da samarin gidan nan darasi ne me zaman kansa duk zan koya maka ,”

sehrish sai take ganin maganar azmi kamar shiriri tace , ynx har akwai mutumin da za ace sai an koyi darasin zama dashi ?

haka suka fara aiki , azmi ce ke yin girkin , yayin da tabarma sehrish ferar dankalin turawa , ga yankan albasa , acewarta tafara da karamin aiki ,

Suna cikin aiki sehrish tafara jiyo karar shigowar motoci , rass taji gabanta ya fadi , da jiniya motocin ke shigowa ,

“Hmmmm wannan alama ce mai nuna cewa masu gidan sun dawo ” a cewar azmi ,

Zuciyar sehrish sai harbawa take yi saboda tsananin firgicin da wa zata fara cin karo ,

“Ka’ida ne daga sun shigo babban falo zasu fara kwalamin kIra ka saurara kaji ,” azumi ta fada tana murmushi ,

Hannun sehrish sai kakarwa suke yi ,

ita dai baza ta iya tantance muryar mutun nawa bace amma taji sauti iri iri

“Azumi ! Azmi !! Azam zam !!!” da karfi suke kwala mata kiran without any respect , cikin sauri azmi ta fice tana ce ma sehrish “pls ka kula da girkin am coming back now ,”

Sehrish ta amsa da toh , daga inda take tana iya hangosu saboda kitchen din irin model design dinnan ne wanda ba kopar shiga gare sa a bude yake bata iya identifying faces dinsu ,

Hankali a tashe azmi takarasa wurunsu tana fadin “welcome back Sirs ,” ko arziki amsa bata samu ba sai complaining da suka soma yi mata, “Ina fata angyara min bedroom dina don bansan kazan ta ! in ma kinsan baki gyara ba let me know ,” daya daga cikinsu ne yayi wannan maganar ,

matsawa tayi kusa dana gefensa don taji shi mai zaice , hannu ysa yana shafa ciknsa yace “Ni matsala ta abunda zansa ma cikina pls kafin na shiga ciki nayi bath na tarar da abinci jere saman dining table if not kinsan sauran ,”

matsawa azmi ta sake yi kusa dana gefensa dayake duk suna a jere kusansu takwas,

” Na fadamiki Injin wanki na ya samu matsala dazu da safe ga shi na tara kayan dauda , gajerun wanduna na ma duk sunyi dirty dafatan kin wanke mun su ,”

Haka ta dinga sauraransu ba wanda baiyi magana ba acikinsu , bayan ta gama sauraransu one by one tace ” Komai da kuka lissafamin na kammala sa , abinci ne kawai shima ynx zan idasa ,”

Kama hanya suka yi kowa ya wuce bedroom dinsa , wasu na upstairs wasu na a downstairs,

Babu abunda ya burge sehrish sai kakin sojojin dake jikinsu , abunka ga handsome guys ga tsawo ga hadaddiyar sura sai abun ya bada citta ????

tunanin ta soma yi a ranta “oh ni ko wanene babban yaya acikinsu , koda yake naji azmi tace ba sojan nigeria bane U.S ARMY ne , zanso nagansa daga ji ya hadu yadda hajjaju ke zuzu tashi ,”

takarasa tunanin tana murmushi ita kadai abunta , shigowa azumi tayi tana fadin “maza tukur a shirya abinci a dining before su fito, ai ina ji girkin ya isa ya kammalu ,”

Wasu hadaddun kuloli ta dauko daga kitchen cabinet kamar ranar aka budesu daga kwalinsu tsantsar kyansu kamar ba abinci za’a zuba ciki ba , saboda yadda murfinsu ke glowing har face dinka zaka iya gani aciki just like mirror ,

A wani faffadan tray ta shirya komai ciki , ta mika wa sehrish azuwan taje ta fara shiryasu a dining ,

Gaban ta na faduwa ta karba tsoranta da wa zata fara cin karo a cikinsu , time din da ta isa dining room din , mutun d’aya ta samu zaune shi ya rigasu fitowa jikinsa na sanye da white tshirt da black short , bai lura da ita sai da yaji cool voice dinta ta sauka a kunnan sa ” sannu da hutawa ” a natse ya dago yana kallonta ,

lokacin da suka hada ido kara ware idonta tayi ganin irin kyawunsa , dan matashi ne ba zai wuce 18years ba , a tunaninsa zai ga mace amma sai ya ga namiji tabbas shi muryar mace ya ji mai dadin gaske a kunnan sa ,

Wani kayataccen murmushi ya sakar mata , wanda yasa ta shiga yanayi , cool voice dinsa ce ta ratsa ta “am nace ko sabon mai aikin da akace za’a kawo mana ne?daga masa kai tayi alamar eh ,
Jinjina kansa yayi tare da d’an tabe small lips dinsa ,
Soma jera abincin tayi , bayan ta gama ta koma ta dauko sauran abubuwan da bata kawo ba ,

Allah Allah take ta kammala jera abincin kafin sauran su karaso , muryarsa ce ta kara katse ta ” chicken pepper soup din nan zaka zuba mun ka hadamin da irish cikin plate din ,” ta amsa toh kamar wata munafuka haka take sunnar dakai , Ji take kamr asirinta zai to nu ,

Plate ta zaro daga cikin set na filattan da takawo , bude daya daga dana cikin kulolin tayi , nan da nan kamshi ya gauraye wurin , saving spoon ta dauko ta soma zuba kazar a cikin plate din , sai faman hadiye miyau take yi , ga hannun ta dake kakarwa ga wani gumi dake sauka daga gefen sajenta ,

Kammala zuba kazar tayi sannan ta bude kular da ke dauke da irish ta zuba masa k’adan muryarsa ta sake ji “yayi mun k’adan ka take mun plate din “

cika masa plate din tayi dam sannan ta tura masa gabansa , cikin sauri ta kama hanya zata koma ciki “spoon din fa ko so kake na dauka da kaina ne sannan a gidan ku haka ake ba mutun abinci ba tare da drinks ba ‘? har zuciyarta taji wannan maganar a tunanin zaiyi saukin kai ganin da farko yayi mata murmushi ,

lallai ta jinjina wa izzarsa , ga cokulan kusa da shi ga kuma drinks din da ta jera amma yafi karfin yasa hannu ya dauka sai da ita ta mika masa ,

guntun murmushi tasaki koma tayi ta mika masa cokalin sannan ta zuba masa lemu a cikin glass cup ta mika masa , yamutsa fuska yayi tare da sa hannu ya karba yana cewa ” gsky kana bukatar training don da ace babban yaya ko captain kayima haka da ka gane barno gabas take don sai kayi tsallan kwad’i ,”

Ya karasa maganar yana kurban lemun da ta mika masa , a wani irin yanayi sehrish ta juya wannan ne karo na biyu da taji an ambaci BABBAN YAYA , hakan nakara sa mata tsoransa a zuciyarsa ,

Komawa tayi kitchen ta samu azumi tana gyara wuraren da suka bata , jin shigowarta yasa ta dagowa tare da cewa “subhanallah meyasa ka dawo ka kammala saving dinsu ne “?

“A’a naga basu fito bane shiyasa na tafo ,” tayi maganar fuska a yamutse sbd rashin natsuwa da take ciki , azumi tace “maza ka koma karka ja mun bala’i , bakasan halin mazan gidannan ba ,”

Ba haka sehrish taso ba , jiki a sanyaye ta kama hanyar komawa dining room din , hannu azumi tasa ta rike habarta alamun mamaki tace “lallai dole na mike tsaye akan yaron nan ! yana abu kamar mace anya wannan ba dan daudu bane ? ta tambayi kanta ,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74Next page

Leave a Reply

Back to top button