ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

……………Sehrish…………………

Bayan sun kammala dinner ɗin, azmee tace
“Sehrish ki je ki yi sallah, bari na idasa jera dinner ɗina, sannan karki manta ki isa a lokaci dan Allah,”
Azmee ce tayi maganar a yayin da take fice wa daga kitchen hannunta riƙe da warmers cikin tray ,
“To aunty azmee ynx kam zan kimtsa,” tana gama faɗan hakan ta wuce bedroom ɗinta, bayan tayi sallar magrib tayo wanka shaf shaf tayi ta kimtsa, cikin dogon wando Jeans da riga ƴar ta maza, ta naɗe gashin kanta taturasa cikin hularta sannan ta laga mayafi daga sama, ta gyara gashin bakinta ya zauna daram,
Tsayawa tayi tana kallon kanta cikin mirror ɗin, murmushi ta ɗanyi kafin tasa kai ta fice, tana Allah Allah acikin ranta,
Babu kowa a babban falon, bi tayi ta wuce time din da tazo harabar gidan adai dai time ɗin motocin su suka soma shigowa hada ta sgr duk ba’a tare da suke ba, amma atare suka iso gidan hadasu kanal yusif dasu irfan fawan da sauransu,
tsayawa tayi tana kallon motocinsu, firfitowa su kayi atare, kowanne cikin kakinsa, sai bayan sun fito sannan wani soja narkeke ya fito daga cikin motar Sgr ya buɗe masa ita, shima ya fito dama jeans ne da t-shirt ajikinsa, ganin sa yasa su kanal yusif ƙarasawa suna gaishe shi,
Gwanin burgewa sehrish tabisu da kallo especially mutumin ta, sai da duk suka shige ciki sannan ta wuce cikin garden ɗin gidan cike da fargabar wa zata tarass,

Ko da ta isa cikin hadaɗɗen garden ɗin sai ta boye bayan bishiya tana leƙensa

Tsaye yake cikin dress na pakistani masu kyan gaske riga dogowa ta wuce guiwarsa sai wano burgujeje irin nasu,

Rigar mai dogon hannu ce purple tasha adon sparking stones, wandon kuma light pink ne zallah ba kwalliya jikinsa , daga gefen kafaɗarsa scarf ne (mayafin da mazan pakstan ke yarfawa a shoulders ɗinsu)

Zuba mishi ido sehrish tayi tana tunanin wanene wannan ? Saboda ya juya mata baya, bazata iya shaidasa ba,

Launin fatarsa da tagani fari tass da kuma kwantacciyar sumar kansa smooth black ya tabbatar mata da cewa bazai wuce Junaid ba ko Fawan ko cikin su twins saboda sune ke da wannan hasken 6ayau,

Shiru tayi tana ƙoƙarin gano kowanene da kanta, amma sam ta kasa canka har sai da muryarsa ta ratsa kunnanta mai sanyin gaske “Sannu da zuwa,”

Murmushi sehrish ta saki tare da cewa “Yawwa sannun ka,”

Shima yace “yawwa meyasa ki ka 6oye a bayan bishiya, kina shakkar ganin kowanene ya kamata ki fito,”

ƴar dariya sehrish tayi sannan ta fito daga bayan bishiyar ta tsaya daga bayansa tace “Wanene kai,’ meyasa bazaka juyo ba mu fuskanci juna ba?

“Zan juyo amma firstly saikin fara faɗamin wanene Ni ki canka kawae,”

Wani irin daɗi ne ya rufe sehrish, natsuwa tayi tana kallon bayansa ciki da son gano ko wanene shi,

Shima shiru yayi yana jin duk wani motsinta, burinsa sehrish ta shaida shi kafin ya juyo mata da face ɗinsa,

“Am waiting 4 u Sehrish,” ya faɗi da murmushi a face ɗinsa,
Shiru sehrish tayi tana tunanin wani abu aranta,
“Idan har zanyi zurfin tunani zan iya gano wanene, na farko wannan hasken shi fari ne sol, fawan kuma hasken fatarsa mai yellow yellow ne, Ayaan da jahaan kuma nasu yayi ja haka launin fatarsu, kai wannan fa kamar junaid ne,”

Tayi maganar acikin zuciyarta, wani tunani ne ya sake zuwa mata,

Junaid shagwa6a66e ne duk yadda yayi magana ana gane wa, yanzu bari na gwada wani abu a sanina da junaid baida jumuri in ya gaji sosai yaji naƙi bashi amsa dole yayi magana da shagwa6a,

Murmushi sehrish tasaki ta tsaya riƙe da waist ɗinta tana jiransa ya hasala yayi mata magana,

Aikuwa maganar sehrish ta tabbata, da yaji shiru shiru bata bashi amsa ba kuma tayi masa shiru,

Cikin shagwa6a ya buga ƙafarsa tare da cewa” wai ba zaiki yi magana ba, so ki ke ki wahalar dani koooo.. .’ yayi maganar tamkar zaiyi kuka,

Fashewa da dariya sehrish tayi cikin tsantsar murna da farin ciki tace ” JUNAID!!! Wlh kaine na gano ka ,” tayi maganar da ƙarfi,

Wani irin farin ciki ne ya rufe junaid juyowa yayi fuskarnan tasa ɗauke da kyakkyawan murmushi ,

Zubawa juna ido su kayi suna ta faman sakarwa juna murmushi, don ita sehrish hada dariya sosae Sam farin cikin ta ya gaza 6oyuwa ????????????

(Nace ba Romeo fa yau sun haɗe da juliet, don haka sai mun haɗu a next week)

Share ????????????????ABBAN SOJOJI????????????

????The father of soldiers????

~hot novel drama~ ????
Mallakin
Hafsat Bature Moh’d

~BossLady~✨

Not edited

page 79-80

daker suka dakata daga yiwa junansu dariya, junaid yace “bismillah sister tukur ga wuri ki zuna,” yayi da maganar yana nuna garden chairs ɗin,
Murmushi sehrish tasaki cikin jin kunyar abunda junaid yace wato Sister tukur, cikin natsuwa suka zauna suna fuskantar junansu haɗaɗɗun kujeru ne irin french bishro design ɗin nan, gabansu akwai table launinsu coffee color,
Sai faman sunnar da kai sehrish take yi tana wasa da yatsun hannunta,
Yayin da junaid ya zuba mata ido,bayan masu ƴan mintina yace “Can we talk”?
“Yeah” sehrish ta bashi amsa
Junaid yace “First of all, naji daɗin ganinki as a woman, ina fata ke ma haka?
Jinjina kai sehrish tayi tare da cewa “Sosae ma,” murmushi junaid yayi kafin yace “in da gaske ne, to inaso ki ɗago da idonki ki kalli cikin nawa muyi magana, sannan ki cire wannan gashin bakin da cap ɗin nan inaso na ganki da kyau,”
ɗan waro ido sehrish tayi tare da cewa “In wani ya ganni fa”?
Junaid yace “ae babu wanda zai zo nan, duk ynx suka dawo agajiye so karki ji komai,
Ajiyar zuciya tasaki tare da sa hannunta ta cire gashin bakinta, ta ajiye shi asaman table ɗin gabansu, sannan a hankali tasanya hannu, ta zame mayafin da ta naɗe hular dashi, sannan ta zame hular gaba ɗaya, ta ajiye su asaman table ɗin duka,
Lumshe ido junaid yayi yana kallonta, a yayin da sumar kanta ta soma warwarowa da kanta ta zubo mata har ƙugunta, tayi mata tamkar hijabi, kwantacciyar suma dark black very smooth,
Cikin sanyin murya ta wanda ya gama kamuwa yace “Masha Allah yanzu nan tukur ɗinmu ne ya koma haka? Ƴar kyakkyawar budurwa,”
Yayi maganar da zolaya, fashe wa da dariya sehrish tayi, sai da ta tsagaita sannan ta samun ƙwarin guiwar cewa “I want to ask you something pls,”
Junaid yace “Ina sauraron ki,”
ɗan gyara murya tayi sannan tace ” yaushe ne ka gane cewa ni maca ce? kuma sannan ya kaji aranka,”
murmushi junaid yasaki kafin yace “Na jima da sanin hakan, but am sorry to say bazan iya faɗa miki ranar da nagane cewa ke maca ce ba, sai nan gaba, sannan maganar ya naji araina dana gane hakan, seriously i felt so happy bansan ma yanda zan misalta ba,”
Wani irin daɗi ne ya rufe sehrish sai faman satar kallonsa take tana sunnar da kai,
“I ave a question too,” junaid ya tambaya,
Cikin sauri sehrish tace “What”?
“It’s just a question pls, don’t feel anything, am… Kece ki ke mun amfani da wayata ko? Ya tambaya yana kallonta,
Wurga ido sehrish tayi ta ɗan kalli ruwan dake gudana wurin, taƙi yarda su hada ido saboda jin kunyarsa,
ƴar dariya junaid yayi kafin yace “tun da bazaki ban amsa ba, bari ni na baki, kece ki ke mun amfani da wayata kina kiran ƴan uwanki, da farko Nasanya security ɗin wayata finger print, wato sai kika rinƙa lalla6owa while i was sleeping kina using da yatsana kina buɗe wa, afterwards dana gane ana mun using da phone ɗinsa saina maida shi face security nan ma ki kayi kokarin ki sa a face dina don ki bude ko ? Anyi hakan ?
Ya tambaya da murmushi a face ɗinsa yana kallonta, sai faman sunnar da kai take yi tana dariya,
Junaid yaci gaba da cewa “ranar dana kama ki a bedroom ɗina, kina rarrafe zaki kin lalla6a zaki gudu, time ɗin na tashi daga bacci, muka haɗa ido dake zaki fice, kawai sai kika fashe mun da dariya ko ba haka akayi ba,’? Ya ƙare maganar tasa da tambaya,
Hannu sehrish tasanya a bakinta, tana ta faman tiƙar dariya shima kansa dariyar yake yi,
Bayan sun tsagaita da dariyar tasu junaid yace “bayan nan akwai time ɗin da kina saving ɗinmu abincin dinner, phone ɗina yayi ringing, nayi picking call ɗin kwatsam sai ki kaji muryar Sister ɗinki, wanda hakan yasanya arazane ki ka saki cup ɗin dake hannunki har ki ka 6arawa Ayaan ruwan coffee mai zafi, Anyi hakan?
Ya sake jefa mata tambayar yana yi mata kallon MAGE TA KAMA 6ERA,
Cikin jin kunya sehrish tace “Am so sorry pls,”
“why are u saying sorry to me sehrish? Ni baki mun laifin komai ba, abun ma sai ya zamar mun kamar drama, naji daɗin hakan,” ya faɗi yana ci gaba da kallonta,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74Next page

Leave a Reply

Back to top button