ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

A kitchen ta Sami azmi ta kammala shirya komai na kalacin safen , duk sai taji ba dadi sukuku ta isa gare ta ta ce “barka da safiya nayi laifi dan Allah ayimun uziri,”

Babu alamun bacin rai a fuskar azmi ta ce ” karka damu tukur, ba wani abu nan gaba dae aguji yin hakan”

Sehrish ta amsa da toh insha Allah yanzu wani aiki zan yi ?

Ba wani aiki kawai abunda ya rage ynx kabi bedrooms din kowannan su ka Sanar dasu su fito su yi breakfast ya kammalu,” azmi ta karashe maganarta ta tana kallon ta,

Cikin zullumi sehrish ta fita ta tunkari jerin dakunan dake a downstairs , na farko ta fara kwankwasa wa shiru ba’a bude ba , kara knocking tayi da karfi , har sai da ya isarwa mai dakin , muryarsa tajiyo ashake yana cewa “who’s trying to disturb me? d’aga murya tayi tare da cewa “tukur ne sabon mai aiki,”

“Shigo ciki” ya ba ta izni , turo kofar tayi tare da kutsa kai ciki, har cikin ranta dakin ya yi mata kyau bedroom kamar na mace saboda kyau ga tsafta sabanin wasu mazan da idan ka shiga dakunansu kamar wurin safkar y’an gudun hijra saboda tsaban tarkace da har mutsi,

“Idan ka kammala kalle kallen naka sai ka sanar dani abunda ya kawo ka,” muryarsa ce ta dirar mata a kunne sai lokacin ta mayar da idonta akansa , kwance yake a baje saman katafaren gadonsa rabin jikinsa yayi covering dinsa da lallausan blanket , Yusif kenan

Cikin en ina sehrish ta ce “am ..emm dama an kammala breakfast ne shine aunty azmi tace nazo na sanar daku.”
ta kammala maganarta ta tana wasa da yatsun hannunta , jin shirun bai ce komai ba ya sa ta dagowa ta saci kallonsa , samun shin tayi yana yamutsa fuska alamar an takura masa cikin lallausar muryarsa ya ce “Idan ina jin yunwa ai ba sai anzo an tayar dani ba ni zanzo da kaina ciki na ne ko cikin wani? ya tambaya yana kallon ta ,

Cikin sauri tace “cikin ka ne” ok fi ce ka ban wuri , ya fada tare da jan bargonsa ya idasa rufe face dinsa ,
Kamar wacce kwai ya fashe mawa a kai haka ta fita salalau salalau , a cikin ranta kuwa tana jinjina ma isa irin tasa ” tab aiki y ganni ni sehrish daga abun arziki, wannan shi ake kira da samun wuri tusar asuba, Allah sarki mukam ya’yan talakawa don uban mutun kar Allah yasa ya nemi abinci har rana ta fadi ya ga in za’a a damu dashi kasha iya barcinka yunwa ta taso ka, ka lallaba ka je neman kason ka wani sa’in ma an manta dakai, su kam wadandannan genius din bibiyarsu akeyi suzo suci suna make wa,”

Ta karasa tunanin nata a dai dai lokacin da tazo kofar dakin the next person , knocking tyi bugu d’aya taji ance “Come in”
turo kofan tayi ta bude Samun shi tayi zaune saman sallaya jikinsa sanye da jallabiya ga kur’ani yana karantawa gwanin burge w, da alama wannan zaiyi saukin kai a cewarta

“Barka da safiya yallabai an tashi lafiya” sai da ya kai aya sannan ya juyo ya kalle ta ya ce “da ban tashi lpy ba zaka ganni ina karatun Qur’ani ne? to fah ta ambata acikin zuciyarta , shin mai ya kawo ka ma tukunna ? ya tambaya yana kallon ta a matsayin namiji,
Muryarta na rawa tace “dama an kammala breakfast ne shine …..” Interrupting dinta yayi tare da cewa “shine me ? kai shashashan ina ne da zaka fadowa mutun haka kawai tunda sanyin safiya,kama hanya ka fi ce tunkan nayi football dakai” (Jahan).

Jiki na rawa Sehrish ta fi ce zuciyarta na bugawa saboda tsananin tsoro, dafe kirjinta tayi domin ta samu natsuwar karasawa ga daki na gaba,zullumin ta kar asamu wanda zai kai mata duka don ta lura cewa fusatattu ne, ba mai sauki a cikinsu farawa da iyawa ta fara fuskantar haka nan gaba batasan mezai biyu baya ba.

Next room kwankwasa tayi tana jira taji an bata iznin shiga amma shiru , sake buga kofan tayi da d’an karfi da alama kowanane mamallakin dakin nan ya datse kofar ne,
Jin alamar ana tunkaro kofar yasa ta natsuwa, bude kofar yayi fuskar nan a daure kamar Alkubus “lafiya”? ya ambata rai a bace.
Har ta bud’e baki zata yi magana tajiyo muryar wani daga can cikin ɗakin yana cewa “Wai wane ne”?

“Wannan shashashan sabon mai aikin ne,” wanda ke tsaye a gabanta ne ya basa amsa, sai lokacin ta gane cewa dakin twins ne wato kamar yadda suke y’an biyu haka ma wurin kwanansu d’aya ,”

Tuni taji zufa ta ke to mata ganin wancan dake daga ciki ya taso , dukkan su sleeping dress ne riga da wando ajikinsu kala daya milk colour masu kyan gaske,

Jerawa suka yi tsaye a gabanta kowanne na kallonta alamar sun ma rasa wane hukunci zasu yi mata saboda ta katse masu baccinsu,

Gudun kar ta ja ma kanta bugu yasa ta ce “Am…Da ma breakfast ne an kammala shine aunty azmi tace a zo a sanar daku,”

Kallon juna su kayi tare da cizon labba atare, Ayaan ne yasa hannunsa ya kamo kunnanta ya idasa shigo wa da ita ciki , ba karamin zafi sehrish taji ba har sai da tad’an saki y’ar kara “ko da gigin wasa next time ka kara attempting zuwa tashe mu bacci na rantse saika yabawa aya zaki sususu kawai,” ya karasa maganar tare da sakin kunnan nata cikin sauri sehrish ta fice tana sharar kwalla don ba karamin zafi taji ba,

Sai da ta samu wuri ta tsugunna ta gama matse yar kwallarta sannan ta tunkari sauran dakunan kowane daki taje da abunda zata tarar na wulakanci, yanzu dai gashi ta tunkari saman bene last room da ya rage ta shiga,

Sai da ta tabbatar ta share dukkan ruwan hawayen da ya zubo mata sannan ta kwankwasa , kusan 3 times tana knocking a na karshen ne taji wata sanyayyiyar murya tace” shigo ciki.”

Comment and share

  *_Hafsat Bature_*
      ~(Boss Lady)~

Page 13-14

Da sallama tashi ga wani irin daddadan kamshi ne ya ratsa hancin ta, har sai da tasa hannu ta d’an matse hancin saboda scent din ya kai mata karo,

Samun shi tayi a kwance tsakiyar gado wani irin sabon salon kwanciya da bata taba gani ba, up yake fuskanta ya rungume fillow a kirjinsa ga wani filon a tsakankanin laps dinsa ya makalkalesa, fuskar nan dauke da murmushi just like always, Junaid kenan sarkin smiling,

Karasawa tayi gaban bed din yadda zaiji ta dakyau ta ce “barka da safiya’ Zuciyarta na mata dar dar gudun karya yi mata abunda sauran su kayi mata,

A hankali ya bude idonunsa ya sauke su akanta “menene”? ya ambata cikin kasalalliyar murya,

“Breakfast ne ya kammala” ta fada tana kallon kyakkyawar fuskarsa da jajayen lips dinsa,

Cikin shagwaba ya ce”wlh naji dadin zuwanka tukur dama tundazu nakeso na tashi kasala ta hanani pls taimaka min na mik’e” ya idasa maganar tare da mika mata hannunsa ,

Waro ido waje tayi domin wannan yafi sauran iyayi, fuskarta tamkar zata yi kuka gaba daya ta rasa me zata yi tun nan sehrish tagane kuskuren da ta tafka na zuwa amatsayin namiji bata da wani zabi fa ce tayi abunda ya ce if not her secrets will expose,

Mika masa hannunta tayi ya ruko cikin nasa, nan take taji wani irin yanayi a tattare da ita mara misaltuwa, lallausar fatan hannunsa ba karamin gigita ta tayi ba saboda softness dinta, a cikin ranta tace “wannan wani irin hannu ne mai laushin gaske da dadin tabawa, daga jin wannan hannun bai taba wanki ba,”

Gam ya ruke hannun nata a yunkurin ya taso ya janyo ta gaba d’aya ta rikito ta fada masa, dalili kuwa karfinsa ya rinjayi nata nesa ba kusa ba,

Wani irin bugu zuciyarta ta shiga harbawa duk tabi ta susuce ta rasa inda zata tsoma kanta, tashi ga yanayi mara misaltuwa, tsigar jikinta duk ta tashi tsaye hai kam, karo na farko da ta fada jikin namijin da ba muharramin ta ba, gashi ko riga babu jikinsa d’an short ne dai-dai guiwarsa,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74Next page

Leave a Reply

Back to top button