ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

………………..SEHRISH………………….
Tsaye take tana leƙen su junaid dake buga ball a cikin filin kwallon dake a gidan ,
ta cikin window take leƙensu, tana murmushi, tashin ta kenan bayan ta koma baccin da suka kammala breakfast,
Jersey ɗin dake jikinsa ba ƙaramin kyau su kayi masa ba, abunka ga farar fata, yellow ne kayan kwallon sai faman tsalle tsalle ya keyi, dama shi indai wurin wasa ne da ci a nan yafi auki,
Tare da wasu daga cikin sojojin dake tsaron gidan suke buga ball ɗin,
dariya kawai take yi masa, ganin sai zura wa da gudu yake yana taro ball ɗin su kuma suna kwace ta,
tunano wa tayi da farkon zuwanta gidan, lokacin da motar Hajajju ta shigo da ita cikin gidan, tabbas tagansu a time ɗin suna buga wasan kwallo,
kamar yadda dae take kallonsu a yanzu, amma awancan lokacin, shi dasu twins ne da fawan suke kwallon, sa6anin ynx da masu gadin gidan suke buga wasan,
“Allah sarki junaid, ji bi yadda yake ta faman shan wahala wurin taro ball suna kwace mashi, maimakon yaji haushi amma sai faman murmushi ma yake yi, shi dae baya gaji da murmushi a face ɗinsa,”
Tayi maganar nan a lokacin da take ƙoƙarin zuge glass ɗin windon, ta janyo labulen ta rufe, tana sauke ajiyar zuciya,
tunanin ta ya koma kan Babban yaya wanda tun da safe take jiran saukowarsa, amma bai fito ba, ko breakfast bai sauko ya ci ba, hakan yasa ta cikin damuwa sosai,
“Bari dae na fita naje na tambayi aunty azmee, ko naje na tashe shi in bacci ya ke yi “?
tayi maganar a fili, cikin sauri ta ƙarasa saman bed ɗinta, ta ɗauki dogon wandonta ta zura, dama daga ita sai riga dai-dai guiwa,
Gashin bakinta kawai ta ɗauko a saman mirror, ta maƙala shi kafin ta fice daga ɗakin,
A hankali take tafiya, a main parlor ɗin ta hangi su Abbansu tare da wani Amininsa Alhajin gaske daya kawo masa ziyara,
Su biyu suna tattaunawa,
saɗaɗawa tayi ta wuce kitchen, anan ta sami aunty aunty azmee tana shirya musu drinks a tray, cikin wasu kofuna masu kyau,
“Yauwa rishi dama yanzu nake ƙoƙarin zuwa na tashe ki, kin barni da aiki ko,” ? ta tambaya tana kallonta,
Cikin jin kunya Sehrish tace”Am sorry aunty azmee wlh, ina shiga bedroom ɗina naje na watsa ruwa, kawai sai bacci 6arawo ya ɗauke ni,”
Dariya azmee tayi azmee tayi tare da cewa “Bacci 6arawo ko? mutun yaje ya saki baki yana bacci, kuma yazo yace wa mutane wai baisan ya akai bacci ya ɗauke sa ba,’
Murmushi sehrish tayi tare da miƙa hannu ta kar6i tray ɗin da azmee ke miƙa mata,
Amsa tayi tana cewa “Aunty azmee wanene baƙon da yazo “?
“Ki je ki tambaye sa mana, ki ce wanene kai zai baki amsa,”
Dariya sehrish tayi jin amsar da azmee ta bata, ɗan zaro ido tayi tare da cewa “tab dana sha mari wlh,”
Azmee tace ” ba wani mari wlh, amsa kawai zai baki da yaren da zaki gane,”
“Ae wannan bugu kenan,” ta faɗi tana kokarin fita, har ta sa kai zata fice ta kuma juyo wa tare da cewa ” Aunty azmee babban yaya fa, bai fito daga bedroom ɗinsa ba ko lpy,”?
“Ki je part ɗinsa mana ki tambaye sa,” ta faɗi cikin zolaya, ɗan ta6e baki sehrish tayi tana jinjina kai tace “wai Allah ! ni asuwa? ɗan wake a hotel,”?
dariya azmee tayi tare da cewa “ynx dae kije ki kai musu, kin tsara surutu kamar ƴan jarida, “
Cikin sauri sehrish ta fice izuwa cikin main parlor ɗin, cikin natsuwa take tafiya tunkan ta isa, tajiyo muryar abokin abban dayazo yana cewa “Ae ni ba ƙaramin daɗin zuwan nan nasu Rafayet da Omar naji ba, koba komai kafin su koma U.s zasu gyara wa wasu zama A Qasar nan,”
Abba yace “Oh damuwarka kenan, baka damu da bala’en da zai jawo mun ba, kwarama Omar shi da sauƙi, amma rafayet kana ganin last da yazo ya rinƙasa ana kawo masa ƴa’ƴan mutane har cikin gidan nan yana hukunta su, babu yadda zanyi dashi, sai dae nabishi da ido kawai, saboda yafi ƙarfi na,’
Dariyar Alhajin yayi tare da cewa “Ae samun ƴa’ƴa kamar Omar da rafayet wlh abun alfari ne, kowane Uba zai so ya mallaki ƴa’ƴa irinsu, gashi ynx asanadinsu darajarka da ta family ɗinku ta ɗaukaka sosai a faɗin duniyar nan, Kowa yabonsu ya ke yi, yakamata karinka alfahari dasu, mu gana mu nan ƴa’ƴan shaggu kamar mata, basa iya ta6akawa ƙasa komai, ga Jabeer nan har asibiti na gina masa in yadawo daga Uk ya ci gaba da kula dashi, amma yaron nan ya watsa mun ƙasa a ido, wai shi yafin karfin ya yi aiki a nigeria, Naji haushi lokacin duk mun lalacewar kasarka ae ƙasarka ce,” Cikin nuna takaici Alhajin yakewa Abban wannan bayanin
da sallama Sehrish taƙarsa cikin girmamawa ta gaishe su, suka amsa mata sannan ta miƙa musu drinks din suka ɗauka suna sa mata albarka,
bayan sun gama ta kama hanyar komawa cikin kitchen, wani irin son Babban yayan ne ya kara shiga ranta, jin yadda Abokin abban nasu ke yabonsa, murmushi kawae take saki, ynx ta kara jin ya kwanta mata luf acikin ranta,
Shiga kitchen ɗin tayi tare da ajiye tray ɗin, azmee tace “yanzu sai ki je, ki gyara masa part ɗinsa ko? tayi maganar tana kallonta,
Sehrish tace “Yana fa ciki, kuma kince baisan atashe shi yana bacci, kuma baisan ƙara, in nayi kwaratsi fa zai ji harya farka,”

Murmushi azmee tayi tare da cewa ” to ina ruwanki da bedroom ɗinsa? Falonsa zaki fara gyara wa, kafin ya tashi sai ki gyara can ɗin ko ?
Sehrish tace “To bari nace”
tafice tana fargaba, tana jiyo muryar Aunty azmee tana cewa “Anaso ana kaiwa kasuwa,”
Ƴar dariya tayi tare da fi ce wa, kai tsaye part ɗinsa ta wuce zuciyarta na ɗar ɗar,
Kamar kullum a buɗe door ɗin parta ɗinsa take, a hankali tashiga tana sanɗa kamar 6arauniya,
Sai da tayi tsakiyar falonsa nasa tasoma tunanin wai me ma tazo yi? Saboda ko’ina agyare yake tsaf ba datti ko kaɗan, sai walwali wurin yake har yau tana jinjinawa haɗuwarsa,
Murmushi tasaki tana wani tunani aranta, wanda bazai yiyu ba, ????
Sai da tagama zagaye falon nasa tana tunani iri iri aranta, sannan ta soma gyara sa, babu wani aiki awurin, kawai ta ɗan yi goge goge ne,
tsayawa tari riƙe da waist ɗinta, so take ta sashi a idonta, zuciyarta ce ta bata shawara da cewa “ki ɗan leƙa sa, mana,”

“Anya? idan kuma idonsa biyu fa? In ya kama ni karairaya ni zae yi Allah,’ ta bata zuciyarta amsa,

“Ke sai ki bari ya ganki? Ae lalla6awa zakiyi a hankali sai ki dan leƙa,’

Murmushi tasaki tare da tafiya cikin sanɗa, ta tsaya a bakin ƙopan ɗakin nasa, taci sa’a kopan a bude take, curtains ɗin ta ɗan janye tana leƙensa, ????????️

Kwance ya ke yana sharar baccinsa, cikin natsuwa a saman Royal bed ɗinsa, kai ka ce da zallar gold aka ƙera gadon, yadda ya ke wani kyalli ajikinsa,

Half body ɗinsa yayi covering ɗinsa da lallausan blanket, hannunsa na dama, ya zagayo dashi har izuwa saitin left ear ɗinsa, yayin da hannunsa na hagu kuma ya ke a saman wide chest ɗinsa,

Bin shi take da kallo kamar kura taga nama, wannan haɗaɗɗiyar sumar tasa, ta rufe masa half face ɗinsa, dogon hancinsa kawai take hange,
Lumshe ido kawai take, ita kaɗae tasan yanayin da ta shiga,
Tana cikin wannan leƙen nasa ko ƙeftawa babu, taji an shaqi wuyanta da ƙarfin gaske, Shaqa ba ta wasa ba,
Wani irin tsoro ne ya ziyarce ta, hankali atashe ta zazzare idanunta,
Muryarsa ce ta ratsa kunnanta da cewa “meyasa ki ke leƙe na !!”?
wata irin zufa ce ta wankowa sehrish, tsananin tashin hankali ne ya bayyana a idonta, lokacin da ta lura cewa babu shi asaman gadon nasa, yaushe har ya sauko yakuma wuce ta, ya zagayo ta bayanta,harya shaƙi wuyanta,
Wani irin fitsari ne mai zafin gaske ya kufce mata, ji kake zirrrrrrrr yana zubo mata,
Muryarsa ce ta sake karaɗe kunnanta, ” baza’a bani amsa ba” ????????????????????????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74Next page

Leave a Reply

Back to top button