ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

tun yana 20years a duniya, wan mahaifiyarmu ya bashi auren ƴarsa maryam, yarinyace mai ilmin addini sosai ga hankali da natsuwa, maca ce mai saukin kai, bata ɗauki duniya da zafi ba,

Itace matarsa ta farko, sun sha sosai kamar laila da majnun, domin mu kanmu shaida ne akan hakan, duk in yana gari tashiga tarairayarsa kenan, idan aka turasa aiki kuwa nesa ba ƙaramain shiga damuwa take yi ba, duk tabi ta susu ce,

Abban mutunne mai son ƴa’ƴa koda yake bashi kaɗai ba, mu dukkan mu haka muke da son ƴa’ƴa zumuncin family ɗinmu yana da ƙarfi sosai, bama wasa da sada zumunci,

Cikin ikon Allah maryam ta samu ciki, kowa ya hau murna musamman ammin mu grandma ɗinmu, dayake maryam mutuniyarta ce tana sonta sosai kasancewarta yar yayanta modibbo,

Haihuwa tafarko maryam ta haifo kyakkyawan ɗanta, santalelen yaro yaci sunansa Ishaq (wato general ishaq) daga shi kuma sai Abbas wanda ynx yake rike da mukamin colonel general, daga Abbas sai brigadier general Abuhaisam gashi nan zaune kuna ganinsa, daga shi kuma sai major genaral Osman dukansu tazarar 2 years ne a tsakaninsu su duka, daga shine maryam ta ɗan huta,

Bayan nan ne tafiya ta kama su Abba izuwa ƙasar america, an tura su zuwa halartar wani special training na sojoji da za’a gudanar, da courses na dabarun aiki,

Hankalin maryam ba ƙaramin tashi yayi ba, jin za’a tura mijinta ƙasar turai, tsoranta kada wata tagansa ta liƙe masa Acan, saboda yana da farin jini sosai, ????

Aiko hakance ta faru domin kuwa da zuwan su Abba u.s wata zankaɗeɗiyar budurwa kyakkyawar gaske ta ƙella ido tagansa taji cewa duk duniya bawan da take so sai shi,

baturiyar ƙasar amurika sunanta Alexandra ita ƴa’ce ga commender in chief na armed forces, ????
Mace mai tsananin ji da kanta, ita a tsarin rayuwarta, Namiji baya gabanta, idan akayi mata maganar aure sai tace, ita jin kanta take yi tamkar namiji don haka ba abunda zaisa ta yin aure don tafi ƙarfin ta zauna a ƙarƙashin wani, idan akayi mata maganar ɗa kuwa, sai tace ita karenta tony ya ishe ta, wani jibgegen kare ne Wanda ta raine shi tun yana jinjiri har ya fara tsufa,

Abba shine namiji na Farko daya karya wannan kudurin nata, At first sight taji duk duniya ba wanda yai mata sai shi~

Kuma gadan gadan taji tana son aurenshi, Iyayenta sun so su dakatar da ita, amma dayake su in yaro ya wuce 18yrs yana da ƴanci ba wanda ya isa ya takamasa burki, har shari’a zai iya yi da iyayensa insun takura masa,

Hakan yasa suka ƙyale Alexandra ta auri Abba, ba tare da sanin family ɗinsa ba, shi kuma soyayya ta rufe masa ido baya ganin kowa in ba ita ba, dama fa su akwai iya tarairaya ga ɗaukar wanka da jan hankali,

A nan los angels california suke da zama a katafaren gidanta, nata na kanta dayake itama ta tara kuma ta fito daga babban gida, kuma ita ma soja ce tana riƙe da muƙamin major genaral,

Sunsha soyayya kamar romeo da juliet, acan kuwa 9ja sunyi mamakin jimawar abba, ganin sauran da aka tura Us tare dashi duk sun dawo sai shi kaɗai,

Ga maryam da ƙaramin ciki, kullum cikin zullumi take akan mijin nata,

time ɗin daya shirya dawowa 9ja yasha wahala kafin Alexandra ta amince cewa zata biyo shi na wucen gadi,

Aiko lokacin sun ga tashin hankali, ganin abba ya dawo da mata jinsin turawa, ran mahaifiyarmu baƙaramin 6aci yayi ba, saboda ta tsani jinsin turawa, sbd tasancewa basu da kunya fitsararru ne, an tada tarzoma a lokacin, gaba ɗaya danginmu sukayi masa caaa akan alexandra,

Amma abun mamaki mahaifinmu Salahudeen ya amince masa, kuma ya tsawatar da kowa akanta, ya hana kowa ya sa baki akan alexandra, haka yayan mahaifiyarmu modibbo ya tsawatar mata akan taja bakinta tayi shiru, haka kowa ya zubama sarautar Allah ido ????

A katafaren gidansa dake abuja suke zaune ya ware mata part ɗinta daban, na maryam ma da ya’yanta daban, kowa baya shiga harkar kowa,

Sam maryam bata kishi da alexandra, tafison su samu zaman lafia a tsakaninsu,amma ita alexandra kishin maryam take ji, bakomai yaja hakan ba face sanin cewa su ba’ayi musu kishiya, basa zama da kishiya,

Cikin rashin sani sai ga ciki a jikin alexandra wanda ya tayar mata da hankali saboda tana shan maganin hana ɗaukar ciki don ita bata buƙatar ƴa’ƴa arayuwarta,

taita faman kiciniyar cire cikin hankalin abba ya tashi, faɗa sosai sukayi a lkcn, yasha wahalarta sbd sai da takai ga har zuƙunna mata yake akan guiwarsa yana roƙonta akan karta cire masa ciki yana so,

dakyar ta amince bisa sharaɗin inta haihu, ba ita zata shayar da yaron ba, kuma ba a nigeria zata haifesa ba, tafi so taje can ƙasarsu saboda tafi yarda da likitocinsu, kada a kashe ta tsoran mutuwa gare ta, ????

haka ta maida Abba kamar ɗan aikinta da matsayinsa da komai haka zai zauna, yana mata aiki komai takeso shi zatayi, ita dai maryam bata cewa komai binsu kawai take da ido ????

Hankalinta kwance saboda haryanzu Abba yana tsananin sonta bai wulaƙanta taba, bai kuma canza mata ba, sa6anin wasu mazan da zaka gani daga inda suka yi sabuwar amarya tofa ita waccen tazama expire product, ????

wata rana yana zaune ɗakinsa saiga alexandra ta shigo da ƙaton cikinta, hannunta ɗauke da farar takarda da wani rubutu ajiki wanda aka rubuta da harshen spanish, ta miƙa masa takardar da biro tace yasa hannu,

Gudun rigima yasa bai tambaye ta takardar mecece ba kawai ya raftaka signature ɗinsa, ajiki tare da miƙa mata , tayi murmushi ta kar6a, ????????ABBAN SOJOJi????

mallakin

Hafsat Bature Boss Lady

subhanallah_Walhamdulillah_Allahu akhbar????

page 47 to 48

Dont worry your self guys, sergeon general is on the way soon insha Allah????

Ya Allah kaji ƙan waɗanda suka rasu, ka gafarta musu, muma in tamu tazo kasa mu cika da kyau da imani, ???? Mutuwa ake kamar hauka, yakamata muji tsoran Allah muyiwa kanmu tanadin kyakkyawan ƙarshe tunkan tazo kanmu, mu kasance a cikin shiri domin akowane lokaci mutuwa zata iya zuwa???? Ya Allah kasa mu cika da kyau da imani, Ya Allah ka haife mana zunubbanmu, Ya Allah ka kare mu daga aikata aikin dana sani???? mu rage dogon buri a rayuwa, mu rage kwaɗayin abun duniya wanda daɗinsa ƙalilan ne, wannan rayuwar bata da tabbas wlh, amma wasu sun mai da ta wurin zama, suna aikata abunda suka ga dama, zalunci iri iri basa tunanin menene makomarsu ???? Allah kasa mu dace ???? wlh sai mun gyara indai muna so muga dai-dai arayuwarmu ????

Bismillah

a na nan lokacin haihuwarta yayi, abba dakansa yakai ta Airport kamar yadda yayi mata alƙawari,
kuma ya cika,

Cikin sa’a Alexandra ta haifi santalelan yaronta na farko, wanda ya gigita kowa, kyakkyawan gaske mai matuƙar ɗaukar ido, komai nasa na mahaifiyarsa ne ya ɗauko, hatta launin idonta blue eyes,

Ta jima a us kafin ta zo nigeria, domin ta gwada musu babynta, aikuwa nan fa dangi suka susuce akansa, amma ta hana kowa ya ta6a mata yaronta, iya kallo daga nesa, jinsa take tamkar gold koda yake darajarsa tafi darajar zinari,

Abba yayi mamakin ganinta tana shayar da yaron, bayan ita da kanta tace anemi mai raino don baxata shayar dashi nono ba inyazo duniya, da alama soyayyar yaronce ta kamata,

A lokacin itama maryam ta haifi nata yaron kyakkyawan gaske wanda duk cikin ya’yanta bamai kyansa, farinciki a wurin abba ba’a magana a lokacin yama rasa ina zai tsoma kansa, saboda ƙaunar yaran nasa da aka haifa masa,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74Next page

Leave a Reply

Back to top button