ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

Wani irin miyau ta haɗiye lokacin da ta samu amsar tambayarta , sai da ta samu natsuwa sannan ta kwaɗ’a sallama, jin muryar mai aikin nasu yasa fawan saurin yin rejecting kiran ya yi throwing phone ɗin nasa saman gefensa, rai abace yace ” wai wanene “
Ko izinin shiga ba ta samu ba, murya na rawa ta ce “tukur ne dama an kammala shirya breakfast ne”
Wani irin dogon tsoki ya ja tare da cewa” Naji sai me”?
Jiki a sanyaye sehrish tabar kofan ɗakin nasa ta wuce na irfan, ita kanta ta shaida cewa yau babu sa’a ynx fargabanta me zata taras ɗakin sauran.
*_Hafsat Bature_*
~(Boss Lady)~
Page 15-16
Kwankwasa kofar ɗakin nasa tayi , da wata irin kakkausar murya taji ya amsa mata da cewa”Uban wanene” kai kanaji kasan yasha ya bugu har takai masa aka.
Saboda tsoro bata basa amsa ba ta yi gaba da sauri, tun a lokacin ta gane cewa tabbas akwai matsala kuma sam bai kamata tana bin kowannan su ɗaki don tayar dasu ba, ta gama yanke shawarar sanarwa azmi cewa baza ta ƙara zuwa ba, tun da cikinsu ne in suna jin yunwa dakansu zasu fito su nema.
Gaba ɗaya a firce take da lamarin kan ta ya gama ɗaure wa, ɗakin Jabeer ta wuce tana sa hannu ta kwankwasa kofa , tana jiyo har mutsinsa ta ciki sallar karya ya kabbara , shiga ciki tayi abun saiya daure mata kai, Sallah karfe 9 na safe.
Har zata juya idon ta ya hango mata kwayoyi na shaye~shaye ga kwalabe kuma a gabansa.
Shi duk a tunaninsa yayansu ne kanal yusif amma jin shiru yasa shi katse sallar ya ɗago ya kalle mai aikin, wani mugun kallo ya wurga mata tare da nuna mata hanyar fita ya ce ” karka kuskura ka ƙara zuwan min ɗakina in ba haka ba saina canzama kamanni shashasha,”
Abun da bai sani ba ita sam ba ta san kwayoyin menene a gabansa ba, a tunaninta bai da lafiya ne shine ya ajiye magunguna zai sha.
Ficewa ta yi a ranta tana cewa” Allah ya ba ka hakuri,”
Saura ɗakin shagwababben sarkin murmushi, har tsoran zuwa ta ke yi saboda manne mata da yake yi,
Tunkan ta shiga take jin muryasa yana faɗin “Coffee i need coffee pls ” cikin magagin bacci ya ke wannan sambatun na neman coffee,
knocking tayi masa kusan sau uku kafin taji muryarsa yana cewa “wanene shigo ciki mana,”
Gyarawa tayi ta shiga ciki samun shi tayi kamar yadda ta saba samun shi irin kwanciyar nan tasa daya saba, kamar wani karamin yaro haka yake,
Karasawa tayi gabansa tare da cewa”barka da safiya junaid , tukur ne,” ta idasa maganar tana kallon cikin idonsa daya buɗe,
A duk lokacin da ta kalle sa wani irin natsuwa da kwanciyar hankali ne ke shigarta, murmushi taga yana sakar mata dimple din nan nasa masu lotsawa guda biyu suka bayyana,
“Ohh tukur ne am really happy to see u, dama yau inaso ka taimakamin tun jiya nakeson wanke sumar kaina na kasa amma yau kam tare zamu shiga toilet ka taimakamin,” a wani shagwab’e ya ke maganar.
Sehrish kuwa waro ido waje tayi jin abun da ya ce wannan da alama wata rana cewa zaya yi tayi masa wanka,
Cikin sanyin murya ta ce “ka yi hakuri dan Allah ba yadda za’ai na bi ka toilet sam a tsarin aiki na a gidan nan ba’a ba mai aiki izinin yin hakan ba,
Wani irin kallo ya wurga mata kafin ya ce” wa ye wanda ya tsara wannan dokar? bayan ni ne silar da aka kawo ka aiki a gidannan, tukunna ma kai ba jinsina bane? to kodai maca ce tayi shigar maza bansani ba,”
Jin wannan maganar tasa yasa sehrish jin faɗuwar gaba tuni ƴan hanjin cikin ta suka ƙaɗa har ta soma tunanin anya Junaid bai gane cewa ita MACACE ba NAMIJI ba !? duk tabi ta rikita kanta
Muryarsa ce ta sake katse ta “Am asking you ! answer me,” dakyar voice ɗinta ke fita “ba haka bane, kawai a ganina bai da ce ba ina matsayin mai aiki nayi hakan,”
“I command you to do that! ae mu ne masu gidan kuma umarnin mu ake bi,”
Cike da isa junaid yayi maganar,ba yadda sehrish ta iya a dolen ta, tabi umarninsa, haka ya tashi yana yauƙi yana cika yana batse wa kamar bashi bane mai murmushin kashe zuciyarnan ba,
Miƙewa ya yi daga saman bed din ya sauko daga shi sai shorts a jikinsa, bin jikin shi tayi da kallo fari sol ba tarin gashin jiki a skin dinsa , ga kirarsa dai dai wa dai dai, kusan hasken fatarsa dana twins jahan da Ayaan ɗaya ne akan na sauran don haskensu ba irin na nan bane zai iyiyuwa cikin iyayensu akwai farar fata, mahaifiyarsu ko mahaifinsu,
“Idan ka gama kallon zamu iya shiga ciki ko” ya ambata yana kallon ta, gaba yayi cikin toilet din tabi bayansa zuciyarta na ɗar ɗar tsoranta kar ya ce zai cire shorts ɗinsa a agaban idonta batasan ya zata yi ba,
Da farga jikin ta na rawa ta dauko ɗaya daga cikin jerin shampoo dinsa na wanke kai, juya tayi da nufin ta nuna masa in da wanda ta dauko yake amfani kar asamu matsala, samun shi tayi yana kokarin cire shorts ɗin jikinsa, aiko a firgice ta saki roban shampoo ɗin ƙasa, ta karasa da gudu ta cafke hannayensa dake a saman mararsa gam ta ruke su, kallon juna suka shiga yi na wani lokaci, shi mamakinsa wai namiji ne ke gudun ɗan uwansa namiji a ganinsa is not a bad thing don ka cire kayanka gaban jinsin ka, ita kuwa miyau kawai take haɗiya gabanta na faduwa sai faman huci take kamar wadda ta yi ƴar tseral, Tuni hancin ta ya soma tsattsafo da zufa, tsoranta wane hukunci zai yi mata a sakamakon abunda tayi, ita dai tayi hakan ne don da abunda zata gani na tsiraicinsa kwara koma meye yayi mata tasan ba laifinsa bane, laifin ta ne da tayi shigar namiji,
Zame hands ɗinta tayi daga rikon da tayi masa, hannayenta ta aza a saman kanta tare da faɗin “nashiga ukuna am so sorry sir am just out of sense,” duk a riki ce tayi maganar,
‘Stop calling me sir! Cos may be am just your age mate, call me wit my name Junaid,
Ya karsa maganar tare da ƙara gyara gyara shorts ɗinsa yace ” get out of my sign,”
Cikin sauri ta nufi hanyar fita har ta 6uɗe kofan tajiyo muryarsa yana cewa” Am watching you!” juya kanta tayi ta kallesa da yatsunsa yayi mata nuni da idonsa alamar zai sa ido akanta,
Cikin sauri ta fi ce tana faɗin ” Insha Allah junaid bazaka gano komai ɗangane dani ba zan ta addu’a ina rokon Allah yaci gaba da rufamin asiri har nasamu na hada kudin aikin Husanna nabar maku gidanku,
ta fada acikin zuciyarta (abunda sehrish ba ta sani ba wannan gidan is part of her destiney)
Azumi ta kammala shirya musu abincin sai da kowannansu ya mula yasha iska sannan suka firfito, one by one duk sun shirya cikin kakin sojojinsu, banda mutun ɗaya junaid wanda ke sanye da jeans a jikinsa tare da farar tshirt mai dogon hannu ta ɗanyi tighting ɗinsa,
Kowannan su ya samu wuri ya zauna, sehrish ce ta fito frm the kitchen don ta fara saving ɗinsu, azmi kuma ta wuce bedroom ɗinta don dama already ta sanar da ita cewa zata shiga ciki tayi wanka don tasha aiki,
Hannu ta har kekkerwa yake yi saboda tsananin tsoran guyabarsu, junaid ta fara kallo tare da cewa”me zan zuba maka’? Kafin ya buɗe baki ya yi magana fawan ya kar6e da cewa”saboda shine babba acikin mu !”
Ayaan ya ce “thats what i was trying to say! Wannan house boy din ba karamin ɗan iska bane shi junaid ɗin special salary ya ware maka ne ɗayasa kke kokarin fara zuba masa abincin? ya tambaya fuska a ɗaure yana kallon ta,
nan fa hankalinta ya tashi ita batayi don wani abu ba ashe abun yana damunsu,
Muryar Jahan ce ta katse ta “Nima na lura da haka in banda iskanci ka rasa wanda zaka fifita sai karamin kanin mu wanda ko aiki baya zuwa sai dai yazauna kamar mace a gida,’ ya ƙarasa maganar yana wurga masa harara.