ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

Juyawa tayi tana kallonsa yadda ya ke kwance yana baccinsa a natse, sama ya ke fuskanta ya wawware hannayensa, murmushi tasaki tare da fadin ‘abun zai zo mun da sauƙi,’
Hawa saman bed ɗin ta yi a hankali cikin sanɗa kamar mage, rarrafe a hankali tayi ta isa inda hannun damansa yake, yatsun hannunsa a buɗe suke gasu nan tsirara masu kyan gaske, bayan wayar ta juya inda thumbprint din ya ke, kwafa wa tayi a yatsansa na tsakiya, yasa mata wrong, matsar da wayar tayi ana gabansa cikin sa’a wayar ta bude, tsananin farin ciki ne ya bayyana a fuskarta, cikin sauri ta sauka ta lalla6a tafita ta tsaya a bakin kofan room din nasa, jikinta har kerma yake yi karta ya farka, tuni zufa ta soma tsastsafo mata a hancinta,
Time ɗin da ta aza idonta akan wayar, Hoton da tagani a wellpepper ɗinsa ne yasa jin zuciyarta wani irin bugu,
Zuba ma hoton ido tayi wato ainihin wani haɗaɗɗen matashin saurayi ne, ko a mafarki bata ta6a ganin mutun mai irin kyansa ba, kwayar idonsa ce tafi ɗaukar hankalinta, blue eyes ne da shi, wannan wani irin zazzafan kyau ne! irin wannan kyan shine mutane ke neman tsari da shi, jikinsa na sanye da kakin sojoji ba ƙaramin daukarsa su kayi ba, yayi hoton ne kamar a shirin film a saman mota yayi irin wannan zukunnawar da suke yi in zasu yi harbi da bindiga, hannunsa riƙe da bindigar yayi hoton, doguwar sumar kansa wanda ya ɗaure ta tsayin ta har bayan wuyansa baka wulik,
Kyawawan lips ɗinsa tabi da kallo dark pink kamar ya shafa janbaki, ga wani dogon hanci tubarkalla masha Allah,
Tayi nisa cikin ƙurewa hoton kallon, sam ta manta da abunda take kokarin yi sai da wayar hannunta tayi ƙarar shigowar sako sannan ta dawo hayyacin ta,
Da sauri ta shiga wurin contacts, numbar goggo ta rubuta ta danna mata ƙira, ba tayi tunanin ko akwai recharge card a phone din nasa ba, amma ranta ya bata cewa ba zama a rasa ba, su da kullum cikin kuɗi suke,
A jiyar zuciya ta saki jin numbern ya fara ringing, sai Allah Allah take suyi sauri su ɗaga before he get up,
Jin muryar goggo yasa sehrish sakin murmushin jin dadi
“Assalamu alaikum goggo sehrish ce! Ina jahad don Allah inason magana da ita cikin sauri,” ta karasa maganar tana waige waige kar wani ya ganta,
On the other hand goggo ta miƙa wa jahaad wayar, cikin dauƙi ta ƙarba tare da fadin”yar uwa ! dagaske ke ce ! Wayyo Allah na farin ciki,”
Dariya sehrish tasaki jin abunda jahadar ta ce, kamar zatayi kuka itama ta ce”I really missed you my sisters, so much, dana ji voice ɗinki i just felt like to cry,” ta karasa maganar idonta cike taf da hawaye,
“sister dama akwai abunda nake na fada miki amma narasa taya zanyi magana dake,”
Sehrish ta ce “yanzu ina jinki pls kiyi sauri ba wayata ba ce ta yaron gidan ce baisan ma na dauka ba,”
Cikin fargaba take sauraron jahaad ɗin”sister doctor ya ce ƙarshen month ɗin nan indai ba ayiwa husanna aiki ba, to ciwon nata zai habbaka sai dai a fidda ita ƙasar waje in ba haka ba mutuwa zata yi, sun sa mana ranar aiki 5 ga watan da zamu shiga….” kuka ne ya ci ƙarfin ta, itama sehrish ɗin kukan take yi haka suka dinga kuka ta wayar, babu mai lallashin wani,
“Idan kin gama wayar ina jira!!!
A firgice ta juya idanuwanta azare jin muryar junaid, rufe idonta tayi tare da buɗe su ashe kunnanta ne suka jiyo mata hakan sam bashi bane ,
Ganin ya fara yi mata gizau yasa ta ce da jahad ta ajiye waya, zasuyi magana next time in ta samu chance irin wannan,
Cikin sauri ta goge numbar goggo da ta sanya, a wayarsa da duk wata shaida da zata tona cewa tayi amfani da wayarsa,
Cikin sanɗa ta lalla6a ta mayar masa da wayar, har time din bacci yake yi,
Haka ta koma ɗakin ta tana sharar kwalla, safa da marwa ta shiga yi tana zagaye ɗakin, tunanin ta yadda zatayi ta samun kuɗin nan,
“Yanzu yaya zanyi! kada husanna ta rasa rayuwarta! sam bata cancanci haka ba, tazo duniya a wahalce kuma ta koma! Ya ilahi i dont ave any other choice fa ce kai Ya Allah, nayi imani dakai, kai kaɗai ne gatan mu, Ya Allah ka kawo mana mafita Albarkacin manzon Allah (SAW) ❤
Dakyar ta samu ta shiga toilet don wanke jikinta, ganin cewa basu da wani aiki a kitchen saboda guys ɗin gidan in suka fita sai da marece suke dawo wa, hakan yasa basa making lunch da wuri,
Don haka tana kammala wankan ta, da alwalarta tafito domin time ɗin azhar ya yi, har ta kammala sallah bata tuna cewa tabar gashin bakinta a cikin toilet ba,
A saman sallayar ta kwanta tun tana shesshekar kuka tana rokon Allah har bacci ya ɗauke ta,
Sehrish ta manta bata rufe kofan ɗakinta ba kamar yadda ta saba, shin na tuna mata ko kuma na kyale ta? tuna wa da cewa ba’a so a tashi mutun in yana bacci indai ba abu mai mahimmanci bane kamar sallah yasa na ƙyale ta, me zai biyo ba?
“Babu amfanin zama da mutun fasiƙi irin ka ! Ka saida mun ƴaƴa ! Saboda son abun duniya da son siyasa kai mutunne ko dabba! hakan baiyi maka ba sai da kabi ƴaƴana ka lalata musu rayuwa wannan wace irin masifab ce?
“Wayyo Allah abba kadaina dukan oumman mu, jini ke zuba a jikinta, oumma ki daina kada ya kashe ki ! Oumma! Oummahhhh!
Da ƙarfi ta ambaci sunan a firgice lokaci ɗaya ta farka, kukan da take a mafarkin har a fili sharkaf haka tayi da zufa, zaune ta tashi a fujajen tana kuka bil haƙƙi,
Dafe kanta tayi saboda wani matsanancin ciwo da yake yi mata, cikin shesshekar kuka take ambaton “umman mu,’ fuskarta duk ta jagule dama dama da hawaye, da alama wani mummunan abune daya taba faruwa a rayuwarta ta tuna,
Haka ta dinga maimaita “Innalallahi wa inna ilaihirraji’un,
Cike da jimami ta tashi daga saman sallayar, agogon dake manne jikin bango ta kalla ƙarfe 4:00 dai dai time ɗin la’asar yayi har yana kan wuce wa,
dole ne ta canza sabuwar alwala saboda tayi bacci mai nauyi,
Cire hijab ɗin dake jikinta tayi ta aza asaman gadon, ta jiƙe sharkaf da zufa, shiga toilet ɗin tayi tana faman sauke ajiyar zuciya, hannun na dafe da chest ɗinta, cire kayan jikinta tayi , ta sakarwa kanta shower , yadda sassanyar ruwan ke sauka a jikinta haka zuciyarta ma ke sauka daga hawan da tayi, (ruwa rahama Ne!) duk yadda kake cikin kunar rai indai zaka shiga ka watsa ruwa a jikinka to tabbas zaka samu natsuwa,
Bayan ta kammala bath ɗin ta karasa gaban mirror ɗin dake cikin toilet ɗin, tana bin jikinta da kallo, tana da tsayi ba laifi , sam bata da ƙiba amma ƙirjinta cike suke da boobs, sannan daga kasa akwai hips sosai faffadan gaske, launin fatarta choculate colour ce, expensive skin colour, tana da sexy eyes masu lumshe wa sometimes kamar na mai jin bacci wani lokacin kuma sai kayi tunanin tana shaye shaye ne, kwayar idonta fara ce tass mai launi brown colour, hancin ta ba dogo bane ƙarami ba ƙaramin kyau yayi mata ba, a bangaren lips kuwa tamakar shape ɗin love ❤ red colour masu tafshin gaske (macen novel ke nan komai nata is 100% ????
Hannu tasa tare da shafa gefen wuyanta inda ke akwai wani rubutu a jikin fatar wurin da bakin rubutu kamar na tattoo aka rubuta (Sb) murmushi ta ɗan saki tuna wanda yayi mata rubutun, mayar da hannunta tayi akan sumar kanta wadda tayi tsayi yanzu ta sauko mata har kafaɗar ta , asalin gashin kanta har ƙugunta ya dira, amma silar hajjaju da ma’reeya suka datse mata shi saboda gudanar da aikin ta a matsayin namiji,