ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

~ABBAN SOJOJI~

Written by
~HAFSAT BATURE~
~Boss Lady~

Page 20 to 21

sai faman wurga ido sehrish take yi,hannu tashiga tafawa tana faɗin “nashiga uku shikenan komai ya ƙare”
Kana kallonta ka ga tsananin tsoro a fuskarta, lokaci guda tabi ta rikice ganin bata da wani mafita fa ce ta roƙi azmi ta rufa mata asiri, don haka jiki na rawa takarasa gaban azmi ta zube saman kneel ɗinta tana roƙonta “nasan nayi laifi amma bani da wata mafita ne don Allah ki rufamin asiri aunty azmi kamar yarda Allah ya rufa miki,”
Hmmm ja da baya azmi ayi tare da cewa”am sorry to say bazan iya rufa miki asiri ba ! laifin zai shafe mu mu biyu, wannan babbar qarya ce a girma na bai kamata na goyi bayan hakan ba, sannan bugu da ƙari sojojin gidan nan suka gane cewa ke maca ce ba namiji ba to tabbas ƙasusuwanki za’a fidda daga cikin gidan nan! kinsan matsalarki ? Cikin sauri ta ce “a’a “
“matsalarki shine kin aikata laifi biyu, na farko namiji suke so a matsayin ɗan aiki ba mace ba, ke kuma kinyi shigar mace kinzo, duk sunyi tsammanin ke namiji ce hakan yasa suka amince da ke rinka shiga har ɗakunansu kina gyara musu da sauransu, nabiyu laifin ƙarya! sun tsani maƙaryaci, kinyi karya baiwar Allah idan har suka son da wannan zancen ko ! Ba ma ke ba ni kaina ta shafa! don haka cikin salama ki tattara kayanki ki bar gidannan kafin su ankara”
Azmi na kaiwa nan ta juya mata baya ta ci gaba da abunda take yi,
Jiki a mace sehrish ta miƙe, hawaye na gangarowa daga idonta kamar an kunna fanfo, cikin sanyin murya ta ce “shikenan…bakomai naji daɗin hakan zan tafi insha Allah,”
Fi ce wa tayi a guje tana shessheƙar kuka, fadawa tayi ɗakinta ta datse kofar ta faɗa saman gadon ( kamar a indian film ????)

Tasha kuka kamar ba gobe lokaci guda fuskarta ta kumbura tayi suntum, idonta suka yi jawur suka ƙankance kamar na ƴan chaina,
Haka ta taso daga saman bed ɗin tana bin bedroom ɗin da kallo “ko a mafarki ban taba tunanin haka zata kasance dani ba, yanzu zan tafi nabar wannan daular, ni bama wannan bane damuwata ba ya rayuwar su husanna zata kasance su da suke cikin wani hali a asibiti, gashi bansamu kuɗin ba, wayyo Allah na, bansan wane irin zunubi muka aikata ba da rayuwarmu bata tafiya adai dai ba, tun kafin mu mallaki hankalinmu mu ke fuskantar ƙaddara iri iri meyasa !?

   Zube wa kasan tiles ɗin tayi tana kuka jikinta har jijjiga yake yi, 

Sam bata ji shigowar azmi ba sai dai mutyarta taji ta dirar mata a kunne” Ya sunanki ? ta jefa mata tambaya ,
yunkurawa tayi ta tashi tsaye tana matse hanci ta ce “SEHRISH”
Jinjina kai azmi tayi tare da ƙarasawa inda take, tafin hannunta ta sa tana share mata hawaye, sam sehrish bata yi tunanin hakan ba,
sannan cikin natsuwa ta ce” nayi takaici dana sa wannan kyakkyawar fuskar zubda hawaye am so sad,” cike da mamaki sehrish ke kallonta, azmi ta ci gaba da cewa “kiyi hakuri ko kusa bazanso na raba ki da aikin ba! duk da ina tsoran abunda zai biyo baya, amma zan iya jurewa don ganin na taimaka miki,” jin wannan bayani yasa sehrish sauke nannauyiyar ajiyar zuciya,
mayar da hannunta tayi a saman shoulders ɗinta taci gaba da cewa” da farko ina so ki fadamun dalilin dayasa ki kayi basaja a matsayin namiji”?
Muryar na rawa ta soma magana cikin sheashekar kuka” ƴan uwana ne basu da lafiya rai hannun Allah an kwantar dasu asibiti, kuma doctor ya ce aiki za’a yi musu, shine nake kokari naga nasamu ƙudi na biya musu, ɗayar ma dr yace in har ya wuce 5 ga watan da zamu shiga sai dai a fidda ita Qasar waje ko tarasa ranta…..’ kukan ne yaci ƙarfin ta,
Cikin lallashi azmi ta ce “daina kuka ya isa haka, na fuskanci matsalarki, duk da ina buƙatar bayani amma bani da enough time, riƙe wannan zamuyi magana an jima yanzu dai taimakon da zan miki shine, zaki ci gaba da aiki a matsayin Namiji kamar yadda kike yi, ko da gigin wasa karki bari su gane cewa ke maca ce ! sannan maganar kuɗi kuma nawa ne ake bukata ?
Azmi ta tambaya tana kallon ta, sehrish ta ce “dubu ɗari tara ne” a tunanin ta azmi zatayi shock in taji kuɗin amma sai taji tace”zan iya ansar miki albashinki na wata na shekara ɗaya da rabi ! a baki a ɗunkule amma inaso ki sani ! duk runtsi duk wuya duk kuma duk irin wahalar da zaki fuskarta da wulaƙanci a wurin masu gidan nan, dole kiyi haƙuri ki jure! kiyi musu biyayya sau da ƙafa, ba maganar barin aiki , in kuma har kika ce zaki bari toh sai fa kin biya sauran kuɗin da kika ƙarba kin amince!!? ????
taji ma tana nazari kafin tace”Eh na amince !!! zuciyarta na wani irin bugawa ba kowa ya faɗo mata a rai ba face Ayaan da jahaan , ynx ana nufin ta ɗaura aure da kaddararta na zama cikin gidan nan! ya ilahi,
“Yanzu account number zaki bani na wanda za’a turawa kuɗin aikin nasu,” azmi ta faɗa tana kallon cikin idonta, tsananin farin ciki ta gani a fuskar sehrish ????
cikin jin daɗi tace “babu a wuri na amma zuwa anjima ko gobe zan samu na kawo miki,” azmi ta amsa da toh sannan ta kama hanyar fita har takai bakin kofa xata buɗe ta juya ta kalli sehrish dake ta faman sakin murmushi tace “kada ki manta ynx kina ƙarƙashin Iko na! komai zakiyi saida umarnina, idan har kika saba hakan, hmmmm,
bata ida ba ta fi ce,
sam sehrish bata damu da hakan ba, ita dai indai akan sisters ɗinta ne toh ko fiye da hakan ma zata iya jurewa,
Jiki na rawa baiwar Allah ta shige toilet ta dauro alwala taci gaba da zabga nafilfilin miƙa godiya wa ubangijin mu Allah subhanahu wata’ala,
Matsalar su husanna tazo ƙarshe, sauran damuwa ta kau, shin yaya kke tunanin rayuwar sehrish zata kasance a gidan ABBAN SOJOJI ? ????
yinin ranar da fara’a a fuskarta hakoranta a washe kamar mai tallar maclean, cikin jin daɗi suka gudanar da aiki a kitchen tare da azmi don shirya dinner,
tunanin yadda zata sake ɗaukar wayar junaid takira husanna ta ce su turo mata account number, har zuciyarta take jin ƙaunar azmi saboda tayi mata rana ! Har abada kuwa ji take bazata taba sa6a mata ba! tayiwa kanta alkwarin zatayi mata biyayya bazata taba bijire mata ba ko taci amanarta ba,

A 6angaren junaid kuwa, bayan ya tashi daga bacci da jimawa ya wuce masallaci daya dawo ya tsaya a filin da suke buga ball na gidan tare da wasu daga cikin sojojin dake tsaron gidan,
yunwa ce tasa shi shigo wa ciki after magrin prayer, muryasa suka dinga ji yana kiran “tukur ! ,
Wani irin farin ciki ne ya lullu6e sehrish, cikin ɗauki ta ajiye wanke wanken da take yi agaban fanfo, na kayan da suka yi amfani dasu,
Karasawa tayi wurinsa yana zaune saman 3 seater, yana daddana wayarsa, cikin girmamawa tace”gani ya ya junaid” ta kirasa da hakanne saboda ya hana ta ce masa yalla6ai, girman jiki ne kawai dashi da kuma tsawo fuskarsa ce kawai zata nuna maka cewa yaro ne sharkaf,
ta6e baki yayi tare da ɗan jefa mata kallo ya ce” ƴunwa nake ji, ” ya faɗa a shagwa6e, yana kallon ta
cikin zumuɗi ta ce ” a shirya ma abinci a dining ko nan zan kawo maka,?
ta tambaya tana kallon wayar hannunsa kamar ta fisge ta saboda ita take bukata,
ɗan yatsina fuska yayi kafin ya ce” No a tsarin gidan nan bama iya cin abinci in ba tare da junan mu ba, duk yunwar da mutun ke ji dole sai an tattara an haɗu a table aci a tare, don haka kawo min coffee kawai, zan jira brothers ɗina su dawo sai mu ci dinner a tare,”
Wannan haɗin kan nasu ya burge sehrish sosai, suna son junansu, juya wa tayi, taje da tadawo hannunta dauke da cup din saman ɗan plate ɗin da ake aza sa, miƙa masa tayi tana kallon fine face ɗinta,
Ƙarba yayi tare da faɗin”thanks”
komawa dining room ɗin tayi, tana goggoge chairs ɗin dake kewaye dashi, daga inda take tana satar kallonsa shi da yake zaune a falo,
Bayan ta kammala ta koma kitchen ɗin, azmi ta samu tana a ciki tana ganin ta ta ce “yawwa mlm tukur ayi maza a fara jera abincin a dining ko,” sunnar da kai ƙasa sehrish tayi cikin jin kunya, azmi tace “gsky hajjaju yar daru ce! da ita duk aka shirya wannan ƙaryar,” murmushi kawai sehrish take yi tana wasa da yatsun ta,
Ba tare da bata lokaci ba, suka soma shirya abincin, tana kaiwa tana jera masu,
Ƙiris ya rage a fara kiran sallar magrib, bayan sun girma shiryawa azmi ta wuce ɗakin ta , sehrish kuwa falo ta wuce, anan ta samu Junaid yana sharar bacci, ya mimmiƙe kafafuwansa a saman doguwar kujerar, Alhamdulillah thanks to Allah ta fadi hakan, ƙyalle ido tayi ta ga inda ya ajiye wayarsa saman chest ɗinsa,
Cikin sanɗa ta soma tafiya a hankali a hankali take takawa, har ta idasa isa gabansa, leƙa fuskansa tayi kyakkyawa mai annuri, dimples ɗin nan nasa a lotse, kamar ba bacci yake yi ba,
Hannu takai a hankali ta ɗauki wayar tasa cikin rashin sa’a ta zame daga hannunta ta faɗi kasa ta daki haɗaɗɗen tiles ɗin dake kasa, har cikin zuciyarta taji faɗuwarnan, tsadaddiyar waya irin wannan, dafe ƙirjin ta tayi tana kallon wayon, ƙarar faɗuwar wayar tasa junaid yunkurin buɗe idonsa daga baccin da yake, cikin sauri ta boye bayan hannun kujerar tana sauke ajiyar zuciya, gyara kwanciyarsa yayi ya ci gaba da bacci, jin sakin ajiyar zuciyarsa yasa ta gane ce ya koma baccin nasa, hannu ta zura ta janyo wayar tana kallon screen ɗinta, Alhamdulillah ta fada ganin ba abunda ya same shi,
Yunƙurawa tayi ta tashi tsaye, tana kallon sa, ya aza hannunsa ɗaya a saman stomach ɗinsa, ɗayan kuma a saman kansa, abun yazo mata da sauƙi, don haka cikin sauri ta jona wayar a yatsarsa, nan take wayar ta buɗe,
murmushin jin daɗi ta saki, wannan hoton ta sake gani a wallpaper ɗinsa na wannan haɗaɗɗen matashin saurayin, har ranta so take tasan wanene wannan sarkin kyawun nan,
Ja da baya tayi a hankali tayi nesa dashi, izuwa gefen stair ta tsaya, contacts dinsa ta shiga ta rubutu numbar goggo, bugu ɗaya wayar ta shiga kuma aka ɗaga, cikin sa’a muryar jahaad taji tana kwaɗa sallama, da farin ciki ta ce”Jahaad ni ce Sehrish! banda isasshen lokaci pls listen to me,” a can 6angaren jahad ta natsu tana sauraron abunda sehrish zata ce mata”Nasamu kuɗin aikin account number zaki turomin cikin gaggawa saboda na fadamiki wayar ta yaron gidan ce nake dauka shi kansa baisani ba,”
tsananin farin ciki ne yasa jahad yin ihu da fadin Alhamdulillah a cikin wayar tasu, ta ce “narasa inda zansa kaina don farin ciki ƴar uwa kice mun kusa barin asibitin nan dama wlh nagaji da zamansa….” sehrish ce ta katse ta ganin zata ja masu lokaci ga tsoran kar junaid ya farka “ke ba surutu zakiyi mun ba ki anso acct number ɗin likitan yanzu yanzun nan ki turamin kada fa ki 6ata lokaci asiri na zai tonu,”
Tana gama faɗan hakan ta yi rejecting kiran, ta tsaya nan tana jiran shigowar saƙon jahaad, jikinta har rawa yake gudun kar junaid ya farka, har leƙen sa take yi taga ko yana motsi,
Safa da marwa tashiga yi kamar mai ɗawafi, Allah Allah take jahaad ta turo saƙon tayi sauri ta kwafa ta mayar masa wayarsa,
tana nan tana jira, tajiyo ƙarar shigowar motarsu Ayaan,da wata irin jiniya motocin nasu ke shigowa, aiko nan take junaid ya soma motsi , saboda tsabagen ruɗu ????, maimakon taje ta ajiye masa wayar ta ruga , sai ta haɗa da wayar duka ta watsa aguje sai bedroom ɗinta.
Ana dara ga dare yayi ????????tashi zaune yayi tare da yin miƙe, da hamma lokaci guda hannu yasa ya rufe bakin nasa, wayarsa ya soma lalube yaga bata nan bai kawo komai aransa ba sai yayi tunanin ko ya barta a room dinsa ne,
Shigowarsu brothers ɗin nasa ne yasa shi, sakin fara’a , a jere suka shigo su 7, ƙarasa wa kanal yusif yayi ya russuna tare da rungumesa yace”barka da hutawa my bro ina fata kana cikin koshin lafiya,” da fara’a ya amsa masa da cewa “am fine bro kun dawo lpy,” kanal ya masa masa da eh, kafin ya wuce, shima khaleed karasawa yayi inda junaid ɗin ke zaune ya rungume sa tare da cewa”My sweet bro ya enjoyment,” bai basa amsa ba sai murmushin da yayi masa, haka irfan da jabeer duk suka rungumesa kafin suka wuce ɗakunansu,
Ya rage saura twins da fawan, harara fawan ya sakar masa tare da wuce wa ta gabansa yana rera waka cikin zolaya yake cewa”Lalatacce lalatacce ne ko a gidansu wannan haka yake,” ɗaure fuska junaid yayi don ya tsani tsokanarsa da fawan ya ke yi,
A tare Ayaan da Jahan (Masoya ????) suka ƙarasa kowanne ya manna masa kiss a cheeks ɗinsa kafin suma suka wuce ciki,
Shima junaid ɗin tashi yayi ya shiga ciki domin ɗauro Alwala saboda liman na ta kwaɗa kiran sallah,
A bangaren sehrish kuwa, tana nan maƙale da wayar junaid a hannunta, zuciyarta na harbawa, sai zagaye ɗakin take tana faɗin, nashiga ukuna ynx ya zanyi in junaid ya nemi wayarsa ya rasa, in kuma ya ganta a hannuna nasan dukan tsiya zan sha, kuma su kore ki daga aiki ace mun 6arauniya, yanzu ya zanyi ni nasamu na mayar masa da wayarsa wayyo Allah na,
Ƙarar shigowar message ne taji ƙirrrr! da sauri ta duba, account number ne jahad ta turo mata, cikin sauri ta laluba cikin drawer chest, inda ta ajiye diary din da take rubutu acikinsa Wanda tazo dashi , biron da ta saka a tsakiyar littafin ta dauko ta bude page tayi copying numbers ɗin, tana gama wa , ta mayar ciki ta ajiye,
Sannan ta yi hanzarin deleting sakon daga wayar tasa, fitowa tayi daga ɗakin tana leken ko akwai mutun, duk basu kai da fito wa,
har tasa hannu zata koma ciki taji alamun mutun, junaid ɗin ne ya fito yana naɗe hannun rigarsa, da alama masallaci zai wuce,
Ba karamin dadi taji ba, yana fi ce wa, ta lallabawa cikin sauri ta shiga ɗakinsa ta ajye masa wayar a saman nightstand,
Fito wa tayi tana sauke ajiyar zuciya, yanzu abunda ya rage mata takai ma azmi acct number ɗin,
ɗaki ta koma, ta ɗauki diary ɗin ta yago papern data rubuta numbar, ta fito ta tunkari ɗakin azmi, dayake ba nisa yana kusa da nata, wannan ne karo na farko da ta fara shiga ɗakin ta,
Sallama tayi, azmi dake zaune saman sallaya ta amsa da “wa’alaikum salam shigo ciki,”
Cikin natsuwa sehrish ta shiga ciki, wuri ta samu ta zauna kusa da ita ta lankwashe kafarta tayi zaman cin tuwo,
Cazbaha take ja, a hannunta ɗan murmushi tayi tace”wai malam tukur ne yau a ɗakin namu kodai mafarki nake ne? Cikin jin kunyarta sehrish ta ɗukadda kai tana murmushi,
“tabbas kuwa shine to mara ba lale marhaban daga ganin wannan gashin bakin naka akwai magana,” dariya ce ta kubce ma sehrish, ta shiga 6a66aka ta,
daga bisa ni ta tsagaita tare da cewa “aunty azmi dama acct number ɗin ne na kawo miki,” ta karasa maganar tana miƙa mata paper ɗin, karba azmi tayi tare da fadin”kin tabbata ta likitance? Sehrish ta ɗaga kai tare da cewa “Eh tashi ce,”
“Toh shikenan kije kawai insha Allah zuwa gobe za’a tura masu kudin,”
Azmi ta fada tana adana takardar a saman carpet din,
Godiya sehrish tashiga yi mata har da matse ƴar kwalla, murmushi azmi tayi tace “Ki gode wa Allah, domin shine abin godiya, kuma shine silar shigowarki gidan nan! ,”
jinjina kai sehrish tayi alamar gamsuwa da bayanan azmi, daga bisa ni ta tashi ta fice,
A bangaren su twins kuwa lokacin da suka shiga ɗakinsu suka tarar angyara ko ina tsaf, jahan ya kalli ayaan tare da cewa “yaushe zaka daina wannan gangancin ne !,” ya faɗi hakan rai abace, cikin rashin sanin laifin daya aikata yace “what do you mean?
tsoki jahan ya saki tare da ƙarasawa gaban dressing mirror, yakai hannu ya ɗauko kwalbar maganin nan ya ce”wannan nake nufi !”
ɗafe kai Ayaan ya yi tare da faɗin “Omg!! am sorry for that, ni kaina na manta ban mayar ba,”
harararsa jahan yayi ya ce “we’re sorry for our self dai ! kai ka sani duk ranar da aka gane cewa muna aikata homo sai kashin mu ya bushe a hannun babban yaya, don haka i warn u this is last time dont repeat it again stupid !,”
ya ƙarasa maganar yana mayar da kwalbar cikin drawer chest ya janyo ya zura ta ya mayar,
Zama ayaaan yayi abed side ransa a bace jin sweet heart ɗin nasa ya kira sa da stupid akan ƙaramin laifi,
Satar kallonsa jahan yayi ganin yadda idonsa suka ciko da kwalla, sam baisan 6acin ransa don haka, ya dawo ya zauna tare da riko hannayensa yace cikin sanyin murya “am sorry my honey nayi laifi ko? ya faɗi hakan yana kallonsa,
Cikin fushi ayaan ya fisge hannunsa daga na jahan, ya kwantar da kansa jikin fillow, binsa jahan yayi ya hau saman jikinsa ya kai bakinsa saitin kunnan sa ya ce “I love u so much i dont wanna see u in angry fushi ba ya yi maka kyau honey,”
A hankali ayaan ya fara washe fuskarsa daga daure war da yayi mata, kiss jahan ya soma manna masa a side face ɗinsa har izuwa wuyansa tamkar zai cinye sa, dawo wa yayi ya sa harshen sa a kunnan ayaan yana ɗan taunarsa, hakan yasa ya fara jin sha’awarsa na tashi, (to fah)

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74Next page

Leave a Reply

Back to top button