ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

Kin riga da kin gane cewa ni maca ce,” ta faɗi hakan da ƴar shagwaba
Azmi ta ce “Oh kin shirya asirinki ya tonu ko? muddin nakira ki da sunanki na ƴan gayunnan to zasu gane cewa mai aikinsa fa maca ce ba namiji ba, daganan zasu ɗauke shi izuwa barrack ɗinsu na sojoji a acanza masa halitta,”
azmi tayi maganar ne da zolaya, yayin da tsoro ya bayyana a fuskar sehrish hannu tasa tare da rufe baki alamar ta shiga uku,
dariya azmi tayi tare da cewa” idasa shigowa mana, ina so zaki yanka mun wasu fruits nan zan hada fruit salad ne, ki duba cikin fridge ki dauko kayan marmarin kizo ki fara,”
karasa wa tayi inda refrigerator ɗin ya ke sai da ta fara daukar bowl ɗin da zata zuba su ciki sannan ta buɗe sa, kaya ne iri iri shaƙe acikinsa, dangin kayan marmari dasu vegitables, ga ɗanyen nama iri iri na dabbobi daban daban,
Zubo su tayi da yawa ta fara wanko su sannan ta dawo ta aza saman table, ta dauko knife ta shiga gyarasu, yayin da azmi ke ta faman ƴan soye soye,
Jin shirun yayi yawa yasa sehrish cewa” aunty azmi wai inaso in san wanene wannan babban yayan dasu junaid suke yawan faɗansa, wai shine babba a gidan nan ne,”?
da ta ambaci sunan shi sai da azmi ta ɗan girgiza, tajima bata yi mata magana ba, sai da tasamu natsuwa ta kana face ” idan na fara baki labarinsa to tabbas zamu kwana muna yi, bashi bane babba ba amma shakkarsa da suke ji yasa yazama babba, wani irin mutun ne mai zazzzafan zuciya, bai da sauki in dai akan aikinsa ne, baya ragawa kowa, baya sauraron kowa, yana da matukar karfi tun daga kan surar jikinsa zai tabbatar maki da cewa mugun karfi gare sa, idan yaga Mara gaskiya kuwa idonsa makancewa yake yi, in fara hukuntasa har sai ya ɗanɗani kuɗarsa, ko ni agabana kwanakin baya daya zo sai da ya kashe mutun 4 acikin gidan nan, ko kai ɗan ubanwaye kayi laifi, haka zaisa a kawo masa kai har cikin gidan nan ya yanke ma hukunci kuma ba uban da ya isa ya tanka, to wama ya isa? Jikan soja,ɗan shugaban sojoji mahaifiyarsa soja, yayyensa sojoji ƙannensa sojoji, shima kuma soja a bangaren kyau kuwa sai dai mu ce Tabarakallahu ahsanul khaliqin, wlh tunda nake a duniya ban taba ganin mutun mai zazzafan kyau irin nasa ba! irin kyan da sai Allah kawai ke tsare mutun saboda bakin mutane da masu kawo masa hari, wani irin miskilin mutun ne ke zan iya ce miki akwai lokacin daya jera kwana uku baiwa kowa magana ba hatta abbansu sai dai kawai yayi nuni da hannunsa ayi masa abu kaza, Isarsa da jin kansa ga izza dayake takama da abun sai addu’a,
Jinjin kai sehrish tayi kafin ta ce “amma meyasa shi bazai dawo gida bane ya zauna cikin ƴan uwansa,”
Azmi tace “ya za’ae ya dawo nan bayan a can us ya taso tun yana yaro a can kuma yake aikinsa a matsayin surgeon general,” maimata sunan sehrish tayi “Surgeon general meke nan,” murmushi azmi tayi saboda ta lura sehrish so take su ƙare firar tasu akan babban yaya ,
“Matsayinsa ne na aiki na faɗa miki bari nayi miki a ware yadda zaki fahimta, he’s a professional surgeon doctor kuma general ne na sojoji,”
Sakin baki sehrish tayi don mamaki wannan matsayi har haka ! surgeon general, tabɗijan can ta ambata tana jinjinawa lamarin ashe mutun inya karanci military surgery zai iya kuma zama general ɗin sojoji lallai iko sai ubangiji matsayi biyu,
murmushi tasaki Cikin zumuɗi ta ce “zanso naganshi ga kyau ga class ga matsayi biyu gsky ba ƙaramin jarumi bane,” a tunanin ta acikin zuciya tayi maganar sai ji tayi azmi tace”Insha Allah muna sa ran zuwansa nan kusa, amma kafin yazo ina tunanin Abbansu zai riga sa dawo wa domin shi ma yayi tafiya zuwa Qasar chaina, wani muhimmin taro ne yakaisu nasu na sojoji,”
wani irin daɗi ne ya rufe sehrish, saboda ta ƙosa tagansa, acikin zuciyarta tace “naso naga ranar da zanyi tozali dashi nagadai wanene wannan babban yayan wayyo daɗi….
Muryar azmi ce ta tsaida ta daga tunanin “meyasa baki tambaye ni sauran matansa da baki taba ganinsu ba sai babban yaya,”? tayi tambayar tare da juyowa tana kallonta,
Sukuyar da kai sehrish tayi tace “saboda tun ranar da hajjaju ta kawo ni gidan nan da sunan sa na fara cin karo,shiyasa na kosa nasan wanene shi,”
Hmmmm azmi tace ” akwai sauran zafafan ma irin su Captain duk wani matsayi da kika sani na soja agidan nan akwaishi, mutum goma ne sauran matasan da baki sani ba, ynx bamu da lokaci amma duk lokacin dana samu natsuwa sosai, zamu shiga garden ko muje swimming pool area akwai kujeru na shan iska awurin saina zauna na baki labarin gidan Abban sojoji,”
Cikin jin daɗi sehrish ta ce “zanji daɗin hakan sosai kinga saina san ta yadda zan zauna da kowa,”
Shiru su ka ɗanyi na wani lokaci kowa naci gaba da aikinsa, can da jimawa sehrish ta sake cewa “last question about babban yaya aunty azmi,” dariya azmi tayi tace “ina sauraron ki,” sehrish ta ce “wai bayan babban yaya menene sunansa ne na gaskiya,”?
“Zan faɗa maki amma da sharaɗi daga wannan tambayar mun rufe babin babban yaya,” acewar azmi a yayin da take sauke kasko daga saman gas,
“Na yarda toh,” sehrish ta ce tana ƴar dariya, azmi tace “Sunan shi……” shiru tayi ba ta ida ba,
Sehrish data ƙosa ta ƙagara taji sunan cikin zumuɗi tace “pls aunty azmi ki ƙarasa mana,”
murmushi azmi tayi dama ita take jira don ta ga yadda take son taji sunan,
gyaran murya azmi tayi sannan tace “Sunan shi RAFAYET!,” ????
kamar yadda sunan ya diro mata a kunnanta haka zuciyarta ma ta bata wani sauti na musamman, cikin sanyi murya ta maimaita sunan “RAFAYET suna mai daɗin gaske,”
daga nan firar tasu nasamata aya.
suka shiga shirya breakfast ɗin sehrish ce ke kaiwa kamar kullum tana jerawa a dining, har lokacin maimaita sunan take acikin zuciyarta “rafayet,rafayet, tarasa dalilin hakan (dama in mutun ya kasance ƙaddarar ka hakan ce take faruwa) ????
Sun kammala shirya komai tsaf, one by one suka soma fitowa, duk sun shirya tsaf cikin kakinsu, banda junaid wanda jallabiya ce milk colour a jikinsa, abun ba’a magana,
Ynx sehrish ta daina bin ɗakinsu, tana tashe su, saboda sunce basa buƙatan hakan, taji dadin wannan saukin da ta samu, mutun ɗaya ne wani sa’in dole sai taje, wato junaid don nauyin bacci gare sa, bai cika tashi dakansa ba sai an tashe shi, gyaran ɗakunan su kawai ke kaita, sai kuma wani abun inya taso,
Kowa yasamu wuri ya zauna ana jefa wa juna kallo, kafin su soma gaishe da junansu cikin so da ƙauna,
Kowanne sai ya faɗi abunda yake so ya ci sannan saita zaro plate ta zuba masa, haka abun ke tafiya,
cikin natsuwa suke cin abincin nasu, fawan ne yayi gyaran murya tare da cewa “Uhm AK47 yau ba magana,”?
tuntsire wa suka yi da dariya su duka hatta shi kansa sai da ya yi murmushi, Ayaan yace “she’s eating food thats why,” nan ma wata dariyar ta tashi, ɗagowa jahan yayi ya saci kallon Ayaan tare da kashe mishi ido, dama suna facing ɗin juna, murmushi ayaan ya yi,
Jabeer daya lura da su ya ce “toh ƴan iska kashe kashen idon me naga ana yi ne,” dariya su kayi su biyun, khaleed yace “there’s something behind they’re trying to hide it,”
ganin za’ayi babu shi yasa shi tsoma baki “abun sirri ne atsakaninsu,” acewar Irfan wanda ke ƙoƙarin ajiye spoon ɗin dake hannunsa saman plate ɗin gabansa,
junaid ya ce “what ever it is, idan kero na yawo zabo na yawo wataran za’a haɗu,” cikin sauri Ayaan yace “ubanka mai bakin ja6a insha Allah baza’a taba haɗuwa ba,”
wannan maganar tasa su fashewa da dariya, ita kanta sehrish dake tsaye akansu daurewa kawai take yi amma bakinta na ƙumshe da dariya ,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74Next page

Leave a Reply

Back to top button