ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

Cike da jin dadi suka fito daga motar su biyar ne, kai ka ce wadanda aka kwato ne daga bakin kura kayansu sun yi uban squeezing, ga shi riga daban zane daban dankwali daban, takalman kafafuwansu wari da wari ne, ga wata irin kwalliya da suka dambara a fuskarsu, janbaki ya sauka daga saman labbansu har kumatunsu, kamar wasu mayu. Ga black point din da suka diddiga a hancinsu har izuwa goshinsu, sai faman soshe-soshen kai suke.

A haka take dauko su daga kauyen kayau ta gyara su ta sama masu gidanje aiki, a nan take samun kasonta ita ma.
Kallon buzun ta yi ta ce “Ka shigo mini da yarinyar.”

Sannan ta kalli ‘yammatan ta ce “Mu shiga ciki amma kusa ni duk wacce ta yi mini hauka kauyensu zan mayar da ita ta je can ta ci gaba da tallar fura a bakin kasuwa.”

Cikin falo ta shiga da su a daidai lokacin ita ma yarinyar ta biyo su, nan fa suka fara kalle-kalle ganin yadda wurin ya hadu, har kokawa suke yi wurin yunkurin hawa saman lumbutsa-lumtsan kujerun da ke a ciki, dakatar da su ta yi ta hanyar yi musu tsawa, “Kul! Kada wacce ta hau mini saman kujeruna, ga carpet nan shimfide ku zauna, haba ku rinka abu irin na mata mana.”

Nutsuwa suka yi kowacce ta samu wuri ta zauna, ita da ma ba iri su ba ce da wayewarta wuri ta samu ta zauna ita kadai, yayin da su kuma suka cunkushe wuri daya kamar kifin gwangwani. Shiga ciki hajiyar ta yi tana kwalama mai aikin ta kira, “Larai, larai! Ina kika shiga haka gida sai ka ce ba kowa?” Karasowa ta yi tana hamma alamun daga barci ta tashi.

“Sannu da dawowa hajiya, wallahi barci ne ya yi awon gaba da ni da ma na sha maganin mura saboda ta takura mini.”

Tabe baki ta yi ta ce, “Ni fa ban yarda da ke kullum shan maganin mura anya ba shaye-shaye kika fara ba?” Cikin zolaya ta yi maganar tana kallon ta,

Dariya Larai ta yi ta ce, “Haba hajiya Allah ya tsare ni dayin shaye-shaye tsofai-tsofai da ni.”
Murmushi hajajju ta yi “Ya yi kyau! Yanzu dai akwai abinci gidan na zo da yara ne daga kauye.”

Girgiza kai larai ta yi, “A’a hajiya sam ban yi tunanin yau za ki dawo ba ai, da na girka muku abinci.”

A jiyar zuciya ta saki kafin ta ce, “Koma mene dai laifina ne da ban sanar da ke cewa yau zan dawo ba. Yanzu dai na san muna da bread, ko shayi ne ki hada musu da indomie.”

Amsawa ta yi da, “To hajiya!” sannan ta juya ta nufi hanyar kicin din.

Hajiya ta nufi dakinta saboda tana bukatar ta d’an watsa ruwa ta canza kayan jikinta.

Rokon Allah yarinyar take yi a cikin zuciyarta, Allah Ya sa ta samu wannan aikin ko ta samu ta taimaki ‘yan uwanta wadanda suke cikin wani mawuciyan hali, muryar d’aya daga cikin ‘yammatan nan ta jiyo tana mata magana, “Ke kin iya kunna kallo ki kunna mana mu kalla.”

Girgiza kai tayi alamar a’a, ba wai don ba ta iya ba sai don tsoron kada hajajju ta yi mata fada har ma ta kore ta ta hana ta samun aikin. Tana jin su suna cewa, “Karyar banza babu wani ta iya kawai ba ta kunna mana ne ‘yar bakin ciki.”

Dagowa ta yi ta kalle su harara ta watsa musu ta ce, “E na iya ba zan kunna ba ne ba ku da hannuwa ne ku?” Tsit suka yi ganin yadda ta daure musu fuska sun yi tunanin ‘yar shiru-shiru ce, ashe ita ma ta iya fada. Fitowa hajjaju ta yi jikinta sanye da kayan barci, riga da wando ruwan madara, ta daure gashin kanta da ribbom, hannunta rike da waya kirar Infinix Hot 10, suna ganin ta suka gyara zamansu cikin natsuwa.

Wuri ta samu ta zauna a saman 3 seater, yadda za ta ji dadin yi musu magana, yarinyar na jingine jikin 2 seater wadda ke bangaren dama su kuma suna duban ta ta sashen hagu.

A nutse ta soma magana, “Ku na riga da na yi muku bayanin komai ko?” Da’ga kai suka yi alamar e.

Ta ci gaba da cewa, “Yanzu abin da ya rage mini shi ne na koyo muku yadda za ku gudanar da aikin naku don ba zai yi yu ku je gidan mutane a matsayin ‘yan aiki ba, a haka kaca-kaca da ku ba tsafta ba. Dole ne kusan yadda za ku tsaftace kanku, da tsaftar muhalli da kuma yadda za ku tsaftace abincin da za ku girka. Kuna bukatar sanin abubuwa sosai daga wajena, kuma insha Allah zan nusar da ku.”

Ta mayar da idonta kan yarinyar ta ce “Yammata kin yi shiru ga shi ni ban san ki ba amma yanzu ina son na san me yasa kike nema na ne?”

Bude baki ta yi za ta fara magana amma ganin yadda ‘yammatan kauyen nan suka zuba mata ido kamar zomaye, hakan ya sa ta kakare ta kama in ina.

Muryar hajjaju ce ta sa su janye idonsu akanta, “Ku fa matsalarku ke nan sai shegen kallo salon gulma ko?” Sunkuyar da kansu kasa suka yi amma kunnuwansu na bude don su ji me za ta ce?

Cikin sanyin murya ta soma magana, “Da ma na ji an ce kina taimakawa ki sama wa yara aikatau shi ne na zo ni ma ki taimaka ki samo mini don Allah!”

Dafe kai hajju ta yi da hannunta na hagu ta ce “Kash! Da na san wannan ya kawo ki da tun dazu na ce ki koma gida saboda yanzu babu wadanda suka yi mini magana akan na samo musu ‘yar aiki, wad’annan ‘yammatan da kika gani su ne kawai suka rage na mika su ga wadanda na yiwa alkawarin zan sama musu ‘yan aiki amma yanzu babu wani da ya yi mini magana. Ki yi hakuri ‘yata!”

Tamkar an d’aga guduma an buga mata a kai haka ta ji, jikinta ya yi mugun sanyi tuni kwalla ta ciko mata a idonta, saboda ba karamin wahala tasha ba, kusan kullum tana fama zaryar zuwa gidan matar neman aiki, tunanowa da ta yi da halin da ‘yan uwanta ke ciki ne ya sa ta ji ba za ta iya hakura ba komai zai faru sai dai ya faru, amma ba inda za ta je sai ta samu aikin da za ta samu kudi, saboda ta san ba wanda zai taimake ta ya ba ta kudi haka nan don Allah face ya nemi wani abin daga gare ta.

Tamkar za ta fashe da kuka ta ce, “Don Allah ki taimaki wallahi ko wane irin aiki ne zan iya yin sa. Ki taimaka mini ‘yan uwata na kwance asibiti ba ta da lafiya kuma aiki za a yi mata, kudin da doctor ya fada ba mu da su kuma ba mu da wanda zai taimaka mana ni ce kawai nake fafutuka akan yadda zan samu na biya.”

Ganin yadda yarinyar ta bi tana rokon ta cikin lallami ya sa ta ji tausayin ta ya shiga ranta, “Ya isa haka, share hawayenki. Nawa likitan ya ce kudin aikin nata?”

“Dubu dari takwas ne.” Ta ba ta amsa tana kokarin goge hawayenta. Jinjina kai hajjaju ta yi jin kudin, “Da a ce ina da su da na taimaka da wani abu amma halin da muke ciki yanzu komai tsada hakan yasa kudi ba sa jimawa a wurina. Amma yanzu abin da nake so na sani ina ne gidanku saboda dare ya yi sosai, na mayar dake gid, idan kuma za ki tsaya nan is shike nan in yaso gobe sai ki koma ko?”

Cikin sauri ta ce “Zan tsaya a nan, ba kowa gidan suna asibiti kuma na yi sallama dabsu babzan sake komawa ba har saibna fara biyan kudin aikin, babzan iya jure ganin su cikin mawuyacin hali ba!”

Hajajju ta ce “To shike nan amma gobe zan bincika kuma za mu je asibitin tare saboda ba na daukar yaro ba tare da iyayensa ko wani nasa ya sani ba!”

Yarinyar ta amsa da, “To!”

Larai ce ta shigo dauke da faranti, ta jera sinkin bread guda 3, sai jug mai dauke da tea da kananan kofuna, a jiye masu tayi sannan ta koma ta dauke sauran abin da ta hada musu a kicin.

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
Hafsat Bature
~(Boss Lady)~

Page 3-4

Tun da y’ammatan nan suka ga bread suka gaza samun natsuw, sai kokarin zura hannu suke su dauka, ganin haka yasa ta taso da kanta ta rarraba musu ta bawa kowa nasa, dawowa larai tayi dauke da karamin tray wanda ta baza musu taliyan a ciki ta ajiye masu, zama sukayi suna ta aikin ci, ita dai a hankali take ci tana kallonsu hannu baka hannu kurya suke cunkusa wa a bakin, bakomai yazo mata a ranta ba face y’an uwanta, in ta tuna irin wannan yanayin sai taji komai ya fita ranta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74Next page

Leave a Reply

Back to top button