ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
Hafsat Bature
~(Boss Lady)~

Page 31-32

Ba ƙaramin zafin marin nan sehrish taji ba, don kuwa har hancinta sai da ya fashe cikin kuka take basu hakuri ” kuyi hakuri bada sani na hakan ya faru ba bazan ƙara ba,
tsawa fawan ya daka mata “hakuri fa ? A wannan babban laifin da ka aikata zamuyi maka hakuri dole ka ɗanɗani kuɗarka kasancewa agidan Abban sojoji kake aiki,!”
duk sai junaid yaji jikinsa yayi sanyi ganin yadda mai aikin yake ta zubar da hawaye amma ba yadda zaiyi kuskurensa ne!
cikin tsananin 6acin rai Jahan ya ruko hannun Ayaan suka shiga ciki saboda ya shafa masa magani don wurin har yayi jawur ya tattare,
dukar da kai sehrish tayi tana jiran sauran hukuncin da zai biyo baya,
Fawan ne yaso ma magana ” ka fara tsallen kwaɗi daga nan har zuwa saman stair ka zakayo ta ɗayan stair ɗin ka kewaye falon gaba ɗaya haka zaga dinga yi har mu kammala cin dinner ɗin mu, bayan nan akwai wankin motoci kusan goma da sukayi ƙura sun jima a ajiye, a wanke su tsaf duk a cikin daran nan nakeson hakan, sannan ba shikenan ba gobe akwai wani horon,’
ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba jin irin wannan muguntar da fawan ya tsara mata, ta razana sosai saboda girman wurin babban tashin hankalin shine tsallen kwaɗi a saman matattakalar bene har biyu ya abun zai kasance?
muryarsa ce ta katse ta “Oya start frm now, we’re watching you banda tsayawa if u do so you will see the trouble,’
Zukunnawa tayi ta fara tsallen kwaɗin ta miki hanya ta tafi , idonta cike taf da hawaye damuwa iri iri, tasha wahala fiye da tunanin mutun tun tana yi cikin daɗin rai har kafafunta suka soma rirriƙewa ga wani irin raɗaɗi da suke yi mata, numfashin ta ne ya soma fita agalabaice amma haka ta jure ta daure taci gaba da yi , lokaci guda ta hada jini da majina a fuskarta hancin ta yasoma bleeding dama tana yi in taji wuya, babban tashin hankalin ma nan take period ta balle mata jini ya soma zuba ta ƙasan ta Subhanallahi ,
tana jin ɗiɗɗigar wani abu ta cikin pant ɗinta yana gangarowa amma batasan menene ba, Allah yaso wandon jikinta baƙi ne bazaiyi saurin bayyana ba, shi dama jinin al’ada sometime bakar wahala na kawo sa a time ɗin da bakayi tsammani ba,
Sam junaid ya gaza samun natsuwa yarasa dalilin dayasa yake jin tausayin tukur ɗin nan mai aikinsu, ganin bazai iya jure ganin wannan zaluncin na fawan ba yasa shi tashi cikin sauri yabar table ɗin duk da bai koshi da abincin ba ya miƙi hanyar zuwa ɗakinsa yana hawa saman stair ɗin suka ci karo da ita alokacin take saukowa , dakyar take numfashi kamar kwaɗo haka ta koma , bin kafafunsa tayi da kallo a hankali ta ɗago da idonta wadanda suka kaɗa su kayi jawur ta kallesa shima a lokacin idonsa nakanta da take zuƙunne hannunta ruƙe da kunnuwanta,
Ido cikin Ido suke kallon juna tazama gwanin ban tausayi baiwar Allah, shi kuma amatsayin namiji yake kallonta tsananin tausayi ne ya kamasa a hankali ya furta “Am sorry” cikin wannan sanyayyiyar muryar tasa, yana faɗin hakan yabi ta gefenta ya haye sama,

Sai da kowa yabar dining table ɗin amma fawan mugu yana nan zaune yana jira mai aikin nasu tukur yagama punishment ɗin daya basa, sannan suje ya nuna masa motocin da zai wawwaken duk acikin daren nan kusan ƙarfe 9,_
JUNAID
tun da ya shiga room ɗinsa ya gaza samun natsuwa tunaninsa yaron nan mai aikinsu tukur bai kamata abarsa yayi wankin motoci cikin daren nan ba saboda shima mutun ne kamar kowa, in akai masa hakan ba’ayi masa adalci ba!
Tunano wa yayi da maganar babban yayansu (talaka da mai kuɗi duk ɗaya suke a wurin Allah babu wani banbanci don haka kada ku kuskura don Allah yabaku wani matsayi aduniya kuce zaku wulaƙanta wanda ke ƙasa da ku domin bakusan Wace rana zai yi muku ba, kuma Allah zai iya kar6e wannan matsayin da kuke taƙama dashi yaba shi wannan wanda kuka ƙasƙantar aranar ya zakuyi ? kowa zai iya kuskure a rayuwarsa amma aduk lokacin da wani yayi maka badai dai ba kazamzo mai hakuri da yafiya domin Allah ma yana gafarta mana in mukayi ba dai dai ba sai mu ƴan adam zamu gaza yin haka bazamuyi koyi da manzon Allah (SAW) ba ?
tuna wannan maganar yasa shi fita cikin sauri ya , cikin gaggawa yake saukowa down stair a lokacin har sehrish ta sume a ƙasan last step ɗin benen, shi kasan fawan baisan hakan ya faru ba saboda wayarsa yake ta faman daddanawa ,
Hankalin junaid ba ƙaramin tashi yayi ba ganin yadda me aikin nasu yake sume a kwance ba numfashi ,
tsallake sa yayi ya wuce inda fawan ke saune sai faman murmushi yake yana daddana waya ,
Kamar daga sama yaji an fizge wayar daga hannunsa, cikin sauri ya ɗago yana kallonsa yace “Junaid wannan wane irin abune zaka sa hannu ka fisge waya daga hannuna kamar wani tsaranka,’
harara junaid ya wurga masa tare da cewa “bansani ba! saboda tsabagen mugunta irin taka kasa wancen mai aikin wahala wadda tasa shi sume wa amma sam baka damu ba ,”
tsoki fawan yasaki tare da sa hannu ya ƙarbe wayarsa ya wuce tagabansa yana faɗin “Matsalarsa ce,”
Binsa da kallo yayi har ya shige bedroom ɗinsa,
Ba yadda junaid ya iya dole ya koma inda tukur ke sume yasa hannu ya ɗaukesa, sam baima san ina ne inda ɗakin kwannansa yake ba ,
Amma yasan cewa bazai wuce kwanar da ɗakin azmi take ba, kama hanyar yayi , ko nauyi baya ji haka ya dauke ta kamar yar baby ,
cikin sa’a ya samu ɗakin,da kafarsa ya turo kopar ɗakin ya shiga da ita , a saman bed ya kwantar da ita
Ransa ne ya basa ya dauko ruwa a freezer yazo ya yayyafa masa , yana sa hannu zai buɗe kofar idonsa yakai a jini dake hannunsa, har sai da gabansa ya faɗi rass ! ya soma tunanin jinin menene wannan !!! ????

Bin jinin da kallo yayi tunani yayi kodai kansa ne ya bugu ayayin da ya sume a gefen stair,
Don haka cikin sauri ya koma yahau saman gadon inda ya kwantar da shi, a hankali yasa hannunsa yana tattare hular dake kanta a ƙoƙarinsa na ya cire hular yaga ta inda jini ke zuba,
Can kuma ya fasa saboda ganin yadda fuskar tukur ɗin ta dame da jini da majina, handkchief ya zaro daga front pocket ɗin rigarsa, ya shiga goge mata fuskarta,
Kwatsam gashin bakin da take manna wa a fuskarta ya ya goce saboda ya jigata gashi dama gam gare sa ruwa ya taba sa sosai ,
Hankalin junaid ba ƙaramin tashi yayi ba ganin ya cirewa tukur gashin bakinsa duk sai yaji ba daɗi yakai hannu domin ya gyara sai yaga ya ballo gaba ɗaya, da ya ƙura ido yana kallon ƙasan hancin sai ya gane cewa dama babu gashin bakin fixing ɗinsa akayi,
Saboda babu hudojin gashi a wurin sai kansa ya ɗaure ya gaza gane menene dalilin liƙa gashin baki,
tabe bakinsa yayi alamar i don’t care, ci gaba da gogewa yayi ana haka sai ya ga gashin girar ta da aka liƙa masa shima ya zame gefe guda, tashin hankali a fili ya ce meke faruwa ne wai
Hannunsa ya sa ya ciro gashin girar duka guda biyun nan take asalin jagirarta mai kyau ga tsari ta bayyana,
Natsuwa yayi ya ƙurawa face ɗinta ido sai yaga fuskar ta koma ta mace sak ! Kansa ya gama ɗaure wa sanya gashin girar dana bakin yayi cikin handkchief ɗinsa ya naɗe su ciki ya ajiye gefen bedside drawer ɗinta,
Ya jima yana kallon wannan kyakkyawar fuskar har lokacin bai kawo wa ransa cewa maca ba ce ba sai da yasa hannu ya tumbuƙe hular dake kanta, nan take gashin kanta ya tarwatse ya warwaro har saman shoulder ɗinta mai kyau ga laushin gaske,
Nan fa junaid yayi zuru yana ganin wannan ikon Allah ( wonders shall neva ends)
ganin ta soma motsi zata farka, yasa shi yin wuff ya dira daga saman bed ɗin ya boye abayan curtins ɗin dakin,
buɗe idonta tayi waɗanda suka cika tab da kwalla, sunyi jawur sun ƙanƙance, wani irin raɗaɗi taji a marar ta, gashi sam ba ƙwarin jiki atattare da ita, wata irin kasala ce ta dabaibaye ta a galabaice ta miƙe tana zubar da hawaye, yunƙurawa tayi tare ɗan matsawa gefe nan taga jini malale a saman bedsheets ɗinta ya baci sosai ,
Wani irin mugun bugu xuciyarta tayi mata saboda ita sam batasan jinin menene ba, saboda bata ta6a yinsa ba wannan ne karo na farko a wannan shekarun nata 17years,
lokaci guda ta fashe da matsanancin kuka ganin jini 6aro 6aro na fitowa daga jikinta, cikin kuka take faɗin “innalallahi wa’inna ilaihirraji’un shikenan na mutu wayyo Allah wannan wane irin ciwo ne naji haka, nasan mutuwa zanyi
tashi tayi a firgice tasa hannu ta cire zanin gadon ta nannaɗe sa ta ajiye sa anan,
gaba ɗaya ta fita hayyacinta ta zabure kamar wata mahaukaciya tama rasa me zatayi , cikin toilet tashi ge tana kukan baƙin ciki ,
A jiyar zuciya junaid yasaki, har yanzu ya gaza gasgata abunda idonsa ke ganin masa, shin wanene wannan tukur mai aikin mu ko kowa ? kamar mace nake gani fa, oh my God mafarki nake ko gaske, kodai idanuna ne ke nuba min hakan taya tukur mai aikinmu zai kasance mace !! Ya jefa kansa wannan tambayar
Hannu yasa tare da murxa eyes ɗinsa don yayi comfirming abinda ke faruwa cewa gaskiya ne its not a dream,
yana nan tsaye la6e a bayan labulen yana jiran fitowarta, saboda ya gane wa kansa zahiran abunda ke faruwa ,
Sehrish kuwa tamkar ranta zai fita, saboda tsoran jinin da ta gani ga kuma ƙyanƙyami daya kamata,
cire wandon jikinta tayi sannan ta cire rigar ma, hannu tasa ta balle abunda take matse ƙirjinta dashi tayi wurgi dashi,
ta firgita da ganin yadda jinin yake gangarowa a tsakankanin cinyoyinta kai kace fanfo aka buɗe,
Cikin tsananin tsoro ta ƙarasa gaban fanfo tashiga dambe da jinin nan ita ala dole sai ta dakatar dashi daga fitowa ????
Tana wanke wa yana sake kwaranyo wa kamar ana ingiza shi,
ganin yaƙi tsayawa yasa ta dakata, ta zuƙunna a wurin tana kuka tayi mai isarta, sannan ta yanke shawarar ta koma cikin bedroom ɗin ta samu wani abu ta cusa, sam ta manta cewa pant ɗinta ɗaya ne kuma ya bace shima, koda me zata sa ?
A haukace ta fito cikin sauri junaid ya rufe idonsa tare da jan labulen ya rufe face ɗinsa, bai jin daɗin tsayawa ba saboda yaga abunda yake haramin agare sa sam babu kaya ajikinta,
Jikinsa ne yasoma kerma nan take yadinga jin zuciyarshi na tashi ynx ya tabbatarwa kansa cewa tukur mai aikinsu zankaɗeɗiyar budurwa ce ba namiji ba, shigar maza kawai take yi saboda wani dalili nata,
buɗe wardrobe ɗin tayi saboda rashin natsuwa duk ta watso da kayan dake ci tashi ga laluben ɗan kyallen da zata sa, wani mayafi ta ɗauko sai da ta riƙe sa gam a hannunta sannan ta tuna cewa bata da pant ɗin da zatasa,
zuƙunne wa ƙasa tayi ta shiga rera wani sabon kukan, gwanin ban tausayi jin har yanzu wannan blood ɗin yana mata flooding a under ɗinta yasa ta koma cikin toilet tana kuka,
Shiga tayi taja kofar ta rufe …
Ganin ta shige yasa junaid saurin fita daga ɗakin, tafiya yake amma tunanin yadda zai taimaka mata yake yi saboda ya gane cewa akwai abubuwan da take buƙata, amma tayaya? bayaso ta gane cewa ya ganta a matsayin mace, baisan wani hali zata shiga ba,
Maganar abbansu ya tuna a inda ya ke cewa
aduk lokacin da kuka ga wani na buƙatar taimako, to kutaimaka masa indai kuna da halin yin hakan, a sanadiyar hakan kuma Allah zai agaza muku a lokacin da kuka shiga wani hali na rayuwa,” Cikin sauri ya hanzarta nufar bedroom ɗinsa , key ɗin motarsa ya dauko tare da kuɗi , sannan cikin gaggawa ya kama hanya ya fita daga main palour ɗin , Babu kowa tsit kake ji amma ko’ina akwai haske kamar rana, saboda an ƙawata gidan gaba ɗaya da wasu irin electric bulbs, Moto park ɗinsu ya nufa buɗe inda tarin motocinsu ke nan, motarsa yayi ya shiga nan take yayi mata key yaja ta, Sam junaid ya manta cewa security guards ɗin gidan soldiers ne kuma bana wasa ba, kuma ba’a basu iznin subar wani ya fita a wannan lokacin ba kosu fawan dake satar hanya su fita night club su suka san ta boyayyiyar hanyar da suke fita, Santal ya miƙi titin da zai sada ka da babban gate ɗin gidan, yana isa wasu gabza gabzan sojoji guda 4 suka tunkare sa kamar zakuna, a dolensa ya dakata da tuƙin ya tsaida motar, jikinsa sai rawa yake yi ba don komai ba sai don uzirin dake gare sa, zuge glass ɗin motar yayi yana kallonsu a yatsine, . “Where are you going in this darkness night,”? ɗaya daga cikinsu ya tambaya yana kallonsa, banza yayi baice musu komai ba don yasan koya ce ɗin ba barinsa zasu yi ya fita, rigima ce zata tashi ƙarshe suce zasu sanar da Abbansu a tada hargitsin duniya, jin yayi shiru yasa ɗaya daga cikinsu daka masa tsawa tare da cewa “maza ja mota ka koma gida ƙaramin yaro dakai sai taurin kai,’ Ɗaya daga cikinsu ne ya kwatsa ma wanda yayi masa tsawa magana” stop shouting at him ! he’s a young lallashinsa ya kamata kayi ya koma ” xukunno wa yayi cikin lallami ya ce masa “pls go back ba’a bamu izni mubar wanin ku ya fita ba daga gida a wannan time ɗin,’ girgiza kai junaid yayi tare da cewa “am sorry to say i won’t go back just allow me to go, duk rigimar da za’ayi sai dai ayi amma ba inda zani i will stay here till u give me the permission to go,’ Ya ƙarasa maganar tare da jingina kansa jikin kujerar motar yana kallonsu fuska adaure” _Hafsat Bature
~(Boss Lady)~

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74Next page

Leave a Reply

Back to top button