ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

Page 33-34

Kallon juna suka shiga yi, ganin cewa ya toge yasa ɗaya da cikinsu sake yi masa magana cikin lallami ” tell me why do u want to go out ? if u need something i can go and buy it for you ,”
Jin hakan yasa junaid jin sauƙi aransa, hannu yasa ya zaro kuɗi kusan dubu goma ya miƙa masa sannan ya cije ya daure ya ce “pads nake so na mata kwali guda sannan panties dozen ɗaya bansan size ɗin ba amma karya wuce na ƴar 17 years “
tsananin mamaki ne ya kamasu jin yace pad da panties, amma basu ce komai ba saboda baya a tsarin aikinsu fira ko tambaye tambaye da ɗan masu gida,
“Sojan yace shikenan, ka koma ciki nan da 15 minutes sakonka zai iso,
Amsa yayi da cewa “thank you i will be waiting,”
Sannan yaja motar a hankali yayi baya da ita ya karya kwana ya koma ciki,
A bangaren sehrish kuwa tagama galabaita, ta jigata sosai tarasa uwar ubanta , sai faman zarya take tsakanin toilet da bedroom , daga taji ya zubo sai taje ta wanke ta dawo ciki yana ƙara zubowa sai ta koma da gudu tana kuka ????

Junaid sai faman zagaye zagaye yake yi acikin babban falon yana jiran dawowar sojan da ya aika, sai faman zullumi yake yi gudun kada yarinyar ta halakar da kanta da damuwa saboda ya lura ta tsorata sosai,
Knocking yaji da sauri ya ƙarasa bakin kofan shiga falon , sojan ne ya dawo hannunsa ɗauke da kwalin pads tare dozen na pant kamar yadda ya umarta , hannu junaid yasa ya karba yana zabga masa godiya,
Sergiant ɗin yace “ga sauran chanjin ” ko dubu biyar bai kashe ba a siyayyar junaid yace ” bana buƙata”
Yana faɗin hakan ya kama hanyar da ɗakin sehrish yake,
murmushi sojan yayi tare da cewa a cikin zuciyarsa “lallaine yaro! iyayenka sun tara ma kana daga zaune kana shan iskar A.C,’
yana faɗan hakan ya juya ya fi ce,
Cikin sanɗa yake tafiya time ɗin da ya isa kofan ɗakin tsawa yayi jikin door ɗin yana sauraren kukanta tana cewa ” Ya Allah kadauki raina na huta, narasa me zanyi bansan menene ke faruwa da ni ba, jini ko ina ya ilahi
lumshe idonsa yayi tare da buɗe su lokaci guda, hannunsa na rungume da kwalin pads ɗin ga panties ɗin dake cikin leda asaman kwalin ya haɗa ya rungume a ƙirjinsa,
“Junaid ynx taya za’ae ka kai mata wannan ? Shin zata ji daɗi kuwa idan ta gane cewa ka gane cewa ita maca ce ba namiji ba? mezai faru idan tagane cewa ka ganta acikin wannan yanayin zata ji daɗi kuwa !?
Natsuwa yayi yana sauraran abunda zuciyarsa ke sanar dashi , rufe idonsa yayi tare da cizon red lips ɗinsa yana mai jin takaici gaza shiga yakai mata taimakon gaggawa, ga kukanta da yake ji ba ƙaramin hurting ɗinsa yake yi ba, tausayinta yake ji saboda bata da kowa anan da zai taimaka mata in bashi ba dayasan halin da yake ciki, Allah sarki daɗin uwa kenan da ƴan uwa da ace tana da ɗaya daga cikinsu a kusa da ita da abun yazo mata da sauƙi,

Jin alamar ta shiga cikin toilet yasa shi yin saurin kutsa kai a hankali ya shiga, ya ajiye mata kwalin pads ɗin a saman gadonta abunda bai sani ba sehrish bata da masaniya akan wannan abun daya ajiye mata,
Jin alamar tana ƙoƙarin fitowa yasa shi yin wuff ya fice, a kofar ɗakin ya tsaya yana sauke ajiyar zuciya natsuwa yayi yana sauraran ta taciki,
Sai faman wiping tears take yi, tayi jaga jaga tafita out of sense ɗinsa, har wata ƴar rama tayi ga azabar menstruation ga tashin hankalin blood din dake bleeding a in between legs ɗinta,
dakyar tasamu ta ɗaura wannan mayafin fari mai sharara ajikinta, tsayawa tayi agaban mirror tana lalube lalaube ita kanta batasan me take nema ba kawai burinta tasamu abunda zata cusa a vagina ɗinta ko tasamu yadaina zuba tana cikin laluben nan ,
Karaf idonta ya hango mata kwalin nan da junaid ya ajiye mata a saman bed, ta cikin madubi ta hangosu,
A firgice ta juya tana kallonsu, cikin tsananin tsoro take takawa a hankali tana tunkararsa har ta isa gabansu,
Tsayawa tayi cak tana kallonsu , ledar sama tabi da kallo dayake ta kana iya hangen set na panties ɗin da ke ciki, tabbas tagane cewa pant ne amma tarasa gane wannan madai-daicin kwalin na menene ????
Karanta jikinsa tayi tare da furta “Dry love” sunan pads ɗin da tagani ajikinsa kwalin kenan,
tunani take wanene ya ajiye mata wannan? anya ba al’janu bane ba? waiwaye ta shiga yi tana kallon gefe da gefenta taga ba kowa sai ita,
Kamar wata sullu6uyo haka ta koma, hannu takai cikin tsoro ta ɗauki ledar panties ɗin ta zaro su tana kallo,
Ba ƙaramin kyau su kayi mata ba, amma bata jin zata iya anfani dasu saboda batasan waya ajiye mata ba,
Ajiyesu tayi sannan takai hannu tasha fa saman kwalin pads ɗin kafin ta janye hannun cikin wani irin yanayi furta ” Ya allah ka tsare ni daga sharrin aljanu, ni dama nasan wannan blood ɗin da nake gani bana lafiya bane, ashe sune suka shafe ni,”
Nan tashiga jera wani kukan, duk a kunnan junaid ganin cewa zasu kwana ido a buɗe ga dare yayi sosai kusan ƙarfe 1:00 ynx ,
Cikin kuka ya sake jiyo ta tana cewa “Dan Allah koma wane aljani ne yake hukunta ni akan ƙaryar da nayi na shigar mace a matsayin namiji don Allah ayi haƙuri a haife mun wlh nima ba da son raina nayi ba..” kuka ne yaci ƙarfinta
Jin cewa yarinyar tayi amanna da cewa aljanune suka kawo mata kayan nan kuma sune suke horar da ita yasa junaid gyara muryarsa cikin wata irin amsa kuwa yace “Ke ! Yarinya ! mune nan ke hukunta ki bisa zunubin da kika aikata ! ,” .
Zaro ido sehrish tayi jin wannan muryar mai ban tsoro tabbas wannan muryar aljanin ce ta faɗa a ranta, nan take zufa ta soma sintiri a fuskarta dukkan ilahirin jikinta kuma ya soma makekketa, ta ƙanƙame jikinta a tsorace tace “dan Allah kuyi hakuri bazan ƙara ba i promised u kuskure ne ku yafe mun wayyo Allah na nashiga ukuna,”
murmushi junaid ya saki dama yayi tunanin hakan yadda take a firgice tsaf muryarsa zata koma mata ta aljanu,
don haka ya ƙara gyara muryarsa ya ɗaga ta sosai ya ce “Munjiiiiiii ! Zamu iya yafe miki amma bisa wasu sharruɗɗa in kuma kika kuskure zamu raba sassan jikinki mu kaisu bayan duniya hhhhhhhhh,”
ya ƙare da wata irin dariya mai razanarwa, nan take fitsari ya kubce mata ta tsorata matuka kuma ta ƙara tabbatarwa kanta da cewa aljanun ne ke maganar saboda ita dai bata ga kowa ba acikin ɗakin,
cikin kuka tace “Na amince komai kuke so zanyi,” .
lumshe ido junaid yayi shi kaɗai yasan yadda yake jin daɗin wannan yanayin,
Hannu yasa tare da gyara makoshinsa yace “Sharuɗi na farko ! Zaki runtse idanunki kada ki buɗe har sai munce ki buɗe in ba haka ba hhhhhhhhhhhhhhh zamu tsoma ki jikin rijiya gaba dubu,”
la66anta har rawa suke yi wurin faɗin “Na amince na amince zann ..zann nama rufe yanzu haka wlh banzan buɗe ba don Allah kada ku sani acikin rijiyar nan banso zan bi umarninku,” ta ƙarasa maganar tare da runtse idanunta cikin tsananin tsoro,
“Kin rufe !!! taji aljanin ya ambata cikin sauri tace “eh na rufe, .
dariya cike fal a bakinsa dakyar yake gumtse ta, a hankali ya tura kofan ɗakin yasa kai ya shiga,
Bin ta da kallo yayi bil’hakki ta damtse idonta garam, kawar da kansa yayi daga kallonta saboda hakan na isa yasa shi cikin yanayi saboda mayafin da ta ɗaura shara shara yake,
Cikin sanɗa ya ƙarasa gaban kwalin pads ɗin yasa hannu ya buɗe sa, zaro dami ɗaya yayi ya ajiye saman gadon, 6an6are sa yayi cikin gaggawa wa ya curo guda ɗaya, sannan ya ɗauko pant guda ɗaya ya shimfiɗa a saman katifar gadon, ya buɗe sa sannan ya ɗauko pads ɗin ya cire ledar jikinsa mai gam, ya manna a tsakiyar pant ɗin ya sanya mata shi da kyau sannan ya ajiye, ɗagowa yayi ya sake kallon fuskarta ba ƙaramin tausayi ta bashi ba ganin yadda eye lid ɗinta ta kumbura, hancinta yayi jawur saboda yasha matsa ga lips ɗinta sun kumbura sosai,
Sai da yasanya mata pads ɗin ajikin panties kusan guda biyar, duk ya jera mata su, sannan ya lallla6a ya fice ya tsaya jikin kofar, yana sauke ajiyar zuciya kafin yayi gyaran murya ya ce “muna baki umarni da ki buɗe idonki yanzu,”
A hankali ta buɗe idonta basu sauka akan ko’ina ba sai kan abunda ya haɗa mata, binsu tayi da kallo gasu nan ajere gwanin kyau, muryar aljanun ce ta sake katse ta ” Sharaɗi na biyu kina sauraron mu da kyau ,”?.
Cikin natsuwa tace Eh ina sauraronku,
Murmushi jubaud yayi tare da ɗaga muryarsa da ƙarfi yaci gaba da cewa ” muna baki umarni da ki ɗauki ɗaya daga cikin panties ɗin nan ki sanya shi in kika kuskure zamu ɗauki gangarar jikinki mu kaita ƙasa ta bakwai,”
Jiki na rawa tasanya hannu ta ɗauki pant ɗaya ta zura a jikinta, nan take taji wani sanyi a ranta, cike da biyayya tace “Aljani na sanya,”
gaza jure dariyar dake cinsa yayi don haka ya kwashe da dariya cikin wani irin salo kamar Aljanun ne ke dariya yace “Hhhhhhhhhh yarinya kinyi kyan kai, don haka ! daga ynx in kina so ki tsira daga faɗawa daga tarkon bakin aljani dole ki rinƙa sanya wannan abun da muka aje maki in ba haka ba zaki fuskanci matsala …..hhhhhhhh,’
Cikin sauri tace ” zan….zanyi komai kuka ce,”
sannan ya ce”Sharaɗi na ƙarshe ! Hhhhhhh yanzu ki hau saman gado ki kwanta da safe zamu kawo miki saƙo hhhhhhh,”
Cikin gaggawa ta haye saman gadon, har ta kai hannu zata ɗauki bedsheet ɗinta ta tuna cewa ya 6ace don haka dole ta hakura, ta ƙudundune kanta, tayi lamo tana jiran bacci yazo ya ɗauke ta,
Ajiyar zuciya junaid ya saki don shima ya gaji ga bacci dake damunsa shida ya saba bacci da wuri,
Jin shirunta ko shesshekar nan ta kuka ta daina yi hakan ya tabbatar masa cewa she’s sleeping , don haka ya lallaba ya tura ƙofar ya zuwa hannu jikin bangon ya kashe mata hasken ɗakin sannan ya tafi,
Tabbas taji ƙarar kashe mata ƙwan ɗaki da akayi amma bata kawo komai aranta ba, don haka tace acikin zuciyarta “daga gani waɗannan aljanun masu imani ne basu cutar dani ba, sun taimake ni, Ya Allah na gode maka
Da wannan tunanin bacci yayi awon gaba da ita,
A bangaren junaid kuwa hmmm ina sam bacci ya ƙauracewa idonsa daga ya runtse ido fuskar Yarinyar yake gani, sam ya gaza sukuni sai fama juyi yake yana rungume fillow a ƙirjinsa ya gaza mantawa da wannan beautiful face ɗin mai cike da annuri ga sanyin kyau launin fatarta ba ƙaramin burgesa tayi ba ya jima baiga mace me qualities irin na yarinyar ba,
(to dama ai macen novel ce ????)

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74Next page

Leave a Reply

Back to top button