ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

Bayan sun kammala ci , hajjaju ta kai isu zuwa bedroom din da ta ware domin irinsu in ta dauko su anan suke kwana sannan ta yi masu sallama ta fice, tana fita y’an matan kauyen nan suka haye saman bed din dake ciki kuma shi kadai ne, bin su da kallo tayi ganin yadda suka wawware kafafunsu saboda kar tasamu wuri tace zata hau.

Murmushi tasaki, “Allah sarki rayuwa ni ina ne bazan iya kwana ba, bed is ur problem, Sisters dina sune damuwata,
Cire hijab din dake jikinta tayi, wardrobe din dake manne a bango, ta bude babu wasu kayan kirki a ciki, zannuwan atamfa ne kawai, saka hijab din tayi ciki ta rufe,
toilet din dake ciki ta shiga, komai na ciki a tsaftace yake, fari kal! Gaban mirror ta karasa tana kallon fine face dinta, fanfo ta kunna ta tarba hannuwanta tana wanke fuskanta, bayan ta gama tasa hannu ta cire head din dake kanta, ta yi holding dinsa a hannunta tana kallon doguwar kitson kalabar da akayi mata guda biyu ta zubo tun daga head dinta har zuwa west dinta, tana da Yalwatacciyar sumar kai dark brown colour very smooth ga kwantaccen saken gefen fuska.

Fitowa ta yi daga toilet din, samunsu tayi sai minshari suke ja tamkar raguna, wardrobe din ta sake bude wa daya daga cikin zannuwan da ta gani ciki ta dauko, ta shimfida a kasa, ta kwanta
Washe gari tunda sassafe suka fita, hajajju ce ke driving yayin da yarinyar take a gefenta , sai kalle kallen hanya take ta glass din motor, hajajju ta ce “Har yanzu baki fadamun sunanki ba ! da age dinki yakamata nasani ko”? tayi maganar ne a lokacin da take kokarin juya sitiyarin motar wurin canza hanya tabi titin da zai kai ka har izuwa asibitin.

Murmushi yarinyar tasaki tare da cewa “Sunana SEHRISH amma Oumman mu tana ce mun RISHI , shekarata 17 cif ,” jinjina kai hajajju tayi tace “Wow nice name and it really deserves , ” cike da jin dadi Sehrish tace “thanks” har suka isa asibitin basu kara magana ,
Sehrish tayi ma hajjaju jagora har izuwa ICU intensive care unit , inda aka kwantar da sisters din nata, lokacin da suka shiga ciki, da gugu wata kyakkyawar yar matashiya ta taso ta rungume sehrish, tsananin mamaki yasa hajajju sakin baki, sai ta dinga ganin tamkar mafarki take yi, tun da Allah ya halicce ta bata taba ganin yara masu shegen kama irin wadannan ba basu da wani banbanci ko miskala zarratin komai nasu iri daya sak , lokaci guda ta rikice takasa gane wacece ma suka zo da ita, wacece sehrish din don ta saje da dayar, hajjaju bata gama mamaki ba sai da taga dayar wadda take kwance saman gadon marasa lafiya ansa mata Oxygen dakyar take jan numfashi gwanin ban tausayi , nan takara rikicewa saboda itama wacce take kwancen Sak kamaninsu ba banbanci hakan na nufi su y’an uku ne kenan.

Kankame ta tayi tana kuka , itama sehrish din kukan takeyi hannunta tasa tana d’an bubbuga bayanta tace “Jahad ki daina kuka hankalina yana kara tashi komai zai tafi dai dai insha Allah, janye jikinta tayi daga nata tace “ina kuka ne ba don kai na ba sai don Husanna dr yace in ba mu fara biyan kudi an mata aiki ba , mutuwa zatayi kuma ynx haka kudin gado ya kare sallamar mu zasuyi ko kudin magani babu ,” hankalin Sehrish ba karamin tashi yayi ba,
Hajajju dake tsaye tana kallonsu, jikinta yayi mugun sanyi saboda tsananin tausayi, ita kanta wadda sehrish takira da Jahad akwai wound a goshinta, anyi mata dressing da bandage duk jini a jikin sa , hannunta ma akwai kanula alamun anyi mata karin wani abu jini ko ruwa , a kagare hajajju take da taji labarin wadannan y’an ukun lallai bakaramar wahalar rayuwa suka sha ba.

Muryar Sehrish ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta shiga “Jahad ga hajajju ku gaisa kuma kiyi mata godiya sbd itace zata sama mun aikin da zan fara yi nasamu kudi nabiya ayi maku aiki,” matsawa tayi gaban hajjaju tana share hawayenta cikin girmamawa tace” ina kwana hajiya ,” murmushi hajajju tasaki tare da dafa kadarta tace “lafiya lou ya jikin naku “? Jahad tace “Alhamdllh ni da sauki husanna ce abun sai kara gaba yake yi don dr yace koda an mata aikin ba lallai ta dawo yadda ake so ba….”

Kuka ne yaci karfinta har takasa karasa maganar , rungumo ta hajjaju tayi a jikinta tana lallashinta ” am sorry my daughter stop crying insha Allah everything will be ok , cikin kuka ta amsa da “zandaina mungde ssai ,” karasawa Sehrish tayi wurin husanna dake kwance rai hannun Allah , gefen gadon ta zauna tana kallonta idonta cike tab da kwalla tace “Allah ya baki lafiya yar uwata ina jin duk wani irin radadi da kike ji a zuciyarki wanda yayi sanadiyar shigarmu cikin wannan halin bazai taba gamawa da duniya lafiya ba Allah ya isa tsakanin mu dashi mugu azzalumi macuci …” a karshe ta fashe da kuka ta kwantar da kanta a saman jikinta , har cikin ranta take kukan.

Tsohuwar dake kula dasu ce ta shigo cikin sauri hannunta rike da magunguna da takarbo masu , a nan tasamu hajjaju tsaye ita da jahad tana lallashin ta , jin alamar shigowarta yasa suka jiyo suna kallon , cikin sakin fuska tace “Sannun da zuwa hajjaju ke ce da kanki ,” murmushi hajjaju tasaki dama sun son juna da alama , ” kwarai kuwa nice gwaggo dama ke ce ke rike da yarannan amma ni ban taba ganinsu ba gsky ,” murmushi gwaggo tayi tace “bakya leko mune shiyasa amma sun jima wuri na ni nake kula dasu ,” jinjina kai hajjaju tayi tace “hakane amma gwaggo jikokinki ne su”? Goggo ta girgiza kai tare da cewa “a’a Allah ne ya hadani dasu nima labari ne mai tsawo , amma ynx bani da kwanciyar hankalin da zan zauna na baki shi , ki bari saina samu natsu,” tana gama fadan hakan ta mika ma Jahad magungunan “karbi nan naki ne dakyar nasamu kudi na siyo su,” godiya tayi mata ta karba , a tare suka taka izuwa inda sehrish ke kwance jikin Husanna , cike da nuna tsantsar tausayi hajjaju tace “Allah ya bata lafiya Allah sarki mutum baya sanin halin da duniya take ciki wani sa’in sai ziyarci asibiti nan zai ga marasa lafiya iri iri gwanin bantausayi hakika na tausayawa wannan yarinyar tana cikin hali Allah ya kawo musu sauki da duk marasa lafiyan dake fama da ciwo ,” amsawa sukayi da amin , har time din sehrish bata dago da kanta ba , ita kadai tasan yadda take ji aranta.

Hajjaju ta mayar da idonta kan Gwaggo tace “idan ba damuwa muje ki raka ni wurin likitan zanyi magana dashi ,”
fita sukayi a tare , wuri Jahad tasamu ta zauna a chair din dake facing din gadon mara lafiyar, kallonsu takeyi su biyun tana kara jin kaunar y’an uwan nata , taji dadin zuwan rishi har cikin ranta , jajircewarta akan ganin sun samu rayuwar mai kyau yana kara mata ninkin son yar uwarta ta, tazama tamkar uwa agare su , alhalin ita age dinsu daya duk da tare suka zo duniya amma sun tsere wa rishi da mintina a wurin haihuwa , tunani iri iri ke zo mata a ranta runtse idonta tayi hawaye na kwaranyo wa daga idonta

Gabad’ayansu sun shiga cikin yanayi , duk sunyi zurfin tunani , numfashinta suka soma ji da karfi da karfi wani irin sauti mai matukar razanarwa , a firgice sehrish ta dago da kanta cikin rudu ta furta “Subhanallah! jahad husanna ta cire oxygen da aka samata,” a rude jahad ta matso kusa da su hannu tasa ta tana kokarin mayar mata roban oxygen din , buge mata hannu tayi tana wani irin gurnani ga zufa sai ke to mata take yi ga wani irin tari da take yi cikin kuka take ambaton “Seh..seh..sehrish ,”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74Next page

Leave a Reply

Back to top button