ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

Lokacin da ta koma gidan dakyar ta samu hanyar shiga mutane sun cunkushe ko’ina,
Ta raza na da ganin wasu matasa guda biyu hannunsu ɗauke da galons na fetur ga ashana a hannunsu kira suke abasu hanya su ƙone mayun, saboda rashin imani matan dake cikin gidan suka shiga basu hanya, haka aka janyo su waje daga cikin ɗakin sai kuka suke yi gwanin bantausayi,
Zazzaga musu fetur ɗin suka soma yi ajikinsu nan take numfashin husanna ya soma hau hawa, jahad kuwa ta ƙanƙameta tarungume ta ajikinta sun rungume juna suna jiran ta Allah ta kasance,
A dai-dai wannan lokacin jiniyar motar ƴan sanda ta karaɗe ko’ina, mota guda suka yo sai a kopan gidan dandazon mutanene da suka gani ne ya tabbatar masu da cewa nan ne address ɗin da yarinyar ta basu,
Tabbas a ranar sunga bakar rana, dakyar ƴan sanda suka kwace su, suka sanya su a bayan kanta suka tafi dasu,
Mamee da mamansu sun sha kuka saboda tausayin ya rayuwar yaran zata kasance ?
Case ya koma hannun police sai yadda hali ya bada, a police station suka kwana ana investigation akan mutuwar tsohuwar, ga baƙar yunwa ga tashin hankali, duk yaran su firgita matuka ga kwanan cell sai uban sauro dake cizonsu,_ ????•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•
ABBAN SOJOJI
mallakin
HAFSAT BATURE
wannan ƙirƙirarran labari ne wasu abubuwa ma daga cikinsa ƙirƙirarsu akayi domin ilmantarwa faɗakarwa da kuma nishaɗantarwa
gargaɗi ko da gigin wasa ban yarda wani yayi amfani da wani sashe na littafin nan ba batare da iznina ba, wahala tace ban shiga harkar kowa ba kuma nima bana so a shiga tawa kowa ya tsaya iya matsayinsa
page 43 to 44
_The Father Of soldiers
Kamar yadda su husanna suka kwana a cell ba bacci itama haka ta kwana ido buɗe, banbancin shine su suna cikin matsanancin hali, ga sauro ga yunwa ga ba wanka komai ya hargitse musu bayin Allah,
Zuciyarta ce ke matsanancin buga mata wanda hakan ya tabbatar mata da cewa, ƴan uwanta na cikin mawuyacin hali, saboda aduk lokacin da wani abu mummuna ya faru dasu sai taji a jikinta,
zuciyarta ce ke matsanancin buga mata, zufa ce ke ta faman sintiri a jikinta, kai kace akwai zafi ne Alhalin yanayin garin sanyi ne,
dukkan ilahirin jikinta sai makekketa yake yi, sam zama saman gadon ya gagare ta, tadawo ƙasa jikinsa ta jingina bayanta, tausayin rayuwarsu ce ta kamasu,
tun suna cikin ciki ƙaddarar su ta soma, sun sha baƙar wahalar rayuwa, ba irin tashin hankalin da basu gani ba, wani lokacin har tambayar kansu suke wai Allah baya sonsu ne? astagfirullah ????
Amma hakan baisa sehrish tadaina nafilfilin da take yi ba, yau ma rashin tsarkin da bata dashi ne ya hanata yin sallolin, addu’o i kawai take faman maimaitawa duk wacce ta zo mata a bakinta,
Amma fa a daren nan tasha kuka, kamar ba gobe, dole mane sehrish tayi kuka domin kuwa halin rayuwar da suke ciki duk juriyar mutun yaji sai ya matse kwalla,
fargabarta wane hali su husanna ke ciki tana tsoran ta rasa jininta, na biyu wane hali mahaifiyarsu take ciki shin tana raye ko ta mutu? na uku wanda shine take jinsa sosai a ranta wato zuwan SGR, BABBAN YAYA,
tarasa me yasa ya tsaya mata a zuciyarta meyasa take jinsa, meyasa take fargabar ganinsa,
Zuciyarta tana azalzalarta akan son ganinsa, idanunta na kwaɗayin sa shi a idonta, Amma a ƙarshe tayi addu’ar Allah yasa ya zama alkhairi agare ta !!!
sai da asuba bayan ta shiga toilet ta canza pad ɗin cikinta, sanna fa bacci yayi awon gaba da ita,
A can ciki kuwa suna shiryawa zuwan Abban nasu, farin ciki a gun junaid ba’a magana, saboda ya gama tsara shagwa6ar da zaiyi masa in yazo, sannan akwai abunda yake burin ya sanar dashi ,
Har garin Allah ya waye sehrish batasan meke wakana ba, aunty azmi ta shigo ta same ta tana sharar bacci, ganin yadda jikinta ke kerma ya tabbatar mata da cewa sehrish ba lafia ba, har jikinta ta ta6a temperature ɗin jikinta yayi zafi,
Don haka bata attempting tayar da ita ba, kawai sai dai ta gyara mata blanket ɗin jikinta, sannan ta fice,
ganin cewa aiki zai yi mata yawa time zai iya ƙure mata, saboda baƙin da zasu zo yau, da buƙatar su kammala girke girken da zasuyi da wuri,
Kanal yusif ta nema ta sanar dashi halin da ake ciki na rashin lafiyar mai aikinsu tukur, taji daɗi da yasanar da ita cewa, akwai chefs da zasu zo kada ta samu damuwa,
tun 7 suka ƙaraso, kwararru ne a fannin sarrafa abinci kala-kala, su biyu ne, chef ummu da abokiyar aikinta momina, azmi taji daɗin zuwansu, nan fa kowa ya naɗe hannun riga aka soma gudanar da aiki,
Tuni ƙamshi ya soma gauraye ko’ina harta cikin hancina, irin ƙamshin da ke tada mutun daga bacci,
Wurin 9 na safe, jirginsu hajiya azeema yayi landing daga legos, ƙanwar Abbansu ce, hamshakiyar attajirar mai kuɗi ce, tatara har sunyi mata yawa, a tare da ita akwai Captain najeeb da Talal ƙannensu kanal yusif ne da take ruƙo a wurinta, saboda bata ta6a haihuwa ba, lalura ce ta same ta na rashin aihuwa, gashi Allah ya jarabce ta da sonsu kamar hauka,
Hakan yasa Abbansu ya mallaka mata su, a wurinta suka taso har suka girma,
Kanal yusif ne ya ɗauko su daga airport, izuwa gidan murna agunsa har ba’a magana, saboda ganin captain najeeb da Talal, an jima ba’a haɗuba duk da suna ƙoƙarin sada zumunci, aiki ne ya ke hanasu wani time ɗin, saboda aikin soja ba aiki bane na zama wuri ɗaya ba,
Bayansu sai general Ishaq wanda ya kasance shina first born a wurin abbansu wato yayansu gaba ɗaya, wanda ke zaune a kaduna state, tare da matarsa yazo shuwa’arab ce suna kiranta da Aunty Babba, saboda tana auren babban yayansu gaba ɗaya, sun zo ne tare da Hafsat yarsu ɗaya tilo, wadda take karantar military nurse, ynx haka ta kammala karbar training ɗinta aiki take yi, ta gaji abbanta kenan
daga su kuma sai mai bi ma ishaq wato na biyu a wurin abbansu, Abbas mai riƙe da muƙamin Colonel general, tare da matarsa yazo (AMANI) itama balarabiya ce ƙanwar Aunty babba ce yake aure, kuma dama ita ta haɗasu,
A nan cikin abuja suke da zama su ma, babu ƴa’ƴa a tsakaninsu soyayya suke sha,
daga shi kuma sai na ukunsu matashin saurayi bai ta6a aure ba,
Bakowa bane face brigadier general Abuhaisam, shi kaɗai yazo daga jos sai security ɗinsa,
Waɗannan sune suka samu damar halarta zuwa tarbar abban nasu sauran kuma suna kan hanya,
Ina fata dai kun riƙe sunan kowanne daga cikinsu saboda in labari ya tashi basai munsha Wahala ba, ????
A babban main palour kowannansu ya hallara, domin dama nan yafi dacewa saboda girmansa da faɗinsa gashi set na royal sofas ɗin dake ciki guda biyu ne a jere,
Hajiya azeema ta hakimce a kujera mai mazaunin mutun biyu, jikinta na sanye da french less haɗaɗɗen gaske ash colour an mata riga bubu dashi, ta kashe ɗaurin ɗankwalin nan irin ture gaka tsiya, amma fa ita ba tsiya bace domin tana da gashi sosai shukune a kanta ta ɗaure da ribbom ya zubo har bayanta, hannayenta na sanye da diamond rings uku uku a kowane fingers na left & right hands ɗinta, price ɗin kowane ring ɗaya yayi 1.5million,
Haka ziririyar chain ɗin dake a wuyanta da earrings ɗinta, sun kai kimanin 200m, agogon diamond ɗin dake hannunta ƙirar graff diamonds ce, farashinta ko ba’a magana, billions ne ke magana ????
Bata jin wuyar kashe wa kanta kuɗi, kai kace ruwan samansu ake tana kwasa, ko kuma daga saman bishiya take tsinkarsu ????