ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE
Babban tashin hankalin shine, Alexandra ta tada 6alli akan cewa yaronta addininta zai biyo kuma tasanya masa suna Alex, nan fa hankalinmu ya tashi, kowa ya harzuƙa akan lamarin,
Ran abba ya 6aci sosai kamar yayi ihu, a ƙarshe daya takura mata akan cewa shifa yaronsa addininsa zai biyo, sai ta ɗauko masa wannan takardar daya sa hannu ajiki wadda akayi rubutu ajikinta da harshen spanish ta nuna masa,
Cikin rashin sanin ma’anar hakan yace “me wannan ke nufi”?
Dariya tayi masa tare da cewa ” wannan takarda dace, ta yarjejeniya dake nuna cewa ka amince ƴa’ƴana su bi addini na! in har ka matsamin zamu shiga court ne ayi shari’a, kuma kada kayi tunanin zaka iya ɗauke takardarnan domin akwai copy ɗinta awurina ba ɗaya ba, signature ɗinka ne ajiki, ????
Hankalin abba fa ya tashi, bai ta6a dana sanin auren Alexandra ba sai alokacin domin takaisa ƙarshe, Ashe wayau tayi masa, tasan hakan zai faru shiyasa tayi rubutun da harshen spanish, shi kuma gudun rigima ya sa bai tambayi menene fassarar abunda aka rubuta ajiki ba kawai yasa hannu, ????
yaso ya tada 6alli akan koma mai zai faru sai dai ya faru , amma maryam ta dakatar dashi takwantar mashi da hankali ta nuna masa cewa, inya bi komai asannu wata rana ita da kanta zata canza, canjin da har yau muke jira amma Alhamdllh an samu ci gaba,
Bakowa bane wannan yaron da ake tada jijiyoyin wuya akansa ba face Surgeon general Rafayet wato BABBAN YAYA,
tun yana jariri bai ta6a kuka da hawaye ba, kuma likitoci sun tabbatar da cewa lafiyarsa garas, amma momynsa har ƙasar waje ta fiddasa aka ƙara dubasa aka tabbatar mata da lafiyarsa, sannan ta yarda,
A lokacin da yana yaro yayi tashen ƙiwuya, ya tsani bakar fata indai launin fatarka ba fara bace irinta mahaifiyarsa tofa kun raba jaha,
Duk bala’inka baka ɗaukarsa, hatta mahaifinsa dake mutuwar son shi, bai yarda da shi duk da hasken fatar abban nasa, tsakaninsu sai dai kallo daga nesa , sai kuma in yana bacci uban ya lalla6a yaje ya zuba mishi ido yana kallonsa,
Shi kuma yaron da maryam ta haifa, ba kowa bane fa ce Marshal omer tazarar satittika ne a tsakaninsa da Rafayet,
Tun suna yara omar ke son wasa da rafayet, amma bai yarda dashi ba duk da kasancewar omar fari ne sosai kamar balarabe, yabiyo mahaifiyarsa Maryam bafullatana,
Gashi shima rafayet ɗin yana son Omar amma tsakaninsu sai dai daga nesa a rinka jefawa juna murmushi ????
daya ƙara wayau hankali ya fara shigarsa, wata irin shaquwa ce ta shiga tsakaninsa da omar, duk da momyn shi bataso yana hulɗa dasu,
kai har takaiga idan dare yayi sai ya saci hanya daga bedroom ɗinsa izuwa nasu, ya haye saman gadonsu wurin omar ya kwanta kusa da shi,
Shima omar ɗin harya gane idan dare yayi, yazauna yaƙi bacci yayi ta zaman jiran rafayet, har sai yazo sannan su kwanta tare suyi bacci,
Maryam kaɗai ce ta lura da hakan, ita dai ba ruwanta, tana son rafayet tanajinsa kamar ɗan cikinta, haka zata je tayi musu addu’a tashafa musu kawunansu,
Ranar da alexandra ta gane hakan akan idonta, taga rafayet ya shiga ɗakinsu omar tsakar dare , aiko washe garin ranar tarinƙa zabga masifa har sai da kowa ya gaji,
Bayan wannan lokacin maryam taci gaba da haihuwa a inda ta sake haihuwar namiji again wanda yaci sunan shi najeeb, gaya nan kuna kallonsa, wato captain najeeb,
daga shi kuma sai Kanal yusif shima gashi nan zaune, daga yusif kuwa sai commender haroon, daga haroon sai Captain adams,
daga adams sai khaleed daga shi kuma sai jabeer da irfan, haka ta haifesu, daga nan ne ta dakata,
A bangaren Alexandra kuwa shiru sbd tace ta kammala nata, abba najin baƙin cikin musamman inyaga Ya’yansa zasu masallaci sun haɗu su duka amma babu rafayet acikinsu,
Ya so ya sake tada 6alli akan yaron, saboda yana da hanyar da zai kwaci kayansa daga faɗawa daga halaka, amma mahaifiyarsa tayi masa tatass akan cewa lokacin da ya aurota dawa yayi shawara, taja masa kunne akan cewa kada ya kuskura ya ƙara tankawa akan alexandra,
A dolensa yaja bakinsa yayi shiru bisa umarnin mahaifiyarsa,
A karshe ya koma yana nuna mata soyayya don yaja hankalinta, y rinƙa binta sau da ƙafa,
dalilin komawar Rafayet us da zama ba kowa bane face wan mahaifiyarsa mr donald, mugun son rafayet yake kamar hauka, duk weekends sai yazo nigeria don kawai ya gansa, kai daga baya ma sai ya kai sau 3 yake zuwa a week sam baya gajiya da zarya daga us zuwa 9ja, ran abba yayi matuƙar 6aci, har dai wata rana ya tambayi donald yace masa wai shi bai da ƴa’ƴa ne? da buɗen bakinsa sai cewa yayi, shiya riga da yayi plan ƴa’ƴa biyu yake so arayuwarsa, yanzu ya samu ya’yan kuma dukkansu mata ne, guda biyun ,
abba tamkar ya shaƙe shi haka yaji, wato tunda yasamu biyun duk mata, shiyasa ya dakata bayan yasan cewa yana son ɗa namiji,
Ba yadda abba ya iya haka ya zuba ma sarautar Allah ido ???? haka donald zaizo yaita kashe ma rafayet kuɗi shida omar, kamar hauka bai gajiya,
bayan wannan kuma abba yaji yana son ya sake samun ƙaruwa da Alexadra, yaje cikin lalama yayi mata magana, sai yaga tana dariya abun ya ɗaure masa kai ,
gyara murya tayi tare da cewa ” na amince zan sake haifa maka ƴa’ƴa har 3 amma bisa sharaɗin cewa zaka amince Alex ya koma wurin ɗan uwana Donald da zama gaba ɗaya, don na fi yarda da ya zauna can sbd zai fi samun tarbiya, zai wataya ya samu rayuwar ƴanci,
.(wai tarbiya a us ????)
Kai tsaye Abba yace ya amince dalili kuwa shine ya gaji daganin rafayet ba sallah ba salati ba karatun ƙur’ani, kwara ma yayi nesa dashi zaifi samun salama,
Amma shima yace yana da sharaɗi guda ɗaya, tace tana sauraronshi,
Abba yace “yaran da zata haifa mashi dole su bi addininsa wannan karan,’
Batayi masa gardama ba tace ta amince, a wannan lkcn ALexandra ta ajiye aikinta gaba ɗaya, sbd ta mallaki komai takeso a ynx, tayi mai isarta ynx lokacin hutun rayuwarta ne acewarta,
A nan ne kuma cikin ikon Allah ta samu ciki, a inda ta haifi twins tagwaye wato Ayaan da jahan, kyawawan gaske Allah ya zuba musu kyau, abba yayi farin ciki sosai, da aka tashi sa masu suna akexandra tace Za6i na wurinta, sbd a yarjejeniyarsu bai ce zaisa ma yara suna ba, don haka tasanwa Ayaan (John) Jahan kuma (James) kowa ya zuba mata ido ????
daga su kuma ta ƙara samun ciki inda ta haifi fawan shima tamkar sauran wurin kyau, kyakkyawan gaske Fari sol, a inda tasanya mishi suna (Michael) nan Ma kowa ya zuba mata ido ????
Bayan shine ta dakata da haihuwar gaba ɗaya, nan fa abba yasa rigimar cewa haihuwa uku tace zata yi masa, ita kuma tace ae inya lissafa da twins da fawan ƴa’ƴa uku kenan, ba dole sai ta yi ciki uku ba, Allah ya kawo mata cikin sauƙi,
Rigima ta 6alle a tsakaninsu daga ƙarshe da Abba yaga ba riba sai ya koma yana lallashinta akan ta taimaka masa ta haifa masa last born, uhmmmmm
A lokacin maryam tana ɗauke da cikin autanta na ƙarshe wanda a wurin haihuwarsa ne ta rasa rayuwarta, bakowa bane fa ce Talal,
Aunty azeema ta faɗi tana nuna sa, jikinsa yayi mugun sanyi, tuni hawaye sun zubo masa, haka sauran ma duk jikinsu ya mutu,
Ita kuwa alexandra dakyar abba ya samu ta haifa masa last born ɗinsa,
Wanda ya tafi da zuciyar kowa, da irin kyawunsa, shi na musamman ne, kowa rububinsa yake tun yana yaro yake fama da athma, ko ban faɗa ba kunsan ko wanene, mahaifiyarsa tasa mashi suna ROMEO, a inda mukuma muke kiransa Junaid,