ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

….,……….SEHRISH…………………….
A 6angaren sehrish kuwa, baiwar Allah jiki fa yayi rau, ido a kumbure ta farka daga bacci, duk ta tsorata da mafarkin da tayi akansu Husanna, tayi wani mummunan mafarki akansu, cikin mawuyacin hali, jikinta ya gama mutuwa, hawaye ne kawai ke rolling down on her cheeks, tana jin zuciyarta babu dɗi, tana kewar siblings ɗin nata, tana jin cewa bata kyauta ba, da tayi nesa da su amma ya zata yi? the hard way is the only way ????

Cikin sauri ta shiga toilet, wanka tayi sannan ta fito, jikinta na ta faman rawa, kayan nan da tafara zuwa aiki dasu gidan at her first day, su ta ɗauko, wato burgujejan wandon nan Falazu,
Wanda ƙafar mutun 5 sai ta shiga ciki ba tare da ya matse su ba, pink colour sai riga ta maza launin ruwan madara (milk) mai ma6allai dayawa ajikinsu da aljihuna, ta gyara gashin bakinta ya zauna raɗau, sannan ta nannaɗe sumar kanta kamar yadda ta saba,
ta aza hukar nan, yar tashi da kwakwa sannan ta aza kuma mayafinta launin wandon daga saman hular ta naɗe shi,
sai da tatabbatar da komai ya zauna raɗau,
Sannan ta fito gabanta na faɗuwa saboda taji alamun bakin nan fa sun iso, suna cikin gidan batasan ya zasu kalleta ba, ko’ina na jikint rawa yake yi saboda zazza6in da take ji,
tun daga inda take ta hango su a zungureran table din, binsu da kallo tayi, musamman aunty babba da Amani da tagansu ƴan larabawa, ga kuma su ishaq da abbas da abuhaisam da sauran duk batasan su ba, amma kamanninsu ya tabbatar mata da cewa yayyansu Kanal yusif ne,
“To fa wanene wannan kuma, baƙon saurayi ku ka yi ne:? .
Sai da sehrish ta firgita jin maganar aunty azeema, lokaci guda kowa ya ɗago yana kallonta ????
Cikin sauri azmi dake tsaye akansu suna saving ɗinsu dasu chef ummu tace “he’s our new house boy, tukur yana taimaka mun wurin aiki sosai,”
Jinjina kai azeema tayi tare da cewa “that’s gud”
ƙarasawa azmi tayi ta ruƙo hannun sehrish tare da janta izuwa kitchen suka tsaya, sannan ta kalle ta tace “meke damunki ƙanwata na shiga na Same ki jikinki zafi baki lafia ne,”
Hawaye ne suka soma zubo ma Sehrish cikin nuna tsananin damuwa tace “aunty azmi dan Allah ki taimake ni, ke kaɗai ce zaki iya taimako na a halin yanzu, ina cikin tashin hankali…’
“tell me whats happening wit u? Azmi ta tambaya,
“Aunty azmee ina ji araina cewa ƴan uwana suna cikin mawuyacin hali, inaso naje nagansu, dan Allah ki taimakamin naje katsina na duba su koda kwana ɗayane ina tsoran na rasa su bani da kowa sai su….. …..’
kuka ne yaci ƙarfinta ta gaza ƙarasa maganar, azmi ta janyota jikinta tare da hugginta ɗinta tightly a jikinta tace….
“I feel your pain sehrish,ina mai takaicin sanar dake cewa bazai yiyu ba hakan!
ɗagowa sehrish tayi daga jikinta tana kallonta ido jawur, cikin muryar kuka tace “meyasa aunty azmi”?
“Banso na sanar dake ba amma ynx dole ne kiji, sehrish kuɗin da na baki na aikin ƴan uwanki, bana salary ɗinki bane kawai, hada kuɗaɗen dana jima ina tarawa domin na yi amfani dasu, na haɗa miki duka sbd na tausayawa halin da ki ke ciki sosai, salary ɗinki bazasu isa ba dole saina cika miki, a yanzu haka da nake miki magana nikaina banda kosisi domin duka na tattara miki su….”
Shiru ta ɗanyi tana wani tunani idonta akan sehrish, ita kuwa jikinta yayi sanyi ba don komai ba sai don jin cewa Azmee hada kuɗinta ta haɗa mata don ta biya kuɗin aikinsu husna, sai taji ta ƙara ƙaunar azmi sosai, tana da matuƙar tausayi, ga kyan hali
“ki daina kuka sehrish, duk kan tsanani yana tare da sauƙi, ki daina sa damuwa aranki, insha Allah ba abunda zai sami ƴan uwanki, Allah yana tare dasu, maganar zuwanki wurinsu zanyi ƙoƙari akan hakan amma ba yanzu ba,’
cike da rashin kuzari sehrish tace “shikenan aunty azmee, nagode sosai bansan da wasu irin kalmomi zan gode miki ba, narasa mahaifiyata amma gashi Allah ya bani ke alokacin da nake cike da jimamin rashin wani nawa akusa dani mai sharemun hawaye na,
Murmushi azmee tayi kafin tace “samu wuri kizauna, me kike so na kawo miki ki ci? tun da safe baki ci komai ba,’ tayi mgnr cikin nuna damuwarta,
“Aunty azmee i cant eat anything now, zuciya ta tashi take yi bani da kwanciyar hankali,’
dafa shoulder ɗinta tayi tace “Calm down your mind reeshi na, just ave a seat, bari na haɗa miki abu mai daɗi mana ki ci, zaki ji daɗi,’
Ajiyar zuciya sehrish ta saki, wuri ta samu a saman dinner table ɗin dake a kitchen ɗin ta zauna, tana jiran azmi,
a tray ta shirya mata abun tattaunawa, ta ƙaraso da murmushi ta ajiye mata tana faɗin”Ina mai tabbatar maki cewa indai ki kasa wannan Cheese burger ɗin abakin ki sai kin manta da duk wata damuwa da ki ke ciki, musamman in ki ka haɗa da Cornflakes ɗin Zan haɗa miki ynx da madara haɗi na musamman ,’
Wani irin sanyi ne ya ratsa reeshi haƙi ka azmi ta musamman ce acikin na musamman, cikin sanyi murya ta furta “thank u aunty azmee kina ji dani sosai, only God can rewards you,’
“Don’t worry your self reeshi i just wanna see you always in happy mood, bana so naganki cikin yanayi na damuwa,’ ta faɗi hakan a yayin da take ƙoƙarin juyawa,
Murmushi sehrish tayi ta zuba wa tray ɗin ido, Cheese burger ce aciki tare da hot dog ga sandwhich, lumshe idanunta tayi aranta tana tunanin me ƴan uwanta suka ci su ????
ruwa azmi ta ɗebo a Dispenser mai zafi cikin tea cup, ta haɗa wa sehrish cornflakes yaji madara da sugar, tasan cewa sehrish akwai son zaƙi shiyasa ta zuƙa mata shi,
Ƙaraso wa tayi ta jiye mata shi a gefen tray ɗin, sannan tace “ko kina buƙatar wani abu ne?akwai sauran abubuwa da muka haɗa masu daɗin gaske,
yar dariya sehrish tayi ganin yadda azmi ke treating ɗinta sai kace ƴar masu gida,
“oh dariya na baki?dama dariyarki nakeson gani kuma gashi naki har dimple ɗin nan naki ya lotsa,’
azmi tayi maganar tana kallonta, cikin jin daɗi sehrish tace “daga ynx zan rinƙa yin dariya aunty azmee tunda kina so insha Allah,’
hannu azmee tasa tare da jan kumatunta tace “yawwa haka nake so my daughter, bari na shiga ciki, keep enjoying ur meal banda loma,’ .
ta faɗi hakan cikin zolaya kafin ta fice daga kitchen ɗin,
tana fita sehrish ta fashe da wani irin matsanancin kuka ba don komai ba sai don, tunawa da ƴan uwanta, kuka take bil haƙƙi da gaske hawaye na sintiri a face ɗinta, Allah sarki baiwar Allah, aduk lokacin da taga abu mai daɗi agabanta zata ci sai ta tuna da ƴan uwanta, wane hali suke ciki? shin sun samu abunda zasu ci kuwa, in ta tuna hakan sai taji ɗaci aranta, maganar oummansu ta tuna a inda take cewa

sehrish ke ce mai wayau acikin ku, dan Allah duk runtsi duk wuya kada ku rabu ko bayan raina, ku haɗa kanku ina son ku sosai ƴa’ƴana rabin raina ????

Hafsat Bature

page 51 to 52

Abban Sojoji

????romantic love story btwn Sehrish & Surgeon General Rafayet????

_Heart touching story abt a Triplet_????

mamaki ya ke ganin taƙi ɗauke eyes ɗinta akansa, kuma bata da niyar daina kallonsa, hannunta har rawa yake yi wurin ajiye spoon ɗin da ta ɗauko,

Lumshe idanunsa yayi a hankali yana ƙare mata kallo acikin zuciyarsa yana cewa “Ya Allah ka mallakamin wannan baiwar ta ka,’

A yayin da sehrish ke cewa”
tsarki ya tabbata ga ubangijin daya halicci wannan kyakkyawar surar Junaid duniya ne????

shigowar azmee ne ya dawo dasu daga wannan tunanin na ƙurawa juna ido kowa ya waske

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74Next page

Leave a Reply

Back to top button