ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

tashi zaune junaid yyi saman bedmattress ɗin yace “zan faɗa maka daddy but firstly tell me ka yi mun tsarabar da nace ?

Abba yace “ya za’ae na manta babyna, ba traditional dress ka ce kana so ba ,na ƴan china? Ae na siyomaka abubuwa da dama ma, suna nan,’

Wani irin murmushin jin daɗi junaid ya saki tare da cewa “abba kayima kanka ƙiyamul laili da ace baka siyamun ba ko, hmmm da kaga rigima,

dariya abban yayi yana kallonsa har time ɗin yana daga kwance, junaid yaci gaba da cewa “amma abba baka haɗu da wata zazzafar ƴar budurwa haka ba acen? Nasan ka da farin jini ,

Cikin zolaya junaid yayi maganar, ɗan zaro ido abban nasu yayi tare da cewa “tab ! ae na gama wlh, Wa ? ni hussein la la la laa, waɗannan fararen basu da guarantee, yadda momynku ta gasa mun aya a hannu, wannan gasuwar ta ishe ni haka, na ɗauki darasi,

Ae ko zan ƙara aure iya nan ne, bazan wuce hausa fulani ba, mata masu kunya, ga riƙo da al’ada ga girmama muji Allah sarki maryam ????

dariyar junaid yayi tare da cewa “su Abba anji jiki, dama ance jiki magayi ne, ynx kaji jiki ko? sai yanzu ka gane cewa matan mu suna girmama muji ko amma ka tashi ka auro mana ….’

bai bari ya idasa maganar ba ya yunkura ya janyosa jikinsa yana yi masa dundu a baya, yana cewa “junaid wai tsaran wasanka ka maida ni ko ? na ta6a cire kaya agabanka ne ? Shiyasa ka raini ko,?

dariya junaid ke ta faman 6a66akawa, shima abban dariyar ya yake yi, haka suke in suka haɗu suyi ta shiririta kai kace ba uba da ɗa bane, ????

………….Sehrish…………………

ta koma cikin ɗaki kasancewar babu wani aiki da zatayi, su aunty azmee da chef ummu da momina duk suke gyara komai,

zarya take ta faman yi a room ɗin nata, zuciyarta husanna da jahad kawai take Calling, aranta tana cewa “meyasa duk cikin abunda bature ya ƙirƙira baiyo wings ba ? fika fiki, a shiriritar ta , da ace tana da fiffike da tuni tayi sama ba tare da sanin kowa ba ta ware sai wurinsu husanna ????

ita ce har wurin sallar magriba tana tunanin abu ɗaya,

Acan ciki kuwa abba , yasamu ya fito shida baby junaid, bayan sun gudanar da sallah kowa ya hallara a main palour ɗin mazan kawai suka zauna, suna kara gaisawa da abban su,????????HAFSAT BATURE????????

~BossLady~

Novel writer of

????????????ABBAN SOJOJI????????????

page 53-54 ????

general ishaq na zaune a 3 seater shi da Captain najeeb da talal,

Abuhaisam na tare da Abbas da kanal yusif atare suma a mazauni ɗaya,

Fawan da khaleed da jabeer da irfan suma duk suna a tare,

Yayin da abba ke zaune tare da junaid a side ɗinsa sai twins,

gyran murya abban nasu yayi sannan yace ” ina kara godiya ga Allah dayasa na dawo na same ku cikin ƙoshin lafiya, naji daɗin hakan sosai, naga wasu sunyi ƙiba, wasu sunyi haske wasu kuma fara ajiye tumbi ????

gaba daya suka fashe dariya, dama indai zolaya ce abban nasu ya saba,

general ishaq yace “wannan dai dani ake, maganar masu ajiye tumbi, kuma na gode,

murmushi abba yayi tare da cewa ” Sorry first born ni na isa na sa dakai, kai fa na fara gani kafin sauran,’

Abbas yace “ƙwarai mu aka fara gani kafin sauran, ƴan shisshigi da kutsu, ‘ yayi maganar yana kallon junaid wanda ya kwantar dakansa ajikin abbansu,

“Ya fi kowa iyayi abba, kamar shi kaɗaine auta nima fa autan ne,’ acewar talal,

fawan yace ” ae wani aikin ma sai in BABBAN YAYA ya dawo nan zaku ga shagwa6a da narkewa da yake mutuminsa ne,

Abba yace “oh wai harynx kuna yiwa junaid irin wannan taron dangin, narasa me ya tsole maku, to bari kuji nan gani nan bari dukiyar uban wani ehe, ya faɗi yana kara janyosa ajikinsa,

dariya su kayi abuhaisam yace “Abba kana sane kuwa da zuwan Lion da tiger?

ɗan zaro ido abba yayi tare da cewa “kai haba ? Badai wannan uban ƴan ji dakan ba, ɗan wurin Alexandra kke cewa ba? Ka ce na tattara kayana na gudu ,”

Yayi mgnr ne cikin zolaya sai kace ba akan ɗansa ake magana ba,

“Abba kana kiran sunan momynmu kai tsaye ko sakayawa baka yi, ina laifin kace ɗan wurin fatima a musulunce dai,”

Ayaan ne yayi maganar yana hura hanci,

dakuwa Abbas yayi masa tare da maimaita sunan ance “alexandara ba sunan ta bane ? ita da kanta tace ko ƴa’ƴanta bataso su kira ta da mommy tafison sunanta Alexandra ko ƙarya nayi?

Kanal yusif yace “aɗan sakaya dai yayanmu, saboda ƙannenmu,”

Abba yace “ynx don rashin kunya, abbas agaban idona kake faɗin sunan masoyiyata kai tsaye? gaban kuma shalelena ?
Junaid ya ƙara rakwabe fuska, dariya su kayi cikin nishaɗi suke firar kowa na ɗan tsoma bakinsa,

Azmi ce ta kawo musu abunsha kowa ya kar6a, dama ka’ida ne duk bayan ƴan minti na sai ansha tea ko coffee ????

tura kopan ɗakin tayi ta shiga tana faɗin “Amani baki ga text ɗina bane nace ki same ni a ɗaki”?

aunty babba ce ta shigo ɗakin da amani ta sauka tana mata magana,

Amani dake kwance saman bed hannunta rike da waya tana daddanawa, jin muryar auntyn tata yasa ta tashi zaune, bakar jallabiya ce a jikinta, kanta ba ɗan kwali sai doguwar sumar kanta data zuba a shoulder ɗinta,

“Sorry aunty na ban ankara ba, na dai ji shigowar message ban duba ba,’

Ƙarasa wa tayi kusa da ita ta zauna a side bed din suna facing juna tace “hmmm amani kenan, wato tunda nayi miki hanyar arziƙi, ki kayi kyau kika ƙara haske, kwanciyar hankali ya samu ki ka daina tako wa kizo inda nake ko? Ko phone calls babu ? A whatsapp ma ina ganin ki online ba magana, wato naira ta zauna ko?

Yar dariya amani tayi “haba aunty na, pls stop saying that, ke fa ce silar shigata wannan daular taya zan share ki ? Ae kullum ƙara gode miki nake, sbd ynx ko a mate ɗin mu ba wadda takama kafa ta wurin arziƙi, ynx fa takai ga ko taro za’a yi na class mate ɗinmu indai ban halacci taron ba to fasa shi akeyi, kowa burinsa na zo ba don komai ba sai don aga wanka leshin da zan ɗauka da zinaran da zan sanya,’

jinjina kai Aunty babba tayi tana ƴar dariya “haka nake son ji my sister, nafi so naga kuna wuta ana binku da fetur, ku zama on top kai kuzama ma topic ɗin gaba ɗaya, inji kawai ana zancen ku a ko’ina,

ta ƙarashe maganar da cewa “ina fata dai baki raga masa ko? Kina tatsarsa sosai kina matso sa sbd kinsan fa abunda ya kawo mu family ɗin nan dukiya muka zo mallaka domin mu raya namu family ɗin,’

Zuru Amani ta ɗanyi tana kallon auntyn tata, cikin sanyin murya tace “Mallakar dukiya kuma aunty? banda kuɗaɗen da muke samu a hannun mazajen mu har wata dukiya zamu mallaka ?

dariya aunty babba tayi tare da dafa kafaɗar Amani tace “ke fa matsala ta dake wani lokacin baki da lissafi, bakya gane wa, ae ynx kowa ta kansa ya ke yi, kuɗi kawai dole mu nemi kuɗi kamar hauka, saboda ynx mun shigo wani zamani da in baka dasu ba’ayi dakai, ka zama tamkar non living thing, masu kudi sune living thing, masu rai kenan,’

Ta ƙare mgnr tana kallon Amani wadda ta ɗan dabarbarce sbd auntyn tata ta fara bata tsoro,

Aunty babba taci gaba da cewa “Oh wai ke da soyayya kika zo kisha wurin ABBAS? Ae ni ban haɗa auranki da abbas ba don soyayya kawai, face don ki rinƙa tatsar mana shi, sannan naga haryanzu babu ciki a jikin ki, uban me kika tsaya jira !?

Hankalin Amani fa ya tashi ganin yadda lokaci guda auntynta ta, ta bayyana mata mummunan ƙudirinta akan family ɗin Abban Sojoji,

Ajiyar zuciya tasaki kafin tace “aunty ra’ayinmu ne yazo ɗaya, shima bayason haihuwa da wuri munyi planing sai nan da 5yrs, ynx soyayya kawai muke sha……. “

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74Next page

Leave a Reply

Back to top button