ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

Katse ta auntyn tayi da cewa “ko ba soyayya ba? Nabi soyayyar da gudu, ashe head fish gare ki sam bakya gane wa, to bari kiji in faɗa miki, ki aje wannan planing ɗin, ki ɗauki ciki kawai ! mun samu mai cin gado, nima nan da kike gani na, ba don lalurar da ta same ni ba, da tuni na jima da sauke wani,

Jinjina kai Amani tayi tana kallonta cikin mamaki,

ƙasa ƙasa da murya tayi kafin tace “ke nifa wani target gare ni akan wasu cikin family ɗin nan, kuma ina mai tabbatar miki da cewa it will work,’

Amani tace “me ke nan aunty”?

wani shu’umin Murmushi aunty babba ta saki kafin tace “BABBAN YAYAN su ! da MARSHAL OMER, “

zaro ido amani tayi tare da dafe kirji tace ” aunty me kike nufi dan Allah, fahimtar dani, kaina ya ɗaure,’

ƴar dariya Aunty babba tayi sannan tace “So nake na sama ma, ƙannan mu gurbi acikin gidan nan ! Kuma waɗannan shahararrun su nake hari ! ta ƙarfi ta tsiya ????

cikin tsananin tashin hankali Amani tace ” Aunty anya ba giya kika sha ba ? kinsan suwa ki ke magana akai kuwa ? Babban yaya fa da marshal omer ?

Cikin jaddadawa Aunty babba tace “ƙwarai kuwa ! Su nake nufi kuma a shirye nake da nayi koma mai zanyi don na asirce su naja ra’ayinsu akan Hayaam da Abrah,”

Zuba wa juna ido su kayi suna kallon kallon, har ynx Amani ji take tamkar mafarki take yi ba gske ba, ƙarfin hali irin na auntynsu ya bata mamaki tarasa wa zata ce sai Rafayet da Omar ? Anya kuwa aunty bata sha wani abu ba?

Katse mata tunanin ta tayi da cewa “na lura har ynx bakisan me nake hari ba, bari nayi miki dalla dalla,

Rafayet da ki ke gani duk family ɗin Abban sojoji ba wanda yakama ƙafarsa wurin tarin dukiya, gashi matashi ga kyau, a binciken da nayi Rafayet ya mallaki billions of dollars nasa na kansa, bayan tarin gidajen dake gare sa a us da sauran countries ɗin da yake yawan zuwa, sannan kuma ya mallaki privet jet nasa nakansa, ga tsadaddun motoci dake gare sa ƙirar bugatti, ƙirar mercedes benz, ƙirar pagani da ferrari da sauransu, ke duk wani abu da kike sani mai tsada rafayet ya mallake sa, shi kanshi tsadar gare sa, ke nifa farko dana fara ganin shi wlh, sai da nayi danasanin auren ishaq, hmmm ke fa bakisan shi ba ko, ae zai zo ne,

Amani ta gama rikice wa da jin irin dukiyar Babban yaya, cike da mamaki tace “wai dagaske kike auntyna ?

Murmushi Aunty babba tayi “ƙwarai ma kuwa, Rafayet he’s among the most richest men in the world, youngest billionaire ne, Kuma yana ɗaya daga cikin most handsome men saboda kyansa da structure ɗin jikinsa,

Jin jina kai kawai Amani take yi ta jin jinawa lamarin, 

Murmushi aunty babba tayi kafin taci gaba da cewa “Bayan Babban yaya kuwa a wurin arziƙi cikin family ɗin nan sai Hajiya azeema, wannan matar da ki ke ganinta ƙuruwa ce wurin arziki,business ɗin golds take yi da diamonds, ina wannan agogon ta hannunta ? Kin ganta ae ko ?
ta faɗi cikin son fahimtar da Amani,
“Eh aunty na ganta mai kyau kamar na sace wlh,’
“Hmmmm to wannan da ki ke gani ƙirar graff diamonds ce, $40 millions a us dollars, a naira kuwa sun kai 24 billions,’
dafe ƙirji Amani tayi gaba ɗaya tabi ta susuce, jin abun take tamkar a mafarki, sakin baki kawai tayi galala jin wannan daular,
Aunty babba taci gaba da cewa “daga ita kuwa sai marshal Omer wurin arziƙi, shima billionare ne duk wani abu da Babban yayansu ya mallaka shima ya mallaka, don dai ya wuce shi da wasu abubuwan, sune kawai nayi bincike akansu, sauran kuwa kowa attajirin kansa ne, ya ki ke gani idan Hayaam ta samu shiga Wurin Rafayet ita kuma Abrah muka kutsa ta wurin Omar ?
Washe baki Amani tayi tare da cewa “ae shikenan kawai ba sauran magana, mun gama kwaɗaice wa,”
dariya su kayi gaba ɗayansu a dai dai lokacin Azmee tayi knocking kopan ɗakin, cikin sauri suka gyara natsuwarsu,

Amani tace “Shigo ciki” tura kopan azmee tayi ta shigo da fara’a a fuskanta tace “dama an kammala dinner ne, naji shiru baku fito ba shine nace bari nazo na sanar daku,”

Me zaku ce game da Aunty babba da Amani dake shirin mallake dukiyar da ba ubansu ya tara ba ?????????????????ABBAN SOJOJI????????????

written story by HAFSAT BATURE

~BossLady~

Page 55 to 56

Yinin ranar jin jikinta take yi cikin wani irin yanayi mara misaltuwa, shi dai gayanan wata ni’ima ni’ima , ga wata irin kasala da ta mamaye ta, sai wani lalaci da take ji, saukin ma aunty Azmee ta sanar da ita cewa bata da aiki ta zauna ta huta kawai, yau ranar hutun ta ce , yini tayi tana safa da marwa frm wall to wall, zullumi iri iri agame da su HUSANNA da JAHAD, ga kuma wani irin bugu da zuciyarta take yi mata, ita dai tunkan ta sa wannan Babban yayan nasu a ido take jin feelings agame dashi (kina ruwa ????)

Har cikin bedroom dinta azmee ta shigo mata da dinner dinta, ba karamin dadi taji ba, kaunar azmi na kara shiga cikin zuciyarta, sbd tana kula da ita kamar yar cikinta, ta damu da ita sosai, Allah sarki,

Zuba wa meatballs din dake shake cikin plate din dake ajiye saman bedside drawer dinta tayi, ga fresh milk acikin glash cup, shiru tayi tana kallonsu, jikinta a mace yake, ga kamshinsa ya cika ta, amma a kullum ji take kamar batayi wa yan uwanta adalci ba, tana cin irin wannan dadin yayin da suke ciki mawuyacin hali,
Zugudum tayi a yayin da take zaune a saman gadon daga baki baki, ta lankwashe kafanta a sama,
Azmi ce ta sake turo kopan ta shigo hannunta dauke da fresh fruit acikin dan plate,
“Ya akai har yanzu baki fara ci ba? me kike jira ?
ajiyar zuciya sehrish tasaki tare da cewa “Aunty azmee zuciyata bata mun dadi in na tuna da yan uwana, sai naji bana son cin komai,
Cikin nuna damuwa azmi takarasa ta ajiye mata plate din a hannunta, sannan ta zauna gefenta cikin natsuwa tace ” kin yi imani da Allah!?
daga kai sehrish tayi tare da cewa”Eh”

“Ina so aduk lokacin da zakiyi addu’a ki kasance mai cike da imani, kiyi imanin cewa addu’ar nan da kika yi Allah ya karbeta, don’t doubt about it sbd karancin imanin kesa muna rasa wani abun, amma muddun ki kayi masu addu’a kina me cike da imanin cewa Allah ya karbeta, ba tare da kinsawa ranki kokwanton cewa Anya Allah ya karbi addu’ a ta kuwa? Ko kuma kinji shiru har ynx ba ki ga sakamako ba, duk ba’a son wannan, kawai kisa ma ranki cewa duk in kikayi addu’ a Allah ya amsa kuma tom insha Allah zaki ga sakamako mai kyau, kuma zakiji natsuwa acikin zuciyarki,”
Jinjina kai sehrsh tayi tare da cewa “ngde aunty azmee kuma insha Allah zanyi kamar yadda ki kace”
Murmushi azmee tayi tare da cewa “yawwa rishi na, ko kefe yanzu dai ayimun wannan murmushin kashe zuciyar nagani” ta fadi cikin zolaya tana kallonta,
Sunnar da kai sehrish tayi tana murmushi, itama azmeen murmushi take yi, hannu azmee tasa ta dauki yankakkiyar abarbar dake cikin plate din dake ajiye a saman hannun sehrish,
A baki takai mata tare da cewa “Ha bakin nasa miki’
Bude baki sehrish tayi tana yar dariya, zura mata abarbar tayi, sehrish ta taune, nan take zakin abarbar ya cika mata baki, takama lasar labba,
Azmee tace “yawwa ko ke fa ynx naji magana, bari na baki meatballs din abaki,”
Cikin sauri sehrish tace “a’a aunty azmee zanci ynx, kunsha aiki kun gaji, gashi ban tayaku ba,’
“Kada ki damu sehrish, ae ni nace ki zauna tun da gasu Chef ummu aiki na tafiya yadda ya dace, ina fata dai bakiyi tunanin BABBAN YAYA ba yau ?”
Ta karasa maganar tana kallonta, cikin zolaya,
Sunnar dakai tayi tana murmushi jin an ambaci sunan da ke mata kaikayi a cikin zuciyarta,
“Bani da amsa kenan, tam ni zan tafi ynx kada ki manta, a daren yau kiyi sallolin nafila, kiyi addu’o’i wa yan uwanku da kuma sauran al’ummar musulmai,”
“Insha Allah aunty Azmee ngde sosai”
Tashi Azmee tayi ta fice ????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74Next page

Leave a Reply

Back to top button