ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

BABBAN YAYA wanda kowa ke shakkarsa ko sunansa aka ambata sai an girgiza, baya wasa da aikinsa, kaifi ɗaya ne,babu mai iya tankwara shi, sam mace bata gabansa a tsarin rayuwarsa baya da burin yin aure gaba ɗaya, cos bashi da interest akansu, mata bibiyarsa suke kamar hauka, ƴa’ƴan manya yayan shuwagabanni ya’yan sarakuna, amma ko kallo basu ishe shi ba, ????
yadda yake kallon namiji haka yaje kallon mace ba banbanci, sam bai da shauƙin soyayya a tare dashi,
Tun saura 30 mins jet dinsu yayi landing , manyan motoci suka isa airport din jibga jibga na sojoji, baka jin komai sai tashin jiniya kamar ana yaki, a cikin motocin akwai na gayu tsadaddun gaske kirar mercedes benz da aka zo daukarsu da ita,
Time din da jirgin yayi landing, cikin isa kowannansu ya fito, yana saukowa daga matattakalar benen, a jere suka sauko gaba daya ido na akan Babban yaya tare da marshal omer, cika ido suke kamar kamar me, a bubbude suke tafiya irin tafiyar nigogin nan, wadanda suka ji karfi, shi marshal omar sam bai kai rafayet tsayi ba amma fa akwai kira ta mazajan gaske,
Masha Allah,
????????????????????????????
Su wa ke farin ciki da zuwan BABBAN YAYA????
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
page 57 to 58

Ci gaban page 57 cikin nan

Not edited like always ????

…………..SEHRISH…………………………………..
Bacci take ta faman sha, hankalinta kwance batasan meke wakana ba, time din da azmi ta shigo ta same ta, tana ta sharar bacci bata yi yunkurin tashe ta ba, saboda tasan halin da yarinyar take ci, akwai damuwa atare da ita sosai, tana bukatar hutu brain dinta ma ta huta ko ta samu natsuwa, hakan yasa ta juya ta koma kitchen domin gudanar da aiki ita kadai, sbd dama an sallami su chef ummu ynx aiki ya rage daga ita sai sehrish,
Azmi bata gajiya da aiki, maca ce mara kyashi, in dai tana girki tana tazbihi a cikin zuciyarta shaf shaf take kammala komai, Ita a tsarinta ma bataso Sehrish na aiki, tafi so ta zama kamar yar masu gida saboda son da take yi ma yarinyar, tana jinta kamar yar cikinta, ❤
bayan ta kammala, da kanta tabi ta jera a dining, a hankali su ka fara fito wa, wadanda yunwa ta koro, lokaci guda duk suka hallara kowa ya zauna,
Abba na kusa da junaid dama suna atare, kanal yusif, da irfan da jabeer da khaleed duk suna a right hand yayin da suke facing din, Aunty azeema, Amani da aunty babba, sai bg Abuhaisam na kusa da Fawan, kowa sai zuba wa cikinsa yake a natse, mutun biyu ne ke basu hallara ba a dining din ba,
sai faman wurga ido junaid yake yaga ko zai ga fitowar sehrish amma babu alamarta, hakan yasa shi jin wani yanayi tsoransa kar ace bata da lpy, dago wa yayi ya saci kallon aunty Azmee dake saving dinsu daga tsaya, a hankali yake motsa lips dinsa yana tambayarta ina Sehrish ba tare da sauti ya fita ba,
Murmushi azmee ta saki tana dan kallonsa, da hannu tayi masa alamar cewa bacci take yi, lumshe idonsa yayi alamar jin dadi aransa, maida idonsa yayi akan Chips din dake gabansa cikin plate,
gyaran murya Aunty azeema tayi tare da cewa “uhm ana ta kulu wash rabu, su yusif ba baka sai kunne,”
murmushi kowannansu yayi, dan dagowa yusif yayi ya kalle ta cikin sanyayyiyar muryarsa yace “Aunty azmee bakyau ana da’amin ana magana,” .
murmushi aunty azeema tayi tare da cewa”dadi na da yusif akwai hankali ga natsuwa komai nasa na bin ka’idar addini ne masha Allah,”
Abba yace “ae ina ji duk cikinsu shine ya biyo halin ummansu komai nata, hatta kyan fuskarsa in ka cire Marshal omar,”
“gsky abba ka tara kyawawan samari masu ilmin addini dana zamani ya kamata ace kowannan su iyanzu ya fidda matar aure tun da aun mallaki komai,”
Aunty babba ce tayi mgnr, wani irin kallo yusif yabi ta dashi sbd baison yaji ana masa maganar aure bama shi kadai ba hada bg Abuhaisam,
“Aunty babba matan ne basu da tabbas, mutun na bukatar tsawon lkc kafin ya fidda wadda ta dace da rayuwarsa, aure baya bukatar gaggawa kuma shi lokaci ne”
Bg abuhaisam ne ya bata amsa, jinjina kai tayi, yayin da yusif yace “you’re right yaya haisam, we’re waitin for the time, in yayi zamu yi ne,”
dan murmushi aunty babba tayi ita burinta tafara tunzura abba akan Babban yaya da marshal omar saboda abun yazo mata da sauki,
“mgnar ku gasky ne, amma abun da nake so ku sani, shi lokaci baya jira ! lokaci tafiya yake yi, this is the right time daya dace ace kunyi deciding akan sama ma kanku abokiyar rayuwa, its very hard to find a righteous partner in this situation of life, rufe ido kawai mutun zai yi ya canka,”
tayi mgnr tana kallon yusif dake facing dinta, kafin yusif ya bata amsa abba ya katse masa hanzarinsa da cewa “kwara ki fada musu, ynz ni ba abun kwatance bane a wurinku ? ina da 20yrs akayimun aure dayake na mallaki komai na rayuwa, in Allah ya baka dama ka damata alokacin daya dace, gashi ynz Allah ya albarkace ni da ya’ya da karfi na ban tsufa tukuf ba, naji dadin hakan sosai, ada ina jin haushin anyimun aure wuri, amma at the end naga amfanin abun,’
Jinjina kai su kayi kanal yusif yace “pls muna barar addu’arku aunty azeema aunty babba and aunty Amani atayamu da addu’a Allah ya bamu mata salihan mata na gari masu koyi da matan Annabi muhammad (S.A.W) Ba shaidanin zamani ba,”
Gaba dayansu suka amsa da (S.A.W.) kafin suka bi da ameen, suna dariya jin maganarsa ta karshe da yace shaidanin zamani,”
Junaid ya kalli abbansu tare da yin kasa kasa da murya yace “Nima abba atayani da addu’a mace tagari,”
Dariya su kayi gaba dayansu don sun ji shi, fawan yace kama cire batun aure a ranka, domin kai da yin aure sai nan da 20yrs lkcn ka kara hankali,”
Harara junaid ya watsa masa tare da cewa “Yanzun ma da hankali na, abunda dan shekara 30 zaiyi in an masa aure nima zan iya fiye da haka …….”
Bai ida maganar ba bg abuhaisam yayi masa dakuwa da hannu tare da cewa “gidanku ! Ja’iri ina maka kallon ustaz ashe kaima dan duniya ne,”
Abbansu ko murmushi kawai yake yi sbd yasan cewa sarai junaid yayi maganar ne batare da yasan me zasu fahimta ba su,
Aunty azeema tace “yaro ya girma abun sai addu’a’
Dariya su kayi gaba dayansu ,
Ba zato ba tsammani suna cikin wannan nishadin, kwatsam su kaji dirar motoci a tsiyace, ba kakkautawa da gudun gaske suke shigowa cikin gidan, lokaci guda jiniya ta karade ko’ina, hankalinsu ba karamin tashi yyi ba Abun kamar a filin Yaji,
Antayo wa suke ciki ajere suke kurdadowa,

Sehrish sai faman toshe kunnata take da pillow saboda jin tamkar za’a fasa mata kanta, ga nauyin bacci tana ji sam ta kasa kakkauran motsi ta tashi, jiniyar motocin dake shigowa har tsakiyar kwalwarta, sai faman matse ido take ta ciccije lebe,
Kamar daga sama taji sautin harbin bindiga mai karfin gaske kamar fashewar bomb haka taji, a wani irin firgice ta wuntsilo daga saman gadon izuwa kasa gefensa, daga ita har pillow kowa ya ware gefen, bargon ne kawai kankame a hannunta, gaba daya dukkan ilahirin jikinta rawa yake yi, sai faman zazzare ido take yi, tuni zufa ta soma wanke mata fuska, da karfi take breathing in har mutun sai natsuwa tsaf zaiji bugun zuciyarta,
Wani harbin da aka sake yi nan take ta fashe da kuka, sbd dama a tsorace take da mafarkin da tayi,
Acan ciki kuwa, lokacin da jiniyar motocin nan ta karade ko’ina nan take fawan ya saki cokalin dake hannunsa, idonsa akan junaid sbd yasan cewa sarai junaid yasan da zuwan bazatan da Babban yayan nasu yayi bai sanar dashi ba, su kam sauran musamman aunty azeema da Abban nasu su bg abuhaisam da su kanal yusif farin ciki a wurinsu ba’a magana, juyawa aunty babba tayi ta kalli Amani wadda itama kallonta take wani shu’umin murmushi suka sakarwa junansu jin wadanda suke hari sun karaso,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74Next page

Leave a Reply

Back to top button