ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

Annoucement ba posting a weekends sbd nasamu damar typing friday ma sai ina hutu amma ko za’a samu ba da wuri ba,”????????????ABBAN SOJOJI????????????*

ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭ ﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ
ﺭﺍﻓﻴﺖ

Story by HAFSAT BATURE ????♥️

~BossLady~

page 61 to 62

“Yanzu buri na shine, mu fara haɗa kudin zuwa wurin bokan nan, Baba Iblis domin gudanar da target ɗinmu,’ aunty babba ce ta katse ta da maganar,” .
Jiki a sanyaye Amani tace “yanzu me ake buƙata? Aunty babba tace “kuɗi nake so daga wurinki, nima kuma zan haɗa nawa don ziyartar wurinsa,
Murmushin takaici Amani tayi tare da cewa “Ita hayaam ɗin baza ta bada komai bane?
Ƴar dariya aunty babba tayi tare da cewa “amma dai kinsan hayaam da shegen maƙon tsiya, bazata bada ko sisi ba, kuɗin ta a gantali suke karewa, mu dai taimaka mata mu yayyenta, mu yi mata inyaso in tasamu shiga wurinsa ni nasa zata ru6anya mana abunda muka kashe,’
Baki a sake Amani take kallonta, oh ashe tasan ma cewa Hayaam ɗin nada kuɗi, ita bazata bada ba sai dai ita gantalalliya, waye zai amfana acikinsu,
“Yanzu nawa kke so kafin zuwa can ɗin”? Amani ta tambaya tana kallonta, cikin salon wayau Aunty babba tace “miliyan ɗaya da rabi nake so a wurinki da farko kafin abun ya nutsa,”
Wani irin kallo Amani take binta dashi, cikin rashin fahimta tace “aunty million ɗaya da rabi fa? daga wuri na kuma , gold ɗina kke so na siyar ne?
girgiza kai Aunty babba tayi tare da cewa “to menene aciki ? Abbas ɗinnnan fa ya mutu akan ki, daga kin kashe masa murya buƙata zata biya,”
Ajiyar zuciya Amani tasaki kafi tace “I will think about it,” murmushi aunty babba tasaki acikin zuciyarta tace “ki gama yi mun aikina, ke ma nakaiki ƙasa, ƴar kishiyar da ta azabtar da mahaifiyata, tasanya mahaifina tsanata, bazata ta6a zaba ƴar uwa awurina ba face maƙiyi ya !!!”
A fili kuma tace “yawwa my sister shiyasa nake sonki, duk cikin ƙanne na cos you’re so special,” murmushi Amani tasaki tana kallonta,
Wannan bokan da suke magana akansa Baba iblis, wani hatsabibin boka ne fasiƙin gaske, wanda ya sharaha, Asiri kala biyu yake yi, akwai Namijin asiri wanda ƙa’ida inzaiyi sa sai ya kwanta da namiji na tsawon kwana uku yana biyan buƙata, na biyu kuma Macen asiri, idan zaiyi wannan asirin dole sai an kawo masa matar Aure wadda bata ta6a haihuwa ba ya biya buƙatarsa na 3 days, shu’umi ne nagaske, muddin yayi asiri to fa sai yaci mutun, ko yayanene, in ba wani ikon na ubangiji ba,
Kuma a haka zakaga mata na rubibun zuwa wurinsa saboda neman abin duniya, wa’iyazubillah ????wanda kowa zai mutu yabarshi !!!!
Around two ya farka, fito wa yayi yana saukowa down, duk sun hallara a palor ɗin suna fira, jin takon tafiyarsa yasa su ɗagowa suna kallonsa, bai bi takansu ba direct bedroom ɗin Abbansu ya shiga, saboda baigansa a cikinsu ba,
Abun da ya faru Abban nacen ɗakinsa yana zarya, shi dai burinsa Babban yaya ya kawo kansa har bedroom ɗinsa ya miƙa masa gaisuwa, if not he will not be calm,
safa da marwa yake ta faman yi, jin tura kopa yasa shi dakatawa ya juyo yana kallonsa, tsaye yake jikinsa sanye da jallabiya fara ƙafarsa cikin slippers, ya riƙe waist ɗinsa yana kallon Abban nasu,
Ƙinyi masa magana yayi yana jira yaga iya gudun ruwansa, shi kam kewar abban nasa yayi sosai, yama rasa wani irin tarba zaiyi masa,
Zuba mishi ido abba yayi ganin yana naɗe hannun jallabiyar dake jikinsa kamar wanda ke shirin yaƙi, yana ganin hakan ya gane mai zaiyi masa,
Cikin sauri yace “wlh kada kace zaka ɗauke ni Rafayet, kar ka kuskura Allah, ka matso saina nannaushe ka….” bai ƙarasa maganar ba, rafayet ɗin ya ƙarasa caraf ya ɗaga abban nasu a hannunsa kamar wani yaro,
dariya abban ya dinga yi yana faɗin “Ka sauke ni rafayet, kada ka balla ni fa, ynx in wani ya shigo ya ganni haka fa, ‘
“bazan bari hakan ta faru ba abbana” cikin wata irin sanyayyiyar murya mai daɗin gaske yayi maganar,
Ko nauyi baiji sai da ya tabbatar da cewa yaci ka abban nasu da farin ciki sannan ya sauke shi, sai faman ajiyar zuciya abban ke saki yana kallonsa, ƴar harara abban ya watsa masa tare da cewa “duk ranar daka ƙara daukata haka, nima saina rama, kadaina ganinka da tsayi kamar fal waya , hakan bazai mun wuya ba,
Matsawa babban yaya yayi gaf da abbansu yace”bismillah” yadda yayi masa tamkar zai rufe sa da duka, hannu abban yasa ya janyo chair ɗin dake gaban dressing mirrior , ya daddage ya hau samanta ya miƙe tsaye, yadda tsayinsa zai fi na Rafayet ɗin sosai, sbd yafi so in zaiyi masa magana yadinga ganin tsakiyar kansa, ????
“Hmmm kayi kewata kuwa? Ni bana gane wa kullum fuska atamke ba fara’a,’ abbansu ne yayi maganar yana kallonsa daga saman chair ɗin dayake tsaye,
“Abba i really missed you just feels like to swallow you,’ yayi maganar yana kallonsa,
Shi kam abban sai murna yake yi, ba don komai ba sai don ganinsa, “amma dai zaka jima anan ko ? Bana so kana jimawa bakazo naganka ba,”
Lumshe idonsa yyi tare da buɗesu a hankali yace”duk yadda kke so haka za’ayi abba,” murmushi abban yasaki, abun da ke ɗaure masa kai har ynx babu fara’a a fuskarsa ba alamar murmushi ko dariya, amma sanin cewa haka mood ɗinsa yake ne yasa baiji komai ba,
“Yakamata mu fita, ku gaisa da aunty azeema da sauran ƴan uwa, kuma nasan kana buƙatar abunda zaka sawa cikin ka ko? Ya tambaya yana kallonsa,
“No am not starve dad, and i will stay here in your bedroom, duk mai son gani na yazo nan ya same ni,”
yana gama faɗan hakan ya wuce saman bed ɗin abban nasu ya kwanta a hakimce,
Saukowa abban yayi yana murmushi aransa yace “wannan shine ainihin jinin Alexendra (alekzendira)”
Fita abban nasu yayi fuska asake duk sun hallara a main palour ɗin ana ta fira,
“Abba ina Babban yayan yake, nagansa ya wuce part ɗinka, nayi tunanin zan ganku atare ne,” aunty azeema ce tayi masa wannan maganar,
“You knew him well, yace duk mai son ganinsa ya same shi acan room ɗina,” jinjina kai su kayi, aunty azeema tace “to bari muje mai son ɗan tsuntsu ae shi ke binshi da jifa,” dariya su kayi gaba ɗayansu, tashi tayi bg abuhaisam ma yabi ta tare da kanal yusif, da sauran banda su fawan,
Sun gaisa dashi sosai, anyi kewar juna asake yayi magana da kowa, amma fa face ɗin nan tashi kamar an ɗinke ta saboda rashin fara’a,
Bayan sun fito ne abba ya kora su fawan da twins wadanda suka samu damar fito wa, munafukan hada sa jallabiya brown colour hannunsa riƙe da cazbaha,
gaba ɗaya suka tafi fawan, Ayaan da jahan dama sune basu je ba, tsayawa su kayi abakin door ɗin suka kasa shiga sbd shakkarsa,
“Enter first pls fawan,’ jahaan ne yace ma fawan, harararsa fawan yayi tare da cewa “kai ka fara shiga mana, ayaan yace “dan Allah fawan kafara shiga we’ll follow ur back pls, kowa ya gaza shiga sai faman jayayya suke yi abakin kopan ɗakin,
Duk wannan surutun da suke yi kaf a kunnan babban yayan nasu yana jinsu, sarai yasan cewa shaggun ne, ƙannensa ba,
“Yawwa Alhamdulillah ga junaid nan shikenan ma, zo ka fara shiga,’ ayaan ne yyi mgna with smile on his face,
Binsu da kallo junaid yyi wanda ya ƙaraso shima zuwansa kenan don ya miƙa masa gaisuwa don ɗazu yaga mood ɗinsa basu samu damar mgn ba bayan ya bude masa ƙopa, shima abban ne yasanar dashi cewa yaje ya same shi a room ɗinsa,
“Baku da gaskiya Allah, yanzu big bro ɗin namu ne kke tsoran zuwa wurinsa, maimakon kuyi kewarsa sosai, sai faman la6e la6e ku ke…..’
Buge masa baki fawan yayi tare da cewa “parrot meye naka aciki, mu dallah zo ka fara shiga,”
Shigewa gaba Junaid yayi suka bi bayansu, sai faman ƴan kame kame suke yi, sai kace ba jininsu bane shi,
Cikin natsuwa suka ƙarasa har sun naɗe riga zasu zauna a 3 seater ɗin dake facing bed ɗin abban nasu, ya buɗe idonsa tare da yi musu wani kallo jiki na rawa suka dawo ƙasa kowa ya lankwashe ƙafa yayi zaman cin tuwo,
Haɗa baki su kayi wurin cewa “Sannu da zuwa babban yayanmu ya gajiyar tafiya,”?
Suka tambaya suna kallonsa, shiru yayi baice komai ba, zuba musu ido yayi yana kallonsu, nan fa suka soma ƴan sunne-sunnen kai,
“Is that how your mom taught u how to greet each other,!? (Haka mahaifiyarku ta koya muku yadda zaku gaisar da juna?
Ya tambaya ayayin da yake tashi zaune daga kwanciyar da yayi,
Cikin sauri suka miƙe zumbur, junaid ne ya fara ƙarasa inda yake zaune a side bed ɗin, hugging ɗinsa yayi tare da manna masa kiss a side face ɗinsa, lumshe idonsa yayi tare da jinjina kai,
fawan ma ya karasa yayi masa kamar yadda junaid yayi, haka su ayaan da jahaan ma duk suka je suka rungumesa tare da manna masa kiss,
Sannan suka koma daf dashi daga ƙasa saman carpet suna naɗe ƙafa suna jiran jin me zaice,’
Shi dai junaid sai faman murmushi yake don murna, ba don komai ba sai don ya gama lissafin kuɗaɗen da zai samu a wurinsa, don yaci alwashin in ya amshi kuɗi wurin big bro ɗin nasu, sai ya yi wa Sehrish ɗinsa Siyayya saboda yasan tana buƙatar abubuwa da dama, ????
“Listening to me !! Bana so ɗaya daga cikin ku yajamin abun magana a family ɗin mu har na koma US , just i don’t wanna hear anyone saying this word again ƴa’ƴan fatima basu da kunya, if that happen you will see the trouble,’
Jinjina kai su kayi tare da cewa “insha Allah babban yayanmu hakan bazai faru ba, zamu kiyaye,’
“You can leave,’ ya basu umarni tashi su kayi jiki ba ƙwari suka fice, banda junaid wanda ya zauna yana ta faman kallonsa,”
“What do you want from me junaid”?.
Ya tambaya yana kallonsa, murmushi junaid yasaki cikin shagwabar nan tasa yace “akwai magana babban yaya, amma in ka huta zuwa gobe,”
wani irin kallo babban yayan yake masa, yana son yaron sosai, duk duniya in dai har za’a samu lagwansa toh ata6a junaid nan zakaga jijiyoyin wuya, yana ji dashi more than u think,
“Ya jikin ka? kana shan maganinka akai akai,”? ya tambaya yana kallonsa,
Junaid yace “yeah am getting well, kawai nayi missing ɗinka sosai,”
“Wow kayi missing ɗina kodai kuɗi na kayi missing, which one i have to know?
Dariya junaid yayi sosai, wato ya karto sa, tsagaita dariyar yayi kafin yace “a’a kafi mun komai mahimmanci arayuwata, kai nayi missing sosai,”
“I miss u too junaid, sbd kai na ɗau hutu sbd inaso nabaka kulawa ta musamman game da athma ɗinka,”
Cikin jin daɗi suke firar tasu, abun gwanin ban sha’awa, sai naji kamar na tsoma baki, amma nasan naushi zansha, ????
duk yinin ranar sehrish batasa ɗan tahalikin nan a idonta ba, saboda bai fito ba balle tagansa, in ma ya fito ɗin bata cin sa’a duk zumuɗin nan nata,
A ranar wuraren ƙarfe 4 Aunty babba ta koma kaduna gidanta, bisa umarnin mijinta, yayin da Amani ma ta koma gidanta cike da zullumin abunda auntyn tata ta kitsa mata zasu aitawar,
tsawon kwana 3 kennan Allah bai haɗa ta da Babban yayan ba, sai dai marshal omar da take gani da sauran da suka dawo, a yau aunty azeema ta koma lagos shima bg abuhaisam ya koma Jos inda yake da zama,
Tara su abban nasu yayi a main palour ɗin, su 3 banda babban yayan saboda yasan maganar bata shafeshi ba, maganar zumunci ne da family ɗinsa, sam basa ga maciji da Ammi, jarababbiyar tsohuwar bata son farar fata, jinsi indai ya wuce hausa fulani ! tom sun raba jaha, har yau bata shiri da ƴa’ƴan fatima, daga abu ya faru sai tace “halan ƴa’ƴan fatima ne, ae ƴa’ƴan fatima basu da kunya, jinsin fitsararru masu jan kunne,” wannan kalmar babban yayansu ya tsane ta, bai mata da wasa in suka haɗu, gashi shegen tsoransa take ji , saboda kwayar idonsa da take blue, muddin SGR na gari to bata zuwa Abuja,’
duka suna zaune saman 3 seater wadda ke facing abbansu dake zaune yana kallonsu, gyaran murya yayi tare da cewa “Alhamdulillah nayi murnar dawowarku cikin koshin lpy , kun jima bakwa ƙasar, tun da Allah yasa kun dawo, sai ku shirya ku shiga dangi, asada zumunci !
Mg Osman ne ya fara magana “haka ya dace abba, ni inaji zan fara zuwa damaturu ne wurin modibbo da sauran relatives ɗinmu, kafin na dawo na ziyarci sauran,”
Abban yace “hakan yayi kyau kai fa Captain ? gyara zama yayi tare da cewa “ni zan wuce kaduna ne wurin yaya ishaq daga nan zan wuce zariya ne, wurin dangi,
“Hakan yayi kyau, naji daɗi sosai amma fa yakamata asamu wanda zai je katsina wurin goggonku saboda kullum mu kayi waya sai ta tambaye ni ina, ƴa’ƴanta musamman kai Omar tafi tambayarka,”
ɗan kayataccen murmushi Omar yasaki kafin yace I will think about it abba, “

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74Next page

Leave a Reply

Back to top button