ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

tana miƙa masa ko waiwaye batayi ba, ta fice jiki na rawa wato tagama rikice wa, wai a hakan ma bata ga fuskarsa da kyau ba,

Kamar wata zararriya haka ta koma kitchen din, duk tabi ta ruɗe she was amazed by his beauty,
Kallo guda azmee tayi mata tagane cewa ba lafiya, cikin mamaki tace “Sehrish lafiyarki kuwa”? da budar bakinta sai cewa tayi “Babban yaya aunty azmee,’ wuce wa tayi gaban kitchen sink ɗin in da tabar vegetables din da take wanke wa,

Bin ta da kallo azmee tayi tana sakin murmushi aranta tace “kaɗan kenan,”
“Sehrish ni zan je nafara jere breakfast din a dining pls ki kular mun da farfesun dana ɗaura,sannan na manta bansanya salt ba ki zuba mun,”

A cikin wasu haɗaɗɗun food warmers ta shirya su, ta jerasu a saman faffaɗan tray ta fice don tafara jerawa,

sehrish sam bata farimtar komai still she’s out of sense , ita dai taji kamar tace ta zuba gishiri,

Cikin rashin sani tasanya Hannu ta ɗauki Ledar detergent, bil’haƙki da gaske taje ta bude murfin sauce pot (tukunyar miya) dake a saman gas, ta zazzage sa duka kaf Aciki , ta kuma ɗauki turner tana motsawa, gaba ɗaya hankalinta nakan surar babban yaya da ta gani, ta mutukar jan hankalinta,
bakomai idonta ke hasko mata ba fa ce wannan doguwar sumar kan tasa mai dan bala’in kyau, ????????????

Shigowa azmee tayi tana fadin “kinsa mun gishirin aciki “? jin muryar azmee yasa ta dawo daga tunanin da take yi, sai lkcn ta ankara da ledar detergent ɗin da ta zazzage acikin farfesun wadda ke a ƙasa, a razane ta dafa ƙirji tana fadin “Nashiga ukuna, wayyo Allah wlh omo na zuba maimakon gishirin !!!?
Sakin baki azmee tayi tana kallonta, jinjina kai kawai take yi, tana jinjina wa lamarin, sehrish kuwa ido yayi luhu luhu duk ta kame kanta,

“Sannu kin ji ? Azmee ta fadi tana kallonta, sunnar da kai ƙasa tayi tana fadin “am so sorry aunty azmee sharrin shaidan ne ba yin kaina bane,’

Azmee tace “sharrin shaiɗan kuma ko dai sharrin babban yaya wanne ciki? cije le6enta kawai take yi itama tarasa meke damunta,
“U did a good job sehrish, u need to ave some rest, aikin ki ya ƙare, sai da anjima in kin dawo hayyacin ki,’ cikin sanyin murya tace “dan Allah aunty azmee kiyi hkr, nasan fushi ki kayi dani, I made a big mistake am so sorry, bazan kara ba”

Murmushi azmee tayi tace “sam ni baki 6atamin rai naba, hasalima tausayin ki nake ji, Je ki huta,’

Kama hanya sehrish tayi ta fice daga kitchen ɗin tana mamakin haukanta na yau akan big bro, (nace ba saura na anjima ko na gobe) ????

Sehrish bata dawo cikin hayyacinta ba sai da tayo wanka, tasamu natsuwa sosai, a gefen gadonta tazauna tana ta faman zabga murmushi, farat ɗaya taji wani irin yanayi atare da ita, har takai ga ko runtse ido tayi shi take gani sanye cikin bathrobe, a tunaninta jinsa yafi ganinsa ashe ganinsa yafi jinsa nesa ba kusa ba, hannu tasanya ta janyo fillow ta kwantar da jikinta a saman gadon, idonta na kallon ceilling,

*tabbas shiɗin burin kowace ƴa mace ne ????
Alƙalamin *HAFSAT BATURE MOHD*

~BossLasy~ ????????

Page 65

Baki washe an samu dinner ????

………………..*………………………

~Husanna & Jahad~

Ƙanƙame suke da junansu A cikin Cell ɗin, cikin mawuyacin hali, sun rame sunyi baƙi, haƙiƙa sun ga rayuwa, yanzu an kammala shirya komai na shigar dasu kotu domin gudanar da shari’a A next week,

ƙarar bude cell ɗin suka ji, da sauri suka ɗago, wata jami’a ce sanye cikin kakin ƴan sanda, mai riƙe da muƙamin inspector,

su biyu ne ita da wani jami’i amma ita kaɗai ta shigo ciki, zuƙunnawa tayi gabansu tana binsu da kallo fukarta cike da tausayinsu,

a tsorace suke kallonta, baka ce babu annuri a fuskarta sai manyan tsaguna a fuskarta na rumawa,
“Idan zaku bani haɗin kai zan taimake ku, ku fita daga haɗarin da kuke ciki,” ta faɗi tana kallonsu

Cikin sanyin murya Jahad tace “komai kike so zamuyi dan Allah ki taimake mu mubar wurin nan, mun gaji, bamu ji daɗin zama anan, kuma bamu so akwai mu kotu a yanke mana hukuncin kisa,” ta kare maganar idonta cike tab da kwallo,
Murmushi inspector eesha tayi kafin tace “tabbas zaku fita, amma bisa sharaɗin in muje kotu zaku amsa cewa kune ku kayi kisan batare da jayayya ba !!!?
Zaro ido jahad tayi tana fadin “sabod me ? taya zamu ansa hakan bayan bamu ne muka kashe ta ba “?
shiru inspector ɗin tayi tana kallonta, da alama yarinyar zatayi taurin kai,
Husanna dake kanƙame gefen jahad tace “Ni na amince zan ce ni nasanya mata shinkafar 6era taci ta mutu, indai zaki fidda mu dan Allah,”
“Husanna !!! kada ki kuskura ki amince wlh ni banyarda ba wlh,”
Jahad ce tayi maganar tana kallon fuskar jami’ar, wadda tabisu da ido,
“Wlh ni na amince dan Allah aunty ki fidda mu, zance ni nayi kisan indai zaki cika alƙawari,
hannu jahad tasa ta rufe mata baki daƙarfi tana cewa “amma sai yau na tabbatar baki da hankali husanna wlh bazan bari hakan ta faru ba sbd we’re not guilty, ‘

ganin sun soma ƙoƙarin ɗaga murya yasa ta dakatar dasu da cewa “You have to trust me, ni turo ni akayi na taimake ku kuma dole sai ta wannan hanyar,
Cikin mamaki Jahad tace “wa”?
Murmushi tayi kafin tace “daga wurin ƴar uwarku SEHRISH,”
Jin ta ambaci sunan sehrish yasa su gyara zama suna masu tsananin mamaki, wani irin farin ciki ne ya bayyana a fuskarsu,
“Dan Allah dagaske ne sehrish zata taimake mu ? dama tasan halin da muke ciki ne, Allah ne ya amshi addu’ar mu zamu fita daga wannan uƙubar,”
Jahad ce tayi maganar da tsantsar farin ciki aranta, husanna kam sam tagaza rufe bakinta murya na rawa tace “Dama nasani Sehrish bazata bari a cutar damu ba, nasan tana son mu sosai, dan Allah a fiddamu daga nan akaimu wurin ƴar uwarmu,”
Kallansu kawai inspector ɗin take yi, wani irin kallo na shu’umanci ganin sun miƙa wuya yasa tace “kun amince zaku amsa cewa kune ku kayi kisan!!”?
Atare suka haɗa baki wurin cewa ehh mun amince,’

ƴar dariya tayi kafin ta fita daga cell ɗin, a harabar police station ɗin ta tsaya jikin motarta, hannu tasa a aljihun wandonta ta ɗauko wayarta ƴar nokia, daddanawa tayi kafin ta kara a kunnanta tare da cewa “Yaran fa sun amince, zasu amsa cewa sune su kayi kisan, yaushe zanji alert na cikon kuɗi na ?
Natsuwa tayi tana sauraron mutumin da ta kira a waya, wanda ba’a bamu damar jin me yake cewa ba,
Dariya inspector ɗin tayi kafin tace “nima fa shu’uma ce kamar kai, muddin banji alert ba na cikon kuɗi na, ina mai tabbatar maka da cewa, zansa su fasa amsa laifin,’
Ta jima tana wayar kafin ta kashe wayar tana tikar dariya (to fa)

A can cikin cell ɗin kuwa, wani tunani ne yazo ma Jahad ita mai hankalin taya akai ƴar sandar nan tasan sunan sehrish !!!!? Kuma taya akai Sehrsh tasan halin da suke ciki ? Tabbas akwai makirci acikin lamarin,

Miƙewa tsaye tayi tana zagaye, can dai tace “husanna so ake mu amsa laifin kisan nan don akashe mu, ba don ataimake mu ba !!
jiki a mace husanna tace “jahad ni nagaji da rayuwarnan, so nake na mutu kuma yanzun nan,!!

hankali atashe jahad tayi hanzarin komawa kusa da ita tazauna tare da dafa shoulder ɗinta tace “Husanna bakya jin daɗi ne,”

“Eh mutuwa zanyi yanzun nan,”
ta bata amsa, bin ta da kallo jahad tayi a tsorace ganin , jini ya soma biyowa ta hancinta, daga magana sai abu ya tabbata, kafin ta ankare husanna ta zube ƙasa, ba numfashi,
Wata irin razananniyar ƙara Jahad tasaki tare da faɗin “Innalallahi wa’inna ilaihirraji’una !!! Nashiga uku !!Wayyo Allah na Husanna ta mutu………..
da gudu police ɗin dake waje suka shigo ciki, sun gigita da ganin halin da yarinyar take ciki tamkar ba numfashi, kuma sun son tabbas ta mutu a hannunsu sai anji dalili,
hakan yasa aka kira women police guda biyu suka ɗauki husanna, hada jahad aka tafi da su cikin mota domin kaita asibiti,
Sai faman kuka Jahad take kamar ranta zai fita saboda tana ji aranta cewa Husanna fa wannan karon dakyar zata rayu,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74Next page

Leave a Reply

Back to top button