ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE
Sandwich ɗin tafara ɗauka tana ci, tunanin ta nakan *RAFAYET* azmee na lura da ita duk wani motsi da sehrish zatayi murmushi take yi, hankalin azmee bai kwanta da irin wannan zauce war da Sehrish tayi ba akan Babban yaya, tabbas soyayyace mai ƙarfin gaske take masa, tunkan tasa shi ma a idonta, da jin sunansa kawai ta faɗa tarko, balle ynx da tasa shi a ido? hakika jikin azmee yayi mugun sanyi tunawa da Junaid, bawan Allah wanda kullum burinsa ya ga yarinyar cikin farin ciki,
Babu wanda yasan da zaryar da junaid ya ke yi izuwa ɗakin azmee, kullum roƙonta ya keyi akan dan Allah taba sehrish kulawa ta musamman, komai sehrish take buƙata, tagaya masa zaiyi mata,
Junaid ba ƙaramin so ya ke mata ba, ????
(Tabbas akwai tashin hankali, ni babban damuwa ta, waɗannan zuciyoyin guda biyu ❗‼⁉
Wane hali zuciyar sehrish zata shiga ita da ta kwallafa rai akan mutun da ya kasance misoganist ! ya ƙi jinin mata, baya sha’awarsu basa gabansa, balle ma maganar aure, shin wane hali zuciyar junaid zata shiga ❓shi da bashi da ƙoshin lafiya, ga soyayyar wadda bashi ke gabanta ba, yayansa take so ❗ wane hali hosanna da Jahad zasu shiga in suka amince da bukatar Inspector Eesha!? shin za’a yanke musu hukuncin kisa ne, ko zasuyi zaman gidan yari ne ⁉ ????????????
Me zai faru idan su Aunty Babba Suka ziyarci Bokan nan na dajin enugu wato baba Iblis wanda muddin yayi asiri sai ya ci mutun jazamun, in ba wani iko na ubangiji ba ???? dole fa ku gyara zama domin yanzu cakwakiyar ta soma ????????????
“Idan kin kammala cin abinci, inaso mu zagaye gidan nan tare dake ki ƙara ganin haduwarsa sosai,” murmushi sehrish tayi wadda tuni cikinta ya fara birkice mata dakyar ta iya cewa “tom aunty azmee, amma sai na fara shiga toilet shaf shaf,’
Azmew tace “dama nasan wannan jazamin ne ae, zuba miki ido kawai nayi Allah, ni zan shiga ciki, in kin kammala ki same ni a bedroom ɗina, kyau ma mu fara sallar azhar naga time yayi,”
Sehrish ta amsa da toh, cikin sauri ta kammala, sbd dama a ƙagare take ta zagaye gidan, ta gaji da zama wuri ɗaya, daga bedroom sai kitchen, shaf shaf ta wanke kayan da ta 6ata, sannan ta wuce ɗakinta toilet ta shiga, bayan ta fito da alwalarta tayi sallah, sai wurin addu’a ta tuno da su hosana, tayi musu addu’a sosai, kafin ta cire hijab ɗin ta tura a wardrobe, dama already dress ɗinta na maza ne ajikinta, gashin baki kawai ta aza, tagyara sumar kanta, ta naɗe ta cikin hularnan tashi da kwakwa, daga sama ta bi da mayafi ta yi kamar turban, ta saki jelar mayafin gefe,
A tare da azmee su ka zagaya, sehrish tasha mamaki, ganin haɗuwar katafaren gidan, ko’ina take bi da kallo kamar wuyanta zai 6alle, muryar azmee ce ta katshe ta da cewa “kin ga nan, wurin motsa jiki ne wato gym, bi da kallo sehrish tayi an kawata abun wurin da komai na motsa jiki, kamar ta shiga ta jaraba itama haka taji, amma taci alwashin watarana sai ta shiga ciki tayi gym itama,
gaba su kayi suka sake zuwa wani room ɗin, “nan kuma ɗakin bincike kenan ,” jinjina kai sehrish tayi ganin wasu matsiyatan Computers gava ɗaya na’urori ne a ɗakin ke sarrafa komai, wurare daban daban ta nuna mata Hada weapon’s room ( ɗakin ajiye makamai) , hada haɗaɗɗen parlor wanda suka ware domin yin kallo acikinsa, an ƙawata shi da faskekiyar plasma tv, ga speakers na sauti, ga ƙawatattun kujeru aciki da sauransu,
daga nan suka fita can harabar wajen, sehrish tasha kallo sai taga kamar tabar 9ja ne, saboda cikin gidan duniya ne, bakomai ya ƙara burgeta ba face swimming pool ɗin da tagani, mai faɗin gaske ruwan ciki yayi blue sky, daga gefe a hada kujerun shakatawa da table, bata ga komai ba sai da su ka shiga garden Aljannar duniya, juyawa tayi ta kalli azmee tare da cewa “har yanzu muna cikin nigeria”? dariya azmee tasaki tare da cewa “of course,” jin jina kai tayi wasu komai na cikinsa kore ne ????, sai aka ƙawata shi da Red & yellow flowers ????????, ga wani tsaftataccen ruwa dake guda na (waterfalls) yana gangarowa daga jikin dutsi zuwa ƙasa ya taru acikin pool yyi kamar lakes, Bakomai ya burge sehrish ba face agwagin dake ciki suna yawa farare,
“Aunty azmee gaskiya gidannan ina kokwanto anya ba hotel bane, girmansa da haɗuwarsa yayi yawa,” tayi maganar tana kara bin ko’ina da kallo, azmee tace “haryanzu fa akwai sauran wuraren da baki gani ba, ynx dai na gaji mu zauna mana,
Wuri suka samu asamn garden chairs ɗin suka zauna auna facing juna, bin ta da kallo azmee tayi ganin tana ta faman murmushi, wato bakomai sehrish ke tunani ba fa ce ranar da zasu fara magana da baban yaya harsu shaku ssae su rinka zuwa garden ɗinnan atare suna kewaya wa, lumshe idonta tayi sbd wata iska da ta ratsa ta, aranta tana cewa “Ya Allah ka nunamin wannan ranar da raina da lafiya ta, ni da shi atare muna strolling Cikin farin ciki,” ????
“Me ki ke tunani ne”? Firgit sehrish ta yi jin maganar azmee a dodon kunnanta , cikin sauri tace “bakomai kawai ina mamakin haɗuwar gidan nan kamar a mafarki,”
Murmushi azmee tayi sbd sarai ranta ya bata cewa, tunanin ta na babban yaya ne,’
"Estate za'a mai dashi" cikin mamaki sehrish ta ce "dagaske aunty azmee? Amma zai fi kyau wlh girman yayi yawa,"
Azmee ta ce “eh naji da jima wa abbansu ya faɗi cewa za’a ƙara wasu part ɗin, yana so zai ware ma kowannansu nasa saboda baison in sunyi aure suyi nesa dashi, yace duk wanda yayi aure zai dawo ciki da matarsa, duk da sun mallaki gidajensu nakansu, amma shi yafi son hakan,”
Wani daɗi ne ya rufe sehrish, kamar anyi mata albishirin cewa itama zata kasance ɗaya daga cikin surukansa da zasu zauna agidan, ????
Bayan sun ɗanyi shiru na wani lokaci azmee tace “i have something to discuss wit u,’
“Menene aunty azmee” sehrish ta tambaya da ɗan mamaki a fuskarta,
“Ko kinsan cewa a cikin sojojin gidan nan akwai wanda yasan cewa ke maca ce ba namiji ba !!”
A firgice sehrish ta mike hannu dafe da kirji tace “Who”? fuskarta da tsananin tsoro,
Dariya azmee tayi kafin tace ” zan faɗa miki but firstly ina so ki mun alƙawarin cewa u will calm urself,”
Jiki a sanyaye ta koma ta zauna zuciyarta na bugu, tsoranta kar ace cikin jarababbun ne wato Fawan ko Twins,
"Aunty azmee wanene dan Allah.. .." tayi maganar tana haɗiye yawu,
Murmushi azmee tayi kafin tace “king of smile”
“Wanene haka azmee”? Ta tamvaya da mamaki,
“Oh baki gane ba tom nabaki satar amsa kije ki gano waya dace da sunan,’
duk iya tunanin sehrish bata gano wa azmee take nufi da King of smile ba, takasa samun natsuwa ta gano sa, sun jima suna fira bfr su koma ciki donyin sallar La’asar,
????????????ABBAN SOJOJI????????????
~????the father of soldierd????~?
????????????????????????????????
ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭ ﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ
ﺭﺍﻓﻴﺖ????????????????????
ﻗﺼﺔ ﻛﺘﺒﻬﺎ ﺣﻔﺼﺔ ﺑﺎﺗﻮﺭ????????
Story & written by
Hafsat Bature Moh’d
~BossLady~ ????
page 68
……….SEHRISH………………………
bayan ta kammala sallar la’asar, kimtsawa tayi kafin ta fito ta wuce kitchen tayi mamakin jin shiru alamun duk sun fita ne, tunanin ta ko’ina Babban yaya ya ke, ta lura baya fita sai dai azo a same shi in da ya ke, tun kafin azmee ta iso, sehrish ta fara ɗauko abubuwan da zasu yi amfani dashi, doya ta fara ferewa tasan suna yawan amfani da ita, tana aiki tana ɗan murmushi, sa6anin da tana aiki cikin damuwa saboda tunanin halin dasu Hosana da Jahad su ke ciki, zuwan big bro ya canzawa sehrish rayuwa gaba ɗaya,
Sam bata ji shigowar azmee ba, sai dae muryarta taji “Sannu da ƙoƙari rishi hakan ya burgeni,”
murmushi sehrish tasaki tare da cewa “Yawwa aunty azmee ina wurina,”
“Lafiya lou ta faɗi tare da shige wa ciki domin fara gudanar da aiki, cikin lokaci ƙankani kitchen ɗin ya fara kamshin abinci,
“Wani kalar abinci ki ka fi so”? Azmee ce ta jefa mata wannan tambayar yayin da ta ke zuba kayan ƙamshi acikin sauce ɗin da ɗaura, sehrish tace “farar shinkafa da jar miya ina son abincin nan sosai aduk lokacin da akayi mana shi a gida zumuɗi muke yi kamar hauka saboda muna jimawa bamu ci ba, shine abinci mafi daɗi a wurin mu,” ta karasa maganar muryarta a sanyaye ba don komai ba sai don tuna wa da hosana, a lokacin da su ke tare da mahaifiyarsu duk in akayi musu tuwo tafi kowa mita ta rinƙa sababi tana cewa “oumma wai mu kullum tuwo kullum tuwo, da rana ayi tuwo, da daddare ma tuwo, in safe tayi ma ɗumamen tuwo, ni wlh nagaji zanje gidan makwabciya in ciyo shinkafa da jar miya hada ma wasilla zata samun, “