ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

……..Junaid…………………….

Da tunanin sehrish ya yini, kasancewar ya fita gidan wani friend ɗinsa daya jima shima bai lpy, yaje duba sa, a can ya yini yana ta jansa da fira, hakan yasa ya jima, bashi ya dawo gida ba sai wuraren magrib ya shigo da motarsa, zuciyarsa cike da son ganin sehrish ɗinsa, da murmushi ya shiga ciki, bakowa duk sun je sallah da alama,

Bedroom ɗinsa ya wuce, cikin sauri ya shiga toilet ya watsa ruwa ya fito, shirt yasanya tare da dogon wando, kullum ya kalli kansa a mirror sai ya furta wannan kalmar wato “Mallakin sehrish,”

(Sai naji dama ni yakewa tanadin kansa da ban bari yasha wahala ba, dama ƙopa a buɗe take musamman ga irinsu Junaid masu kyawun hali) ????

Jin takon takalminsa yasa sehrish ɗagowa, wadda ke tsaye tana ta faman jera abincin a dining, ita ta riga azmee fitowa bayan sun gudanar da sallar la’asar, zuba mishi ido tayi atlease tayi kewarsa sosai don tun safe rabon da tasa shi a idonta,

Shima farin ciki ne ya dabaibayesa ganin muradin ransa, ƙarasawa yayi yaja kujera ya zauna yana kallonta,
Cikin sauri tace “me zan zuba maka,”
“duk abunda yayi miki,” kai tsaya ya faɗa,
Jim sehrish tayi shiru ta tsaya da jeran da take yi, maimaita maganar da yayi yanzu acikin zuciyarta tayi wato daya ce “duk abunda yayi miki amaimakon yace duk abunda yayi maka tunda amatsayin namiji take,”

ɗan ɗagowa tayi ta saci kallansa, har ynx idonsa na akanta fuskarnan ɗauke da murmushi,

Jiki a sanyaye ta zaro plate haɗaɗɗiyar jallop din taliya ta zuba masa, tare da haɗa masa da Cokali aciki ta miƙa masa,

“Thanks” ya furta tare da soma cin abincin, ganin yana ɗiba da zafinta yasa tace “ka bi a hankali kana ka ƙone,”

ɗagowa yayi ya kalle ta da buɗen bakinsa sai cewa yayi “kada ki damu zan kula”

daram taji gabanta ya ƙara faɗuwa, yau junaid yasaki layi sai kiranta ya ke da sunan macen ta,

Jin ƙarar dirar motoci ya tabbatar mata da cewa sun dawo, nan da nan taji zuciyarta ta bada wani sound, saboda tasan hada mutumin ta aciki,

Shigowa su kayi atare suna ta faman fira, kamar ba’a tare suke ba,

fawan da khaleed ne suka fara shigo wa tare da su Irfan da jabeer banda su twins,

tayi tunanin shima zai shigo ne amma babu shi, haka abbansu ma, da kanal yusif,

kai tsaye suma suka wuce izuwa dining ɗin suka ja kujera kowa ya zauna,

“Sannun ku da dawowa” acewar junaid,

Su ka amsa su duka, cikin sauri sehrish ta shiga yin saving ɗinsu,

“Ina yaya Ayaan da Jahan su ke, banganku atare ba? Su basu dawo ba ne?

Junaid ne yayi wannan tambayar,
Fawan ne ya basu amsa da cewa “taya muma zamu sani? mun jima da rabuwa dasu, su sukansan inda suka je”

Jabeer yace “ko tsoro basa ji, babban yaya ya neme su, su basusan su kame kansu ba, kamar yadda mukayi,”

“Ka rabu da shaggun jiki magayi,” acewar irfan,

   ~Hafsat bature~  ✍️

Keep sharing ????????????????ABBAN SOJOJI????????????

~????the father of soldiers????~

????Romantic Love story between Hosana& Marshal Omar????

????HAFSAT BATURE BOSS LADY????

page 69&70 ????

“Ka rabu da shaggun jiki magayi,” acewar irfan,
haka su kayi ta fira suna zuba abinci acikinsu,

Bayan sun kammala sehrish ta kakkwashe dishes ɗin da sauransu duka tayi kitchen dasu, har time ɗin azmee bata fito ba har sai da ta kammala wanke komai da su kayi amfani dashi sannan tashigo agajiye tana faɗin”kin ji shiru ko wlh bacci ne yayi awon gaba dani shiyasa ban fito ba,
“Babu komai aunty azmee kwarama da kika huta sbd kina aikatuwa ssae,”

Azmee tace” hmmmm nasaba ne, bana gajiya da aiki,

shiru su ka ɗayin kafin rishi ta kuma cewa “Su babban yaya basu shigo ba, shi a part ɗinsa za’a kai masa abincinsa ko anan down ?

murmushi azmee tayi tace ” a can ake kai masa amma in yakasance dinner ne, wani time ɗin kuwa anan su ke haɗuwa suci gaba ɗaya, ke zaki kaimasa ?

“Eh zan kai masa,’ cikin zumuɗi sehrish ta bata amsa,

“Shikenan amma akwai wani abu da zan faɗa miki u ave to know it,”

Sehrish ta ɗan yi jim kafin tace “menene shi”?.

“Babban yaya fa, baya son kallo sai fa kin kiyaye, because in ana kallonsa yana ji ajikinsa, sannan in ya tambayi abu ko menene kawai ki ce akwai, karki kuskura ya ce yana buƙatar wani abu akawo masa ki ce bamu dashi, ya tsani wannan ki kiyaye ! Sannan baisan kwaratsi ko kaɗan, sannan shi mutun ne mai tsaftar gaske, ko da gigin wasa kada ki kuskura ki bar abun ƙazanta a part ɗinsa ko min ƙanƙantarsa ko da ajikin ki ne, ke ma ki ƙara tsaftarki abisa wadda ki ke yi don daga yanzu ke ce zaki rinƙa kula da part ɗinsa,”

Wani irin daɗi ne ya rufe sehrish, jin cewa itace zata rinƙa kula da part ɗinsa, koba komai zasu samu kusanci da juna, ????

Azmee ta ci gaba cewa “and then he doesnt repeat words in yayi magana, dole yayi magana aji farat ɗaya, sannan in yana bacci ba’a tashin shi, don naushi ya ke kaiwa bana wasa ba……’

Katse ta sehrish tayi da cewa “In time ɗin sallah ne fa? Shima ba’a tashin sa? ta tambaya tana kallon azmeen wadda ke daga tsaye,

Azmee tace “Abun ajinin sa ya ke ! muddin lokacin sallah yayi dakansa ya ke farkawa, sometimes kuma alarm ke tashinsa,

Jinjina kai sehrish tayi aranta tace”akwai matsala, Anya kuwa zan iya ? ta tambayi kanta,

Muryar azmee ce ta dawo da ita “zaki iya mana, matukar ki kasa natsuwa,”

Wata tambayar sehrish ta ƙara jefa mata,
“Aunty azmee wai babban yaya ɗan wrestling ne?

“Meyasa ki ka tambaya”?

sehrish tace “naga yanayin kirar jikinsa ne, wlh irin ta tasu ce,”

Hmmm azmee tace “shi da ya ke soja, sojan ma bana wasa ba, wanda ya amsa sunansa ae fiye da wresting ma yana yi,”

Murmushi sehrish tasaki Aranta tace “a shirye nake dana zama tamkar baiwarsa wurin yi masa biyayya sau da ƙafa, zan yi komai zan yi iya ƙware wata don naga yasan da zamana acikin gidan nan,
tayi maganar atime ɗin da take jera dishes din da takammala wanke wa, a cikin shelves ,

Atare da azmee suka idasa gyara kitchen ɗin su kai mopping da komai,” daga bisa azmee ta wuce ɗakinta bayan ta sanarwa sehrish cewa idan sun dawo ta tabbatar da ta kai musu dinner ɗinsu,
Kasa bacci tayi burin ta, taji shigowar Babban yaya, domin takai masa dinner ɗinsa,

Murmushi kawai ya ke saki ynx ya yanke shawarar zai sanar wa sehrish da cewa yasan ita mace ce ba namiji, rungume ya ke da pillow a ƙirjinsa, night dress ne ajikinsa riga ce ta wuce guiwa, ya baje a saman gadon abban nasu yana jiran dawowarsa,
Ƴunkurawa yayi ya ɗan tashi zaune, yana tunanin taya zai sanar mata batare da ta tsorata ba, gyara murya yayi kamar yana agabanta ya ce “Sehrish na riga da nagane cewa ke maca ce, don haka ki kwantar da hankalinki, ni mai sauƙin kai ne bazan bari kowa yasani ba, i promise u, ni burina ki ɗauke ni tamkar ɗan uwanki na jininki, nima zan ɗauke ki amatsayin sister ɗita……..’
dariya ya saki bayan yagama tsara wannan maganar, ajiyar zuciya ya saki tare da cewa haka yafi dacewa na tunkare ta, na sanar mata, Allah yasa kada ta razana, ko taƙi accepting ɗinsa as her brother,

Koma yayi tare da kwantawa idonsa na facing ceiling, fuskarnan da murmushi, har cikin ransa yarinyar ta kwanta masa luf~~~

Har bacci ya soma ɗaukarta, taji dirar motocinsi, cikin hanzari ta buɗe idonta, murmushin farin ciki tasaki, tashi tayi zaune tana jira su kammala shigowa kafin takai masu dinner ɗinsu, zuru tayi tana jiran shigowarsu, tana jiyo muryar abbansu da kanal yusif suna magana, amma bata jiyo tasa ba, tamasan baza taji tashi ba, saboda wata irin Voice ce dashi bata da sauti sosae, wata’ƙil sai ransa ya 6aci sannan Za’aji tsiwarsa,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74Next page

Leave a Reply

Back to top button