ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

Sai da ba da kusan 30 mins, sannan ta tashi cikin sauri ta gyara kanta, kafin ta wuce kitchen, sai da tafara kaiwa kanal yusif nashi a room ɗinsa, sannan ta wuce kaiwa Abbansu nashi shima,
Da sallama tashiga,atare da junaid suka amsa mata, cikin natsuwa ta shiga da tray ɗin mai ɗauke da food warmer tare da plates da spoon, sai jug da cup,
Kwance suke atare shigowarta yasa su tasowa zaune, cikin girmamawa tagaishe da abbansu, da sakin fuska ya amsa mata,
umarni ya bata da ta ajiye mashi anan ƙasa, ajiyewa tayi a hankali kafin ta tashi, suka haɗa ido da junaid ya kashe mata ido,
gabanta ne taji ya faɗi, sai ta ga abun kamar a dream, tafiya take zata bar room ɗin nasu, tasake juyawa tare da kallonsa, again ya sake kashe mata idon,
Cikin sauri ta fice tana mamakin wannan abun, amma tariga tasawa ranta cewa “Junaid yana da ta6in hankali,” wasu ɗabi’un nasa yayi mata kama da na masu psychiatric disorder ????
A ɗan kayataccen tray ta shirya mashi nasa, gabanta na faɗuwa ta tunkari upstairs apartment ɗinsa,
A buɗe tasamu kopan parlor ɗinsa, haske everywhere, bata gajiya da kallon hadaɗɗen parlor dinsa, sallama tayi taji shiru idasa shiga ciki tayi, asaman table ta ajiye masa shi, tsayawa tayi tana tunanin ya za’ae yasan ta an Kawo masa dinner ɗinsa, ran ta ne ya bata cewa ta shiga cikin bedroom ɗin nasa tayi informing nasa,
zuciyarta na ɗar ɗar ta tunkari cikin bedroom ɗin nasa, a hankali ta ɗanyi knocking door ɗinta, gabanta na faɗuwa,
shiru tayi tana jira abata umarning shiga, sexy Voice ɗinsa ce ta ratsa kunnanta da cewa “Come In”
Ajiyar zuciya sehrish tayi, tare da lumshe idonta, wani irin sanyi ne ni’imataccen gaske tare da ƙamshi su ka ziyarci hancin ta, a hankali ta idasa shiga ciki tana wurwur ga eyes ɗinsa can ta hangosa, daram taji wani irin bugu azuciyarta,
daga shi sai ɗan pant na maza ajikinta, yana tsaye at the front of the mirror Allah yaso ya juya mata baya, ba ita ya ke fuskanta ba, da taga tashin hankali,
Zuba wa surar jikin shi ido tayi cikin tsananin tsoro, dogo ne bana wasa ba, ga wannan ƙirar karfin tasa, idonta ta saukar akan zanen tattoo ɗinsa mai tsananin kyan gaske A farar fatarsa, bata ta6a lura dashi ba sai yau,
sam tarasa buɗe baki ta faɗi abunda ya kawota sbd kallon Kyakkyawar surar Babban yayanmu, ????
hannayensa na cikin sumar kansa, yana shasshafa mata mai, sai salƙi take kafin ya ɗaure ta yasa ke ta izuwa bayansa, mayar da hannunsa yayi acikin jerin tsadaddun turarukansa dake agaban mirror ya ɗauko kwalbar turaren (Imperial Majesty) haɗaɗɗen turare mai wani irin fragrance mai ratsa sassan jiki, sai wane da wane ke mallakar irinsa,
Feshe jikinsa ya yi dashi ta ko'ina kafin ya mayar ya ajiye,
Ya jima yana mamakin wanene ya shigo masa bedroom ɗinsa haka, ya ba da permission ɗin a shigo amma shiru ba aƙara magana ba,
gyaran murya yayi alamar son jin bayani daga wurin wanda ya shigo masa ɗaki,
gyaran muryar da yayi ne ya dawo da ita cikin hayyacin ta, cikin sauri murya na rawa tace “am…dama…dinner….ne ….na kawo……yana a parlor,
“Its okay, wait 4 me there, am coming now,” ya faɗi yana kai hannunsa saman bedmatress ɗinsa inda ya ajiye sleeping dress ɗinsa da zai sanya,
Jiki a mace sehrish ta fice, tana cizon lips ɗinta, haƙiƙa tagama narkuwa cikin tsananin ƙaunarsa ????
A parlor dinsa ta tsaya tana jiransa kamar yadda ya umarta, hannunta na a chest ɗinta dafe da saitin Zuciyarta, surarsa kawai idonta ke tariyo mata, Murmushi kawai take saki Big bro ya gama tafiya da ita, ????
Sam bata ji fitowarsa ba, sai da ya ƙaraso ya zagayo inda royal sofa ɗin suke sannan ta ankara,
Wani sabon kallon tabi shi dashi, sleeping dress ɗinsa sunyi matuƙar yi masa kyau, koda ya ke shine yayi musu kyau, irinsu Babban yaya sune suke wa kaya kyau, wato masu sa kyau tayo kyau ko bata da kyau ????
Riga da wando ne ƴan ƙasar indonesia masu laushin gaske, irin wanda ko mutun baijin bacci yasa su dole yaji shi, maroon colour masu zanen flowers milk colour ajikinsu, daga sama rigar bata rufe ƙirjinsa ba, dama shi bai cika sa kaya waɗanda ke covering chest ɗinsa ba, bai sanya links na rigar ba,
Cikin natsuwa ya zauna saman 3 seater, sam sehrish tagaza janye idonta akansa balle tafara saving ɗinsa har sai da taji voice ɗinsa a ears ɗinta yace “Ni zanyi saving kaina ne!? ya tambaya fuska a ɗaure,
Cikin sauri sehrish ta ɗauke ɗan bowl tare da buɗe warmer ɗin dake ɗauke da Chicken pepper soup, tasanya saving spoon ta Shaƙe masa shi, wani irin aroma ne ke tashi daddaɗan gaske, ajiye masa tayi sannan ta zuba masa white rice acikin plate, bayan nan ta haɗa masa da drink mai sanyi,
Natsuwa tayi bayan ta kammala zuba mashi duk abinda ya dace, ta ɗan ja baya zata juya ta fice sbd tuna mgnr azmee na cewa Bayason kallo, muryarsa tasake ji ya ce “In na kammala wazai kai kayan kitchen!”? tsananin mamaki sehrish kawae take yi, ashe yana magana har haka, acewarta, muryarsa ba ƙaramin daɗi take mata ba, tayi mamakin yadda yake furta yaren hausa duk da kana ji kasan bai saba da ita ba, in ka gansa bazaka ta6a tunanin cewa zai iya magana da hausa ba, saboda yanayinsa,
Cikin hanzari tace “Ni” jinjina kansa yayi, ya ci gaba da cin kazar dake gabansa, murmushi ta ɗan saki tasamu wuri ta tsaya, da tazara tsakaninsu, amma komai yakai hannu zai ɗauko cikin sauri sehrish ke ɗauka ta zuba masa in na zubawa ne, in kuma nasha ne ta tsaiyaya masa, har ya kammala sam babban yaya baya wasa da cikinsa, yana basa haƙƙinsa yadda ya dace,
Sehrish ta tsaiyaya masa ruwa ya wanke hannunsa acikin wani bowl, sannan ta ciri tissue ta miƙa masa ya goge mouth ɗinsa dashi,
Haka tabi shi da ido harya tashi ya wuce cikin bedroom ɗinsa, ta lura bacci yake ji yadda taga yana lumshe idonsa,
Sai daga bisani ta tattare kayan ta fice tana mai jin kewarsa atare da ita, kafin zuwa gobe ta kuma sashi a idonta, cikin kitchen tamayar da kayan sai da ta wawwanke dishes ɗin acikin daren sannan ta wuce nata room ɗin tana mai cike da shauƙinsa,
Ta jima ba tayi bacci ba, su twins basu dawo cikin gidan nan ba sai around shabiyu na dare, Time ɗin ma kowa yayi bacci, cikin sanɗa su ka wuce room ɗinsu,
a cikin ƴan kwanakin nan rayuwar sehrish ta canza sosai, wani irin azababben so take mashi, wanda har ya kai ga ko sallah take yi da tunaninsa aranta, daker take samu ta dai daita natsuwarta wani sa’in,
Junaid kuwa sam ya gaza gaya mata abunda ya shirya zai sanar mata, ƙarshe azmee tace yabarta ita da kanta zata sanarwa sehrish ɗin, a yayin da sehrish ke wannan haukan sam Rafayet har yau bai ta6a ɗagowa da idonsa ba, yasa cikin nata, bae masan wanene ba ko wacece ba ke famar ɗawainiyar kai masa abinci da gyara masa part ɗinsa ba, abunda yasani shine yana samu kyakkyawar kula agurin kowanene ma ????
Hafsat Bature…………………………………………………………
…………..Katsina state…………….
Zaune take ta haƙimce a saman 3 seater, ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya, hannun ta na riƙe da remote, ta ƙura ido tana kallon faskekiyar plasman dake manne jikin bango tana facing ɗinta,
Ko kyaftawa batasan yi, dayake shirin ta ake yi, wato shirin daɗin kowa na Arewa 24, maimaici ne take kallo, sai faman washe baki take yi tana fadin “Oh koya za’a kaya tsakanin mlm na tala’a da hajiya fatima akwai bada ƙala a wurin nan,’ ta faɗi tana jinjina kai, ita kadai abunta, acikin matsakaicin parlor ya hadu iya haduwarsa ba hayaniya, ga komai cike da tsafta kwal,