ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

In the morning
Around 10:30am makeup artist dinan ta iso gidan a time din duk sun hallara a falon hajjaju , bayan sun gama gaisawa , ma’reea ta bukaci ganin Sehrish , kwala mata kira hajajju tayi fitow tayi da sauri ta iso inda suke , bin ta da kallo mareeya tayi frm head to toe , sannan tace “Wannan ae mai sauki ne , naga tana da tsayi jiki ne dai babu sosai , abunda za’ae kayan maza za’a samo riga da wando oversize saboda su kara mata girma , sannan wadannan abubuwan , tayi magana tana nuna kirjinta da hannunta ” dole a matse su don naga suna da girma ssae tubarkalla , ” cikin jin kunya rishi ta dukar da kanta kasa , murmushi larai da hajajju sukayi , su kuwa y’an matan nan dake baje a kasan carpet dama basu da burki washe baki suka shiga yi wato anzo dai dai inda suke so ,
Hajajju tace “ynx me za’a sa a yi tighting dinsu “? Ma’reeya tace “mai sauki ne akwai wani abu da muke amfani dashi na matse tumbi shima zai iya yi ,” hankalin rishi ba karamin tashi yayi ba har bata son lokacin da tayi subul da baka ba tace “in suka bace fa ya zanyi ,”? gaba dayansu suka kwashe da dariya mareeya tace “wato kada su bace a rasa nayiwa miji gayu ko ,” cikin jin kunya ta dukar da kai , larai tace ” dagaskiyar ta fa nono ae yana daya dagacin abunda ke kayatarda maza in suka bace ae ba magana ,” ta karasa magana tana dariya , duk kunya ta gama kamata,
Ma’reeya ta ci gaba da magana “Sannan naga kamar tana da tsayin gashi ko,”? hajajju tace “Sehrish cire hijabin mana tagani , hannu tasa ta cire hijabin ta rungume a kirjinta ,
Hada baki sukayi wurin cewa “Tubarkalla masha Allah ,” ma’reeya tace ” yarinyar kamar balarabiya wurin tsawan gashi, gsky ni kishi nake da wannan gashin naki don haka dama dole indai zakiyi acting a matsayin namiji sai an datse miki shi ya koma guntu kamar nawa dai”, nan fa hankalin ta ya tashi saboda tana bala’en son gashin nan nata , kamar zatayi kuka tace “don Allah hajajju karki bari ayimun aski ni inason gashi na ,” takarasa maganar tana kallon hajjaju ,
Murmushi hajajju tayi tace ” Sehrish ba Aski zata miki ba rage miki shi za’ae , ke da zaki neman kudi wake ta wani gashi , “
Shiru tayi tana wasa da yatsun hannunta , larai tace “Gsky yarinyar nan da ace a matsayin mace zata je aikin nan tsaf zata auren mai gidan,” hannu hajiya tasa abaki tace “ke ! tab y’ay’an sa kuwa da sun yi farfesu da namanta sojoji fa akace hmmm !! ” dariya sukayi su duka , mareeya ta cigaba da bada bayani “Sannan dole a canza mata suna daga SEHRISH zuwa TUKUR ,” a tare suka hada baki wirin cewa “Tukur kuma !”? murmushi ma’reeya tayi tare da jaddada masu maganarta ta ” kawai kuwa ! sannan zan sa mata gashin baki irin na maza wanda ake fixing dinsa tare da eyebrows na kanti.
*_Hafsat Bature_*
~(Boss Lady)~
Page 7-8
Hajajju ta ce “Gashin baki dai. wannan dana nasani ? amma me amfanin hakan “? ma’reeya tace “Wannan wani salo ne kuma ina tabbatar miki da zaiyi aiki , duk da sehrish yarinya ce har a fuskarta amma indai nasa mata gashin baki dana jagira , zata kara suffanta da namiji zata koma kamar d’an daudu kuma dama in kin lura yanayin jikin y’an daudu basa da kiba sai tsayi ,”
Gaba daya sun amince da maganar ma’reeya , shiri na musamman akayi ma Sehrish a washe garin ranar cikin riga ta maza milk colour mai maballai a gaban rigar , sai wani burgujejan wando falazu da aka sama ta kamar kafar agwagwa haka yake pink colour , sun matse mata kirjinta , shafe ta koma kamar babu su , an datse dogon gashin kanta an barmata guntu irin nawa sai suka samu kallabi irin launin trouser din suka nannade mata shi akai kamar rawani , kallabin nada tsayi sai da yar jela ta zubo ta gefe , sai ta koma kamar d’an chali chali , ga gashin bakin da suka sanya mata , ya hau radau ya zauna , haka jagirar da suka samata , ta zauna cuf , duk wani abu na ado na jikin y’a mace babu shi a tattare da ita yanzu ,
Shin koya wannan wasan kwaikwayon zai kasance ? mezai faru ranar da suka gane cewa sehrish macace ba namiji ba ? Kowa yasan ya sojoji suke ????.
Tunda a sussuba suka kama hanyar zuwa abuja , ita da hajjaju , zuciyarta sai dar dar take yi mata , a natse hajjaju ke driving dinsu , yayin da sehrish ke gefenta , idonta nakan glass din motar , tana kallon yadda suke wuce wurare daban daban , zahiri tana kallon bishiyoyin da suke giftawa na cikin dajijjikan da ke a side road kamar suna gudu da kafafuwansune , a hankali zuciyarta ta sauya mata akalar tunaninta izuwa rayuwarsu ta baya , nan take taji wasu zafafan hawaye na sintiri a idonta , zuciyarta ce ta soma yi mata magana “Sehrish kowane d’an adam yana da irin tasa kaddarar, Allah yana jarabtar bayinsa ne domin ya gwada imaninsu , kiyi kokari ki cinye wannan jarabawar , ki rungumi kaddara a duk yadda tazo miki dama can rutacce ne daga Allah dukkan tsanani yana tare da sauki ! Allah yana sane daku kuma shine gatanku ,”
Hannu tasa tana clearing face dinta saboda bata so hajjaju tagani , tunanin y’an uwanta shine yafi komai tayar mata da hankali , bata san wani gidan mahaukata bane zasu juri daukar nauyin haukan ta ba idan akace yau husanna tarasa ranta , haka abubuwa suka dinga zuwa mata aranta har suka isa garin abuja, wuraren karfe 2:30 na rana ,
Wannan ne karo na farko da ta fara yin tafiya mai nisa irin wannan ,
tunda suka shiga take kallon manya manyen gine gine , har suka iso gidan da zasu wato gidan Abban sojoji , sehrish ta razana da ganin katafaren ginin mai matukar girman gaske da daukar hankali , irin gidan da ta saba gani a cikin mafarki,
Lokaci da idonta suka sauka kan Narka narkan sojojin dake tsare da babban gate din gidan sai da taji gabanta ya fadi rass , bakake ne wulik dasu sanye cikin uniform dinsu , ga bindigu rike a hannunsu , ga wasu guns din soke a west dinsu ,
Wani irin miyau ta hadiye ganin an tsaida motarsu , nan take taji zufa na gangaro mata ta cikin sumar kanta , guda biyu ne suka karaso inda motar tasu take , d’aya ne yasa hannu yayi knocking , hajjaju ta zuge glass din , ita kanta a tsorace take cikin en ena tace “barka dai sannu ku da aiki ,” amsa yayi da “yawwa muna bukatar sanin daga ina kke kuma wurin wa kka zo “?
Da sauri hajjau ta dauko wayarta cikin yar purse dinta ta shiga neman number abban, yatsun hannunta sai kakarwa suke , kira d’aya tayi masa ya daga , bayan sun gaisa ta sanar masa da abunda ke faruwa, ya umarce ta da ta basu wayar , mika musu tayi daya daga cikinsu yasa hannu ya karba tare da karawa a kunnansa , juyawa hajjaju tayi tana kallon sehrish wadda tuni ta ta gama tsuma , ta nannade wuri d’aya ta matse jikinta , idon nan sunyi furi furi kamar wadda tayima sarki karya , muryar sojan taji yana cewa “take your phone , u got permission to go in , but firstly we must check the car ,” kallon sehrish tayi tare da cewa ” mu fita zasu bincika motar ,” bude mota sehrish tayi ta fita , itama hajjajun ta fito , suka tsaya suna jiran su gama binciken nasu ,
Matsawa Sehrish tayi kusa da hajiyar tayi kasa kasa da murya tace “hajiya amma nan barrack din sojoji ne ko “? cikin rashin natsuwa hajjaju tace ” A’a gida ne na sojoji dae not a barrack ni bana cikin kwanciyar hankalin wadannan sojojin sun firgitani , sai kace wasu masu safarar miyagun kwayoyi za’a tsare mu ! that’s why ban cika son zuwa gidannan ba ! ,” takarasa maganar tana yatsina fuska ,