ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

Tsohuwa ce amma ba tukuf ɗin nan ba, tana da hasken fata, jikinta na sanye da riga da zani na atampa, ta coge ɗaurin dankwali, daga ganin ta kasan taji hutu ga kuma kwanciyar hankali da natsuwa,

“Saude ! Saudee !! saudatu wai ina ki ka shiga ne? kin shanya ni ina ta faman jiran ki, da alama watan barin ki agidannan ya tsaya,” ????

tsohuwarce ta fadi tana murguda baki kamar wata yarinya,

Cikin sauri wadda aka kira da sunan saude ta fito daga kitchen hannun ta ɗauke da plate wanda naman kaza ne acikinsa jar suya

Karasowa tayi tana faɗin “dan Allah goggo ayimun afwa, wlh bata ida soyu ba ne shiyasa,’

hararar ta tayi tana yamutsa fuska tasa hannu ta kar6i plate din tana cewa “Last warning, in ki ka kara, zaki tattara kayanki ki koma can ƙauyenku aci gaba kiwon shanu baki ba ra6ar A.c ,”

Shiru saudatu tayi tana tamke fuska, ta tsani taji ance za’a maida ta ƙauyansu, gashi kullum tsohuwar cikin yi mata mita take bata gajiya,

hannu tasa ta ɗauki tsokar naman ta tusa abaki, tana tauna tana yamutsa fuska,

“Anya kuwa saude kinsa farin magi aciki kuwa,” ta tambaya tana kallonta yayin da take lasar naki,

A ƙule saude tace “bansanya ba, babban likita ya hana,!

dagowa tayi baki asake tana kallonta “saudatu ! Rashin kunya ko? Ki kalli tsabar idona ki ce babban likita ya hana ! shiya haife ni koni na haife sa dazai hanani jin daɗin rayuwa!?

Cikin ƙunkuni saudatu tace “Ke ki ka haifesa, amma ae don lafiyarki yayi hakan….’

tunkan ta idasa magana, goggon ta jefe ta da ƙashin ciyar kaza a fuska,’

Hannu saudatu tasa ta shafa wurin da ta jife ta, kafin ta kalle ta tana zumbura mata baki,

“Ke ki kiyaye ni Allah ! wato ya daure maki gindi kina iya shegen da kika ga dama ko ? Cikin sauri saude ta dafe kai cikin jin kunya tace “dan Allah goggo wannan maganar ba daɗin ji Allah, gatsar ba sakayawaa,

Baki asake goggo tace “ba shakka, yau yarinya zatayi fiffike ta koma gidan ubanta,’

Kafin Saudatu ta bata amsa, sukaji dirar motoci a cikin gidan da jiniya,

Kallon juna su kayi atare, saudatu tace “goggo meke faruwa ne, ko kinyi da wani zai zo ne ? ni naji kamar jiniyar motar ƴan sanda,”

Murmushi goggo tasaki tare da ajiye plate ɗin kazarta, kasa tana cewa

“Kin manta muna da rundunar sojoji a family ɗin mu ???? Shiyasa nake gargaɗinki kibi ni a hankali, kiyi mun biyayya ko kin gama da duniya lafiya, cikin zolaya tayi maganar, dariya saudatu tayi,

adai~dai lokacin marshal omar ya shigo wanda dirarsa kenan,

sanye yake cikin jeans da farar t shirt mai dogon hannu tabi shape din jikinsa, surar kirjinsa ta bayyana muraran, fuskarsa na sanye da face mask, ba karamin kyau yayi ba, koda yake dama jinin kyau ne su,

tun da ya shigo baki asake saudatu ke kallonsa kamar ranar ta fara ganinsa,

Cike da wannan tafiyar tasa ta nigogi majiya karfi yake tafiya,

Tsananin farin ciki yasa goggon katsina harba plate ɗin kazarta ya watse ƙasan carpet ba tare da ta sani ba, kamar karamar yarinya haka ta watsa a guje ta rungumesa tana fadin “Wata sabon gani, mafarki nake ko gaske, Oh ni Omar,

Sakin shi tayi tana ta faman zabga murmushin jin daɗi, a hankali yasa hannu ya ɗan zame facemask ɗinsa yana kallonsa fuskarsa da fara’a ya ce “Goggo na har ynz dama baki daina wannan tsalle tsallen ba sai kin 6alla ƙafa ?

dariya tayi ta ruko hannusa tana fadin” wlh duk cikin farin ciki ne Omar, ji nake kamar in zuba ruwa a ƙasa in sha,

zama su kayi atare, sai lokacin saudatu ta samu damar gaishe shi ” sannu da zuwa ƴa’ƴa Omar,’

“yawwa” ya bata amsa without looking at her, idonsa na akan goggonsa wadda ke ta faman binsa da kallo, hannu tasa ta shafa fuskarsa tana faɗin “Oh ni Omar haka ka zama, tukunna ma dai yaushe ku kazo daga U.s ɗin? kuma ya naganka kai kaɗai ina sauran suke ? tare da matarka ku ka zo ? ta haihu yanzu ko ?

Zuru yayi yana kallonta, aransa yace mai hali bai ta6a canzawa in banda zafin ɗumi irin na goggon katsina Yaushe yayi budurwar balle akaiga maganar aure da ƴa’ƴa?

ajiyar zuciya ya saki kafin yace “wacce amsa ki ke so na fara baki gaggona ?

Murmushi ta dan saki tare da cewa “ni ba wannan ba ma, Oh ni Omar wai kai ne ka zama haka ! kazama kamar dodo, Ka tara ƙirar karfi ba mata, kyau ace akwai inda za’a rinƙa sauke nauyin nan,…

Cikin jin kunya saudatu dake tsaye ta juya tayi cikin kitchen, domin kawo masa abun sha,

dafe kansa yayi tare da cewa “Omg !! goggo shiyasa ba kowa ke son zuwa wurinki ba, sbd in ki ka fara zuba kamar radio mai jini,’ ya faɗi yana yamutsa fuska saboda baisan hayaniya arayuwarsa,

Hannu tasa tare da rufe bakinta tace “nayi shiru tom, ka da kace zaka daina zuwa wurina bari nayi shiru,

dawowa saudatu tayi hannunta rike da tray da ta zuba masa snacks da abunsha a cup, ajiyewa tayi agabansa,

hannu yakai ya dauki lemun domin ya kur6a, muryar goggon ce ta katse sa da cewa “dole nayi magana Omar, Oh ni Jibi yadda ka tara nonuwa a kirjinka sai kace dai za’a sa akwatin nono na mata a suturta……”

ae baisan lkcn da ya ajiye cup din ba ya miƙe tare da cewa “Ni zan tafi, kunyartar ta isa haka,”

saude dake a wurin tuni ta sulale ta gudu,sbd tayu matukar kunya ta, da sakin layin da goggon take masa,

Cikin lallami ta tashi itama tsayen tana cewa “haba ɗan shalelena, duk fa cikin murnar ganin ka ne,’

ta6e bakinsa yayi tare da cewa ” no goggo tafiya zanyi, dama bani kadai nazo ba akwai yara na dake a waje suna jira na,”

Sam bataji daɗi ba, jin zai tafi tayi tunanin zai tsaya ya kwanar mata ne, itama tasan cewa surutunta ne ya ja mata, sarai tasan cewa bayason ɗumi haka,

Cikin sanyin murya goggo tace “toh baza ka tsaya ku gaisa da Babban likita ba ? kusan kullum sai yayi mgnr yaushe zaku zo daga America,

marshal Omar ya ce ” yana ina ne ? Ko yana on duty ne ? goggo tace “Eh tun da safe ya tafi asibiti aiki,’

“Okey may be na leƙa masa bfr na wuce kaduna gobe da safe, ‘

“Yanzu omari tafiya zakayi daga zuwa,’ ? tayi mgnr kamar zata yi kuka,

“Calm down your mind gaggo na, Captain adam da su mg Osman na nan zuwa, duk zagi gansu, nima zan dawo insha Allah, ynz akwai mahimmin aiki a gabana ne shiyasa,”

Jin sunan waɗanda zasu zo dayawa yasa ta washe daga ɗaure fuskar da tayi,

“Aiko da naji daɗi, in suka zo, zan masa a ayi musu fura, in suka zo suyi ta sha,”

Murmushi Omar yasaki ya fice yana faɗin “Zaki ga saƙona gaggo,”

Cikin jin daɗi tace “ina jira ɗan Albarka, ta ɗaga murya tana ci gaba da cewa “Allah ya haɗa ka da kaddarar ka acikin garin nan,’

sarai yaji ta fita yayi yana ɗan murmushi, yarasa dalilin dayasa, tsofaffin nan suke disturbing ɗinsu akan aure aure ????

tunkan ya ƙarasa inda motocinsu su ke, da sauri wani sergeant ya buɗe masa mota ya shiga A jere motocinsu suka fita,
sai da ya tafi sannan saude ta fito tana cewa “wlh goggo sam bakya kyauta, shikenan daga tsufa ya fara kama mutun sai yaita ƴan sambatu yana sakin layi ynx abunda ki kayiwa ƴaƴa omar kin kyauta “?
ta tambaya tana kallon goggon wadda ke zaune saman kujera, baki asake take kallon sauden,
Jinjina kai tayi tare da cewa “ba shakka raini ya shiga tsakanin mu, gobe goben nan zaki koma ƙyauyenku ni nagaji dama liƙamin ke akayi aka manna bin ba don naso ba,’ ta faɗi tana hararar ta,
Riƙe ƙugu saude tayi tare da cewa “to kisa ni ba inda zani je, koma tafiyar zanyi ƙafa ta ƙafar Babban likita ,’
“Saboda ke ki ka haife shi”? goggon ta tambaya,
Saude tace “bani na haifeshi ba, amma zaki ga yadda soyayya ke aiki……’ bata idasa ba goggo tabi ta aguje itama ta tashige ciki da sauri, dama sun saba,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74Next page

Leave a Reply

Back to top button